Showing 54001 words to 57000 words out of 258256 words

Chapter 19 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

ga matar ka na sunna da sunan wai tana duban ka ai duk abinda zakuyi ku
tsaya iya waje ku yi shi.
Lilliya ta dago kai tai mata wani kallon banza tace ke wacece da zaki zage ni da
sunan karuwa ai karuwancin ma isa ne ko.
Tace OK yanzu zaki san ni ko wacece ya dago da sauri yana ce mata will you keep
quite.
Take ta har zugo mashi maman biyu batai mata magana ba ta mike zuwa kofa ta sa
mashi key ta rike ke din a hannun ta.
Waya ta dauko tai kira dashi aka amsa mata sai lokacin suka kulla da ita Lilliya
ta dago tana cewa may zaki yi in bariki ne nafiki iya wa tace bissimillah ina son
yau inga iya barikin naki.
Taso taja da ita jacket din dake jikin ta tacire sai uniform din ta ya baiyyana
dakatar da abinda tai niyar yi mata tayi tana cewa haka kawai zaki zageni.
Karyan bariki kike yau zan gwada maki akwai wa yanda suka fiki suka riga ki
shiga bariki da lasisi.
Mari takai mata naji dadin hakan daga inda nake tsaye a rakube jikin kujera.
Taso turzawa amma karfi ba guda ba take ta murde ta kafin tai wani abu aka fara
dukan kofan ta je ta bude sai ga kartan sojojin tsaye a kofa ko wani a cikin
shirin shi.
Hakkuri ta fara badawa harda shi munafukin yana cewa madam don Allah ayi hakkuri
rashin sanin ke wacece yasa tai maki haka.
Arest her tace da su take ko suka kamata saura shi tace shima a tafi dashi
fuskata babu burbushin rahama take maganan.
An fice har dashi a gidan wani dadi ya kamani sai hawaye bata ko tsaya ta kaina
ba ta fice gidan itama ta bisu.
Daga inda nake tsaye a cikin fargaba da tsoro na mara masu baya ina tsaye motocin
su suka wuce dasu.
Ko ba koma yau maman biyu ta daukan min fansan wullakacin da ake min a gidan don
ya gama zagine ke nan a kanta ta shigo gidan ta samay ni daki ina kuka nasan abinda
ya kara harzuka ta kenan.
Ina zaune takure a cikin damuwa sai gashi ya dawo duk ya jirkita azotana da
yadawo zai hauni da duka da zagi yadda ya saba ne.
Sai gashi naga sabanin hakanan ya dawo ya bukaci ruwa masu zafi zai gasa jikin
shi dashi sai kuma dan abinda zaici.
Yana zaune bayan ya fito wanka ga abinci a gaban shi yace Safiya ina daki na
amsa masa na fito kujera ya nuna min da hannu alaman wai na zauna.
Sannu a hankali na kai zaune saman kujeran ina fuskantar shi tare da sauraren
abinda zai fada min a lokacin.
Yace kin dai ga yanda wanan matar suka yi a gidan nan ko na dago kaina a hankali
ns dubeshi ya tsare ni da idawan shi.
Na sake dukar da kaina kasa ba tare da na amsa mashi ba yace yanzu dai ba wanan
ba abinda nake so dake shine.
Kiwa ita madam din nan magana a sake Lilliya don ba karamin tsaro sukai mata ba
yau kawai duk ta jemay saboda tsaro da horo irin nasu na sojoji.
Ban san cewa girman ta da kimarta yakai haka ba sai yau din nan da na gani ke
kaidace zakiyi magana a saki Liliya da sauri inba haka ba abin zai jawo min matsala
sosai gani zaune gida banda lafiya.
Banyi magana ba naji yana cewa umurni na baki ba son jin raayin nake so ba ki
mata magana a sake ta.
Na nisa nace shike nan kiran yace eh shike nan nake so ki fada mata a sake ta.
Na mike ina ce mai ai da kai kai mata magana zai fi don zata fi jin maganan ka
sama da nawa do ni ban san ta inda zan dauko mata zancen ba.
Rashin mutunci tai mata ta dauki mataki ta dauka irina ne da kuke wa son ranku a
gidan ku taka ni iya son ranku a zauna lafiya.
Ni banga laifin maman biyu ba da ta dauki mataki ga marasa mutunci irin ku wayan
da basu san darajan aure ba.
Ke ya isa ya dakatar dani ta hanyan daga min hannu shi yace umurni fa na baki in
kina son kanki da lafiya gidan nan kiyi abinda na umurce ki da shi.
