Showing 45001 words to 48000 words out of 121650 words
Hanan ne. Sauran part din gidan na sauran yaransu ne su Mami idan sunxo se su
bude su Zauna.
Tunda tayi sallama Yaya Hanan dake zaune ita daya cikin parlour ta taso ta rungume
Sulaim tana fadin
Oyoyo Autar Mami.
Oyoyo Yaya Hanan
Ihunsu ya janyo hankulan mutanen gidan, Amaturrahman ce ta Fara fitowa itama tana
buga nata ihun kafin Hajiya ta fito Cikeda farin ciki. Cikin parlour suka zauna
anata gaishe gaishe kafin Hajiya tace
Ummu tashi kuje ki dan watsa ruwa kar maghariba tayi, Jafaru kaima wuce dakin Najib
ka watsa ruwa.
Duka suka Mike Don Dama abinda suke jira kenan, Amatu ce ta kaita dakin hajiya don
sun San indai tazo nan take sauka, wanka ta Fara yi Allah ya taimaka tana period
hakan yasa bata dauki bashin sallah ba. Gefen kujera ta zauna ta janyo wayarta,
missed calls kalakala haka ta tarar, a hankali ta Fara da Baba ta sanar mishi sunje
lapiya sannan ta kira Mami kafin daga karshe ta kira Junaid.
Yaya ina yini?
Lapiya lau Auta kunje lapiya?
Lapiya lau kowa Yana tambayarku.
Kanshi ya gyada yace
To ayi Hutu lapiya, Duk inda ya kamata ki tabbatar Kinje.
Kanta ta gyada kafin sukai sallama ta Mike Don ficewa se kiran Salim ya dakatar da
ita
Haba princess Kinsan yadda kike wahalar da zuciyar Salim kuwa.
Dan murmushi tayi tace
Ni din?
Ke mana inda Kinsan yadda kika hana Salim sakat I don't think zaki cigaba da gasa
ni fa.
Dariya tayi daidai shigowar Yaya Hanan, ta bita da kallo sannan ta shige ciki,
itama sulaim din se tace
Kaga a gajiye nake ka Bari mayi magana anjima
Ina kika je?
Ya tambaya
Naje jega ne
Dama ke yar jega ce ?
Kasan jegan ne?
Farin sani kuwa amma Kada ki damu ki huta zan baki mamaki.
Kashe wayarta tayi a ranta bata ji komai game dashi ba, ita haka kurum ma take jin
Bata wani aminta dashi ba. A parlor kowa na zaune har Alhaji Kasim Baffa shida Yaya
Najib da Yaya Ja'afar suna zaune se zuba hira ake, gefen Baffa taje ta tsugunna ta
gaishe dashi, Cikeda farin ciki ya amsa Yana saka mata albarka tareda yiwa Anty
Zahra addu'a wanda hakan yaso bata atmosphere gurin.
Tana gama musu kunshin ta mike tsaye Tana buga Hamma tareda kashe torch din
wayarta, seda tayi mika kafin ta shiga daki Don shirin wanka, tana shiga ta Fara
daukar wayarta tayi dialing number Sulaim, bugu daya ta dauka
Hajiyan Kebbi kunje lapiya?
Khulthum ta tambaya Cikeda kulawa, itama sulaim Daga dayan barin tace
Bakiga text dina bane? Ina isowa na miki.
Kanta ta girgixa tamkar tana gaban Sulaim din tace
Ban gani ba Wallahi, kunshi nake yiwa wata Amarya.
Cikeda jin dadi Sulaim tace
Ranki ya dade, kina wuta fa
Dariya Khulthum tayi tace
Kinganni shiryawa zanyi Yusuf zan raka dinner abokinshi.
Dinner Kuma? Ke Khulthum
Rabu dani naje naga gari Kede ki zauna kiyi ta ninkaya a son Yaya!
Tsaki Sulaim tayi tace
Your skull is thick Wallahi, se anjima.
