Showing 222001 words to 225000 words out of 258256 words

Chapter 75 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

fushi dake komai Safiya ta taba a gidan nan damun bi ta naki inna kona
shi zamuyi a lokacin.
Likita yace ai wanan ciwon yafi kanjamau saurin kisa yanzu baga safiya ta gyagije
ba kamar ba a yi ba da ta fake magani .
Ai ba a gudun mai kanjamau kamar may irin cutar nan don saurin dauke gare shi
sosai ga wa yanda ke kusantan ka sai kawai mukaji inna ta saka wani irin kuka mai
kama da ihu a lokaci guda duk muka rudu ga kowa na tsoron shiga dakin wurin ta don
kada ya kamu da ciwon.
Nayi kundunbala na fada dakin ina bata hakkuri sai fadin take safiya dole inyi
kuka cutar nan kila kasheni zaiyi safiya.
Ina naje dana dauko wanan mumunan cutar a jikina yaya sani shima ya shigo daka
ciki muna bata hakkuri likitan yace idan zamu shiga wurinta mu dinga saka takukumi
a hancin mu dau saukin shakan nufashin ta.
Mun fito muka sallami likitan na bashi duk wani abin bukata har zuwa lokacin da
alluran zai kare.
Shigowan Saadatu ke nan gidan da goyon ta wanda yayi wayo sosai yaron ganin mu a
kofan dakin inna yasa hankalin ta ya tashi bamu ko gaisa ba take tambayan mi may ke
faruwa ne ta gamu cirkocirko haka tsaye ?
Bakomai na fada ina karban dan dake goye a bayan ta amma sai yaron yaki zuwa
wurina don kiuya irin na yara da yake dashi.
Dakin ta shiga ta ga uwar a zaune a tsakiyan falon ta tace inna yaya jikin naki
tace da sauki nan dai ta dan tsaye, tsaye jim sai ta fito waje.
Lokacin na koma bangare ummi na ina batun aika yaro yakai ma mahaifiyar Amina
sokon a gidan su sai da nagama bada sokon na juyo gareta ina Saadutu an shigo
ashe ?
Gaisawa mukayi tare da tambayan lafiyan su sai godiyan abincin da ta aiko min
dashi daren jiya din da tayi shima nayi mata godiya akan shi.
Tace kai don Allah nasan ai bazakici ba na dai aiko ne kawai kada dan uwanka yazo
gari baka aika mai da komai na sannu da zuwa ba.
Kika ce wai ba zanci ba toga ummi nan tambaya kiji sai da naci fiye da rabi
nakuma shanye miyar tas wallahi taji sadi don fuskanta yanuna hakan.
Tace ikon Allah har abokiyar zama na fadin wai zan dai kawo ne amma ku yan birni
ai ko kallon wanan abincin bakuyi ai haka dai na daure na kawo maki shi.
Nace aini banki ba kullun kina kawo min irin wanan din don ina son shi sosai
wallahi samu dai ne ban yi a can.
Ikon Allah na katse ta da fadin yaya Adamu maigidan ki yake dariya tayi tace
mutumin ki yana nan lafiya wallahi sai dai yanayin garin da muke ciki yanzu kawai
amma ya daina halin nan yanzu lafiya lau muke dashi sai abinda ba a rasa ba.
Tace ai yaji dadin kudin da kika aiko mai kwanaki har ya fara sana a sai wa yanda
suke sana,an tare ashe suna bishi kudi nan sukayi karan shi karshe har da na wurina
muka hada aka bashi yanzu yana zaune bai komai kuma.
Na tausaya mashi nace mutum magidanci ya zauna ba sana,a haka ai abin baiyi ba
wallahi tace ai yace yana nan zuwa ya gaida ke da zuwa.
Nan Ainau ta shigo gidan itama da goyon ta muka hade mu uku duk sun girmay ni
amma samun wuri da kuma maganin da nake sha wanda ya hurani na danyi kiba ba sosai
ba.
Anan muka wuni tare da su inda na dauko masu tsaraban su na basu sai farin ciki
sukeyi da murna ga abinda na basu din.
Sai yamma suka tafi gida inda nace masu idan na huta zan shigo gidajen nasu mu
gaisa na dan raka su na dawo na dibi ruwa zan watsa ma jiki sai ga shafiu ya shigo
da Abba a hannun shi yana fadin wai ga Adamu nan mijin Saadatu yazo gaida ni ya
shiga ya gaida inna da sauri na mayar da rigan dana cire a jikina kafin ya shigo
dakin ummi din mu gaisa dashi.
Da sallama ya shigo ina saman kujera na mike ina ce mashi ga wurin zama nan ya
zauna yace a a zai zauna kasa na hana shi dole ya hau kujeran ya zauna.