Fuskan shi babu alaman sauki gare shi don haka na juya na tafi kawai ba tare da
nai wani magana ba.
Da safe nai sammakon zuwa gidan maman biyu nayi sa a tana gida kasa na zube ina
mata godiya ga hawaye na zuba a idona.
Ta ce assha safiya tashi tashi don Allah may ye hakan ai dole a tausaya maki don
kinyi karanta da irin wanan rayuwan.
Dudu fa baki kai ashirin ba amma kike fuskantar wanan bahangon mijin naki mai
rayuwan kazan ta.
A gaskiya dani wata ce a cikin zurian ku da sai ince a raba wanan auren don baida
alaman nadama ko gaba duk kaga namiji yakai haka alamarin akwai ban tsoro cikin sa.
Nace yanzu ma shi ya turo ni akan nazo na baki hakkluri a sake ta wai idan ba
haka ba zan gane kurena gare shi.
Tace da sauri kinji ba na fada maki ai baida nadama ko kadan ai dana sani abarshi
can shima amma sai na tausayama luluran da yake ciki.
Gaskiya naso yin wani abu akan zaman nan naku amma sai ina ganin kamar ciki ne
dake .
Nai saurin dagowa ina duban ta a gidimay nace ciki kuma anty tace tabbas indan ba
hasashe nake yi ba kina da shigan ciki.
Gabana yai mugun faduwa tace yaushe ne rabon dakiyi jini a tare dake ?
Nai shiru ina nazari can nace gaskiya wata uku kenan tun da nayi ina gida ba
sake yi ba.
Tace shit,
Zargina ya tabbata gaskiya akanki na dade dama ina zargin hakan amma zan sa aimaki
test a gani.
Yanzu ki ci abinci zanyi waya a sake ta don ba imani ke ga irin su ba tare suke
da yan daba sai dai da yake zamu kafa hujja akan in wani abu ya samay ki nan da
shekara biyar itace.
Naga tasa akawo mata abinyin test ta auna fitsari na ya nuna positive alaman ina
dauke da cikin wata ukun.
Nai bakin ciki da jin wanan labari kwarai da gaske munyi sallama zan tafi take
cewa in kwantar da hankalina killa sanadiyar cikin nan in samu sauki a gurin shi
don wasu maza nason yara.
Ta dan bani shawarwari masu mana ta cika ni da abin arziki na bar wurinta zuwa
gida zuviya ciki da bakin cikin labarin cikin dake jikina.
Yana zaune ya kura ma tv ido na shigo bako kin dawo sai cewa yayi yaya kin samay
ta a gida ?
Nace eh na samu dama zata sa a sake ta saboda kai koda banje ba din tace abin da
tayi matane ya bata mata rai ai.
Bai yi magana ba kuma naji ta yadauki waya kowa yake sanar ma zancen sakin nata
oho nadai ji ya dade yana waya din.
Nikan abinda ya damay ni ya damay ni zancen cikin dake jiki nakewa bakin da
nadama ina tausayawa rayuwan da abin cikin cikin nawa zai taso ya ga ubanshi nayi a
duniya.
A haka ma ba tarbiya yaya za a ce aiwa yara tarbiyan rayu kirikiri bani shiga
mutane duk da bariki ana cewa ba ruwan wani da wani .
Ina ganin barikin dane bana yanzu ba don wata mace da tazo kitso ya dawo ya shigo
murtun compound din tace .
Na dis yeye man you marry , .
Dis man too dey follow women .
Murmushi nayi mata kawai ban bata amsa ba sai wata da take zaune ne tayi mata
magana da cewa hakana fa ba kyau.
Sai tayi shiru damuwa ya isheni da fargaban halin da zan shiga nan gaba a garin
mutane .
Sai wuraren sha dayan rana aka sako lilliya daga hannun sojoji bayan tasha dan
banzan wahala.
Haka ya daure ya fara fita tun wanan ranan baya zama gida yana wurinta acan
kafar ta karasa warkewa a hanya.

********* ********* *********
Yau na tashi jikin ba dadi ga damuwa dana sawa raina ga kuma halin maigidan ba
sauki akan komai.
Kwace nake a falo saman dogon kujera nayi da daya da kafana ko zan ji dadi jikina
misalin karfe biyar na yamma.
Can na fara barci naji dawowan shi gidan yana gauran kofan shigowa gidan gabana
ne ya fadi don ganin shi a murtuke da fuska.
Innalillah wa,inna ilaihi rajiun Allahuma Ajirni min musibati waakhimi min kharir
minha na anbato a raina.