Dariya Khulthum tayi ta kashe wayar ranta fal ko ba komai yau zataje gurin da bata
taba Zuwa ba. Fitowa tayi daure da towel taje ta sheka wanka kafin ta dawo daki
tayi shafe shafenta kafin wani Lokaci ta fito tayi dau kamar a saceta, fuskarnan
dolled up. Kunsan fa Sulaim kyakyawa ce babu karya, fatarta tana da haske amma
bawai can ba, zama a iya saka ta layin matsakaita, asalin skin color dinta me kyau
ne Amma saboda yadda take bleaching skin din yasa tayi haske kamar rana. Fuskarta
round face ce me manyan idanu hancinta Yana da tsayi, bakinta matsaikaici ne sede
batada cikar gashin gira hakanan eyelashes dinta ba can dogaye bane Amma bazaka
saka Khulthum a matsayin marar kyau ba, kallo daya kayi mata se ka Kara Balle uwa
uba jikinta, shape dinta me kyau bata cikin gajeru haka bata cikin masu tsayi
average height gareta. Tanada hips wanda ya kawata ta yake saka ta jin ita din tayi
Saar halitta, tana ji dashi tamkar kwai.
Wani cord net peach dinkin fitted gown ta saka wadda ta kamata sosae daga kasa ta
bude, high heel ta dakko Baki ta saka, haka dankunnenta bakake sannan ta daura wani
bakin scarf yayi kyau, ya amshe ta haka ta fito Tana fitarda fitinannen kamshin da
sai wanda ya kai zuciya nesa ne zai iya jurewa.
Tana fitowa sukai kicibis da Mama wadda dawowarta kenan daga suna itada A'isha,
matar badai yawo ba. Kallonta tayi tace
Khulthum ina zaki da daddare haka.
Agogon dake manne a hannunta ta kala takwas da rabi sannan ta dubi wanda tayiwa
kunshin tace
Zan fita ku bawa Amira kudin ta aje min
Ta fada Tana nuna Amira don duk gidan sunfi shiri da Amira hakanan tafi yadda da
ita, se kuma ta dubi Mama wadda tayi jagalo tana kallon Khulthum din tace
Dinner zanje, anjima zan dawo?
Ta fada Tana juyawa Don ficewa, Mama ta dubeta tace
To yanzun saboda Allah wani Irin biki ne se dare, kalleki ko lullubi babu, a haka
zaki fita?
Kafarta ta buga tace
A haka ake zuwa, kuma ba dadewa zanyi ba fa.
Badon Mama taso ba tace
Allah ya kiyaye ki kula da kanki.
Bata jira cewar su ba ta fice, nan A'isha ta zauna dabas tana mamakin Khulthum
Yaushe idanunta suka bude har haka, to idan an Fara biki 8pm Yaushe zaa saka ran
tashi kenan?
Yar president tana wuta fa! Kalla batafi two hours ba yadda tayi dolling fuskarta.
Daya daga cikin yan kunshin ta fada, amaryar ta girgixa Kai tace
Ni kuma na raina mata Wallahi yadda ake zuzuta ta banyi tunanin nan ne gidansu ba.
Mhmmm ga shegen girman kai!
Ke ni abinda yake dauren Kai yadda bata girmama iyayenta, Zuwa na kusan biyar kenan
amma Karki so kiga disrespect.
Fitowar A'isha ya saka sukai tsit. Ita kuwa Khulthum tana fita sukai karo da
natacce kamar yadda ta rasa mishi yanzun wato Ashir, dauke kanta tayi tamkar bata
san Allah ya halicce kamar shi ba, shima se ya bita da kallo tamkar idanunshi zasu
fado kasa har ta bude motar Yusuf tayi wa kanta masauki. Haka yana nan Zaune Yusuf
yayi reverse ya fice abinshi. Ashir ya runtse idonshi tareda kaiwa iska naushi,
Allah kadai ne bai saka zuciyar Ashir fashewa ba, shi kanshi baisan lokacin da ya
dauka yana zaune kan Lifan dinshi ba. Yanzun ya daina mamakin Khulthum abu daya ya
yanke gobe zai sameta ayi Wacce xa'ayi don ya gaji, yanzun ya fahimci kwatakwata
Khulthum ba shi ne a gabanta ba, ya tuna wata magana da ta taba fada mishi cewar
matsawar ta samu me kudi to zata iya barinshi tayi aure me kudi, don haka better
yayi kudi. Dukkan tunaninshi ya tafi a wasa take amma yanzun ya tabbatar da gaske
take.
A FABS event center dake Magajin Rumfa nan ake kayataccen bikin, Tunda suka shigo
taji ta kaskanta, taga mata iri iri Maza daban daban Kala Kala. Sede babu halin
jamming dasu don Yusuf ya kafa ya tsare, basufi 20 minutes ba yace mata ta tashi
zata rakashi wani guri, kamar kada ta tafi haka taji don Bata gama feeding idanunta
ba. A cikin harabar Royal Tropicana Hotel yayi parking lokacin agogo ya buga Tara
daidai. Kallonshi tayi yayinda yake kakkashe sauran abin motar yace bai ko kalleta
ba
Muje ko?
