Showing 1 words to 3000 words out of 152206 words
[4/28, 9:59 AM] khaleesat Haiydar ✍️: *If you should come across this post plss say a prayer for my late
father, Allah ya sabunta masa rahama, ya gafarta masa da duk musulman da suka riga mu gidan gaskiya,
Allah ya kyautata makwancinsu gaba daya, ya sa mutuwa hutu ce a garesu, Allah ya yafe masu
kurakurrensu, Allah ya bamu guzurin tar da su* 🥺
**All thanks to Allah S.W.T for the chance and privilege to commence this new book, yanda muka fara
lafiya Allah ya sa mu idar lafiya*
_Hmm ga fa Halysaah, Allah ka bani ikon delivering babu cece ku ce_
*This first page goes to all the members of Mayraah Conversation, i love and appreciate you all*🥰
✨✨HALYSAAH✨✨
✍🏻
By _Khaleesat Haiydar_
1....
Tsaye take ta jingina da trunk din bishiya a wani babban garden dake dauke da shukoki iri iri da suka
kawata wajen, tsuntsaye sai shawagi suke a garden din happily making a chirping sound as the sun set
slowly, the view was so beautiful and breathe taking, duk da yanda ta kafe view din da ido gaba daya
hankalinta baya gun, she was just staring at the setting sun absentmindedly, tayi nisa cikin tunanin da take,
daga gefenta wata ma'aikaciyar asibiti ce in her mid 40, likitar ta dafa ta tana kallonta cikin kwantar da
murya tace "Magariba ya gabato mu je kiyi alwala ko" Kallon likitar kawai take babu ko kiftawa kamar
bata fahimci abinda take cewa ba, sai ga hawaye ya fara taruwa idonta tana sauke numfashi a hankali,
likitar ta kama hannunta ta jawota jikinta calmly tace "C'mon sweet heart, are you breaking ur promise
already?" ta kwantar da kanta jikin likitan hawaye wasu na bin wasu a fuskarta, likitan ta lumshe ido tana
patting dinta duk jikinta a sanyaye, a tare suka juya jin footstep a garden din, ya tsaya daga inda yake bai
karaso ba yana kallonsu, likitan ta fara gaishesa cikin girmamawa, zame jikinta tayi daga na likitan ta juya
masa baya alamar ko ganinsa bata son yi hawaye na zuba idonta, ji take kamar numfashinta zai dauke
kamar ko da yaushe, ta fashe da matsanancin kuka ta dafe trunk din bishiyar dake gefenta, ko amsa
gaisuwan likitar bai yi ba ya juya ya fice daga garden din, da sauri likitan ta kamota ganin faduwa zata yi,
ta fara kokarin zaunar da ita akan lallausan carpet dake shimfide wajen trying to calm her down tace "Haba
kanwata, me yasa baza ki cika min alkawarin da kika daukar min ba?" Muryarta na rawa tace "Kiyi hakuri
bazan iya ba wallahi" Rungumeta likitan tayi tana bubbuga bayanta a hankali wani mugun tausayinta na
shigarta, tayi attending to different cases in her career as a medical Doctor amma babu wanda ya taɓa daga
mata hankali ya tsaya mata a rai irin na baiwar Allahn nan, she wish she can take away her pains, she wish
she can make her happy once more, she wish she can make her forget the past and face the present, a
hankali likitar tace "Halysaah...." khaleesat ta daga rinannun idonta tana kallon likitan, likitan tace "Kiyi
hakuri Halysaah, kiyi hakuri" Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, likitan ta daga ta tana rike da
hannunta suka bar garden din zuwa babban compound din gidan.
Few years back!
