Showing 21001 words to 24000 words out of 121650 words

Chapter 8 - MACE A YAU by Shatuuu

Shatuuu   

12 May 2026

139

joint na cold stone yayi musu
ordering suka zauna cikin motar suna sha yake mata bayanin kanshi tunda taji yace
babanshi senator ne kuma d only heir of them tasan tayi babban kamu. Gaba daya
Khulthum ta manta cewar wai ta fito Kai dinki ne seda Hu yace

Baby da me kika fito yi ne.

Bakinta ta rufe tace

Kasan saboda yadda ka shagalta Danni I totally forgot dinki zan kai.

Dariyar shima yayi yace

Lucky Hu!

Bai tambayeta inda take Kai dinki ba se kawai taga sun tafi wani tailoring centre a
nan wajen new hospital road, yawancin duk budurwar da yayi nan yake kaita a mata
dinki, irin designers dinnan Don haka Khulthum tayi shiru Tana tunanin yadda zata
iya kai dinki gurin, Amma ta waske suka shiga gurin, yadda suke da mutanen gurin ya
tabbatar mata akwai sabo sosae tsakaninsu within 30 minutes an gama komai Harda
billing kuma take ya biya through POS hakan ya kara mishi daraja da martaba
idanunta. Suna fitowa ana kirayen sallah maghrib hakan yasa yace

Bari muje na kaiki gida, yau munsha yawo.

Murmushi tayi tace
Gaskiya kam.

Suna tafe Yana mata tambayoyi saboda yadda taga yanada kudi kuma tasan ba wani abu
bane yasa ta fada mishi Daga inda take, baiyi mamaki ba saboda ya Lura dukkan
guraren da sukaje are new to her, ko da wannan ma zai shawo kanta Tunda akwai son
abin duniya tun a yau yayi marking.

Seda yayi mata takeaway me kyau kafin ya nufi inda ya Dakkota lokacin sallar
maghrib ta wuce ana shirin sallar ishai.

Nuna min Kwanar da zamu shiga.

Kanta ta girgixa ba dadi ranta tace

Mota bata shiga

Se taga bai wani damu ba hasalima wayar ta ya karba Bayan ya gama jujjuya ta sannan
ya saka numbers dinshi yayi saving mata kafin ya kirayi kanshi shima yayi saving a
tashi. Daga haka sukai sallama ta fito Tana jin tamkar kada ta fito, kamar yadda
kullum take tafiya haka ta cigaba da tafiyarta sede tana zuwa tsakiyar layinsu taji
an sha gabanta, idanunta ta dago don ganin wanda yake muradin zagi, se kawai taga
Ashir tsaye, yana tayi mata wani Irin kallo me Cikeda tuhuma da zargi. Itama
kallonshi take tana karantar mood ensa, Baki daya ranshi a bace yake. Ganin haka
yasa ta saki murmushi tace

D kayi ta jirana ko? Wallahi.......

Hannu ya daga mata hakan yasa tayi tsit yace

Waye ya fita dake ya kuma dawo dake a mota? Meye Sanye jikinki haka

Ya fada Yana nuna bingilin mayafin da ta yafa a kanta Wanda iya wuya kadai ya
tsaya, wareshi tayi tace

Ni? Akace an fita dani? Wa na sani? Yan unguwa nan munafukai ne.

Se kawai yayi murmushi ganin yadda Lokaci daya take raina masa hankali, bai kuma
cewa komai ba ya bata hanya Don ta tafi sede ko an inch ta kasa takawa hakan da ya
gani yasa yace

Kije gida Seda safe. Yana fadar haka ya buga Lifan dinsa within an eye blink ya bar
gurin, itama cigaba tayi da tafiyarta har ta isa gidan tundaga zaure taji Mama tana
cewa A'isha

Kin Dakkowa Khulthum Kwanukan ta ko? Se ta dawo baki wanke ba tazo Tana mana diban
albarka.

A'isha dake zaune kofar daki Tana yankan farce da fitila tace

Tai ta zuwa mana ina ruwan wani.

Kafin Mama tayi magana se suka tsinkayi sallamar Khulthum, inda Mama kawai take ta
kalla tace

Na dawo Mama.

A... A.... Sannu da zuwa.

