Showing 81001 words to 84000 words out of 121650 words
lumshe idonta saboda yadda wakar
ke ratsata, wani duka Mama ta kaiwa cinyar ta wadda ta bayyana saboda kwanciyar da
tayi zaninta ya tattare, wani tsalle ta buga wadda yasa wayarta faduwa kan simintin
dakin, idanunta ta bude idonta Cikeda masifa se taga Mama ce amma dukda haka tace
Mama ya haka?
Ubanki nace, tun dazun Baban A'isha ya turo kizo amma kika ki zuwa saboda kin
shahara ko?
Tsaki ta saki tareda daukar wayarta wadda tuni ta fashe, gashi babu screen guard,
ihu ta kwalla tace
Haba Mama Wallahi nidai Baki kyauta min ba.
Wani dukan Mama ta kai mata tace
Tashi muje.
Mikewa tayi tana kunkuni ta nufi inda Baba yake Zaune, ranshi a hade wai kar ma
taga fuskar da zata kawo mishi wargi, itama bata ran tayi tamkar me shirin wata
tsiyar. Yadda ta tsaya tsegege ta kama kugu yasa Mama Dalla mata harara, amma se ta
dauke kanta tana Kara hade fuska tamau. Ba karamin bata ran Baba abin yayi ba yace
Ke!
Kin jiyowa tayi seda Mama tace
Khulthum bakyaji? Ba dake yake ba?
Juyowa tayi tace
Mama Ke yace fa! Bakiji ba?
Zauna
Ya furta Yana danne bakin cikin dake addabar zuciyarshi, yasan komai Khulthum ta
zama har dashi , Tunda ya bata yarinyar bai hanata yin komai saboda tana bashi
kudin cefane gashi yanzun babu Wanda ta kyale cikinsu. Kanshi ya girgixa Cikeda
takaici kafin ya dubi Mama yace
Duk inda na wuce se anyimin magana akan Khulthum tana Tara maza don haka na gaji ko
dai ta fitar da miji tayi aure ko kuma ta koma malumfashi.
Yana aje numfashi tace
Gobe zaa zo gaisheka.
Tana gama fadar haka ta mike zuwa Dakinsu ta kwanta, Mama ta biyota tana ta fada
amma Khulthum ko kallonta Batayi ba, hakan yasa Mama ta dinga kuka Tana fadin
Wannan shi ne ladan haihuwa Khulthum, Kinyi daidai Yarinya wannan Itace sakayyar
goyon da nayi miki!
Khulthum bata motsa ba har su A'isha suka dinga rarrashin Mama kafin ta tafi ta
kwanta zuciyarta tana gobara!
Washegari ta kasance juma'a, kamar yadda Musbahu a ranar Bayan anyi sallar juma'a
yazo shida Kabir ya gaishe da Baba Alkasim wanda ya gayyato abokinsa guda daya.
Cikin mutunta juna suka gaisa, nan Musbahu ya sanar musu yana son Turon iyayenshi
wani satin ayi finalizing komai. Anan Baba ya sanar mishi asalin Khulthum iyayenta
na malumfashi Don haka zaiyi magana da babarta aji. Da haka aka tashi maganar bai
nemi ganin Khulthum ba duk yadda Kabir Ke rokonsa Amma yace bai da wannan lokacin
ya bada kudi a Bata ai kuwa tayi murna don Musbahu bata ga wani lokacin batawa tayi
soyayya ba kudin dai.