Ni kuma na koma daga kofan kuryan dakin ummi na fara gaida shi yace kunzo lafiya
nace Alhamdullahi yace to barka da arziki ashe an sauka murmushi nayi yace bamu ba
da komai ba sai kuma ga sako na gani nagode nagode kwarai Allah ya kara rufa asiri.
Nace kai haba bakomai wallahi kasuwa dai yana tafiya yanzu ko na tambaya kamar
banji komai ba a kan shi yace tau Alhamdullahi zamu ce hajiya don ba a cewa komai
sai hamdala.
Amma gaskiya yanzu komai ya tsaya ne cak wallahi kudin da kika turo min kwanaki
na fara dauko mai jerka biyar dashi tunda wa yanda muka fara sana, a dasu sukaga na
dan samu suna bina kudi sai sukayi karana dole na hada kan kudi na biyasu abinsu
shine yanzu nake zaune ina zaman ba sana a .
Kin san ance wanda ya amshi kudi hannu mace yana tare da gori komai daren dadewa
to abinda ya cini ke nan dama yan uwan matane suke bani yanzu kuma wanan abin daya
gitta har na auri saadatu sai suka karbe dukiyan su a hannu na suga yadda zanyi
watau.
Dariya nayi nace baduk mata suke haka ba ai wasu dai ne haka suke shiyasa nima
banyi maganan komai da Saadatu ba har tazo ta wuce ta dai fada min kamar yadda ka
fada min yanzu din yanzu a misali idan na baka dubu dari biyu zasu isheka ka fara
sana,a mai dan kauri dasu.
Hajiya dari biyu ai ba karamin kudi bane yanzu nace to zan baka sai ka fara mu
gani ya katseni da cewa har zuwa yaushe zan maida maki kudin ina mikewa nace a a
baka nayi halal malak kaja jari dasu ba rance na baka ba ni kyautan su na baka.
Zamowa yayi saman kujeran da yake zaune da farko ya hada hannayen shi biyu a wuri
daya ya fara zabga addua da fatan alheri a gare ni.
Nace ba sai ka fadawa kowa ba Adamu nidai bukatana a gareka shine ka rike min yar
uwata amana don Allah ka kula dasu dukan su ukun matan kane.
Godiya ya kara min yana kokarin tura kudin da ya karba a hannu na cikin aljihun
rigan shi tare da yi min sallama har yake kofa ya juyo yana fadin gobe gobe in
Allah ya kaimu zanyi asubancin zuwa birni wurin saro man in sayo.
Nan dai ya fice cike da farin ciki nikan yana fita daga dakin na mike don duk zafi
nake ji a jikina ina son in dan watsa ruwa inji sayi.
Kafin wani lokaci gari kowa yasan na zo wasu idan sunga mota a wajen gidan mu ne
suke tambayawa a fada masu.
Wasu kuma idan na aika masu da tsaraba suke sanin na zo garin ban fara fita ba
sai da na kwana uku yan uwa da abokan arziki suna zuwa gaida ni suna kuma aiko min
da abinci da dan abin marmari don kulawa.
Har da makwata dana ba tsara ba sun shigo taro na da gani dan da na haifa wasu
dai gulma ne ke kawo su ganina kawai suga yadda ake fadin na koma yanzu.
Gidan mummy mahaifiyar Amina kawana na fara zuwa inda musa driver ne ya kaini
gidan shi da security din mu na dade gidan muna hira da mummy inda nace ai zan
shiga wurin Amina kafin in koma in Allah ya yarda.
Ina fitowa na wuce gidan su mama jummai na gaida su suma duk inda naje sai na
jima a gidan daga wurin su na dawo gida.
Duk abinda nasan inna naso wanda akace tace na sa yaya sani ya sayo mata inda
nayiwa yaranta nasiha su kula da uwar su don Allah.
Wanda ba kowa ta jawo hakan ba ga yaran gidan mu sai inna din don batayi zoton
abin zai shafe ta ba haka.
Washe gari gidan Ainau na fara zuwa tun da safe muka fita sai karfe daya na
bargidan na wuce gidan saadatu .
Gidane may irin dakunan nan ajere suke guda hudu sai baranda ba wani siri da
mutum zai iya yi ba a ido yan uwa ba.
Yaran gidan sun kai bakwai saadatu ne ke da daya a cikin su na samu wata mata da
daure gaba tana tuka tuwo a tsakar gidan inda suke girki.
Yin sallamana yasa sauran fitowa daga dakunan su mai tuka tuwon tunda tayi muna
sannu da zuwa ta mayar da kai ga aikin ta bata kara juyowa gare mu ba.