"Talk to Abdul about it, nasan bazai taɓa yarda da haka ba, and he will definitely find a way out for u
immediately..." Khaleesat ta daga manyan idanuwanta tana kallon kawarta Safiyyah, kamar bazata ce
komai ba sai kuma ta sauke idonta a hankali tace "That will be another huge burden Safiyyah, u know how
expensive apartment can be in this state, gida da akwai tsada sosai, kuma na fa ce maki ni bazan sake
tambayarsa komai ba, ko kuma ince yayi min wani abu...." Safiyyah tace "Cabdi, to in ba ki tambayesa ba
kina da wanda zaki tambaya? Balle ma kinsan halinsa lokaci daya tsaf zai juya situation din nan against
you, i think gwara kawai ki sanar masa yafi maki kwanciyar hankali" Khaleesat tayi shiru tana nazarin
abinda Safiyyah ta ce, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza kai tace "It's fine Safiyyah, ba sai na
gaya masa ba i will cope in sha Allah, after all we have just a year and a half to go" Safiyyah na kallonta ta
kamo hannunta tace "Ko zaki dawo wajena sai in gaya masu kawata zata zo ta ɗan zauna da mu zuwa wani
ɗan lokaci?" Khaleesat ta girgiza kai tace "Let not inconvenience them Safiyyah, kar ki damu kawai, i will
sort my self out...." Safiyyah tace "No, i will talk to Ya Musty about ur current situation khaly, nasan bazai
ce a'a ba, matarsa ce dai gagarumar er iska, and do i even care? Ba ki ma san me take min ba yanxu a gidan,
duk dare bata girki da ni sai dai in nemi abinda zan ci tunda kinsan Ya Musty night shift yake, ni kuma
dama kin san i prefer junk food, kawai sai in hada cornflakes in sha abu na" Khaleesat tayi murmushi tace
"Shine kike son in bi ki zuwa gidan a haka ko? You are very funny" Safiyya ta juya ido tace "So what?
Naga ai ba kanta zaki zauna ba in kin dawo gidan, Yaya Mustyn nan fa is my cousin brother ko kin manta
ne? Saboda haka ko taki ko ta so dole in zauna a gidan har in gama karatuna, very wicked and self centered
woman, wallahi kar ki wani damu in dai nayi ma Ya Musty magana kawai ki dauko kayanki ki dawo gidan
ko zuwa gobe ne...." Khaleesat tace "Aa gaskiya don't even start that Safiyyah, i will cope with my present
situation with time, nasan zan saba gradually, beside it's something that is normal kawai dai ni ce nake
damun kai na saboda addinina da culture dina da dai wasu abubuwan da baza a rasa ba, any way... it's fine
Safiyyah" Tana fadin haka ta kalli wayarta dake hannunta jin shigowar notification, tace "I think my Lyft is
here Sophie, sai gobe in Allah ya kai mu" Safiyya ta sauke ajiyar zuciya tace "Ohk then, take care of ur self,
i will stroll home too" a haka suka rabu, Khaleesat ta nufi Lyft din da tayi ordering zai maida ta gida.
Khaleesat na kitchen wajen karfe goma na dare ta gama girka Noodles da zata ci for dinner kenan taji
alamar an bude kofar parlor, a hankali ta karasa juye Indomie dinta a plate ta dau fork ta saka sannan ta
wanke pot din ta ajiye, ta bude fridge ta dau bottle water ta fita daga kitchen din, hanyar dakinta ta nufa
direct, dai dai corridor aka bude kofar wani room that is just few steps away from her own room, ko kallon
direction din bata yarda tayi ba tana kokarin bude kofar dakinta taji ance "Hi, good evening, we didn't get
to meet when i was here in the morning I guess you've already left for school then, you can call me Jay, and
i am ur new House mate, I moved in this morning...." Sai a sannan Khaleesat ta juya ta kallesa amma bata
ce komai ba, ya gyada mata kai yace "Jay" babu yabo babu fallasa tace "I see" Ganin zata shige daki yace
"A minute pls" Ta juya ta sake kallonsa da wani expression, a takaice yace "Ke bahaushiya ce?" Ta ɗan
hade rai tace "I don't know what u are talking about" Yace "Oh ohk, i am asking for a permission..." Ita dai
