Showing 6001 words to 9000 words out of 121650 words

Chapter 3 - MACE A YAU by Shatuuu

Shatuuu   

12 May 2026

469

lokacin don haka
yanada rufin asiri sosae, matarshi kwaya daya Maryamu se yaransu biyar Lukman,
Fatima, Aminu, Sauda da Hafsa. Baki dayansu babu Wanda baiyi karatu ba hatta matan
saboda shi yayi karatu yasan dadin karatun hakan yasa duk yadda ake tsegumin shi
seda yasa sukai karatun. Lukman shi ne soja a cikinsu kuma yana rike da matakin
General , Umma Fatima classroom teacher ce Tana aure da yaranta a Ningi, Mama Sauda
kuma Nurse ce Tana FMC birnin kudu tana aiki sannan Tana auren wani Barrister shima
dan garin ne, se Anty Hafsa Itace take aure a Niamey kasar Niger. General Lukman
soja ne mijin Hajiya Nafi wadda asalinta yar kebbi ce sun hadu da ita a saudiyya
sunje aikin hajji anan Bayan sun dawo aka Yi dukkan wasu formalities sannan sukai
aure. A maiduguri suka Fara zama sannan suka koma Abekuta anan ta haifi Junaid me
tsananin Kama da Uncle Aminu tamkar shi ya haifeshi. Baiyi shekaru uku ba aka maida
Baba aiki Minna hakan yasa Mami wadda Barrister ce kawai tabar aiki da Gwamnati
Sede private Tace idan sukai settling ta samu tayi joining wani abun sannan ta
dakko kanwarta Zahra ta rike wadda ta auri uncle Aminu daga baya. Seda Junaid yayi
kusan shekaru biyar kafin Mami ta haifi Jabir, Bayan shekara uku ta haifi Ja'afar,
har ta fitar da rai da haihuwa wajen shekaru Tara sannan ta haifi Auta Jawad.
Junaid shi ya gado Mami shi yayi Law a university of Nsukka yayi serving a Niger
sannan ya dawo gida lokacin sun koma baki daya kaduna anan cikin Jaji, a high court
yayi practicing na shekara biyu sannan ya koma ABU yayi masters sanann yayi
academician anan ya hadu da Subay'a ita kuma tana banking and finance, asalin
Subay'a yan Kano ne mahaifinta dan Rano ne mahaifiyarta yar Bichi suna da kudi
sosae kuma yan Boko ne gashi basuda namiji ko daya baki dayansu mata ne hakan yasa
sukeda zumunci Don haka idan Kaje gidajensu zakaga haka suke tafiyar da rayuwar su
iri daya a cewarsu uwarsu batada da namiji so babu Wanda zaiyi disrespecting dinta
Shiyasa ya kasance basu girmama dangin miji. Danshi na farko Ahmad Wanda Keda
shekaru shida se na biyu me shekaru uku Muhammad. Yanzu haka he's a lecturer a
faculty of Law cikin BUK. Jabir shi ne na biyu his father's son, sosae yake kama da
baba kuma shi ne soja me rank din Conel Yana Delta shida matarshi Imratu yar jigawa
ce a garin Babura ta social media suka hadu, tana level 3 akai Auren a UDUS haka
dai aka samu ta kammalla karatun suka tattara Zuwa delta. Tana da kirki tasan
mutuncin mutane sede basu taba haihuwa ba hakan yasa suka daga hankalinsu Amma Baba
da kanshi yayi musu nasiha akan komai na rayuwa MUQQADARI NE, kada su manta hakan
wannan yasa suka Kwantar da hankalunsu, tsakanin subay'a da Imratu babu wani
kyakyawan muamala saboda Imratu bata son raini itakuma kullum kallon kaskanci take
mata hakan yasa Basa shiri ko kadan haka nan Jabir basu shiri da subay'a wanda ya
kuma shafar ita Imratun. Ja'afar shi ne na uku pharmacist ne Yana aiki a cikin
kaduna bashida aure, shima kusan halinsu daya da Jabir sede shi mutum ne me
kulekulen yan mata shi kanshi bazai iya irga yan matanshi ba saboda yawansu, gaba
daya ya fisu kyau hakan yasa yake ganin jin yakai, ko Baibi yan mata ba definitely
Za'a bishi. Amma Duk Wannan yan matan yana son Sulaim Yana ganin Ita kadai ce taste
dinsa Don currently tare suke, yana ganin ita reserve dinshi ce Sede besan hakan
kuskure ba ne Don duk Abinda yake Sulaim na sane dashi . Jawad shekara daya kawae
ya bawa Sulaim shi ne abokinta wanda ko abu ya sameta shi take Fara fadawa yana ABU
yana engineering.