Da daddare ya gabatar da kudirinshi ga Gwoggo.... Kuzo kuga murna gurin baiwar
Allah, nan ta dauki waya ta Fara kiran uncles dinshi akan wani satin zaaje nema
masa aure, yadda take murna yasa zuciyar Musbahu karyewa ya bar gurin yana jin ya
tsani Abinda yake aikatawa.! Sede wani kuskure daya da aka tafka Gwoggo bata saka
an bincika wacece Khulthum ba Tunda tana ganin a nutsuwar Musbahu bazai kawo abin
kunya ba, su kuma dangin Khulthum Dana ubanta Musbahu yayi musu girman da zasu
bincike shi! Tirkashi
_Just a smile and the rain is gone, can hardly believe it... Yeah! There's an angel
standing next to me reaching for my heart!_
Sun jima sosae a tsaye a gurin yana rungume da ita, yana bubbuga bayanta ita kuma
tana ta hawaye a jikinshi. Kasa yayi da kanshi saitin kunnenta ya hura mata iska
wadda tasa babu shiri ta saki ajiyar zuciya tareda kankame shi. A hankali ya kamo
hannunta zuwa kan gadon da ta baro, seda ya zaunar da ita tukun ya janyo farar
kujerar dake gefen gadon ya zauna Yana dubanta da idanunshi wanda Lokaci daya tayi
Kasa da nata saboda bazata taba iya jurar abubuwan dake fita daga nashi idanun suna
shiga cikin nata.
Dove! Kinsan how your tears are piercing my heart, inda Kinsan yadda nake jin
kukanki tunanin zaki iya yin fushi balle kuka.
Hannunta tasa Wanda yasha lallai ta goge fuskarta tare da sakar mishi tattausan
murmushi, lokacin ya lura da zanen henna hakan yasa ya riko hannyenta ya kura musu
ido kafin ya fara shafa su cikin wani Irin salo da Hannunsa Wanda yasa su jin
tamkar electrical current ake passing jikinsu, a hankali ta janye hannunta saboda
abin affecting dinta yake sosae, langwabar da Kai yayi shima ya turo bakinshi yace
Rowa ba kyau!
Murmushi tayi ta rufe fuska da hannayenta, Tana jin mahaukacin farin ciki da bata
taba mafarkin shiga Irinshi ba, hannun ta Mika mishi a hankali tace
How does it happened?
Tashi yayi ya dawo gefenta ya zauna, baki dayansu suna jin numfashin junansu,
lafayar ya fara warewa har ya cire ta gaba daya sannan ya ajeta a gefe ya dago
fuskarta ya kalleta yace
Dove! Kinsan me yasa nake kiranki Dove?
Kanta ta girgixa, ajiyar zuciya ya sauke yace
Doves are beautiful and very gentle, gentility dinki da kyau da Allah ya baki shi
yasa kikai suiting da Wannan sunan..... I love you my Dove so much, na miki
alkawarin kasancewa a tare dake Duk runtsi duk wuya, ba lallai ki samu farin cikin
da kike tunani ba ko kuma kike mafarkin samunshi ba amma Inshaaa Allah xanyi iya
bakin kokari na!
Hawaye ne suka gangaro mata tayi saurin kauda su, Tana jin dukkan damuwarta ta yaye
dukkan wani kuncin ta Yana yayewa kamar evaporation na steam.
Lokacinda muka gama magana da Mami nace mata na hakura, I was shattered, I
threatened her inason Tace min nazo ta bani ke amma haka raina a mugun bace na taho
Kano, I was lucky duk yadda hanyar batada kyau amma haka Allah yasa na iso kano, se
a cikin gari sannan bansan yadda akai ba kawai nasan munyi Karo shikenan. Se jiya
Mami tace kin fita da yan Mintina na farka, I was lucky kaina ne kawai ya bugu amma
brain din is OK, bacin rai da nake ciki yasa na zama unconscious. Gashi at least
Bayan accident I was able to have you! I love you baby.
Hawayen dake mata zarya a kumatu ta goge ta bude Baki don yin magana ya hanata
maganar ta hanyar hade bakinsu waje daya.