kallonsa kawai take, Ya gyara tsayuwarsa yace "As u can see it's late already now, can i use some of ur
portable water and Beverages before i get mine tomorrow if you don't mind?" Khaleesat ta dauke kanta a
takaice tace "Ohk" Yace "Alright" Daga haka ta shige dakinta ta kulle kofar ta saka key, ko da ta gama cin
Indomie din bata ji zata iya bude kofa ta fita kai plate din kitchen ba, daga karshe kawai ta bar shi a wajen
bayan ta shiga bandaki ta wanke bakinta ta dauro alwala ta fito ta zauna edge din gadon dakin ta dau
wayarta, Miss calls din Abdul ta gani har biyu wanda yayi mata tun karfe shidda, ta sauke ajiyar zuciya tana
duba agogon wayarta dake nuna mata karfe goma da kusan rabi, meanwhile karfe kusan biyar kenan na
asuba agogon Nigeria, bude WhatsApp dinta tayi ta dubasa taga yana online, hakan yasa ta masa WhatsApp
call, yana dagawa tayi kasa da murya ta gaishesa a hankali, Bai amsa ba yace "Yanzu kika ga kirana?" Ta
sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Kayi hakuri, yanzu naga kiran wallahi" Yace "You mean tun daxu
wayarki baya gun ki kenan?" Tace "Not really, tun dai da na dawo schl nake karatu, in few months time
zamu fara exams" Yace "I see, shi ne yasa kika ga ban yi deserving lokacin ki ba don zaku fara exams, ta
yaya ma wayarki zai yi ring ki ce baki sani ba in ba rainin hankali ba?" Rasa abinda zata ce masa tayi, don
wayar a silent yake kuma ya hanata barin waya a silent on several occasions, to avoid further issues sai bata
ce masa wayar a silent yake ba, a hankali tace "Kayi hakuri, wallahi ba haka bane, i am sorry..." Yace
"Sorry for ur self, malama so nake ki gaya min kina ina har wayarki rang twice baki ji ba? ur lectures today
terminated by 4pm Baltimore time, so ina kika je daga nan?" Ta rufe ido ta bude don ta fara gajiya da
tuhumar tasa, After few seconds ta marairaice tace "Ina parlor ne ina karatu, wayar kuma na daki" Yace
"Kin fara zaman parlor kenan, when did that start? House mate din taki ta dena shigowa da saurayinta ne
gidan?" sai da gaban Khaleesat ya fadi, A hankali tace "Bata nan, taje LA jiya" Yace "Sau uku kenan ina
kiranki a satin nan baki dagawa sai sanda kika ga dama ki biyoni, that nonsense shouldn't repeat it self
again, a kanki aka fara karatu ko ni zaki gaya ma karatun Exams?" Shiru Khaleesat tayi lkci daya hawaye
ya cika idonta, a ɗan fusace yace "Baki ji na ne?" Cikin sanyin murya tace "Naji, kayi hakuri hakan bazai
sake faruwa ba in sha Allah" Yace "Good, you can go to bed" Tana goge hawayen da yaki tsaya mata tace
"Nagode, sai da safe" Shi ya katse call din ta ajiye wayarta gefen gadon ta dora kanta a pillow hawaye na
zuba idonta, after a while ta mike ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta dawo ta kashe wutan dakin tayi
addu'an bacci ta kwanta.... Washegari Friday da wuri Khaleesat suka gama lectures dinsu, suna zaune a
exact spot din jiya ita da Safiyyah dake waya, sosai Khaleesat tayi nisa tunanin da take har bata san sanda
Safiyyah ta gama waya ba, dafa kafadarta da Safiyyah tayi ne ya dawo da ita duniyar tunanin da ta shiga,
Safiyyah tace "What is wrong Khaleesat, ina ta magana baki ma san ina yi ba, tunanin me kike haka?"
Khaleesat ta ɗan kirkiri murmushi tace "Kawai ina kewar Ummanmu ne da siblings dina" Safiyyah ta
girgiza kai tace "Ban yarda ba, there is definitely something that is bothering you" Khaleesat ta kauda
zancen tace "Ke da George ne ke waya ko?" Safiyyah tayi kasa da murya tace "Pls gobe weekend ki shirya
mu tafi Virginia Leesat, George is throwing a party for his birthday tomorrow, kuma za mu je Beach, don
Allah kar ki ce a'a, we need to take a break and rest our brain, ba ko da yaushe karatu ba kamar mu muka
kawo boko duniya...." Khaleesat dake ta kallonta tace "Ke yanzu sai ki kama hanyar Virginia Safiyyah??"
