Showing 90001 words to 93000 words out of 121650 words

Chapter 31 - MACE A YAU by Shatuuu

Shatuuu   

12 May 2026

134

Saar uwar 'ya'ya ba, kwatakwata yarinyar tafi kama da yaran da basuda
uba Amma bansan abinda mahaifinta yake ba har uwarsu Ke wannan hidimar.

Tsakin takaici Mami ta saki tace

Ka manta Ance shima haka yake fama, kawai kaddarar Junaid ce hakan, Shiyasa bazan
saka baki ba akan hukuncin da zai yanke mata ba, kawai bazan Bari ya saketa ba amma
lokaci yayi da zai daidaita gidanshi.

Hakane Nafisa, Amma ya kike ganin zaman Ummu_Sulaim da Junaid zai kasance?

Dariya Mami tayi don ta fahimci me Baba yake nufi, Kada yarshi tayi bora.

Wannan is sort already, yanxun yace Malta zasuje early next month, kafin su dawo
ginin da yake ya kammalla, Kaga kowacce da gidanta.

Sallamar Ja'afar yasa Baba bai bada amsa ba, sema wani muhimmin zance da ya fado
mishi ganin Ja'afar din, shima ya kara kyau dukda yayi rama a fuska amma kana
kallonshi zaka San Hutu yana aiki a gurin. Zama yayi kan carpet ya gaishesu, suka
amsa sannan Baba yace

Ja'afar Babanka Ibrahim dazun ya kirani akan maganar ku kaida Haulat!

Haulat? Haulat kuma

Ja'afar ya fada a birkice, Wacce Irin magana kuma

Eh Haulat dai, babanta yace ta fito da miji zai mata aure tace Kai kuke tare.

Da sauri yace

Wallahi karya take Baba, Mami......

Karka sake ka kira Sunana, Haulat kake denying, sau nawa ina ganin pictures din ta
cikin wayarka, Mamanta Tace min har Abuja Kake Zuwa zance.

Baba yana kallon Ja'afar yadda yayi kicin kicin da fuska Cikeda tashin hankalin jin
inda yake neman afkawa. Haulat ita daya Allah ya bawa Alhaji Ibrahim Kasim kanin
Mami da Anty Batuul wanda suke Zaune a Abuja, Haulat babu laifi tana da kyau kuma
tanada tarbiyya Sede yarinya ce shakwaf da batafi 16 years ba amma tanada girman
jiki, kuma tana daya daga cikin yan matan Junaid sede Itace me least wadda yake
ganin zai iya aura se gashi an rikeshi rum a hannu!

Kai Ja'afar yimin bayani, ya zancen Maminku yake?

Da gaske ne Baba, amma ni ba sonta nake ba.....

Yaudarar ta kake, kasan duk Abinda kake ina sane dashi, kasan haka kayiwa sulaim
ko?

Sulaim kuma Mami? Ni nace miki

Bakace ba, I read it a diary dinta, Hanan fa?

Kanshi ya dafe wanda yake Sara mishi kamar zai fadi, waye ya mishi wannan ta'asa,
Baba kasa magana yayi saboda mamaki, ranshi a bace yace

Wallahi ko baka sonta Ja'afar Seka aureta, kuma wannan shi ne magana ta karshe. Ki
zama cikin shiri next week zamu tura a bamu Haulat a Karo na biyu Bayan Sulaim!


Subay'a na hanya, who will volunteer to sweep her room for her, ya haduwar zatayi
da Junaid da Sulaim matafiyan Malta? Ina labarin mutanen Texas da A'isha? Ga
Ja'afar ya ballo aiki, Ina TitαΦ da Amaryarshi.

Tell me your opinion about this page and what might happen next.

[8/26, 5:03 PM] Shatuuu❤:
Shatuuu ♥️ *MACE A YAU*
45

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad


*Ina masoya Anty Sumayya Abdulkadir Takori? Ga dama ta samu cikin sauki da kudi
kalilan zaki karanta littafinta na _A BARI YA HUCE...._*


Jirgin daya taso Daga Murtala Muhammad INT'L Airport dake Lagos ya sauka a Aminu
Kano INT'L Airport dake birnin Kano. A hankali passengers ke fitowa kowanne da
yanayin da Fuskarshi ke ciki, wasu gajiya, wasu yunwa, wasu excitement, wasu tsoro
ne karara kwance akan fuskar tasu kamar Hajiya Subay'a wadda tamkar kace mata kett
ta zura a guje saboda tsabar yadda take a firgice batasan abinda zata tarar ba a
wajen Junaid don ita a halinda take ciki bata Sulaim take ba so take ta fara kashe
kurar kafin ta koma kan Sulaim din.