Uncle Aminu neurosurgeon ne matarshi Anty Zahra, daga Zuwa wani course Germany shi
kenan suka retaining dinshi yake musu serving acan. Duk wata Niima da Allah yake
bawa mutum sun samu haihuwa ce kawai Allah bai kawo ba, sunje asibitin Amma shiru
har suka hakura Se kuma kwatsam Sega Anty Zahra da ciki, murna kam ba'a magana haka
suka ta murna suda danginsu. Wata Yana kaiwa lokacin shi ta haifi yarta mace me
Kama da ita sosae sede Bayan ta haihu ta Fara wani Irin bleeding na fitar hankali,
Duk yadda akaaso tsayar dashi abu ya faskara hakan yasa Uncle Aminu signing aka
cire mahaifar baki daya, hakan yasa Bata kuma haihuwa ba Daga kan Sulaim. Baki
daya suka dawo Nigeria a gidan Mami suka zauna akai suna Yarinya aka saka mata
Ummu_Sulaim Daga nan suka tafi birnin kudu inda tayi watanni uku kafin suka koma
Germany. Kowa nasan Sulaim musamman yaran Mami Tunda basuda mace a gidan Tun
lokacin Baba yaso karbarta amma ganin kamar itakadai ce abinda suka mallaka yasa ya
hakura. A Kwana a tashi Bbu wuya gurin ubangiji haka Sulaim tayi ta girma har ta
shiga secondary school dinta, sun sota ta sosu sun bata dukkan abinda Allah ya
wajabta iyaye su bayar to babu abinda Sulaim ta rasa, sun mata gata kuma sunyi mata
tarbiyya.

On the fateful day, Tana tashi Daga school taki bin school bus don tayi da Mummy da
Daddy dinta akan da kansu zasu zo daukarta sede kafin nan ma Sega mota daga office
din Daddy anzo tafiya da ita, duk tunaninta basu samu dama zuwa bane Shiyasa, sede
tana Zuwa compound dinsu taga an taru ga reporters, police, Nigerian Ambassador da
sauran mutanen embassy, se gawarwaki guda biyu an rufesu da farin likafani, Tunda
ta zo gurin kawai taja ta tsaya bata yi gaba Balle tayi baya Tanan dai a tsaye ta
kusan Mintina goma kafin aka fahimci zuwanta, Alhaji Salisu shi ne Ambassador din,
riko hannunta yayi ya isa da ita inda gawarwakin suke ya bude fuskokinsu, Mummy's
ce da Daddy tamkar suna raye babu digon ciwo jikinsu, itadai kawai shiru tayi tana
ta kallonsu amma ta kasa furta komai, addu'ar da aka saka ta tayi ma take kasa tana
nan har aka zo tafiya dasu don musu sallah saboda Baba general ya wakilta
Ambassador yayi duka necessary saboda bazasu samu tasowa ba se Washegari. Haka
Sulaim na kallo aka tafi dasu amma hawaye ko dis bai digo mata ba, akai musu sallah
aka binne su sannan aka tafi da Ita Nigerian embassy dake kasar, Tunda taje Matar
Alhaji Salisu take ce mata

Sulaim Mummy ta rasu Daddy ma haka, bazaki kara ganinsu ba kiyi kuka kinji

Amma ko dis ta kasa gashi ko uhm bata furta ba itadai ta zama gata nan gata nan dai
ita kamar statue haka ta zama. Har su Mami suka iso Sulaim Batayi ba duk yadda taga
ana kuka Tana son Yi Amma ta kasa, seda aka gama komai aka taho da ita Nigeria anan
ta Fara wani Irin kuka me Cikeda tashin hankali, shi kenan se ta dawo musu da
mutuwar sabuwa aka Fara wani mourning din. Tasha kuka Sulaim kamar bazata taba
dariya ba, don seda aka Fara hadata da therapist kafin aka samo kanta. Hakan yasa
ta bata shekara daya bata fara school ba. Jawad shi ne abokinta na farko Bayan Mami
kullum suna tare se Ja'afar Wanda ya nuna mata soyayya me tsayawa a zuciya, shikam
Junaid ba a gari yake ba amma yanada matsayi cikin zuciyarta saboda duk lokacinda
ta ganshi se Daddy ya fado mata kuma dake farkon tafiyar Daddy Germany da Junaid
yayi hakan yasa sukeda abubuwa da yawa ita dashi in common.