Safiyyah ta hade girar sama da ta kasa tace "To menene, it's just a 4 hours ride from Maryland, kamar fa
ace daga kaduna zuwa kano shi ma in mota bai yi gudu ba, pls for once ki zama social mana Khaleesat, ke
baki gajiya da zama guri daya ne a kasar nan? Baki gajiya da karatu? ranan Monday fa za mu dawo in sha
Allah, kuma babu wanda zai san mun je wani Virginia, dama Ya Mustapha na riga na gama plan din abinda
zan ce masa, ke da ba ma ki da wanda zai sa maki ido kike mis using opportunities haka, da mun koma
Nigeria fa shikenan, tafiyar nan maza ne hade da mata" Khaleesat ta girgiza kai tace "Lallai... Ni dai ina
baki shawara kar ki je Safiyyah" Safiyyah tace "Bana ma son shawaran, abinda mu goma za mu je"
Khaleesat tace "Toh Allah ya tsare hanya ya dawo da ku lafiya" Safiyyah ta mata wani kallo tace "Baza ki
je ba kenan dai?" Ba tare da Khaleesat ta kalleta ba tace "Kema kin san bazan je ba ai" Safiyyah tace "Ke
kika sani, mu dai za mu je wallahi" Safiyyah na kai wa nan ta mike tace "Sai ran Monday" Khaleesat na
kallonta a hankali tace "Wai tafiya za ki yi? Da sauran time fa Safiyyah" Safiyyah tace "Aa toh me za mu
zauna yi a schl bamu da aji? Yau kuma kece ke cewa da sauran time duk son ki da komawa gida da wuri?
Ikon Allah" Khaleesat ta kasa cewa komai, ita har ranta take jin ta tsani gidan nata yanzu, she no longer see
the home as her comfort zone, and she don't think she can cope staying together with an Hausa Guy under
same roof, da ma bature ne ko kadan bazata damu ba kamar yanda ta damu yanxu, har ta taho school bata
hadu da sabon Housemate din nata ba da safe, Safiyyah ta ɗan buda ido ta koma ta zauna tace "Ohh now i
remember, wai saboda new House mate dinki? To wai ke meye damuwarki ne da shi? Yayi harkan gabansa
kiyi naki ne fa a gidan, ko magana in baki son ya maki you just call the cops a maki iyaka da shi, just dial
911 and that's all, balle nasan kilan da kyar aka kukuta masa ya taho makaranta kasar nan to kuwa ina zai
tsaya bata lkcnsa akan abinda ba shi ya kawo sa ba, don dai in wani Shege ne shi bazai zauna a shared
apartment ba a USA, kuma 'ya yan masu kudin nan sun fi iskanci su kuwa talakawa abinda ya kawo su
kawai suke yi, kiyi ta kanki kawai shi ma yayi ta kansa, kar kiyi mamaki ta scholarship ya zo kasar ma"
Khaleesat dai kallon Safiyyah kawai take, Safiyyah ta kyabe baki tace "Tashi mu je gidan, ni banda Ya
Musty bazai yarda ba da ba sai in tattaro in dawo gidan naki ba mu zauna kawai" Khaleesat ta marairaice
tace "Plss ki sake masa magana ko zai bar ki mana, ai sanda ya hanaki kinga bamu dade da fara makarantar
ba" Safiyyah tace "Kar ma ki bata bakinki mutumin nan bazai yarda ba, tashi mu je in raka ki, in House
mate din ma yaga kina wani yin abu a tsorace renaki zai yi wallahi, yi zaki yi kamar kema er gari ce kawai
sai ki ga ya fara shakkar ki a gidan" Khaleesat ta mike tace "Kar fa muje kiyi ta Hausa, just pretend we are
not Hausa" Safiyyah tayi dariya tace "Kece dai is not Hausa, ni kam Bahaushiya ce cikakkiya kuwa" A
haka dai suka bar makarantar suka nufi gidan da Khaleesat take.... Khaleesat ta bude handbag dinta ta ciro