Bata expecting kowa ya zo daukarta ba Tunda babu Wanda yasan tazo din haka ta tari
napep wanda if she can remember vividly bata tunanin ta taba hawa commercial ride
Tunda take a rayuwarta. Kwatance tayi mishi yana ta basarwa tareda ciccin magani ya
amsa zaije, seda ya kalleta tsaf yaga yadda kudi ya samu gurin zama yace 600 zai
karba, bata ja ba haka ta hau suka nufi gida, gabanta Yana ta faduwa lokaci lokaci
tana share hawayen da yake bin kuncinta. A kofar gate din ya ajeta tareda nade
hannunshi Yana jiran ta fito amma ina tayi nisa sosae cikin duniyar tunanin da take
akan abinda zata tarar idan ta shiga, ko wanne irin tarba zata samu, tasan bazai
taba sakinta ba amma zai iya hukuntata da mafi munun hukunci shi ne Silent
treatment halin Junaid ne ya kyaleka akan laifinka Sede ya barka da guilty tension
haka yake.

Juyowa me napep din yayi ganin yana ta mata magana Bata bashi amsa ba, ya juyo yace

Hajiya ki sauka ki bani kudina ina ta miki magana kinyi min banza.

Dagowa Subay'a tayi ta share hawayenta tace

Yi hakuri Malam.

Tsaki yayi ya ciro cigar daga pocket dinshi yayi lightning tareda Fara zuka,
Jakarta ta bude ta ciro purse Amma babu Nigerian currency se na can inda ta baro,
jikinta har rawa yake tace

Bari na shiga na dakko maka kudin dan Allah anan babu.

Wata ashar ya saki tareda bule ta da hayakin bakinshi wanda yasa ta fara tari babu
kakautawa don idan akwai Abinda Subay'a ta tsana shi ne warin cigar

Amma Kinci uwar rainin hankali, da Kinsan bakida kudi xakixo ki shigar min napep na
kawo ki!

Subay'a ta kullu take Hali ya motsa ganin yadda kankanin yaro yake mata rashin
kunya, Amma a hankali ta dinga petting kanta tana fadawa kanta yanxun is not the
right time tayi haka, kawai ta lallabashi ta samu ta bashi kudin taje taga yadda
gidan yake ciki.

Kayi hakuri mana shiga kawai zanyi na kawo maka.

Tsaki yayi hakan ya kara bata mata rai amma ya zatayi, yau tana jin tamkar ba
Subay'a bace, kamar ba ita ba wadda fuskar wargi mutum bai samu Balle Ya kawo mata
hauka amma imagine Yau Itace wannan kanin bayan nata yake mawa haka. Trolley dinta
taja ta Fara knocking wabda shima ta kusan shafe Mintina goma kafin me gadin yazo,
ranta a matukar bace tace

Bakasan aikin ka ba kenan wawa kawai!

Shi baima bi ta kanta ba yayi ciki abinshi hakan ba karamin mamaki ya bata ba, to
Meke faruwa? Her remaining dignity is lost also? Ta tuna yadda jiki na rawa
ma'aikatan gidan ke mata biyayya amma yau Itace ko matsayin gaisuwa Bata samu ba.
Kanta ta girgixa Tana jin wani daci cikin ranta wanda har bakinta take iya jin
dacin. Ciki ta shiga gabanta Yana dukan uku uku, lokacinda ta tura kofar parlour ta
shiga Seda ta runtse idonta saboda wani yanayi da ya ratsa ta, gidan da ta bari ba
tareda izinin Junaid ba, Ta tsallake yaranta wanda take jin duk duniya ba abin da
takeso tamkarsu Amma a haka ta tsallakesu ta tafi biyawa zuciyarta bukatarta. Da
sallama dauke a bakinta ta karasa cikin tsakiyar parlour, ko ina tsit se kamshi
wanda ya zama bakonta da take iya shaka, komai ya canja an canza komai in just 3
months kawai, se taji ta tamkar bakuwa, tamkar is the first time of her being a
gidan.

Jin shiru yasa ta nufi kofar dakinta don shiga Sede Tana rike kofar taji Atika na
fadin

Wacece?

