Showing 177001 words to 180000 words out of 258256 words
Chapter 60 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu
zamay jiki zuwa inda kaunar shi take wacce baaba ke riko a
gidan a wurinta nake jin ashe ya gyara ma sauran sisters din shi dakunan su a nan
garin kamar yadda ya gyarawa Aisha nata.
Naji dadin jin wanan labarin da ta bani nan muka zauna ina fahintar wani abu a
cikin hiran ta sai da zai fita ne hajiyan ta kirani na fito muka tafi.
Muna shiga part din mu na kai mashi runguma ya juyo yana kallona da mamaki nace
Uncle naji abin alherin da kayiwa su anty suwaiba unangiji ya saka da alheri ya
kara budi.
Murmushi yayi ya kamoni zuwa jikin shi tare da subbatan goshina sai ya soma
magana kamar mai rada bakin shi a daidai kunne na yace ba wanan godiyan nake so ba
kin dai ji abinda baaba tai muna addua a kai.
Kunya ne ya kamani na kara shigewa cikin jikin shi sosai ina dariya don kunya ina
fadin insha Allah soon.
Ya jawo ni ya kara matseni sosai yana fadin da kyau bari ma yanzu mu fara gwada
sa,ar mu mu gani ko zamu dace dariya ya bani da haka muka kwanta barci don muna da
gajiya dama.
Washe gari muka tashi da aikin rabon kaya wa yan uwa da abokan arziki don motar
kaya ta isa da daddare sosai ne.
Saboda hakan ne muka bari sai da safe banga zarah ba tun jiyan da muka iso tana
gidan iyayyen ta tunda muka zo.
Saida muka share kwana uku muna abu guda ana hudu ne muka dawo abuja sai dai
uncle ya hanani zuwa gida in kai wa mutanen gida abinda ya saya masu da kaina a
cewar shi sai mun dawo zamu tafi gaida su.
Yaya Sani aka kira nayi mashi bayanin komai da wayan da zai ba na hada dashi da
kayan suka tafi nan muka fara shirin tafiya wanda ni ta fanni na ba wani shirin da
nayi don a shirye din nake dama.
Ina murnan tafiya sai ga shi yana fada min gidan anty zamu sauka indan mun tashi
daga nan abinda ya sani cikin damuwa ke nan kuma.
Shiko naga ko a jikin shi bai damu ba kamar ba wani abinda ya faru tsakanin mu
tun farko da ita sai ni ya bari da tarin damuwa a zuciyana.
Ana gobe zamu tafi ne dadare muna zaune falo yake cewa dani wai may ke damun ki
ne kwanan nan naga kin shiga damuwa ?
Gwauro numfashi na sauke tare da kakaro murmushin dole a fuska na nace babu komai
may kaga ?
Ya tsuramin ido kafin yace dani tun fa ranan da mukayi magana dake na sheda maki
lagos zamu fara tsaya muyi kwana biyu naga kin ta da hankalin ki a gidan nan.
Ajiyan zuciya nayi wanda ya baiyana a fili nace uncle bawai nadamu bane kawai dai
ina tunanen yadda zan hada fuskana da ita ne bayan abinda ya faru a tsakanin mu
din.
Murmushi yayi ya kamo ni zuwa jikin shi yace kin san ko muna waya da ita a yan
kwanakin nan kuma ni bata nuna min komai akan abinda ya faru din.
A raina nace kaika ai ba zata gwada ma komai ba nice dai matsala dama a tsakanin
ku ji nayi yace dani kin dai san ba zan taba barin ta muzanta baki ba kina a
maysayin mata ko ?
Nace amma uncle abinne da nauyi wallahi yadda anty ta rike ni ace haka ya kasance
a tsakanin mu aikasan da nauyi wallahi.
Yace koma dai may ne yanzu sai ki bari idan mun je ayita ta kare yafi wanan boye
boye da kike yi mata kamar mara gaskiya a tsakanin ku.
In ke kina da laifi ai itama tafiki laifi a wanan magana don ko dani dake itace
ta hada mu don may daga baya zata kawo wani zance kuma.
Haka dai yayi ta karfafa min gwaiwa har na danji raina ya dan sake koma may nene
gara dai ayita ta kare ma nace a zuciyata.
Washe gari yan uwa da abokan arziki sukayi ta zuwa sallaman mu yaya don sai da
yamma ne zamu tashi.
Yaya saadu da anty Aisha kusan anan suka wuni damu shiga na alfarma nay duk da ba
wasu kaya na kwasa ba ga tafiyan.
Mun sauka lagos da karfe shida da wani abu hotel muka wuce bamu tafi gidan ba a
ranan anan hotel din muka tsaya.