Tare da su khadija muke muka shiga dakin saadatu din daki daya ne single da gado
da mirrow sai drower gadon dake gefe an dagwara mai roses guda guda da ledan kasa
malale a dakin .
Kujara mai zaman mutum uku damai zaman mutum daya sune a dakin zama mukayi aka
fara gaisuwa a tsakanin mu saiga wanan matar da tafita tare mu dauke da kwanon sha
cike da ruwa ta kawo muna.
Tana fadin safiya ko ai yanzu bata gane ni tunda an dade ruwan na karba na sha
nace wallahi kan ban gane ki ba yar uwa tayi dariya tace mune senior ku don muna
gaban ku da shekara uku sai dai ni ban gama ba nayi aure lokacin mai yawo dasu
Aisha sani na kusa da gidan ku.
Nan dai suka shiga min bayani ita da Saadatu saida na gane ta nace ankoyi haka
tace gamu mun hade da yar uwarki muna auren miji daya yanzu.
Allah sarki nace kuna lafiya yaya yara yaron ta karba a hannun kauna na yar wurin
mama da muka zo da ita tace tubarkallah yaro yayi wayo sosai.
Mun dayi hira ta fita dakin mukaci gaba da hiran mu na abinda ya shafemu na gida
maigirkin taba dan tuwo kasan kwano a kawo muna mukace a maida mata a koshe muke
mu.
Sai lokacin ta shigo tana fadin bazakuci abincin mu ba nace gidan Ainau muke
sunci taliya acan ni kuma na koshi yanzu ganye kawai nake son in samu inci.
Ta juya ta wuce saade tace ganye kike so nace eh tace barin nemo yaro ya sayo
maki sai khadija tace baga maimu na ba abata taje ta sayo bakin kasuwa mana.
Dubu daya na zaro a jakkana na bata tace na nawa nace ta sayo na duka ido suka
zaro mun a lokaci daya suna fadin har ganyen dubu daya haba dai.
Na dari biyu dai ko daya nace kuba zaku ci ba ne sukace zamu ci yar uwar zaman
saade ne ta shigo dakin tana fadin ko zaki sha fura ne a sayo maki nace ganye dai
nake son ci ga kudi na bada a sayo min tace wa zai sayo sai khadija tace maimu zata
sayo.
Ta sake tambayan da kuli zance ko soya min za ayi nace da kuli dai za a gyara min
tace to ki sayo na dari biyu di sai kayan hadi sai saade tace kuje kiyi mata
bayanin abinda zata sayo.
Suka fice dakin nan dai mukaci gaba da hiran mu sai ga maimu ta dawo ba, a jima
ba aka gyaro ganyen sallah muka farayi muka zauna gaba dayan mu muna hada hannu
muke ci a katon tire dukkan mu.
Khadija ce take fadin amma anty saade kunfi zaman lafiya da wanan matar data
gyara muna ganyen nan tace ba ruwanta ai bata da fitina amma ita dayan haka take
kamar innar mu wurin fitina.
Kullun sai tayi fada da wani cikin mu kan diya ko kan girki sanan tana muna kurin
yan uwanta na da kudi a cikin mu har gori tayi min da muka taba fada.
Wai yar uwar tawa da nake kuri tana birni bata ko san dani ba a duniya sai ta
kashe take bamu dariya nayi nace badai kina da mai kashewa ta baki din ba ai yafi
babu.
Tace ina ma kika sani dana dawo wurin sunan yaron nan da naje cewa tayi kuma wai
naje nayo maula ne gurin ki ai ba shiri a tsakanin mu da ya dakin ku.
Nace fita batun ta don Allah irin matan nan ne da sai su zuga ka har ka aikata
abinda baka tashi yi ba tace ai na gane ta yanzu ban biye mata.
Khadija na bawa makulin mota don bamu fito da su malam musa ba mu kadai muka fito
yau, nace ta je ta dauko min kayan dake bayan seat a farar leda.
Ta fita sai gata ta shigo da ledan nan nanuwa saade turamay zani da sabulu nace
tabawa kishiyoyin nata.
Tace duka safiya nace kada ki damu girman ki nake ja maki a hakan ai fita tayi
sai nabi dakin da kallo don in san abinda zan mata a dakin nata don ace inna batai
mata komai ga auren nata wai bata son auren.
Ta dawo sai gasu tare sun shigo dasu sukayi godiya suka fita khadija ke fadin
dama Atikan kawai kiba wallahi nace ai ba ayin hakana kuko.
Nace saade yanzu kina ganin dakin nan yana daukan fridge da kayan kallo kuwa tace
aiko bai yi zan sa afita da kuje daya sai in samu wuri nace to yayi sai ki gwada mu
gani mikewa nayi nace barin shiga dakin senior dina mu gaisa na suri jakkana na
fita daga dakin.