Idanunta ta dan runtse tare da aro jarumta ta juyo Tana facing Atika wadda ta fito
Daga dakin Sulaim, Tana kallon Atika Bata wani canja yanayin fuskarta ba da ta
ganta, hakan ya ruguza mata lissafi tareda sakar mata da gwiwa. Amma haka ta dake
tace da Atika wadda take Mata wani kallo wanda Subay'a ta kasa fassara manufar
kallon Amma yafi kama da you lose!

Ina mutanen gidan?

Daidaita kanta tayi ta tsugunna kamar yadda ta Saba Don kuwa Subay'a na nan
matsayinta Koda sakinta Junaid yayi Balle da aurenshi har yanzun a kanta.

Tun shekaranjiya suka tafi kaduna.

An fadi Yaushe Zasu dawo?

Kanta ta girgixa tace

A'a Ammiey bata fada ba.

Cikin rashin fahimta Tace

Wacece Ammiey?

Anty Sulaim!

Ta Bata amsa take taji Wani abu ya tokare mata makoshi Jin Sulaim ce Ammiey!
Juyowar da kanta tayi tana murda kofar amma a rufe hakan ya tabbatar mata Junaid ya
tafi da key din, purse dinta ta bude don neman spare key Amma fit babu shi don kuwa
ta barshi anan tana sauri bata dauka ba. Kallon Atika tayi da take rurrufe kujerun
parlour da ledarsu hakan yasa tasan mutanen gidan ba yanzun Zasu dawo ba kuma alamu
sun nuna sun bawa ma'aikatan Hutu. Batare Tace komai ba ta dauki Jakarta da trolley
ta koma don tasan anan gidan a yanxun she's not welcomed. Tana fita ta tarar me
napep din ya gama shaka tana tsayawa yace

Amma Hajiya wannan rashin mutunci ne ko ki bar mutum a tsaye Yana jira.

Hakuri ta shiga bashi sannan ta lallaba shi ya kaita gidan hajiya, nanma Bata samu
hajiyar ba amma ta aika mishi kudindhi kafin tyi wanka ta kwanta ta Fara kuka
saboda bata taba wulakanta Irin na Wannan ranar ba, dole ranar ta shiga history
dinta!

Meye kuke ganin makomar Subay'a a gidan Junaid?

Wayarta dake gefe tana faman ringing ta kai hannu Wanda yasha lallai Baki me azabar
kyau, tafukan hannayenta Baki daya jan lallai ne tamkar a India. Ita kanta Khulthum
kara kallon kanta take not believing Itace wannan, buri Yana daf da cika, Tana daf
da zama mata, Amarya kuma uwargida uwar yaran Musbahu me TitαΦ! Tun ranar da aka
kawo lefe bata kara fita ba idan ba ya zama dole ba, shiri kawai take don bata
bukatar ace batai fitting ba a matarshi ba kamar yadda mutane suke fada, wasu na
ganin kawai don wata manufa zai aureta yayinda wasu Ke ganin asirce shi tayi. Koma
dai me nene Khulthum dai Kwana biu kacal ya rage ta shiga daga ciki.

Gidansu ya cika har makota don komai da zaaci Musbahu ya kawo kuma Tun ranar da ta
iske shi office dinshi basu Kara haduwa ko jin muryar juna ba, wabda hakan ko a
jikinta Don ko taso damuwa idan ya hankado mata uban kudin se taji ta manta dashi.
Hakan yasa babu Abinda sukai na kananan mutane komai ya tafi yadda Khulthum Take so
yadda kuma ta tsara. Su A'isha sun zama yan kallo don seda ta samu Mama take Mata
korafi akan kudin Musbahu amma Mama tace bata son gulma aikuwa ta rufe bakinta ta
cigaba da harkarta itada Ashir wanda ta riga ta damke shi a hannunta. Yana Texas
inda ya fara karatu cikin nasara don yayi mata alkawarin komai na lafawa zai dawo
ya aureta su samu yadda zasui.
Hello Sulaim

Sulaim dake zaune gefen Mami tana cin abinci tace

Khulthum longest time.

Idanunta ta dan lumshe tareda fadin

Ina nan. Dama zan fada miki gobe Za'a Fara bikin.

Wanne biki?

Sulaim ta tambaya don ita rabonta da Khulthum ma tun data kirata tayi mata godiya
da bangajiya basu Kara communicating ba dukda Sulaim ta kikirata akan school, test
da exams bata picking, tayi mata text se tayi replying da ta bar school tuntuni
hakan yasa Sulaim Bata Kara komawa ta kanta ba, don Tana ganin tafi karfin
wulakanci a gurin Khulthum din.