A haka ta dangana ta Fara school inda ta karasa secondary dinta shi ne ta Fara
law..... Sulaim kenan.

Khulthum Itace yar Mama (Hadiza) ta farko , mahaifin Khulthum malamin wata
islamiyya ne a wani kauye a malumfashi, shi ne mijin Mama na farko wanda uwar miji
da danginshi suka hanata sakat Seda ya saketa da cikin Khulthum haka ta koma gida a
Kano babu dadewa ta haifi Ummu_Khulthum shi kuma Malam Sule Allah yayi masa rasuwa.
Bayan ta yaye Khulthum tayi wani auren shi ne ta haifi Amir, A'isha, Maryam, Amira
da auta Osama. Mahaifinsu aikinshi shi ne hada guga da dinkewa Dan haka se ranar da
Allah ya kawo ciniki akeyi da Wannan Za'a kukuta ayi cefane, to yanzun anzo era da
kwatakwata kusan a birni guga bashida amfani shi kuma sanaar da ya iya kenan. Hakan
yasa suke cikin bakin talauci. Dadi daya se Khulthum ta iya kunshi takeyi, Idan
akace sallah tazo to gidannan ba'a rufeshi saboda mutane, se ya zamana Yarinya Tana
da abin batarwa to most lokuta ita ke bada kudin cefane hakan yasa ta raina su,
raini na fitar hankali kuwa, dakuna biyu ne a gidan amma kayanta ne kawai a ciki
yaran nasu na gurin iyayensu idan ka shiga gidan tunani zakayi cewar Khulthum ce
yar gidan sauran su ne agola. A haka aka Fara daukarta tana zuwa gidajen masu kudi
tayi lalle wannan shi ya fara bude mata ido taji tabbas bazata iya cigaba da zama a
wannan halin ba.

Ashir shi ne saurayin ta na karfen kusan kowa tare ya sansu dukda itadin tana kula
wasu amma a zuciyarta Ashir shi ne reserve dinta, to kuma se ta shiga makaranta ta
Fara ganin kankarrrun masu kudi, yan karya hakan yasa akalar Rayuwarta ta Fara
juyawa. Wannan kenan.

To people of Allah kunji asalin kowa! Ya kuke ganin xa'ayi? Yanzu zamu shiga cikin
labarin sosae.


Shatuuu ♥️
[6/23, 10:17 AM] Heedaya Bunu: *MACE A YAU*
5
✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad

Sulaim! Sulaim!! Sulaim!!!

Mtsssss

Sulaim ta buga tsaki jin yadda ake kwala mata Kira, ita a karan kanta bazata iya
tuna Yaushe taji ana kiranta irin haka ba, gyara zamanta tayi babu alamun ko niyyar
zataje kiran da Subay'a ke yi mata, haka ta cigaba da revising books dinta don Bata
fiye son barin karatu ya tarar mata ba. Tana nan Zaune se ga Atika ta shigo ko bata
fada ba tasan aiko ta akai hakan yasa tace

Kije ki ce mata gani nan.

Ba tareda Atika tayi magana ba ta fice sannan Sulaim ta Mike ta fito fuskarta babu
walwala, Subay'a na zaune kan daya daga cikin cushion din da suka kawata parlour,
Tana cikin abaya baka kasancewar Friday ce basu saka suit, dawowarta kenan daga
office don ko kaya bata canza ba. Kafarta daya kan daya tana ta girgixa ta ga
fuskar nan a murtuke.

Ance Kina kirana?

Sulaim ta tambaya lokacinda ta tsaya akan Subay'a bawai Sulaim tana da rashin kunya
bane no, idan kaja girmanka tafi kowa girmamaka amma idan ka nuna mata Kai Bakada
mutunci zata saka wannan rigar don ku daidaita differences dinku.

Bakiji tun dazu Inata kwala miki kira ba.

Subay'a ta fada a kufule, zama Sulaim tayi tace

Na jiki mana kawai naga kiran yayi yawa ne.....

Yimin shiru fitsararriya..... Tashi kije na fasa fada.