Ina jin khadija na fadi zataje tayi mata dumus ke nan tunda kinga ta dauki jakkan
hannunt ban tsaya bana fice daga dakin.
Tana gani ta kama washe baki tana sannu da zuwa dakin nata gwanin ban tausayi
wallahi kai mata muna cikin wani hali a rayuwan auren mu har na tuna da dakunan su
ummi na da.
Sai a kai mace da kayan mutunci gidan su amma sai a kashe kayan da miji ba zai
damu da ya sayawa matar wasu ba tunda a tare ake amfani dasu sai dai ita mace ne
zata kama kulla kulla har ta samu ta dan saye nima nasan da ina gidan Ahmed da har
yanzu da dan gadon katakon dake daki na zan ta rayuwa.
Mun dan zauna ina tambayan ta wa yanda mukai karatu a tare tana bani labarin su
hannu na tura a jakka na na kirga dubu ashirin na aza mata a gadon ta nace ayi
hakkuri akwai abubuwa da yawa amma wata rana zakiji sakona da yardan Allah.
Na fice tun bata fara yi min godiya ba na shiga dakin dayar mai kurin arzikin
gidan itama babu komai a dakin sai wani tsohon gadon na katako da wasu rubabun
kujeru manya a dakin dubu biyar na bata na fito bayan mun gaisa da ita.
Ina shiga nace ku taso mu tafi saade sai na sake dawowa maimu da hindutu ne ke
rige rigen karban jakkar hannu na khadija tace naga alama mai kamar dai dake za a
koma Abuja nan ko ?
Nace maimu da hindatu kan ai tashina tashin su tunda ke kin gudo ban yarda in
rasa abokin hira a gida ni kadai sai mummy.
Nan suka shiga masu sheri suko yaran sai murna sukeyi zasu tafi abuja khadija na
fadin kuje kuyi zaman kurkuku ai ba shiga ba fita sai zaman gida.
Na bude mota muka shiga na tayar ina masu horn duk suka daga muna hannu muka tafi
sai gida tun dawowan mu na dan leka inna wacce yanzu maganin ya fara bata reaction
tana yawan galabaicewa sosai na samay ta zaune yaya Sani ya sawo mata lemo mai bawa
tana sha.
Na gaida ita na fito na shiga wuri mama itama na gaida ita na koma dakin ummina
ina fadin wai kamar nayi wani abu yau duk na gaji ummi na sai dariya take yi cikin
jin dadi da kulawa.
Mun dan taba hira wanda kusan hiran na kishiyoyin Saadatu ne sai nace maimu
dake lake dani ta kira min yaya sani a waje idan yana nan tashi maimu ummi tace
ashe kin samu yan rakiya Abuja ne yanzu maimu ke fada min da su za a tafi wai ?
Nace haka nake so ummi shima yayi mi maganan hakan don yaso khadija ta zauna
damu amma taki kanta na rawa.
Ummi tace bar ta kawai mara hankali ba komai ya hata zama ba sai wanan sauryin
nata mara mutunci da take son dauko muna wahala taki zama.
Nace nima dai ummi yaron bai kwanta min a raiba wallahi don ba yan mutunci bane
ta rasa wanda zatayi soyayya dashi duk garin nan sai zurian su inna.
Gaskiya nima hadin bai min dadi ba gaskiya ummi ai ta samu wasu a bauchi da muka
tafi ban dai sani ba ko har yanzu a kan shi take.
Ummi tace kinga ko bata fada ba don karnaji nayi mata fada tana tsaye daga kofan
kuryan ummi tana sauraren mu ta turo baki gaba.
Ummi tace tsayin may zaki zo ki muna a kai in kina tsayawa kima kan ki fada tun
wuri gara ki tsaya ga masu son ki na kwarai don dai ni ba yarda zanyi da wanan
zaben naki ba.
Juyawa tayi ciki da fushi tana magana kasa kasa nace ji wawiya don Allah ana fada
maki gaskiya har kina ganin laifin mutane akai.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/13/20, 7:47 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , ,


7️⃣9️⃣7️⃣
🧕9️⃣7️⃣9️⃣


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Shigowan yaya sani ya katse muna maganan da muke akan khadija din don ko ba komai
baza mu so yaji muna sukan dan uwan mahaifiyar shi ba a fili.
Ya shigo yana fadin yanzu maimu da hindu suka tare ni a hanya suna fadin wai
dasu zaki tafi idan zaki koma ?
Nace a sanyaye haka nake so indan zan samu baba ya yarde min don gidan yana min
girma ba kowa a kusa dani.
Yace ai ba wani matsala bane idan mijin ki zai yarda da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login