Showing 102001 words to 105000 words out of 121650 words
kallon Mami yayi wadda ta
hade rai itama don da gaske Junaid so yake ya bata kunya.
"Junaid me nasha fada maka akan rayuwa? "
Kanshi ya girgixa Cikeda kosawa ga kukan Subay'a na taba zuciyarshi tareda karya
mishi zuciya Amma dukda haka abinda yayi niyya bazai fasa ba
"Hakuri of course Mami!"
A hankali Subay'a ta dago idonta Wanda yayi jawur hatta fuskarta tayi ja, kallon
Mami tayi sannan ta dubi Junaid da ya kara hade rai, Mami tace
"A yau ba'a matsayin mahaifiyarka nake maka magana ba, ina maka magana a matsayin
wannan babbar kawar ta ka....."
Da sauri ya katse ta, ta hanyar dawowa gefenta Daga kasa tareda rike hannunta yace
"Mami don't please.... Mami please!"
Da sauri Subay'a ta Mike har tana tripping foot dinta, tsoron abinda kunnuwanta
zasu iya jiye mata suke takeyi, tasan abu na karshe saki ne su zama zawarawa itada
uwarta. Ajiyar zuciya Junaid ya sauke tare da fadin
"Mami ranar da zan tafi Malta, kin tambayeni me zan yiwa Subay'a idan ta dawo? Nace
sakinta zanyi ko? "
Kai Mami ta gyada don ta rasa bakin magana saboda yadda aka daure ta da jijiyoyin
jikinta.
"Kika roka mata hakuri da sassauci, nayi hakuri saboda darajarki amma Wallahi
tallahi, billahil azim se Subay'a taje gida ta koyi Menene aure! Se ta gane ni
Allah yace na shugabance ta! Nine leader ni nake aurenta ba ita ba! Inason ta nutsu
ta gane kuskurenta. Mami kada ki hanani, hakan is an opportunity Allah ya bani na
daidai ta gidana... I'm sorry"
Ya karashe maganar Yana daura kanshi akan cinyar Mamin, yau an tuna da kenan. Itama
Mamin tausayinshi ne ya cika mata zuciya ta shiga shafa kanshi tare da fadin
"Hakan yayi, kayi hakan is ok amma ina son duk Abinda zai faru ka kalli Ahmad da
Muhammad, taci darajar haihuwarsu, ko a alkiyama filin hisabi wani yana cin
albarkacin wani. OK? "
Kanshi ya gyada yana jin sanyi Yana ratsa shi, Mami ce ta Fara mikewa tayi dakinta
don kuwa hankalinta duka yana kan Sulaim wadda ta shige daki, tana shiga ta sameta
as expected ta hada kanta da gwiwarta tana ta kuka me cin rai, gefenta ta zauna ta
janyo ta jikinta tana patting bayanta alamun rarrashi haka tana jin babu dadi cikin
ranta, wannan shi ne Abinda ta gudar wa Sulaim din tun farko, Auren mijin wata, to
ya zasui kaddarar ta ce!
"Me kike ji auta?"
Cikin kuka da yarinta Tace
"Mami ina jin abu ya tokare min wuyana, zuciyata zafi take min, kirjina yayi min
nauyi, Mami bana son Yaya!"
Da sauri Mami ta toshe mata Baki tareda fadin
"Kar na kuma jin kin fadi haka, kishi yake damunki kuma it's normal kaji kishi akan
abinda kake so, kishi halal ne, Nana A'isha Harda Nana Khadija wadda bata taba
gani ba tayi kishi da ita, Tasha barar da abinci idan an kawowa manzon Allah SWA
Daga dakin Nana Safiyya kasancewar ta great cook. Kinga ba laifi kikai ba amma ina
son daga yau kada ki kara kuka Dan kinga Subay'a, inason Kiyi amfani da kishinki me
da ilimi ki kwaci mijinki, mace ce kamar ki, Baki fita ba bata fiki ba, me biyayya
da wanda ya iya zama da miji shi zai kwace miji, shi zaiyi winning Sulaim.