Imagine! Wanann ne Karo na farko da Khulthum ta fita takai isha'i a waje, ba tareda
sunsan tun asali ina taje ba kuma yanzun babu Wanda zaice Daga ina take.... Akwai
sakaci sosae na rasa dalilin da yasa iyaye irinsu Ke sakaci da whereabouts din
yaransu, talauci ba hauka bane is a trial and test that are never meant to be easy.
Saboda Kai talaka ne Seka bar yaranka sakaka kamar tumakai kada ka manta cewar yara
Allah ne ya baku amana and you must account for every deeds da kukai a nan duniya.

As expected zata yi magana kan Kwanukan ta amma ta share ta shige daki ta cire
kayanta sannan ta fito tayi wanka, tana fitowa mama tace

Khulthum yaronnan Ashiru yazo nemanki Tun rana.

Juyowa tayi tace

Mun hadu dashi, anyi abinci ne?

Ta tambaya Tana duban inda kitchen din yake,

Eh anyi, a zubo miki ne?

Kanta ta girgixa tace

A'a

Daga haka komawa daki tayi inda ta tarar da A'isha tana kife kwanuka, kamar bazata
tanka ma taba se kuma ta kasa kasancewar hakan ba halinta bane tace

A'isha waye ya dauki Kwanukan nan?

Banza Aisha tayi mata hakan kuwa ya harzuqa ta Tace

Ke dan ubanki ba dake nake ba

Inkana son zagi nemi yaran ghetto na fada ina kallonsu, juyowa Aisha tayi tace

Kada ki kuma zagin ubana

Ubanki

Ta bata amsa almost immediately,

Na zageshi akwai abinda zaki iya yi ne?

Dariya Aisha tayi tace

Mutumin da bai bar babarshi ba ai ba abin mamaki bane Don kin zagi ubansu, Sede ki
sani wanda kike zagi shidinne Gatanki ba gantallalun danginku ba.

Hey! Khulthum case, dama ance Baki yasan me zai fada amma baisan Meye martani ba.
Taji Ciwon abin hakan yasa ta durfafe ta suka fara kokawa, Dama Tun suna yara
Khulthum ce Marar karfi, yanzu haka ma Bata canza zani ba, kafin Mama tazo Aisha ta
jibgi Khulthum gashi Daga ita se zanin wanka wanda tuni ya nemi nashi gurin.


Da sauri ta yar da wayar tare da fitowa parlour a sukanne, yadda ta bude kofar
kadai will tell you Abu take so, gaba daya idanu Baba da Mami suka zuba mata hakan
yasa se spirit dinta ya ragu, ta tako a sannu ta zauna daidai kafar Baba Tana
gaisuwa, shima da dukkan faraa ya amsa mata yana tambayarta karatu da kuma su
Junaid and family,
Duk suna lapiya sunce a gaisheku.

Murmushi yayi ya cigaba da kallonshi se Sulaim tace

Mami ina Wayarki?

Dakina

Daga haka ta koma dakin Mamin ta dakko wayar ta zauna gefen gado ta kuma kiran
Junaid, Duk tunaninsa Mami ce amma yana jin muryar Sulaim ya gyara zamanshi tare da
sake rike wayar a ranshi yace

This girl will be the death of me!

Are you there?

Ta furta mishi,

Am there Sulaimi, ya kikaje?

Alhamdulillah!

Ta bashi amsa se kuma sukai shiru baki daya hakan yasa sukaji tamkar gaba daya
globe ya daina rotating round the universe, tamkar Lokaci ya tsaya ne cak! Seda
Junaid yace

Have you eaten?

He always ask that, bata son Meye hadinshi da abinci ba, kanta ta gyada tace

I've eaten, abincin Mami kayi missing.

Dariya ya danyi yace

Nima Wifey ta bani me dadi

Dif taji Abu ya tsirga mata Wifey ta maimaita kafin tace

I've to go zanyi bacci.

Kafin yayi magana ta kashe wayar se taji duk yayi spoiling mood dinta wai Wifey! Ta
dade da wayar hannunta tana tuhumar kanta dalilin da zatayi fushi Dan ya ambaci
matarshi, to idan bai ambaci Subay'a ba Sulaim zaice. Haka tayi ta reminiscing abin
cikin ranta a haka Mami ta iske ta, ta dade a tsaye Tana kallon ta ba tareda Sulaim
din tasan da shigowarta ba. Taba ta tayi hakan yasa tayi firgigit tace

Mami.......

Kallon da Mamin tayi mata yasa ta kasa karasa Abinda zata fada se sunkuyar da kanta
da tayi. Amsar wayar daga hannun ta tayi tace

Kije kiyi shirin bacci I know you must be tired ko?