Ya shigo yana ta faman kalle kalle har ya kai zaune saman kujera tsoro ya kamani
don ban an damay ya shigo ba.
Na dago cike da natsuwa da girmamawa na furta sannu da dawowa bai amsa min ba sai
taba da ya ciro cikin aljihun shi yana kokarin kunawa warin taban ya gauraye falon
lokaci guda.
Na mike da sauri zan bar falon sai lokacin yai magana yace ke mayye haka kuma ?
Ina kokarin tare aman da yazo min a baki nace zan zan zan sai na mike da gudu na
fada dakina direct makewayi na shiga nai ta shega amai aciki.
Bina yayi da kallon mamaki bai yarda dani ba, ya mike ya bini yana tsaye nake ta
aman sai da nagama na mike zan fito naganshi a tsaye ya rike kugun shi.
Gabana ya sake faduwa yana min wani irin kallo na tuhuma mai kama da bai yarda
dani ba yace ke mai ke samun ki ke amai haka.
Na amsa dakyat da cewa ban da lafiyane .
May ke damun ki koma may nene ke kika sani don ni banda lokacin ki ya juya har ya
fara tafiya ya juyo yana ce mun ki sani ban son kazanta a gidana.
Na yamutsa fuska nace kona bata ma aini ke gyarawa ba wani ba ya juyo yace may
kika ce ne ?
Nace bada kai nake ba ai yace shgiya naga randa bakin nan naki zai mutu da bakar
magana dibi yadda kika murje kikai wani bulbul dake duk abincina kike cinyewa ga
banza.
Yafice na sauke ajiyan zuciya na zauna nadan huta na fito kai tsaye kitchen na
fada don girka abinci don nasan a gida zai kai dare tunda ya dawo da wuri.
Na gama aiki da kyat na shiga na watsa ruwa don lokacin sallah ya gabato ina
zaune ina lazimi naji ya kwala min kira.
Na taso dagani sai yar doguwar rigan da anty ta bani ranan da naje gurin ta tace
ta gani ne dataje sayayya ta sayo min shi.
Na fito abincin da na aje mai yana bude na sauke idanuwana akan abincin dake
gaban shi din.
Ya watso min harara yana cewa wani irin abinci kika dafa haka nace shi kadai ya
saura muna a gidan shiyasa na dafa taliya ne nai jelop din shi.
A fusace yace what, what are you saying ?
Kina nufin har abincin da na sayo yakare komay ?
Na girgiza kai nace yaushe rabon da ka sayo abinci a gidan nan wanda ka sayo din
ai shi na dafa lokacin da bakada lafiya masu jiyan ka suka cinye.
Ya dakatar dani da hannu yana fadin ya isa haka maganan ya isheni sai ki zauna ki
cinye dama haka kike so ai.
Ya dauke makulin motar shi dake saman tabur yabar gidan yana faman huci.
Sai da muka share kwana uku cur ban da lafiya kuma ba a girka komai a gidan.
Ina kwance daki ina fama da kai na nidai kamar kar maman biyu ta ambaci cikin nan
wahala ya soma zuwa min.
Sai kawai gashi ya shigo min daki misalin goma na dare don rashin imani irin
nashi sai ji nayi ya afka min .
Na soma kuka ya gama ya daga yana cewa may ye haka tsiyan azo wurin ki kenan
walahi ki damu mutum da munafukin kukan ki.
Na dago ina cewa azo min haka kamar wata karya ni kadai nasan abinda nake ji a
jiki na yanzu haka ji nake kamar baya na zai tsage san nan ban ci komai ba tun
safe ga yunwa na damuna.
Yakai kofa ya juyo yana cewa ai sai ki samu abinda kikaci ko kije asibiti adubaki
nace da nawa zan tafi asibitin yace ke kika sani.
Washe gari ma da ciwon na tashi don da dare banyi barci ba ciwon mara ya hanani
shakat a rayuwa na.
Ban fito ba har ya gama shirin shi zai fita komay ya gani sai ya leka dakin nawa.
Ina kwance ina faman murde murde a saman gado ni kadai a dakin ya leko yadan dade
tsaye akaina sai ya karaso bakin gadon yana cewa.
Wai ke may ke damuwan ki ne haka kike faman murde mude a gado ke kadai a dakin ?
Da kyat na bude bakina nace cikina ke ciwo sai kaina dake sarawa kamar zai balle
min nake ji.
Ya fita da zai dawo sai gashi da magani da maltina da peak milk mai sanyi a leda
da kayan abinci ya sayo.