Inason ki maida hankalinki ki manta Yana da mata, ki Kafa kanki a gurinshi, kiarki
Bari wata ta kwace shi kinji? "
Kanta ta gyada har lokancin kukan bai tsaya ba amma ta rage, kuma radadin ya ragu
sosae
"Uwargidan mutum ita ta kafa shi, ita ce foundation dinshi, Duk yadda ta zubar da
darajar ta Tanan matsayin uwargida wadda ta sanshi. Ko zaku shekara talatin tare
bazaki taba sanin shi kamar yadda tayi ba, haka duk lalacewar uwargida idan miji ya
rabu da ita, duniya se ta zageshi, Bana son ki daga hankalinki akan hakan ina fada
miki don kisan matsayinki, zaman mijinki kike not for any other person. Ki kwantar
da hankalinki sanann ban yadda ko kallon banza Ya hadaki da Subay'a ba, ku gaisa
that's all nothing more kinji? "
Kanta ta sake gydawa tana jin damuwar da take ciki ta Fara yayewa, Mami uwa ce ta
gari cikin hikima ta dinga koyarda Sulaim yadda zata kwaci kanta, bata barta tayi
bacci ba Seda ta cire mata inferiority complex dinnan ta gina mata jin ta isa,
Junaid ba mijin Subay'a bane ita daya aa mijin sune dukkansu me kyan hali ita ce
tauraruwa a zuciyar shi.
Washegari tun safe suke aiki da Mami da Sulaim don Imratu cikin jikinta me saka
morning sickness ne hakan yasa ko fitowa Batayi ba. Gaba daya Sulaim zuciyarta da
gangar jikinta kewar Junaid suke Don rabonta dashi tun jiya, ko sallama bai zo yayi
musu ba da zai kwanta. Sun kusa kammalla aikin kamshin turaren shi ya iso cikin
kitchen din wanda yasa Sulaim saurin lumshe idonta saboda nutsuwa da ta mata dirar
mikiya, shigowa yayi ciki tareda tsugunnawa ya gaida Mamin wadda ta amsa kamar ko
Yaushe, fita tayi don basu guri tareda fadin
"Auta ki karasa"
Tana bada baya ya matso ya rungume ta tareda sakar mata wasu trails na kisses a
wayanta, Kara ta dan saki tareda janye jikinta tana murmushi ta riko hannunshi
tareda fadin
"Good morning "
Harar ta yayi yace
"Ba wannna maganar, jiya kika sha bacci ko missing dina Bakiyi ba, ni kuma ina can
Inata missing dinki"
Kashe gas din tayi sannan ta juyo Tana facing dinshi tayi dage kasancewar ya kereta
a tsayi, a hankali ta hade bakinsu guri guda tana mishi wani seductive and sensual
kiss, seda ta gama sannan ta rungumeshi tare da fadin
"Ka yadda I missed you? "
Da sauri ya gyada kanshi don ya yadda kam. Baki daya suka hadu don cin abinci amma
babu Subay'a, Imratu dake ta shan kunun gyada ta dubi Mami tace
"Tace na fada miki ta tafi kano"
Babu Wanda ya kuma maida maganar suka ci sannan Mami ta hada Junaid, Jabir , Imratu
da Sulaim ta Kara musu nasiha. Wajen laasar Mami ta rako Sulaim da yaran zasu tafi
Kano.
Maimakon gidan da suka saba zama se sukai parking kofar wani flat duplex akan BUK
road, kallonshi tayi kamar yadda take kallonta, kunnenta ya matso dashi yace
"Wancan gidan aro ne, wannan namu ne ni dake and our babies to come"
Shatuuu ♥️
[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
52
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
*Of course, you know that this page is yours the people of Maman mama novels, ina
godiya sosae da goyon bayanku.....*
A'ISHA ASHIR
Bari mu leka muji yadda rayuwar Wannan bayun Allah ta kasance bayan Auren Khulthum.
Rayuwa ta mika musu, abubuwa sun sauya ciki Harda Fara makarantar Aisha wadda ta
samu gurbin karatu cikin North west University wadda iyayen Ashir suka dauki nauyin
karatun. Amir shima yayi nisa cikin karatun da yake ga kuma budi da Allah yayi
mishi gurin kasuwancin da Khulthum ta dade tana mishi dariya, wato saida gwanjo.
Sede gashi Allah ya albarkaci abin har ya fara gyara musu dan gidan da suke ciki,
wannan abin ba karamin faranta ran Malam Suleiman yayi ba domin yasan tabbas Allah
ya amshi adduar da ya dade yana Yi.
Ranar wadda ta kasance asabar tun sassafe A'isha ta tashi kamar yadda ta Saba, babu
Wanda ta tada haka ta fito daga daki ta Debi ruwa tayi wanka sannan ta dawo daki ta
gyara kanta ta shirya cikin doguwar rigar farin material me fatsi fatsin Baki.