Washegari Misalin karfe takwas da rabi, akazo handing over, Junaid na zaune kan
carpet yayinda Sulaim ke kwance kan gadon ta kudundune tamkar ita ce marar lapiyar
a cikin duvet. Hirar da nurses din keyi da Junaid yasa ta farka ta yaye bargon Zuwa
wuyanta tana binsu da kallo. Daya daga cikin nurses din tace
Amarya Anya jinya kike kuwa? Kin wullo mana patient kasa kin hau gado.
Dariya sukai Junaid yace
A'a sister Karki takura mata fa.
Dariya suka kuma Yi sister tace
Dariya take kamar ba ranar take ta kuka ba kamar ranta zai fita.
Haka dai aka gama sukai mishi Allah ya sanya alkhairi da fatan Karin lapiya. Suna
fita ya rufe dakin da key sanann ya dubeta yace
Sakko Kije kiyi wanka.
Mika tayi bbau musu ta sakko ta nade blanket din ta gyara gadon sannan ta nufi
bayi, ta jima tana wankan sannan ta fito da hijabi jikinta lokacin baya dakin,
hakan yasa tayi saurin ciro kaya a jakar da Amma ta kawo mata, wata simple gown ce
baka se inner wears dinta, Seda ta saka sannan ta shirya tayi shafe shafenta kafin
ta gyara gurin, tayi kyau kamar ba ita ba, kofar ta nufa daidai lokacin Junaid ya
sako kai ya bigeta tayi baya zata fadi yayi saurin tarota jikinshi. Ajiyar zuciya
ta sauke ta biyo bayanshi suka Fara breakfast. Seda suka gama tsaf yace
Dove are you happy ko tursasa ki nayi kika aureni?
Da sauri ta girgixa kanta tace
I'm so happy that I can't express exactly how I feel, Amma nasan zaka fahimci how
exactly I feel, felt and feeling and I love you so much!
Hannunsa ya bude mata babu musu tayiwa kanta masauki jikinshi!!!
*I lay my love on you, it's all I wanna do, every time I breathe I feel brand new,
you open up my heart show me all your love and walk right through......*
Shatuuu ♥️
[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
✍️SHATUUU♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣shatuuu095@wattpad
Assalamu alaikum Sweerie pies..... how's Sallah fatan kowa yayi sallah lapiya?
Amin.... Allah ya maimaita mana Dearies.
Inshaaa Allah zaku iya jina anytime from now, Allah ya karba ibadunmu. I've seen
your comments and votes, Wallahi I can't ask for more... You guys are the best, I
love you so very much.... Allah ya bar mu tare. Aci nama lapiya!
Shatuuu ♥️
[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
41
✍️shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣shatuuu095@wattpad
Monday Morning
Mikewa yayi daga kan carpet din da yake Zaune akai Tun bayan Idar da sallar asuba
yake Zaune a gurin yana tilawa, gaba daya a takure yake jin kanshi tamkar anyi
chaining dinshi haka yakeji, ya gaji zaman asibitin nan Tunda shidai yanzun yasan
lapiyarshi kalau babu Abinda Ke damunshi, amman baya son ya nemi discharge din
Tunda su suka kwantar dashi suka San Meye matsalarshi.
Inda Dove dinsa take ya isa, ta kudundune cikin Duvet cover abinta se sharar
baccinta take, Tunda sukai sallar asuba ta koma ta kwanta, gefenta ya zauna ya yaye
cover din hakan yasa tayi juyi ta turo mishi karamin bakinta, murmushi yayi yace
Dove makaranta fa, is already six.
Bata fuska tayi ba tareda ta dago ba tace
Ni ba zanje ba gaskiya.
Idanunshi ya dan zaro Yana murmushi yace
Why?
Ni ba patient relative ba ce.
Wannan karan seda yayi dariya yace
Kinji ki da me kikeyi min? Come on tashi Kada ki makara.
Zumbura Baki tayi ta Mike Daga gadon Tana ta Bata rai tana fadin
Dama ba sona ake ba, if not me yasa zaace se naje school.