Ina ne nan?
Ta tambaya gabanta na faduwa
Bakiga Hotel aka rubuta ba ko bakya ganewa ne?
Wani mugun yawu ta hadiya tace
Kaje ni zan jiraka daga nan!
Kallonta yayi yace
Me yasa kike abu kamar baki waye ba? Muje Karkiyi dare
Tsoro sosae cikin idanunta tace............
Shatuuu ♥️
[7/29, 6:16 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU*
22
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
I'm so sorry people of shatuuu kingdom.... Labarin haka ya tafi dole haka zaayi.
Nasan Kuna son Khulthum amma kui hakuri don't throw me out of the kingdom
pleaseeeeeeeeeeeeeee
Idanunta a runtse amma ba bacci take ba Sede hawaye da suke zuba daga idanunta, me
take ji yau nadama ce? Wadda batada amfani ko kuwa? Mikewa tayi ta dubi wayarta
dake gefen pillow dinta, unlocking tayi don duba karfe nawa, it's 1am na dare amma
idanunta babu alamar akwai wani abu waishi bacci, yau tana tunanin ta karyata
maganar da bahaushe yace Bacci barawo ne! Yau duk satar shi bai isa satarshi ba,
baccin ma dama ce kuma samun guri ne amma yau tasan babu Wannan damar babu Wannan
gurin. Mikewa tayi ta dubi Amira da A'isha dake bacci sadidan amma ita ya kauracewa
idanunta. Gefe daya ta koma ta hada kanta da gwiwarta ta saki kuka a hankali me cin
rai amma kasancewar dukka bacci suke me nauyi yasa babu Wanda ya farka.
*Some hours ago*
Idanunta Cikeda tsoro tace
Bangane Abinda kake nufi ba Yusuf, Dan.....
Bai bata damar karasa maganar ba ya samu damar hade bakinsu guri guda, cikin
nitsuwa yake Bata sensual kiss me tafiyar da hankali da kuma sanya nutsuwa ga wanda
ake yiwa. Sede komai is based on nutsuwa da kwanciyar hankali, Khulthum ta rasa
duka kokarinta kawai ta kwace kanta sede waye yace mata shi Yusuf din rukon wasa
yayi mata. Kuka sosae take tasa hannayenta Baki daya tana dukanshi amma ko gezau
baiyi ba, Seda ya nutsu kafin ya sake ta, Yana mata wani Irin duba irin na goggagun
yan duniya wanda suka kware a bariki, se lokacin ta lura Baki daya he's not that
gentle yusuf she knew wannan Ya koma mata wani iri Wanda batasan ta yadda ma zata
muku describing dinshi ba.
Meye kike kuka? Is just a kiss
Hannushi dake saman kafadarta ta doke, cikin idanu take kallonshi hawaye na bin
kuncinta tace
Dama ba so na kake ba? Dama yaudara ta kazo yi, jikina kake so?
Kallonta yayi ya langwabar da Kai kalar tausayi yace
Come-on Baby, zuciyarki da jikinki duk mallakin Khulthum ne kinga don naso abu daya
daga cikin ai ke naso. Ki share hawayenki I didn't mean to kinji, mistake ne Babe.
Muje na kaiki gida.
Rufe fuskarta tayi da palms dinta ta shiga kuka Tana tayi amma Marar sauti, bata
san ya takeji a zuciyarta ba amma kunci ne fal a ciki tana ganin tamkar rayuwarta
ta tarwatse kenan. Shikam Yusuf pretending kawai yake amma haushinta yakeji fal
zuciyarsa, Tana tunanin taci banza ne, karya take ai bani gishiri in baka Manda dan
haka definitely se yayi Abinda yayi niyya. Shi da take tambayarshi Dama Baya sonta
ne mamaki ta bashi, Bayan bai taba ganin kwayar so cikin idanunta ba se zallar
zalama da son abin duniya, Tunda ita son abin duniya take to tabbas zai bi hakan ya
karbi abinda yake so.
Har kofar gida ya rako ta lokacin goma saura, Seda ya saka ta gyara fuskarta don
kar a fahimci wani abu sannan ya kara assuring dinta shi he never mean any harm,
kawai sonta ne yake saka yake jin wani mugun feelings akanta wanda tasan idan da so
definitely akwai Sha'awa.