Dukda ba mai tsada bane amma yayi mata kyau, fitowa tayi ta hura wuta sannan ta
Fara Sharar tsakar gida, ta hada wanke wanke tayi a lokacin Amira ta fito Tana ta
murtsuka idanu, kallon A'isha tayi tace
"Kai Yaya A'isha duk ke daya kika yi wannan aikin?"
Harara A'isha ta makawa Amira tare da cigaba da aikinta sannan tace
"Waye zai biyewa lalacin ki, kamar ba mace ba ace se yanzun kike tashi a bacci"
Baki Amira ta turo tace
"Rayuwarki tayi tsauri Yaya A'isha, amma ina yiwa Yaya Ashir samun ki"
Sunan kawai da Amira ta ambata Seda wani sihirtaccen murmushi me kayatarwa ya kubce
daga kyakyawar fuskar A'isha, Dama ita din ma'abociyar murmushi ce amma na Ashir na
daban ne. Ita kanta ko cikin mafarki ko burika Irin nata bata taba tunanin zatayi
soyayya da Ashir ba, Ashir daban yake wanda samun mutum kamarshi se an sha wuya,
kullum rana se A'isha ta kara godewa Khulthum akan bar mata Ashir da tayi.
Halayenshi kadai sun isa ya sace zuciyar mutum dashi. Mutum ne me takatsantsan akan
dokokin Allah, hardly Kaga ya ketare abinda Allah da manzonshi sukai Hani akan,
mutum ne that's very caring dukda ya kasance baya kasar amma bai taba jera hour
biyar ba tareda ya ji muryar A'isha din ba, hakan yasa suka mugun sabo da kuma
shakuwa da junansu.
Da farko kasa sakin jikinta tayi saboda tana ganin kamar ana amfani da ita ne wajen
huce haushi Amma a hankali yadda yake tsumata da Wannan zumar tashi yasa ta bada
Kai bori ya hau. Cikin nitsuwa suka dinga shimfida soyayya me Cikeda amana, karko
da kuma fahimtar halayen juna, cikin kankanin lokaci sukai clearing differences
dinsu hakan yasa basu sha wahala ba.
Amira dake gefe tana kallon Yayar tata da tayi zurfi cikin tunanin Ashir wanda ko
bata fada ba hakance don wani Irin soyayya me rikitarwa ce tsakaninsu. Daki ta koma
jiyo ringing din wayar A'ishan, murmushi tayi ganin Ashir dinne hakan yasa tayi
saurin kai wa A'ishan wayar tareda fadin
"Gashi nan dan halak ya huttar dake"
Maficin dake hannunta ta wullawa Amirar wanda ta zulle Zuwa daki Tana dariyar
kunyar A'isha. Se kira na biyu ta samu ta dauki wayar dan tuni wancan call din ya
katse
"Yau Queen da rowar murya kika tashi? "
Dan murmushi tayi tace
"Ni na isa, tana daki wayar"
Kanshi ya jinjina tareda fadin
"Dan Allah Queen ki dinga hutawa da Wannan ayyukan da kike, ace kullum mutum tamkar
inji yayi ta aiki babu Hutu Haba mana! Shiyasa dole a matso da date din aurenmu!"
Dariya ta saki a hankali wadda take nuna Irin nishadin da take ciki, shima lumshe
idonsa yayi yace
"You will not answer me right? Anyways Dama zan miki zancen next week zan dawo"
Da sauri ta Mike wani Irin farin ciki Marar misaltuwa ya mamaye mata jikinta da
zuciyarta tace
"I'm so happy blood, Awnnnn!"
Haka suka Bata Lokaci me tsayi suna waya har ta kammalla ayyukanta, lokacin sukai
sallama shima don ganin mutanen gidan sun Fara fitowa ne. Tunda Mama ta fito take
shiwa Aisha albarka, har zuciyarta take jin dadin wannan halin na A'isha ko ta so
ko taki A'isha tafi Khulthum sau dubu kuma Tun ranar da Khulthum ta bar gidan taji
wata nutsuwa ta saukar mata, taji tamkar an sauke mata wani babban nauyi ne daga
kanta, haka bata ji wani kewar ta ba, to ta yaya zataji Bayan nemar mata magana
kawai take yi, yanzun hankalin kowa ya kwanta tunda bata nan.