Washe gari ma da yafita bai dawo banan ya barni ina ta barci abina hankali
kwance sai bayan karfe biyu ya dawo yai wanka ya ci abinci yake fada min in shirya
muje mugaida anty din da mijin ta.
Kayan da Anty Aisha ta zabar min don in sa idan zamu gidan na saka wani lace ne
da suka sayo dubai lokacin da suka tafi sayayyan auren mu da ita shine na saka.
Sai sarkan gwalal da zaikai kimanin kudin nigeria milayan daya da dan kai wanda
shi yafi tsada a cikin kayan da suka sayo da wasu takalma masu dan hill da duwatsu
masu kyan sin shiga da lace din sune a kafana da jakkan su.
Na gama tsab ban san yana zaune yana kallona ba sai da na gama shiri na na dago
zan yi mashi magana na samu ya kafa min idanuwan shi a kaina.
Murmushi nayi ina isowa wurin shi da sauri yace ashe matar tawa ta iya shiga ne
haka ban sani ba.
Yace ai wanan shiga zaki sa yau madam ta rude tace koba safiyan ta bane da ta ke
dauka yar kauye bata dace dani ba.
Ya miko min hannu a haka muka fito zuwa lifter muka sauka kasa inda muka shiga
mota muka kama hanya.
Ko a hanyama sai faman zolayata yake yi wai zan hana shi tuki da kamshin turaren
da na sa a jikina yace turaren yana da dadi shi nake son ki dinga amfani dashi ko
yaushe.
Mun isa gidan musalin karfe hudu na marance lokacin na tabbatar da daddy yana
gida don motar shi da nagani a waje abinda ya sani sauke ajiyan zuciya ke nan don
nasan ko maue zai zo muna da sauki tunda yana gida.
A tare muka fito zuwa cikin gidan inda ya danna bell din shiga cikin gidan ba
ajima ba na jiyo tafiyan mutum xuwa bude muna kofan nace ko yaushe suka fara rufe
kofa haka kuma.
Zuciyana sai duka yake uku uku fargaba da tsoro suka mamaye min zuciya a lokaci
daya sai dai hakan bai hanani yin addua a bakina ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/22/20, 5:53 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , ,
6🧕🏿161
6️⃣
6️⃣
1️⃣ 1️⃣
NOVEL DIN NAN NA KUDI NE DON ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA YAR UWA DON
ALLAH ZAI SAKA MIN A KAN KI, , , ,
A hankali kofan ya bude shike gaba ina daga bayan shi cikin fargaban ko wa zai bude
kofan a lokacin gabana sai danka yake uku uku.
Muryan Faiza ce naji tana fadin a yaya sannu da zuwa ya amsa mata kamar yadda
yake amsa muna a can baya idan muna gaida shi a gidan idan ya shigo.
Fara takawa yayi don shiga gidan na bishi a baya wanda sai lokacin Faiza ta ganni
taa sake dan ihu da karfi sai kuma taja bakin ta har da rikewa tace ashe tare kuke
cikin washe baki tana nuna farin ciki da gani na a lokacin.
Gaba dayan su har daddy suna falo zaune a lokacin da twins din ta Fati ce kawai
bata cikin su jin muryan shi da twins sukayi yasa suka mike gaba dayan su suka
nufashi da murnan su.
Suna gani na kuma sai suka barshi suka nufoni tare da fadin anty safiya oyo,yo
duk suka fada min a jikina nima rungumo yaran nayi zuwa jikina cikin shaukin junan
mu da andade ba a hadu ba.
Daddy ke fadin kar ku karya mummy naku mana wurin murna lokacin shi har ya kai
inda suke zaune yana kokarin zama.
Dayar tace anty safiya shine kika gudu kika barmu muna ta kewan ki kin dawo ke
nan inji dayar take tambayana cikin kallon fuska na.
Nace na dawo yan biyu ba gani kin ganni ba ba na fadi ina kara rungumay su a
jikina cikin jin dadin ganin su da nayi yau.
Mummy ga anty Safiya ta zo suke cewa uwar tasu data mayar da hankalinta ga uncle
suna gaisa wa dashi bayan ya zauna.
Tace da yaran naga safiya kuda kuke kewanta sai ku tare ta nidai ba wurina tazo
ba sai in wurin ku tazo hakan yasa na karasa gurin ina fadin haba anty kiyi hakkuri
mana.
Dariya daddy yayi yace kin ji tun ba a kai ko ina ba ma ta baki hakkuri na karaso
ina durkusawa a gaban su tare da gaishe su.