Batace da ita komai ba ta Mike kuwa ta koma dakinta ta cigaba da bitar ta sede tayi
murmushi idan ta tuna karonsu da Subay'a. Ta dan jima a zaune taji zaman ya isheta
hakan yasa ta Mike ta fito hannunta rikeda wayar ta, babu kowa a parlor hakan yasa
ta samu dogon cushion ta kwanta kafin ta Fara neman layin Ja'afar, a iya lissafinta
Kwana biu kenan basui waya ba kullum ya kira tayi bacci ita kuma Bata samu damar
returning masa call din ba.

Hello Sweetm

Shi ne Abinda ya fara fada Yana amsa call din, murmushinta me kyau tayi wanda
wushiryar dake bakinta ta bayyana se ta Fara rikidewa zuwa fuskar Junaid, Don ita
da babanta take kama kuma Junaid photocopy Uncle Aminu ne.

Hi Luff

Ajiyar zuciya duka suka sauke, shima daidaita kwanciyarshi yayi tareda rike wayar
da kyau yace

Kinsan yadda Nayi missing dinki kuwa, gaskiya kano zanzo na ganki.

Dariya ta saki a hankali daidai bude kofar parlour amma saboda yadda ta shagala
Bama tasan an shigo ba.

Kai da Yaushe nazo har zaka dinga ihun kayi missing dina, though I missed you too
Se yayi dariya yace

Kaji ta Ashe Kema Kinaji, to ya komai hope babu Wanda yake hunting life dinki?

Haba dai waye ya isa bayan ka kankane ko ina, Sulaim is for Ja'afar babu wani.

Tarin da taji yasa ta dago a hankali ta dubi gurin, Junaid ne a tsaye da dukkan
alamu ya jima da shigowa, idanunsa da suke farare sun Dan canja kadan, gaba daya ya
zuba su akanta, yadda yake kallonta yasa ta duburburce ta Yi saurin kashe wayar
tareda mikewa Sede kafin ta tako inda yake har yayi gaba ya nufi inda kofar parlour
shi take. Komawa tayi ta zauna tayi shiru a ranta tana fadin me yasa yake min irin
kallon nan kamar Nayi masa laifi? Ko dai wani abunne? Gaba daya se ta kasa sakewa
hakan yasa ta koma daki Tana ta jujjuya abin, a saka Ja'afar ya kara kira amma se
taji bata bukatar sake magana dashi haka tayi ta ringing Batayi picking ba Daga
karshe Tayi picking Daga muryarta ya fahimci bata mood din hakan yasa yayi mata
sallama donshi ma aikinsa yake.

Junaid kam a parlonshi ya cire takalman kafarshi tare da Adana su cikin rack dake
gefe, cikin bedroom dinshi ya shiga wanka yayi, haka Yake neat tamkar na mace,
Junaid Nada tsafta kuma yanada kula baya tarayya da kazanta hakan yasa ko baa gyara
mishi ba zaiyi sparing Lokaci ya gyara da kanshi. Komai da ya cire seda ya maida
shi inda ya dace, towel ya daura ya shiga bayi ba tareda ya Bari abinda ya faru
tsakaninshi da Sulaim ya dawo masa ba. Haka yayi wanka yayi Alwala sannan ya fito a
tunaninshi Subay'a ta shigo amma har lokancin babu Wanda ya shigo kuma sunsan ya
dawo. Jallabiya yasa Fara tas hade da hularta, ya jika jikinshi da turarenahi wanda
ko kudi ya baka indai daga jikinshi ya fito to Seka ji wannan kamshin saboda yadda
ya kama jikinshi.

A parlor yayi tunanin zaiga Sulaim nan ma Bata nan haka ya wuce massallaci akai
maghrib sukai meeting na magidantan unguwa sannan akai isha'i kafin ya dawo gida.
Ko dining bai kalla ba ya wuce parlonshi yayi kusan Mintina ashirin Subay'a bata zo
ba, hakan ya kara dagula masa lissafi ta barshi da abinda yake ji mana, inda tasan
yadda zuciyarshi take ciwo a halin yanxu baya tunanin zata barshi shi daya, kuma
wannan halinta ne ba wai yau ta Fara ba yayi maganar har ya gaji amma bata fasa ba
but yau Yana ganin xa'ayi sabon zama.