makulli ta bude kofar shiga gidan suka shiga parlor Safiyyah na biye da ita a baya, Safiyyah na gyada kai
jin wani kamshi da parlon yake tace "Da alama bai dade da fita ba ma" Khaleesat dai bin parlon take da
kallo ganin duk reading materials dinsa ne saman kujera ya tula a kai, Safiyyah tace "Kinga don Allah ki
saki ranki ki ci gaba da harkokin ki Khaleesat, a Maryland fa kike a Amurka ba Kano Nigeria ba, ki dinga
abu irin na wayayyu mana pls" Wani kallo Khaleesat tayi mata ta ajiye handbag dinta tace "Ance maki in
bature ne ko wani yare ni zan damu, kawai my issue here is about him being a Hausa Guy, har fa tambayata
yayi jiya ko ni bahaushiya ce" Safiyyah tace "Ohh kun ma yi magana kenan...." Khaleesat tace "Ni ban
kulasa ba kuma ban nuna masa ni Bahaushiya bace, i will just pretend i am from Morocco" Safiyyah ta
dinga dariya har da saukowa daga kan kujera tace "Gashi kuwa an ma fi saninsu da fararen mata kyawawa
na ajin karshe, tsaf zai yarda daga can kike, kinga da larabci ya zauna daram a bakinki sai kiyi ta zabga
larabci nasan ba lallai yana ji ba, daga haka zai kama kansa yayi zaton ke balarabiyar gaske ce... sai ma
Abdul yaji kuna gida daya da Bahaushe kilan Baltimore yayi maku kadan wallahi, shi sa nace ki gaya masa
kika ki" Khaleesat ta ajiye jakarta bata sake kallon Safiyyah dake ta dariya ba tayi wucewarta kitchen tana
tunanin me zata dafa masu dama ko breakfast bata yi ba ta fita daga gidan, tsaye tayi kitchen din tana
kallon cartons din bottle water kusan bakwai wanda duk yafi tsada a state din, sai kuma ta juya ta kalli
beverages masu yawa da ya ajiye kan cabinet, ta karasa cikin kitchen din ta bude babban fridge zata dau
kwai da za ta dafa masu Noodles, kallon fridge din ta dinga yi ganinsa fully stocked with everything, tun
daga tsadaddun drinks kala kala, fresh milk, varieties of fruits, with many eggs, muryar Safiyyah taji a
bayanta tace "Kai kai kai, shi ya zuba abubuwan nan a fridge Leesah?" Khaleesat ta juya ta kalleta looking
speechless, can dai ta dau eggs din da zata dauka ta kulle fridge din ta tafi inda foodstuffs dinta suke shi ma
taga kayan abinci ya siyo, Safiyyah ta rike haɓa tace "Duk a kudin scholarship din yake facakan nan? Ko
dai bashi da hankali ne bai san bin komai ake a sannu a kasar nan ba" Khaleesat dai ta dau Noodles dinta ta
bar wajen tana kallon Safiyyah tace "Ga Indomie ki dafa mana, ina son inyi magana da Ummanmu kafin
Aunty Sha'awa ta fita kasuwa" Safiyyah tace "Ohk to" Khaleesat ta bar kitchen din ta dau jakarta ta wuce
dakinta, WhatsApp dinta ta bude ta shiga contact din makociyarsu Sha'awa tayi mata voice note kamar
yanda ta saba a duk sanda take son magana da Ummanta. Sai kusan karfe hudu na yamma Khaleesat ta raka
Safiyyah zuwa gun Lyft din da tayi ordering don tun daxu Cousin brother dinta ke kiranta ganin bata dawo
gida ba, Safiyyah ta shige motar ta kulle tana daga ma Khaleesat hannu, sai da Lyft din ya bar wajen sannan
Khaleesat ta juya tana tafiya a hankali ta nufi apartment dinta, dai dai apartment din taga mota yayi parking
a space din da aka tanadar don parking