Daddy ya amsa min cikin daddin rai da sakin fuska yace yau yar gidan antyn ta ne
gidan namu nayi dariya ina noke kaina a tsakiyan kafafuwa na don kunya.
Na dago kaina cikin kunya ina gaida ita ta amsa min ba wani walwala a fuskan ta
da cewa lafiya lau yaya gida.
Uncle ya maiyar da bayan shi a makariyan kujeran da yake zaune yana fadin yau dai
ga kaunar ki nan na kawo maki don damuna da take yawan yi akan ki.
Murmushi tayi tace aikuwa ga Safiya na gani a gabana yau ga kuma uncle nidai
kaina na duke sai da daddy yace tashi mana ki zauna saman kujera Safiya nace a
kunyace daddy nan ma yayi mun ai.
Na kara dukar da kaina kasa nace daddy nan ma yayi min a lokacin ne faiza ta iso
wurin dauke da tire da abin sha a sama.
Ta dire a gaban mu tana cewa yau ga amarya a gidan mu anty ta ce ga fa amarya da
akai muna rowan buki a gidan tazo
Daddy yace aure yayi kyau dukkan su sai wani sheki suke yi da annuri tace
sulaiman ba amma itakan ai auren ma rama ya sakata yi.
Murmushi uncle yayi don yasan gatse tayi min kawai da wata manufa ta fadi maganan
ta ya mika hannu ya dauki goran ruwan yana ballewa tare da kafa bakin shi akai
bayan ya goge bakin goran da hannun shi.
Ga ruwan nan tace dani cikin rashin fuska a gare ta na dan dago kaina nace da ita
na koshi sai dai anjima tace yayi sai ta juya ga uncle din sukaci gaba da magana
dash.
Nan su yan biyu suka shiga hira dani ina dan basu amsa a hankali tana kallona ta
gefen ido tana mamaki a ranta yadda na juye kamar bani bace a lokaci guda.
Kayan dake jikina kawai ma abin kallo da yadda na tsara kwalliya kamar wata
balarabiya dani babu inda nake da mukusa a jikina.
Ya gyara zama tare da fuskantar anty din bayan ya kai duban shi gare ni yaga
yadda nake zaune a takure gashi kuma matar gidan sai basar dani takeyi a wurin.
Dan uwan nashi ya fuskanta tare da fadin mu zamu koma yaya dama na kawota ne ta
gaishe ku kafin mu tafi da sauri daddy din yace tun yanzu zaku tafi ba a ko gaisa
ba.
Ido da ido ya kalli anty din yace matar gidan ce naga bata maraba da zuwan mata
na gida so ba zan juri ganin wanan a tsakanin su ba.
Saboda may daddy yace idan bata mara ba daku ai mu da twins muna maraba daku don
wurin mu kuka zo.
Yace na dauka abin da ya faru a tsakanin su ya wuce don da nasan har yanzu madam
tana rike da ita a zuciyar ta ba zan kawo ta gidan nan ba.
A yadda yayi maganan ya nuna ranshi ys baci ga abinda tayi muna ya juya inda
nake zaune yana fadin tare da mikewa tsaya yace tashi mu tafi.
Dago kai nayi ina kallon shi tare da dan marairaicewa nace Uncle kayi hakkuri
ka bari a bata hakkuri ta yafe min.
Tare suke hada baki wurin fadin ta yafe maki da kikai mata may zaki ce ta yafe
maki inji daddy ya fadi yana mai kura mata ido.
Yadda sukai mata yasa taji nauyi da kunya ta fara kamay kamay tana fadin yanzu
may nace ina wanan maganan an wuce shi ko.
Uncle yace cikin girgiza kai madan bayi expecting din haka daga wajen ki ba don
kece ki ka nuna mun Safiya a gidan nan duk abinda mukayi mun yi biyayya ne bisa
umurnin ki.
Banji dadin yadda haka ya kasance a tsakanin ku ba a sanadiya na na dauka kin
fahinci ni kowaye zuwa yanzu ni mutum ne da ban magana biyu a rayuwana.
Don , , , , daddy ne ya katse uncle da fadin ya isa haka please sulaiman dauki
matar ka katafi Allah ya tsare Allah ya baku zaman lafiya.
Sulaiman don Allah kuyi hakkuri da kai da Safiya in Allah ya yarda haka ba zai
sake faruwa ba ta fadi tana duban sulaiman din.
Daddy ya rausaya kai yana nuna ma uncle kujera ya zauna lokacin ne su twins ke
cewa in tashi in zo inga gadon da daddy ya sake masu a dakin su.
Dole na tashi na bisu dakin nasu nan suka samu daman sakewa inda daddy yai
mutaukar nuna mata bacin rai ga yadda ta tare ni.