*Present*
Asabar fari tayi sallah sannan ta samu bacci ya dauketa, kasancewar babu inda
zataje yasa se karfe goma na safe ta tashi lokacin Mama ce kawai a gidan. Da shirin
wanka ta fito ta fara lekawa dakin Mama tace
Ina Kwana Mama.
Lapiya lau Khulthum, me ya samu idanunki suka kumbura.
Kanta tayi saurin juyar wa tana ganin kamar Maman tasan Abinda yayi transpiring
tsakaninta da Yusuf.
Mmm.... Kin.... Ga... Bacci ne
Kanta ta gyada kafin ta bar gurin da hanzari to avoid further questions. Seda ta
shirya kafin ta dauki wayarta tana ganin ya kamata ta fadawa Sulaim abinda ya faru,
ko ta bata shawara. Sede tana Fara ringing tayi saurin katse kiran saboda tana
tunanin me zata fada mata, Bayan sau nawa tana mata fada akan kule kule yanzun ai
dariya zatayi mata batasan wannan ba Sulaim bace, ba kowacce kawa ce Sulaim ba
she's one among millions, kuma ba zata taba barinta cikin wannan halin ba......
Tunaninta ya katse lokacinda Sulaim tayi returning call din, babu yadda zatayi haka
tayi picking Din sede kafin ta kai ga fadin Abu Sulaim din tace
Kin kyauta Khulthum ko dan birthday wishes dinnan babu kowa yayi min banda ke.
Kai Khulthum ta girgixa Wayyo bestie's birthday ta manta amma taji rashin dadi,
cikin lallabawa tace
Ayya! I'm sorry Wallahi kaina ke ciwo yanzun tashi na kenan.
Ayya Allah ya baki lapiya.
Amin..... Happiest birthday dear
Murmushi Sulaim tayi tace
Thank you.... Kinsan wannan Salim da na baki labarinshi?
Kanta ta gyada tace
That Arab?
Yawwa Kinsan Mamanshi ce Egyptian, babanshi kuma full blood shuwa ne. Shekaranjiya
that's ranar da naje Jega yake cemin yasan jega he'll surprise me, dazu wajen 8 na
safe naga blinking din location dina kamar ana tracking dina......
Me ya faru?
Khulthum ta katse ta idanunta a warwaje, Sulaim ta buga tsaki tace
Labari fa nake Baki Kiyi shiru, se nayi saurin kashewa Kinsan ko Mintina ashirin
ba'ayi ba Yaya Najib yazo yace nazo nayi bako, I was like waye? Tunda banda AP da
kowa kinga jiya birnin kebbi muka wuni, Amma Hajiya tace na wuce Kada na wulakanta
mutum. Unbelievable Salim ne Zaune Kan motarshi Yana ta fitarda murmushi. Ya dinga
tsokanata wai naji tsoro kar ayi tracking dina. Ya kawomin birthday gifts dinshi.
Seda tayi shiru kafin Khulthum tace
Amma yayi surprising dinki gaskiya. Amma Sulaim kina sonshi ne?
Wani disgusting look ta bawa wayar tamkar tana gaban Khulthum tace
Nope he's very charming tsoro yake bani gashi ni inada Ja'afar dina amma kinga
Salim dinnan idanunshi ya bude da yawa, Kinsan he tried hugging me seda na dakatar
dashi kafin wai missing dina yasa yaji he can't resist.
Ikon Allah
Shi ne kawai Abinda Khulthum ta iya fada don da zata iya da ta fada mata amma she
can't saboda tana jin nauyin maganar.
Kinsan halin mazan kenan fa yanzun, kowa slight space yake nema kiga ya kawo miki
zancen banza, Na fattake shi shida birthday gift din saboda kada yayi tunanin dan
ya bani wani stupid birthday gifts dinsa yana nufin ya siyi jikina kenan. Shiyasa
nake ce miki duk wannan su Yusuf din kiyi hankali dasu don idanunshi kawai is
telling you he's not a good person kada Kina amsar abin hannunsu Dan naga yanxu
ba'a kyauta dan Allah se dan compensation da wani abin.
Kede Allah ya kyauta haka.
Daga haka suka kara hira sannan sukai sallama, nan Khulthum ta zauna gefen katifar
tana tunano zantukan Sulaim, ko dai Abinda take fada gaskiya ne? Ko dai Abinda ya
fada karya ne? Amma taga nadama karara cikin idanunshi sannan idan......se kuma ta
kasa karasa wancan sentence din don tasan she's deceiving herself.