Dariya yayi kasakasa Yana shafa kanshi, shikam Allah ba karamin so yake mishi ba da
ya bashi Sulaim, Tunda Mami da Baba suka mishi albishir bai kara daina murmushi ba,
she gave him every reason to smile, she never cease to amuse him. Yarinyar tana
tafiyar da soyayyar ta kamar yadda ta fada mishi xai gani gashi kuma yana gani.
Seda ya linke Duvet din sannan ya fita don yasan bazata iya shiryawa ba idan yana
nan. Masifar kunya ce da ita don common peck ya bata se tafi 10 minutes idonta a
kasa. Balle kwanciya dama se ya bari tayi bacci sannan yake hawowa gadon ya kwanta
idan ba haka ba ta dinga mutsu mutsu kenan.
Zama yayi Yana ta kallon yadda ake hadahada cikin asibitin, ita kuwa seda ta leko
taga baya nan sannan ta fito ta shafa manta na Jergens ta fesa turarruka a jikinta
sannan ta dakko wani lace zata saka ta tuna Monday ce yau black and white, hakan
yasa ta maida ta dakko Bakar abaya Fara tas da Polk dots na baki a jikinta, powder
ta shafa hade da balm ta kalla kanta tayi murmushi ganin yadda ta fito tayi kyau.
Kanta ta taje ta gyara zaman ribbon din sannan tasa hula baka ta Fara gyaran dakin
lokacin bakwai ta buga. Kafin ta leka kiranshi taji ya bude kofar ya shigo a nutse
bakinsa dauke da sallama haka idanunshi kur a kanta yana jin wani sonta na fuzgar
shi hade da nutsuwa cikin zuciyar shi.
Kan carpet ya zauna lokacin tana tsiyayo ruwan zafi Daga flask zata hada tea, tayi
kicinkicin da fuska ita a dole fushi take. Tana gama hadawa ta zauna gefen gado ta
Fara sha tana ciccin magani tare da kawar da kanta Duk kuwa da tasan kallonta yake,
shima share ta yayi Yana murmushi ya maida hankalinshi kan newspaper da aka kawo
mishi.
Seda ta gama ta dauki madaidaicin veil Baki me Polk dots farare mahadin Abayar
jikinta tai rolling sannan ne ta dubeshi tace
Yaya zan tafi.
Kanshi ya dago tareda zare glasses din idonsa yace
Zo kiji.
Babu musu ta nufi inda yake ta sunkuyo, hannunta ya kamo ya zaunar da ita yace
Yayan akewa fushi? Da fushi zaki tafi school?
Kanta ta girgixa, kallonta yayi yace
To Kiyi min murmushi na gani mana tawan!
Murmushin ta sakar mishi hakan yasa ya janyota jikinshi tareda rada mata abu cikin
kunne, kwace jikinta tayi tana dariya shuma yanayi yace
Kin yadda?
Kanta ta girgixa tace
No!
Zaki sani
Ya bata amsa kafin ya Mike ya dakko wata Leda me kyau yace
Amma tazo jiya Kina bacci tace na baki.
Karba tayi ba tareda ta bude ba ta Mika mishi tace
Ka aje min idan na dawo zan duba.
Kanshi ya girgixa yace
A'a kije kya duba a school.
Babu musu ta karba suka fito tare Yana ta tsokanar ta wai amaryar Asibiti, itama
tana ce mishi angon Asibiti, a haka suka zo station din nurses ya dan tsaya yace
zai rakata gate zata tafi makaranta. Sallama sukai suma suna ta tsokanar ta, har
gate ya rakata inda Jawad ke jiranta cikin mota, Seda yaga ta shiga kafin ya juya
yana jin kawarta cikin jikinshi da zuciyarshi, hakika Sulaim tanada kaso mafi girma
cikin zuciyar shi.