Ya samay ni a falo na yi laga laga dani ya miko min maganin da maltina yana cewa
ga magani ki sha.
Nai mamaki ganin magani harda maltina ya sayo min babu kunya babu alamanta ya
zauna yana cemin tashi ki sha.
Da taimakon shi na hadiye maganin sannan ya hada min maltina da madara yace in
shanye kafin ya fito.
Bayan kaman minti shirin sai gashi ya fito ya dubeni yace yanzu ya fada maki ko
yana nan ?
Nayi ajiyan zuciya nace ya fada min nace na gode yace na taimaka maki ne don nima
kin taimaka min da banda lafiya don haka arama ma kura aniyan ta.
Na ciza baki na yunkura ina cewa aiko kura ta gode in don Allah akai mata.
Ya harare ni yace gunma ki wartsake don ba zan dauki nadewa a gado ba tunda kun
hanani hurda da yan mata na yanzu.
Na saurin kallon shi ina cewa wa ya isa ya hanaka da abinka muka ganka mu mun isa
wanan sai Allah daya hallice ka ai.
Sai kawai naji ya kyalkyale da dariya sai nai saurin dago kai na kalle shi cike
da mamaki yau shike dariya haka kamar ba shi ba.
Yace ashe kun san da haka da baki wahalan hada baki da matar sojs tashigo abin
da bai shafe ta ba.
Ya fice ban sake jin duriyan shi ba sai dare sai gashi ya dawo min a cikin maye
yana ta tsuki burutsun shi a gidan.
Ina daki ya samay ni a haka na dan dago ina kallon shi naga ya nufo ni gadan
gadan sai na fashe mai da kuka don na san halin fitinar shi sarai ba imani ne dashi
ba.
Yace a cikin maye ke ke may nene haka ?
Na yun kura na tashi da kyat ina cewa don Allah yaya kayi hakkuri wallahi ban
iyawa banda lafiya ne.
Na gaya maki zan maki wani abune kawai kawai yana inda inda ya kasa fadin abinda
zai fada din ya juya yana suruntun abinda banji ba ya fice dakin.
Na lumshe idanuwa na a hankali ina sauke ajiyan zuciya ganin ya fita natashi na
rufe kofan dakin nawa.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , ,


1🧕🏿919
1️⃣
1️⃣
9️⃣ 9️⃣


YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDINE IDAN BAKI BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE.


Kwanaki goma sha uku da aukuwan wanan lamari yana zaune a falo ya harde kafa yana
shan ruwan kwalba da sigari yana sha yana yamutsan fuska kamar an sashi dole ya
sha.
Na fito daga daki rike da cup a hannu na ban san yana zaune wurin ba sai ganin
shi nayi yana korawa.
Da sauri na wulkita zan juya dakin da nafito ganin haka yasa shi mike a ida yake
zaune din ya nuna ni da hannu.
Ke ban san sau nawa zan fada maki cewa idan ina zaune kika gani ki daina gudu
kamar wata mara gaskiya dake.
Nikan ban masan yana yi ba don na dafe bakina da hannu daya kar amai danake ji ya
fito mun a falon.
Ganin yanayin da nake ya dakatar dashi ga fadan da yakeyi din ya kafa min idanu
yana kallona a cikin zargi.
Yace Safiya ciki gare ki ne ko may ban sani ba don tun ga kwanaki naga kina
wanan aman na tsiya.
Nikan ban ma san yanayi ba ina tsugune na dafe kaina sai kakarin amai da nakeyi a
ban dakin .
Hakkali a tashe ya sake magana da cewa kefa nake tambaya na dago da kyat ina
cewa cikin yanayin ciwo warin taban nan ne ke wahal dani.
Ya ja tsuki ya juya yabar wurin dakin shi ya shige da bacin rai bai fito ba haka
nima ban fito ba na kara dunkulewa cikin dakina.
Kwana biyu baya gidan ban san ina ya shiga ba ga komai ya kare min don haka na
shirya zuwa gidan maman biyu.
Yanayi na kawai ta kalla tasan ban jin dadin jikina yace wai ko kunje asibiti
kaina girgizamata kawai alaman a a.
Safiya kamata yayi ki fito ki sanar dashi zancen cikin nan amma ba wai ki boye ba
don ba zai yuyu kibar ciwo a jikin ki ba don ciki ciwone.
Nace to Anti shidin ne almarin shi har yanzu ba canji kin ga tun kwanaki ya gane
bana jin dadin jikina amma don rashi imani yau kwana biyu kenan baya gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login