Bayan sun kammalla cin abincin Baba ya dubi A'isha yace
"Ya kamata kuje ku ga dakin 'Yar uwarku, ko mai ya faru ina son ku manta da hakan,
Ummu_Khulthum yar uwarku ce"
Kai A'isha ta gyada tana jin komai ya wuce dama ita bata rike Khulthum ba don kuwa
tasan ba'a canjawa tuwo suna Yana nan a tuwonshi! Tare suka shirya Mama kamar ta
Goya su da taji inda suke haramar Zuwa, dukda Tunda Khulthum ta saka kafarta ta bar
gidan babu Wanda ta taba Kira da sunan gaisuwa, se Mama dince kan kirata time to
time.
Tunda aka sauke su A'isha kofar gidan Baki daya suka saki Baki da hanci suna kallon
wannan tafkeken gidan, mamaki cike a zuciyar kowannensu saboda babu Wanda yazo
ganin daki don ba'ayi rabuwar arziki ba Balle har su raka ta in fact lokacin
bikinta ma gaba suke me tsanani. Seda A'isha ta kira Mama ta tabbatar mata gidan ne
sannan suka kwankwasawa, kasancewa securities din sun saba da kawayen Khulthum masu
didif didif a gidan suka Barsu suka shiga tareda nuna musu part din Khulthum din.
Daidai zasu shiga Musbahu na fitowa daga part din Sanye da jallabiya brown,
Fuskarshi babu digon annuri an dinke tamkar anyi masa sakon mutuwa, a tare suka
gaishe shi kawai se ya samu kanshi da amsawa saboda kana kallon Amira Kaga Khulthum
saboda yadda suke kama da junansu sosae,
"Ku shiga ciki mana tana nan "
Ya fada Yana basu guri tareda Kare musu kallo, kana kallonsu kasan talauci yana
damunsu Amma a idanunsu zaka fahimci they're contented. Gaba daya bin parlon sukai
da kallo saboda tunda suke a rayuwarsu basu taba gani Balle har su shiga makamancin
gurin. Zama sukai kan kujera shi kuma ya nufi dakin don kiranta, tana kwance inda
ya barta ko hannu ta Kasa dagawa, kamshin turaren shi da taji yasa ta mugun firgita
don babu Abinda take tsoro yanzun a rayuwarta shi ne Musbahu, azabar da yake mata
Allah kadai yasan hakan amma tasan kaddarar ta ce hakan!
"Kinyi baki"
Bai jira amsarta ba ya fito Bayan yasa a kawo musu abinci, baki daya A'isha tsoron
karbar da Khulthum zatayi musiu take, da Khulthum bata da komai take rashin mutunci
Balle gata da kyakyawan miji na nunawa duniya, ga kudi da katon gida. Ai se abinda
yayi gaba, suna nan Zaune zaman kurame Don babu me magana cikinsu se gata ta fito,
ta kintsa kanta cikin voile Red dinkin skirt da Riga, tayi kyau amma tayi Baki,
idanunta sunyi ja tareda fadawa ciki, fuskarta kadai zaka kalla ka gano tsantsar
damuwa da tashin hankalin da take ciki, tana ganinsu A'isha ta nufe su da sauri
tareda rungume su dukkansu, sunyi mamaki canzawar ta da kuma Wannan ramar da tayi.
Tsakiyar su ta shiga tana jin kamar an jefata a Aljannah, dadi kamar me daga baya
ta kwashesu Zuwa dakinta tana ta musu hira har suka saki jikinsu suka ci abinci.
A'isha karshen gado ta koma ta kwanta tare da amsa kiran wayar Ashir, tunda ta Fara
wayar hankalinta Baki daya ya bar dakin da mutanen dakin, Khulthum na ankare da ita
Tana ta son jin da wanda A'isha ke waya hakan yasa ta tambayi Amira wadda ta bata
amsa da
"Yaya Ashir ne"
It takes a huge of sacrifice typing this peace..... Dan Allah kui manage dashi.
Shatuuu ♥️
[9/6, 6:55 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
53
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
*Thank you for patiently waiting, thank you for the prayers! Amarya na dakinta*
Amira bata jira gama ganin reaction din Khulthum ba ta cigaba da fadin
"AI an saka ranar biki, wata uku ya rage yana zuwa Hutu xa'ayi bikin su tafi tare.