Tana zuwa school sukai sallama da Jawad ta nufi class, inda suka saba zama taje ta
zauna babu jimawa Aimana da Khairi suka iso kamar wanda suke Daga guri daya. Cikeda
farin ciki suka zauna suka sata a tsakiya. Khairi ta dubeta tace
Sulaim wannan kyau haka, ga kamshin amare da kike fitarwa.
Aimana tayi saurin fadin
Wallahi, kinga sati biyu kawai ta zama very matured se kyalli take.
Gyara zamanta tayi tana jin ta inda zata Fara su fahimce ta, cikin nitsuwa tace
Kuyi hakuri nasan kuna ta nemana a waya baku sameni ba, Wallahi Yaya yayi accident
I some how fainted..... Idanu suka zaro.... To muka taho Kano na bar wayata a
Kaduna. Tohm kuma yau Kwana biu aka daura mana aure ni dashi.
Maimakon ganin bacin rai saboda bata fada musu ba, se gani tayi suna ihun murna har
hankulan mutanen class ya fara dawowa kansu, Salma kwalam, Hidaya da Halimatou suka
zo jin kwakwafi Aimana ta Mika musu invitation da Sulaim ta karbo hannun Junaid
ashe shi ne sakon Amma din, su Mami sun yanke zaayi biki in a week time don ta tare
basu son a ja abin, event din Kamu ne se dinner da friends din Junaid suka hada
mishi anan Kano.
Aimana ce ta dinga raba invitation card Khairi tana harhada yadda abin zai kasance
da yadda zasu fitarda anko a samu a sati daya. Ranar gaba daya haka ta kare sun
manta da wata Khulthum Seda Sulaim tace da Aimana
Bani Aron Wayarki na kira Khulthum na fada mata.
Nan Khairi ta Fara dariya tana bawa Sulaim yadda Aimana sukai da Khulthum, Aimana
Cikeda bacin rai tace
Ki bar shegiya kawai, Allah naji haushi Allah ya hadani da ita.
Sulaim tace
A'a ai ya wuce ki rabu da ita kawai, bani number idan naje na Kira da wayar Friend
(Jawad).
Rubuta mata akai jikin paper sannan kowa ta kama hanyarta, ta dan jima tana jiran
Friend amma bai zo ba gashi bata da waya kuma, batayi azancin dakko kudi ba. Mikewa
tayi ta nufi office din Ridwan daidai sun fito shida Sagay, da Mai Sogha da Dr
Halliru, gaishesu tayi Ridwan Yana musu bayanin ita ce amaryar Junaid, gaba daya
sukai mata Allah sanya alkhairi suka basu guri, anan ta samu ta fada mishi Abinda
Ke faruwa,
Muje na kaiki dama can zanje.
Godiya tayi mishi tabi bayanshi suka tafi a motarshi, maimakon Asibiti se suka nufi
gida, kamar zatayi magana se ta kyaleshi har suka iso yayi parking yace
Ki fadawa Junaid ina waje ina jiranshi.
Kanta ta gyada ta sake godiya sannan ta shiga ciki, Tunda ta bar gidan ranar jumaa
da daddare bata kuma dawawa ba se yau, cikin nitsuwa ta Koda Yaushe ta shiga gidan
daidai Jawad zai fito Yana ganinta ya fara fadin
Dan Allah Friend Kiyi hakuri Wallahi Mami ta aikeni.
Hararashi tayi tace
Ba ruwana da Kai.
Dariya yayi yace
Se Amaryar babban yaya!
Dariyar ta Kara saki tayi ciki tana jin farin ciki sosae a ranta. Koda ta shiga da
Muhammad ta Fara cin Karo yana kuka yana kiran sunanta, take taji gabanta ya fadi
tuna cewar Ashe akwai uwarsu fa, ita Wallahi ta manta ma gaba daya ta manta da
rayuwar wata Subay'a don idan Suna tare manta wa take da wata Subay'a.