A sanyaye ta Mike batace komai ba ta fita a dakin yayinda Mami ta shiga call log
dinta Eldest ta gani wanda ya tabbatar mata Junaid Sulaim ta kira. Call duration ta
duba wajen 7 minutes hakan yasa taji abu ya darsu a zuciyarta amma koma dai Menene
she will keep eyes on both of them.
Shatuuu ♥️
[6/27, 3:29 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
8

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad

Daidai bugawar agogon dake Makale jikin bangon dakin daidai fitowar Subay'a daga
parlonta, tana sanye da Abaya beige color tayi rolling da milk din mayafin da
sukaxo tareda abayar. Junaid na zaune kan two seater gabanshi system dinshi ce akan
center table se kafafunsa da ya daura akai. Aiki yake sosae Don Tun Azahar yake Abu
daya sallah ce kawai ke tashinshi. Tun kafin ya san da zuwanta turaren da take
using me dadin kamshi ya bayyana kanshi, lumshe idonsa yayi a hankali kafin ya bude
su ya zube a kanta, ko bata fada ba yasan fita zatai saboda kayan dake jikinta,

Papa aikin ne har yanxu?

Ta tambaya Bayan tayiwa kanta masauki a gefenshi, kanshi ya gyada tareda dagowa ya
furzar da iska me huci yace

Wallahi kua Mimi dake haka yaran Ke ce mata.

Shagwabe fuska tayi wadda tasan baya taba resisting ta saka hannunta a kan sumar
shi wadda babu gashin ma saboda yadda ake saisaye ta akai akai. Tace

Sulma ta haihu an hour ago.

Dagowa yayi Sulma sister Subay'a ce tare akayi musu aure shekara takwas kenan amma
bata taba haihuwa ba se yau shi baisan tana da ciki ba ma. Murmushi ya saki yace

Mashaa Allah Alhamdulillah! Me ta samu?

Baby girl!

Addu'a yayi sannan ya cigiba da aikinsa duk da yasan abinda ta ke nufi amma se ya
share ta. Ta kusan 5 minutes ganin idan ta zauna haka Itace a cuce hakan yasa tace

Papa ina son Zuwa ne.

Bai kalleta ba yace

Se da safe is already late yanxun.

Baki ta turo tace

Haba mana Honim har na fadawa Yaya Suhaila tazo mu wuce tare.

Pen din hannunshi ya aje tare da rufe system din ya dago ya zube idonshi cikin
nata, kasa jurar kallon tayi hakan yasa tayi kasa da kanta, babu alamar wasa yace

Subay'a kullum kin fison ki nuna min abinda kike so shi zaayi? Abinda zuciyarki ta
Raya miki se kin yishi. Banda kin raina ni ma se da kika shirya kika hada
connections dinki sannan zaki zo ki fada min? Nace ba zaki je ba idan kuma ban isa
ba ga hanya nan.

Yana Kai aya ya Mike ya fara tattara kayanshi ranshi a bace saboda ganinshi raini
ne kawai dan ta samu yana tolerating dinta shi ne zata dinga duk Abinda ta ga Dama,
shi ba irin sauran mazajen yan uwanta bane da zasu dinga biye wa matansu.

Tashi tayi ganin ya nufi daki ta bishi, ranta a bace amma Tunda ita take neman abu
dole ta yi kasa da kanta. A bedroom ta sameshi Yana jona system dinshi, a hankali
ta bude Baki zatayi magana yayi saurin daga mata hannu yace

I've said enough kiyi yadda kike so, idan Kinje ya rage naki..

Bata jira komae ba ta fice daidai shigowar Suhaila parlon, dama ita daya ce shi
mijin na waje dan haka tana shigowa ta Fara fadin

Subay'a fito mu tafi ko ma dawo da wuri.

Yadda taga Subayan yasa tace

Kada kice ya hanaki Zuwa?

Kanta ta langwabar Cikeda bacin rai tace

Wai se gobe.

Baki Suhaila ta tabe tace

Ke kuma se goben kenan? Kowa ya tafi se ke daya zaki zauna se Kace tsoronshi kike
ji, ni Wallahi na rasa me ke damun Junaid dinnan.

Ba Abinda yake damuna, magana ce na gama amma idan Ke kike auranta you can go with
her.

Haka suka tsinkayi muryarshi Yana fada Ashe Tun shigowar Suhailan ya fito dan
daukar Flash dinshi. Itama Suhaila Bata da mutunci tace

Oh haka kace to Wallahi se taje, Sede kayi duk abinda zakai.