Bikina mana

Ta fada sounding serious. Idanu Sulaim ta zaro tace

Aurenki Khulthum amma se ana gobe kike fadamin? Anya Khulthum are we still friends.

Dariya Khulthum tayi tace

Ki manta kawai abubuwa suka hade min Kede se kinzo.

Kai Sulaim ta girgixa tamkar Khulthum na ganinta tace

Bazan samu damar Zua ba saboda anjima jirginmu zai tashi zuwa Malta Allah ya sanya
alkhairi.

Daga haka bata jira amsarta ba ta kashe tareda kallon Mami wadda da dukkan alamu
bayani take jira. Briefly tayi mata bayani tare da fadin

Ko ina gari Mami ba Zuwa zanyi ba Balle kuma bana ma garin

Mami batace komai ba se dariya da tayi sannan kuma tace

Kin gama hada komai na tafiyar? 7pm sharp jirginku zai tashi.

Turo Baki tayi tace

Ni Mami bana son tafiya na barki.

Ja'ira rufe min baki.

Dariya Sulaim tayi tana fadin

Kai Mami yanzun kin daina so na.

Ta fada Tana sake turo bakinta Cikeda shagwaba. Hararta Mami tayi ta maida fuskar
ta serious I tace

Sulaim! Inason ki maida hankalinki ki rike mijinki, kiyi mishi biyayya sau da kafa
kinji? Karki manta bake daya bace kuma komai Daren dadewa Subay'a zata dawo gida.
Nasan Junaid Yana sonki nasan bazai wulakanta ki ba inason ki rike darajarki saboda
duk yadda mace take ita Gem ce a priceless one ma kuwa. Yanzun Auren Duk ya koma
wani iri amma dukda haka ba duka aka taru aka zama daya ba, inason kisan cewar idan
maza suna da laifi a aure to mata ma akwai tasu problem din. Inason ki dage Kiyi
ibada Koda hakan ne kawai zai sadaki da Aljannah......

Mami ta jima tana mata nasiha da bata dabarun zama wanda jikinta yayi sanyi tamkar
an watsa mata ruwa. Suna gamawa ta wuce daki don biyar na yamma tayi tasan duk inda
Junaid yake to yana hanya. Wanka ta Fara yi sannan ta shirya cikin Abaya fuschia
pink da bakin heart pattern a jiki. A hankali ya bude kofar ya shigo jikinshi Sanye
da trouser na kamfanin marks and Spencer se milk din top ta Zara se silver wrist
watch a hannunshi na hagu me kyau na kamfanin Frank Miller. Yayi kyau sosae amma
Sulaim bataji Shigowarshi ba saboda nisa da tayi wajen daura bakin wedge sandals a
kafarta kuma ta kasa, se kawai taji hannunshi ya zura mata igiyar. Dagowa tayi ta
dubi inda yake tsugunne ya maida dukkan hankalinshi kan Abinda yake, murmushi me
kyau ta saki daidai lokacin da ya dago idonsa ya zube cikin nata wanda Lokaci daya
ya shagaltar dasu Seda wayarshi dake cikin Aljihu ta Fara vibration kafin ya mika
mata hannu ta Kama suka fito babu Wanda yayi magana.

Baba ke driving da kanshi se Junaid a gefenshi, Bayan seat kuma Mami ce da Sulaim
wadda ta kwantar da kanta akan kafadar Mamin tana jin wata kewar Mamin na ziyartar
ta kamar kada ta tafi amma Junaid is everything for her, he's her entire world that
revolves around the globe, he mean everything, idan tace everything she mean komai
da komai na duniyar nan a bayan Junaid yake a gurinta. Seda sukai sallama dasu Mami
Sulaim Harda kukanta, Junaid Yana ta dariya sannan suka wuce aka gama screening
komai ya kammalla kafin sukai boarding jirgin wanda ya tashi zuwa birnin Valletta
dake kasar Republic of Malta!




Shatuuu ♥️
[8/26, 5:03 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
46

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad

Halooooooooooo.... Pipul of wattpad here's a page for all the votes, comments and
recommendations. thank you very much Jazakumullahu khairan!