Mama ce ta leko don jin shirun yayi yawa, Tana daga labulen suka hada idanu se Kuwa
Khulthum ta Mike da sauri tamkar Marar gaskiya ko dan dama batada gaskiyar ai.
Kizo wani na nemanki.
Gabanta taji ya fadi Amma haka ta Mike ta dauka hijab wanda ta manta rabon da ta
saka shi ta nufi zaure, yaro ne in his mid teens ya mika mata envelope babu bayani
ya juya. Itama cikin daki ta koma Don tasan me aikenan Yusuf ne Don kuwa ga kamshin
turaren shi na Oud wanda kamar signature dinshi ne a komai nashi ya kama. Tana
zazzage envelope din seda gabanta ya fadi sababbin 1000 naira notes ne a Mike
basukai bandir ba amma sunfi rabi, da sauri ta kwashe kar wani ya shigo, se karamar
takadda yayi rubutu na ban hakuri da sake jadadda mata son da yake mata tareda
rokonta ta manta da abinda ya faru jiya.............
Shatuuu ♥️
[7/29, 6:16 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU*
23
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
*Where are all the talented and intelligent Writers online? Ina son fadar a little
thing about writing, the moment kika dauki pen, phone, Tab ko system with the
intention of writing online, To tabbas you've sign your life into seeing love,
kindness, gratitudes , Bullshit, Criticism, negativism especially idan Kinyi suna.
This is life but one thing you need to tell yourself is how ready I'm to face this
challenges? How strong is my threshold to withstand all this? By now it's supposed
to be we are All used to abubuwan readers. Sede I'm pleading on behalf of the
grateful ones, the righteous ones kada muna hukunta su da laifin wasu, is not right
gaskiya. What matters is hakuri and appreciation, always look at the positive side
of things not the negative side. _Sor for this I dedicate this page to every writer
whether in touch or apart, pick up your pens, phones, tabs and systems and continue
writing, perhaps through this we can change even if it's a single life....._ Thank
you*
Hannunshi rikeda wayarshi kirar Samsung, Yana zaune kan kujera a main parlon gidan
yana scrolling through Daily trust application dinshi da yake karanta news, yayi
nisa sosae a karatun yaji alamar email ya shigo mishi hakan yasa ya katse don duba
Menene. Gyara zamanshi yayi ganin Abinda bai taba tunani ba a Kwana kusa. Shekara
daya kenan da ta wuce Mami tasa shi yayi applying wani conference da ake na
Barristers annually a Estonia dake Europe. Abin is very educational and Yana bada
opportunities sosae amma kafin mutum ya samu se yayi shekaru yana applying amma
shiru, to yanzun ga approval email Daga gurinsu na yayi registeraton.
Farin ciki sosae ya Mamaye shi da hanzari yayi forwarding email din wa Mami sannan
ya kirata yace ta duba. Yana zaune yayi registeraton online kafin ya Mike zuwa
dakinshi ya canja Daga jallabiyar jikinshi Zuwa wani brown trouser da shirt baka,
agogon da baya taba fita babu ya dakko brown ya daura kan Farar fatar Hannunsa,
bude bedside drawer yayi ya ciro passports dinshi Dana Subay'a saboda yaga tafiyar
is in 10 days time ne so dole yayi making komai in a snappy kada a samu matsala.
Bata nan taje office shi kuwa yau Baki daya babu inda yaje Yana gida shi daya se
missing Sulaim da yake, a lissafinshi gobe zata dawo Amma Tunda ta tafi sau biyu
kawai sukai waya ranar da ta isa jega, se bayan yayi mata depositing kudi cikin
account dinta tace mishi ai taga alert din that's all! Hakan da takeyi Sagar mishi
da gwiwa take, Tana nuna bata ma lura da halinda yake ciki ba kenan? Tana nuna ko
kadan bata damu ba. A tsarinshi tana dawowa he'll let the bomb out of the shell
amma wannan tafiyar ta zame mishi tsaiko amma da zarar ya dawo it's over sede
rashin fadar ya zama tarihi Don zai fada ne ko zuciyarshi ta nutsu. Yana ta driving
Yana kiyasto idan yace
Sulaim I love you! Yadda zatayi yasan zata bude wannan idanun nata masu sake daga
mishi hankali, kila ta turo wannan 1cm bakin