Kunsan hali ya banbanta hakan yasa bai ko daga kai ya kalleta ba ya wuce bedroom
dinsa, Suhaila ta dubi Subay'a wadda jikinta yayi sanyi tace

Zo mu tafi?

Ina? Na fasa kinga ranshi ya baci kawai nazo da safen

Ta fada Tana me jin takaicin Junaid, su takwas suke gurin hajiyar su amma baki daya
Junaid shi ne me matsala bai taba yadda an juyashi ba kamar yadda ake juya sauran
sirikan kuma lokacinda ta aureshi tunani suke sun auri wawa Ashe ba anan abun yake
ba. Cikeda bacin rai Suhaila tace

Karki cemin threat din Wannan hopeless element din zai sa ki fasa zumunci? Idan
akwai me Zuwa gurin Sulma ai a bayanki ne.

Itama tana jin hakan amma Tunda take da Junaid Bata taba ganin ya Daga murya haka
ba, it's unlike him Wannan yasa taji tsoron fitar take.

Nidai kawai kije Yaya Suhaila kinga kar na bullowa kaina wani aikin.

Wata harara ta watsa mata Tace

Kinsan Allah kafata kafarki wawuya kawai.
Haka Suhaila taja Subay'a suka tafi, Junaid dake jin komai ya saki murmushi ya fito
lokacin har sun bar gidan. A cikin mota kasa sakewa tayi, suna gaisawa da Ishaq ta
bame bakinta, tana jin yadda suke hira amma ita kam babu Wannan damar a haka suka
iso Standard hospital dake tarauni lokacin goma Harda yan Mintina amma dakin da
take kamar rana, Tun a parking space suka hadu da mijin Safina, Surayya da ita
Sulma din. A waje ya tsaya suka shiga ciki a cikin su takwas Samina ce kawai bata
nan itama sun je Mexico ne itada yaranta, Tun dazu da taji labari take jin tamkar
tayi tsuntsuwa ta taho amman babu Hali. Suna shiga suka samu hajiya tana zaune kan
wata kujera dake dakin su kuma sauran suna kasa an shimfida carpet se hira suke
yayinda Sulmar idanunta ke a runtse tun dazu take son ta runtsa Tunda an sha artabu
amma by mere kallo abin bazai samu ba. Suna zama aka Fara sabuwar gaisuwa se hira
ta kuma ballewa, Sulma ma haka ta shiga anayi da ita. Mukhtar mijin Suhaila ya
shigo Yaga baby sannan yayi musu barka ya koma waje hakan yasa hajiya tace

Subay'a ke ina naki dan ka gadama ko bai gadamar ba.

Kafin ta bada ansa Suhaila tayi caraf tace

Kinsan hajiya me yayi mana...... Nan ta kwashe komai ta fada musu, wani mugun zagi
Salima ta saki tace

Shiyasa kika shigo jiki a sanyaye, Ke wacce Irin Shashasha Allah ya hada mu da ita?
Ke me miji ko to Samina ma da bata kasar jibi zata iso.

Ba haka bane.....

Rufe min baki

Hajiya ta fada

Sau nawa ina ja miki kunne akan mijinki, yaro daya kusan shekara takwas kin zauna
Yana juya ki Kece koma baya cikin yan uwanki, to ki sani har ayi suna babu Wanda na
daukewa zuwa yaga Sulma don gobe gidana zan tafi da ita.

Da sauri Sulma tace

Gidanki hajiya? A'a munyi dashi gida zan zauna.

Suhaila ce ta maka mata harara se Safina cewa tayi

Ikon Allah, wannan fa rule ne is not yadda kukai dashi haka ne policy yake kuma
haka zakiyi biyayya.

Kanta ta kada tace

A'a gaskiya....

Dallah rufewa mutane baki

Surayya ta fada waaddda kusan shi ne lokacinda tayi magana, hajiya kuwa kawai
kallonsu take a ranta tana tunanin yadda zata daidaita su.

Basu suka fito ba se 11pm har da Rabi, dukkansu suka fito Sunata hira da dariya,
masu drivers suka shiga masu miji suka bisu shikam mukhtar ranshi a tsananin bace
yake Amma babu damar magana a haka suka isa gidan Junaid, mukhtar ya fita ya buga
amma shiru Wasawasa sunfi Mintina goma suna bugawa babu Wanda ya bude musu gashi
akwai echo kasancewar dare yayi sosae, gaba daya suka fito Subay'a ta rasa inda
zata saka ranta taji sanyi, gaba daya ta rasa a duniya abinda Ke mata dadi kuma ta
kira wayarshi a kashe haka tasu Atika da gateman hakan yasa tana kuka tace
Kinga abinda nake fada miki ko Yaya Suhaila dama nasan Wallahi Junaid se ya bata
min rai.