Tun daga parlor yarinyar da keyiwa hajiya hidima a gidan ta sanar mata Subay'a ta
dawo tun dazun, da hanzarin ta ta nufi dakin dan Zuwa ganin lafiya saboda tun
shekaranjiya su Suhaila suka kirata suka sanar da ita sun dawo basu same ta ba,
baki daya hankalinsu a tashe yake haka itama hajiyar hankalinta a matukar dunguzume
yake. Koda aka tambayi Sulma itama cewa tayi bata fada mata ba don ta manta sunyi
maganar haka wannan kwanaki biyun ya kasance cikin matsaltsalu kashi kashi.

A dakinta ta samu Subay'a kwance kan gado ta kudundune cikin bargon dake ninke
gefen gadon , da sauri hajiya ta iso ciki har tana tuntube, bargon ta yaye wani
dumi ya bugeta ta Hangi Subay'a kwance tana ta karkarwar sanyi, ajiyar zuciya ta
sauke kafin ta zauna gefen Subay'a tareda yaye ilahirin bargon wanda yasa Subay'a
bude idanunta wanda sukai ja ba idonta harta fuskarta tayi jawur tamkar tumatir
saboda azabar kukan da tayi, Tana jin Duk duniyar ta ishe ta, ji take ta tsani
komai don se yanzun wani azababben kishi ya dirar mata anyi mata kishiya? Mijin ya
tafi da kishiyar tata? Hawaye masu dumi suka sake gangaro mata wanda ya tilasta
mata lumshe idonta saboda barazanar tsagewa da kanta keyi, ita kanta tasan tunda
tazo duniya bata taba kukan da tayi Yau ba, Kai ita totally ma bata taba tunanin
zata tsinci kanta cikin wannan rayuwar ba, Bata taba kawowa a hankali ta cewar
Junaid zai iya kallon wata mace da admiration Balle har zuciyarshi ta kwadaita
aurenta, ta tuna dimbin son da ya nuna mata lokacin yana neman aurenta, ta tuna
yadda ya dinga fadi tashin samo mata farin ciki amma ita ko sau daya she never
reciprocate, Abinda take son gani shi ne Tana juyashi kamar muciyar tuwo to every
direction she desires, Wanda hakan ya fara jefa rayuwarsu cikin matsaltsalu don sam
Junaid yaki daukar wanann abin. She remembers maganganu na lallashi, fada, nasiha,
threats da yayi mata Daren da taje mishi akan zata wuce Cyprus, har ce mata yayi
he'll refund hajiya abu daya yake so ta zauna dukda babu tsiyar da take mishi Shida
'ya'yanshi don aikinta da family dinta is her number one priority amma haka ta
tsallake komai ta wuce! Idan ba rashin adalci Irin nata ba, taya take expecting
Junaid ya zauna tsawon watanni shida shi daya ba tareda mace cikin rayuwar shi ba?
Duk kuwa da cewar mutum ne shi me kokarin masking ainahin Abinda zuciyar shi take
ciki amma ina bata yi musu adalci ba so dole rayuwarta ba zata taba tafiya daidai
ba!

"Oh ni! Uwar Mata Subay'a me zan gani haka? Meye ne yake damunki?"

Idanun Subay'a ta kara lumshewa a ranta tana fadin duk ke kika sani a halinda nake
ciki don dai ke uwa ce!

"Subay'a tashi ki fada min Abinda Ke damunki"

Bude idonta tayi a hankali ta kalli Hajiya wadda hankalinta yake a tashe saboda
yadda fuskarta ke a dugunzume, a hankali ta bude bakinta tace

"Hajiya ki bar ni kaina ciwo yake min kamar zai fashe"

"Assha, kwanta ki huta"

Kafin Subay'a ta kuma furta wani abu ladidi ta shigo bakinta dauke da sallama ta
tsugunna tare da sanarwa Hajiya Alhaji Yana jiranta a parlor, mikewa tayi jikinta a
sanyaye ta fito inda Alhaji ke tsaye Yana waya, tana fitowa ya maida wayar aljihun
gaban shaddar jikin shi, ya jiyo yana fuskantar ta ran shi a bace fuskar shi a
murtuke, abune da Hajiya a iya zamansu sama da shekaru talatin baza ta iya tuna
ranar da taga Fuskarshi a haka ba, ga wani wulakantaccen kallo da yake binta dashi
Irin Shekeke dinnan. Se kwarjini da taga ya kara, baki daya taji ya cika gurin har
taji tsoronshi ya darsu cikin ranta.

Kut ta hadiye wani abu daya tokare mata tare da kirkiro murmushi zatayi magana amma
yayi beating dinta yace

Bani keys din part dincan na gefe yanzu.

Idanunta ta sauke Kan shi, kawai se ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login