Har yake cewa bata san Allah ne ya rufa mata asiri da anty uwa da Uncle ya yarda
da auren diyar anty Uwa da kashinta ya bushe.
Karshe tace amma anan zaka barta sai dare ka dawo daukanta don karkace ban kula
maka mata don naga tun yanzu ka nuna min matarka kake so dani.
Dariya suka kwashe yace ba dole ba ai safiya ta yi don yarinyar ce data san
kanta wurin komai na rayuwa ya fadi hakane don ta san bada wasa yakeyi mata ba.
Ta mike tana fadin barin rafi wurin Safiyan in barku kar kuma nayi wani laifi ga
mai gidan again nan ta mike ta barsu da dan uwan nashi.
Muna daki da yaranta sai gata ta shigo dakin kallon da take min yasa na dukar da
kai cikin fargaban abinda zata fada min din.
Sai da ta samu wuri tavzauna take ce min Safiya kin san baki kyauta min ba don
kin yaudare da sauri na dago ina kallon ta don jin kalman yaudarar da ta kiramin
din.
Tace kin san kun shirya komai da Sulaiman kika boye min hakan sai jin zance
buki kawai nayi gun mutane amma ke baki sanar min ba.
Nace anty bansan da auren nan ba ba fada maki tun farko daga zuwa tambaya aka
daura muna aure dashi.
Nakiraki kuma in maki bayani baki saurare ni ba a lokacin kin dauki zafi dani,
duk yadda na so ki fahince ni kin ki saurararona a lokacin.
Tace ai dole a daura maki aure daga zuwa tambaya tunda kuna matse ku samay shi
kada ya kubce maku a hannu.
Naji wani zafi a raina nace haka ne anty don masu son su samay shi a lokacin muna
da yawa da yake Allah yayi nice matar ai an daura dani ba shiri.
Kallo na tayi kamar zata yi magana sai kuma tayi shiru kawai ta murmusa a ranta
tace eh lalai kin zama matan manya a yanzu safiya .
Amma a fili sai tace dani yaya zaman ku da yan uwan sulaiman din yake yanzu na
gyara zama nace da ita lafiya kalau muke satin da ya wuce ma muna bauchi din mun
tafi sallaman su kuma ya kai masu kayan azumi da na sallah.
Da sauri ta kallo ni tace what har sulaiman yayi rabon kayan azumi da sallah banda
labari wa ya saka ya dauko mashi kayan da ya raba bana.
Nace yan uwanshi yaba nauyin yin hakan don sune sukayi rabon da muka je acan
shiru tayi na dan lokaci sai tace zan ganshi inji yadda akayi hakan ya faru.
Nan dai muka zauna wanda duk hiran namu bugun cikina take yi amma sai in nuna
mata ban san komai ba a kai har ya turo yan biyu kirana wai zamu tafi.
Tare muka fito da ita daga dakin take cewa dani kin dai san namiji ba ai mashi
farar daya don haka duk abinda kike samu sai ki turo ai maki tanadin shi yafi.
Nace to anty insha Allah zan dinga turowa sai dai na fahinci uncle ba irin mazan
dake ba mace kudi bane haka na amma yana kashe min kudi ga duk abinda nake so.
Tace may ye baki dashi yanzu dole ne kisan yadda zaki juyashi ya dinga sakar
maki kudi kina turowa nan ana maki tanadin su.
Ina gyara gyale nace insha Allahu anty duk abinda nake samu zan dinga turowa gare
ki da zaran na samu tace koke fa haka yasa muka fito muna dariya sau mazan suka
dauka mun shirya a tsakanin mu ne.
Daddy ne ya nuna ma uncle din mu yace gani ba dama nace ma ai sun fi kusa kaga
kamar ba yanzu muka shirya su ba.
Nan dai muka samay su tana kara jaddada min karfa ki manta da sakona nace in sha
Allahu anty.
Gaban daddy nazo na durkusa gaban daddy tare da sunkuyar da kaina ina fadin daddy
zamu tafi yace ubangiji ya kaiku lafiya ku dawo lafiya safiya ayi ta hakkuri shi
zaman aure dan hakkuri ne.
Har waje suka rakomu muka wuce suna daga muna hannu sai da muka bar area din na
sauke ajiyan zuciya a fili.
Uncle yace dani yanzu dai hankalin ki ya kwanta kun shirya da anty ki ko nace ai
hakan yafi don da ba haka ba bazan taba samun kwanciyar hankali ba a raina.
Amma cikin zuciyana kuma tunanen anty din nake yi ashe dai duk