Tsaki Suhaila tayi hakika Bata taba katari da dan iska Irin Junaid ba, ita tunanin
hakan bai zo mata ba shikam mukhtar dadi yakeji a ranshi Yana inama yanada courage
din Junaid. Haka Suhaila ta kira hajiya ita kuma Tace subay'a tabi su ta Kwana a
can.

To fa people kunji wannan!

Tunda ta fita Junaid ya sanar dasu su rufe gida sannan kowa ya kashe wayarsa yana
ganin is high time ya kamata ya fito ma Subay'a a yanayin da take so dama bahaushe
yace idan kida ya canja to salon rawar ma canjawa yake.

Haka Subay'a Tana gani suka nufi gidan Suhaila dake gaba dasu, Tun tana kuka
Suhaila Na bata Baki har ta share ta. Haka wannan Daren ta rabashi tana tuntuni da
da nasani Marar amfani. It's too late to cry when the head is cut off.

Shikam Junaid baccinsa yayi dukda yana missing Sulaim komanta maganarta, shagwabar
ta, murmushinta da ita kanta don tun ranar da sukai waya taje kaduna basu sake
magana ba dukda dimbin urge din dayake jin akan son jin muryarta amma a haka ya
hakura shi lallai Lokaci baiyi ba.

Da Asuba ya hada musu kaya shida yaran ya sallami duka cooks din sannan ya zubawa
Matar gidan kayanta yawanci na office ne sannan ya rubuta wani abu cikin takarda ya
bawa driver dinsa da key din motarta akan yakai mata gidan Suhaila, shikuma ya
tasar mawa Kaduna shida yaran.

Turkashi!

Seda ya gama parking sannan ta bude kofar ta fito, idanunta suna cikin wani glasses
square shape fari me fadi Wanda ya rufe kusan har kusa da cheeks dinta yayi mata
kyau kuma ya bawa hancinta dayake dogo damar fito da aihnahin pointedness din nasa,
fuskarta babu ko fara'a akasin yadda asalin Sulaimi take, cikin nitsuwa take takowa
har tazo daidai kofar parlour taga an bude Ja'afar ne, Fuskarshi shima babu walwala
amma yana ganinta tamkar dama ita yake jira ko kuma nemanta yake oho musu, hannunta
ya jawo wanda yasa tayi saurin kallonshi tareda kicinayar kwacewa amma ya damke da
kyau seda ya kaita har bakin motar shi kafin ya sake mata hannun aikuwa kamar jira
take ta sakar mishi duka a kirjinshi tareda fadin

Don't ever touch me kaji na gaya maka.

Murmushi yayi yace

Ba wannan ne damuwata ba, the fact that kawai dan kin ganni da wata se kiyi ta
fushi? Kwananki uku Amma you shun my calls ina miki magana kina basarwa Duk saboda
wannan to shikenan Sulaim am sorry she's just a friend and nothing more I'm really
sorry bazaki kara kamani da irin laifin ba. I'm sorry please Luff.

Tunda ta Fara magana take kallonshi wani side na zuciyarta na fada mata karya yake
wani kuma want to believe him Sede na farkon Yafi rinjaye amma se ta bashi another
chance Tace

Yaya Ja'afar I will never take shit from you ever again, never! Da nayi amma yanxu
the world is vast I can't, Nasan halinka kuma duk wanda kake tare dasu na sani amma
I never taught it can go to the point where kacewa budurwarka I'm your baby Sis. I
won't take that. Idan yan matanka kake so Dan Allah kaje ni bazaka Bata min Lokaci
ba.
Wani madaukakin mamaki ya addabe shi da gaske Sulaim ce ke blabbing words dinnan?
Eh gaskiya university ba karya bace, wannan ba karo bane na farko da ta ganshi da
wata ba amma she never fuss on it se yau tabbas akwai aiki gaban Maza.

Naji it's OK zan kiyaye yanzu smile mana.

Harara ta maka masa ta juya Don komawa ciki sede kamar ance daga kanki taga Junaid
a tsaye jikin railers da suka kawata balcony saman, ya zuba hannayensa cikin
pockets din wandonsa yana kallonta, wani Irin kallo yake mata me Cikeda dimbin
tambayoyi, tuhuma da kamar you failed me haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login