Wanda ya dauki nauyin karatun nashi ya hada da nata"
Wani yake Khulthum tayi tace
"Ikon Allah, to Allah ya kaimu "
Tana fadar haka ta mike ta fita daga dakin, Rana ta farko a cikin rayuwarta da ta
Fara jin tayi kuskure, Rana ta farko da ta Fara jin wani abu yana bin zuciyarta na
Anya ta yiwa rayuwarta daidai? Taji anya akan turba me kyau take? Jingina tayi da
kofar dakin dake gefe idanunta na cikowa da wata zazzafar kwalla, a hankali wasu
abubuwan na rayuwarta suka Fara bayyana a idonta, tamkar wani flashback a film haka
suka dinga bayyana mata, tabbas kwadayi mabudin wahala ne, tabbas wanda ya hau
motar kwadayi zai sauka a Tashar wulakanci, gashi nan bataje ko ina ba ta fara
gani, kwatakwata Watannin ta biyu kawai cikin gidan amma gashi Anyi mata mummunan
tabo cikin zuciyarta da rayuwarta baki daya. A halin yanxu babu Abinda take
matsanancin tsoron ji Irin muryar Musbahu Balle ta ganshi, idan kuwa hakan ta
kasance ba karamar gigicewa take ba saboda irin axabtuwa da take, ta yi kukan tayi
Allah ya isa wa Maimuna ta Kuma tsine mata yafi cikin carbi Don Tana ganin ita ta
Fara kaita ta baro ta, Sede Khulthum ita ta Fara cutar kanta, ita ta Fara kashe
kanta da hannuwanta kamar yadda tayi destroying kanta ba tareda taimakon kowa ba.
Kuka sosae Khulthum ta tsaya a gurin Tana yin, kuka Marar sauti Marar dadi dake
fitowa Tun Daga karkashin zuciyarta, kuka ne takeyi na rashin makama, na bakin
cikin halin da ta jefa kanta ciki, kuka take sosae tamkar ana cire mata wani sassa
Daga jikinta. Ta dabbaka a kukan da take taji hannu an dafa kafadarta ko bata juyo
ba tasan waye Musbahu ne, take jikinta ya dauki rawa da kyarma tamkar kura ta hadu
da zaki, kukan da take dif ya dauke se hawaye dake sakko mata a fuska, juyo da ita
yayi tana fuskantar shi Sede maimakon ganin Fuskarshi a murtuke kamar kullum se
taga sassauci a Fuskar tamkar "pity" a kwance wanda suna hada ido yayi saurin tamke
fuskar tashi a ranshi Yana kokarin yakice tausayinta da ya Fara rinjayar shi daga
zuciyarshi,
"Bakin sun tafi ne? "
Da sauri ta girgiza kanta batareda ta iya furta kalma ko daya ba saboda yadda ta
kidime, Fuskarshi ya kara daurewa yace
"Ku shirya muje gaba daya"
Yana fadar haka ya fice, wani farin ciki taji ya sauka a ranta at least zata fita
daga gidan. Dakin dayake kusa da ita ta fada ta wanko fuskarta amma dukda haka
alamun kuka na nan hakan yasa ta dauki kwalli ta zizara akan idanunta tareda shafa
powder sannan ta dauki ciro lace me kyau da akai dinkin gown me tsari, Seda ta
shirya ta karewa kanta kallo jikin mirror, tasan in har mace ake nema to tabbas ta
kai mace, babu inda zaka kushe ta wala halitta ko kyaun fuska amma tayi fatali da
wannan baiwar ta Allah da ya bata kawai ta dorawa kanta matsanancin kwadayi da yayi
clouding mata vision dinta har ta kasa ganin wutar data tunkaro ta, Lokaci daya ta
tuno ranar da ta iske Musbahu a office farkon haduwarsu abinda ya fada mata wanda
kusan gugar zana ce amma dayake burinta a rayuwa kudi ne kawai yasa bata fahimta
ba, here she's today ko hakkin Ashir tasan bazai barta ba, mutumin da ya so ta yayi
hakuri da halayenta amma tayi fatali da hakan ta ki aurenshi.
A hankali ta tura kofar dakin dasu A'isha suke ciki, dukkansu sun shirya tamkar
Dama jiranta suke Tana shigowa suka Mike, kallonsu tayi tace
"A'a ku tsaya tare zamu fita"
Kai A'isha ta gyada tana mamakin yadda bakin Khulthum Ya mutu, ga wata rama Marar
tsari da Khulthum din tayi, gaba daya ta koma wata iri kamar ba ita ba, matching
veil ta dakko ta yafa sannan ta dakko wata Leda ta shiga zuba kayan kwaliyya da
atamfofi tana gamawa akai knocking softly jikin kofar, wata Irin muguwar faduwar
gaba ta ziyarce ta har Seda ledar hannun