Tsugunnawa tayi ta daukeshi tana lallashi suka shigo ciki, Mami ce a Zaune Kan
kujera se Junaid a gefenta yana nuna mata abu cikin wayarta, sallamar ta yasa baki
daya suka dago idonsu suna kallonta, zama tayi akan carpet tace
Mami ina yini?
Lapiya lau Sulaimi ya makaranta?
Alhamdulillah.
Ta fada sannan ta dubi Junaid wanda ke kallonta tace
Yaya ina yini?
Hararar ta yayi, sannan ya amsa, kanta ta dauke don ta fahimci Abinda yake nufi
tace
Yaya Ridwan Yana waje Yana jiranka.
Da sauri ya mike yayiwa Mami sallama ya fice, kallon Mami tayi tace
Mami zanyi wanka.
Jeki se kin fito.
Kwanaki haka suka cigaba da ja sosae ana ta shirye shiryen gagarumin bikin Ya'yan
gata, ranar alhamis suka wuce kaduna gaba dayansu, sun tarar gidan ya cika da
mutane, Tunda sukaje Mami ta dakko su Aliyah suka shiga Kara kimtsa Amarya, ranar
jumaa Aimana, Khairi, Khulthum wadda ta shammace su Taxo don basu taba tunanin zata
zo ba, don da Sulaim ta fada mata cewa tayi itama shirin nata bikin take. Ranar
Friday akai Kamu na idon duniya wanda ya amshi sunanshi kamu, Amarya tayi kyau
kamar babu gobe, yan class dinsu Hidaya sani Lawan, Halima Ahmad Ya'u da Salma
Hassan Kwalam suka halarta, Yan SHATUUU's KINGDOM kamar kasa sunyi kyau kuma sun
kayata gurin haka mutanen Maman mama novels da Kainuwa Fans group duka sun bayyana
cikin ankonsu me kyau.
Dab da zaa gama komai Junaid yazo da tashi tawagar, akai pictures sannan aka kamasu
tare. Washegari ya tashi Saturday ranar Mami tayi yini, gidan ya cika sosae anci an
sha anyi biki.
Ranar Sunday da safe Mami da Baba, Junaid da Sulaim suna zaune Baba yayi musu
nasiha sosae akan aure da kuma hakkokin junansu, Mami tayi nata sannan aka rufe
taro da addu'a, da yamma suka isa Kano inda ta tare dakin Junaid akan zai karasa
ginin shi, ita Sulaim batayi kuka ba saboda bataga dalilin kuka ba tunda jinta take
tamkar taje yawo kaduna ne ta dawo kano.
Karfe Tara aka fara kayattaciyar dinner wadda ta samu dubban mutane suka halarta,
sunyi kyau Sulaim da Junaid kafin wani Lokaci hotunansu ya baza media.
Shatuu ♥️
[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
42
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
_Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu gorgeous damsels! Barka da sallah!
Allah ya maimaita mana many years to come. Ga barka da sallah na hope you guys will
like it?_
Hannunshi cikin nata suka iso kofar parlon, takan tuna lokacin da suke dawowa daga
school, kaduna a matsayin cousins to yau gashi ta dawo a matsayin mata, matar aure
kuma matarshi. Wani sanyi taji Yana ratsa mata jiki har ya kai hannu ya bude
parlon, shi dinne dai, yasha gyara an canza kujeru da carpets din. Saman kujera
suka zauna a gajiye saboda yadda suka gaji. Idanunta ta daga ta dubi agogon parlon,
karfe goma Harda rabi kallonshi tayi taga ya zuba mata dukkan idanunshi, sunkuyar
da kanta tayi taji wani nauyin shi ya kamata. Hannunta da har lokancin ke cikin
nashi ya matsa yace
Bacci?
Kanta ta gyada, Mikar da ita tsaye yayi, suka nufi parlonshi, wani niimantaccen
kamshi ne gauraye da sanyi suka dokesu, komai na