Yana nan Zaunen Sega ta shigo, tayi kyau babu karya, lace ne jikinta skirt da riga
wanda yayi mata kyau tayi kwalliya a fuskar ta, dankwalin ta daura shi yadda ya
dace gashi se kamshi take hakan se ya saukar masa da nutsuwa yaji duk ya zubar da
makaman yakin nashi, amma a ranshi Yana Raya idan suka cigaba da haka lallai zai
zama kullum shi ke cutuwa amma yau Tasha. Kamar tasan me yake tunani tana isa gun
da yake zaune ta riko Fuskarshi ta Fara bashi wani hot kiss wanda ko minti bai cika
ba ta kashe masa dukkan jikinsa tasa ya manta da wanzuwar wata mace Bayan ita.
Subay'a kenan.

A dining kowa ya hallara banda uwar gayya Sulaim har lokancin tana iya hango
tsagoran bacin rai idanun Junaid ta kasa manta hararar da ya zabga mata dazu hakan
yasa taga gwara tayi zamanta idan suka gama cin abincin ta fito taci nata, amma
hakan bata samu ba Don kuwa aiko Ahmad yayi akan tazo abinci is ready. Turo Baki
tayi kamar Junaid dinne yazo da kanshi tace

Kace na koshi

Shikuwa ya juya Yaje ya isar da saqon shi, share maganar yayi ya fara cin
abincinshi, Subay'a na mishi hira, Sede ya kasa jurewa don ya Saba da ganinta
gefensu tana tauna abinci da wannan mitsitsin bakin nata, wayarshi ya janyo ya tura
mata
_Come on fito Kici abinci _

Tana jin shigowar message din tasa hannunta ta janyo wayar Don tunaninta Ja'afar ne
ashe me gayya me aiki ne, baki ta Kara turowa tareda buga kafa Cikeda shagwaba
kamar yana gabanta tace

Mhm Mhm Bazanci ba.

Shikam bawan Allah gaba daya hankalinsa Yana kofar dakinta ita kadai yake da
muradin gani amma taki fitowa ita kuma Subay'a bata Lura ba, a haka ya kara tura
Mata wani text din

_Don't let me come and meet you a dakinnan, ranki zaiyi mugun baci wallahi_

Yadda text din ya nuna mata seriousness dinsa yasa ta fito Tana ta cin magani, da
idanun shi ta Fara arba yayinda ya lumshe idanun shi Yana jin yadda sanyi ke zagaye
jikinshi, haka Kuma ya sauke ajiyar zuciya wadda har Seda Subay'a ta dubeshi.

Zama tayi ta janyo plate ta bude abincin, baki daya daga shinkafa, macaroni se
salad. Abincin kenan kullum su ake sarrafawa ita kuma ta gaji, ga abinda ya faru
daxu ga tursasawar Junaid akan taxo taci abinci ga yanzu idanunshi da suka hanata
sakat, kawai se ta kifa kanta ta Fara kuka.... A'a abin mamaki duka suka bita da
ido, wani mugun tsaki Subay'a taja tareda mikewa tace

Jimana bataciyyar Yarinya, zaki samu a gaba da kuka.

Daki ta wuce abinta yaranta suka bita dukda son su lallashi Antynsu amma Subay'a ta
buga ta tsare. Shikam Junaid Daga kukan yasan tsantsar shagwaba ce amma dukda haka
se kukanta ke sukar mishi Vena cava. Fork din hannunshi ya aje yace

Sulaim

Kanta ta dago Baki daya fuskarta ta baci da hawaye, kallonta yayi yace

Ya akai, don nace Kici abinci?

Pouting face dinta tayi tace

Ni bashi nake so ba.

Murmushi yayi wanda yasa yayi kyau sannan ya zaro ido a ranshi yace Anzo gurin

Me kike so.

Seda ta gama share fuskarta sannan tace

Tuwo!

Kuma yadda ta fada irin seriously dinnan, wani kallo yake binta dashi with full of
mamaki sannan ya dubi wall clock din karfe Tara ta gota, kallon fuskarta yayi yaga
yadda take kallonshi kuma da alama jira take yace a'a ta sake Daga mishi hankali.

Atika!

Ya Kira a nutse, within seconds Atika ta iso Cikeda mamaki Don shi baya saka aiki,
yana kallon fuskar Sulaim yace

Tuwo nake so yanzu
Kallon time tayi tace

To Yallabai!

Daga haka ta wuce kitchen dake sunada miya cikin fridge. Daga haka bai kara magana
ba ya bar mata dining din ya koma kan cushion tareda maida channel din zuwa
aljazira yana kallon news. Itama share shi tayi ta cigaba da zamanta Tana jiran
abinci, to 10 Atika ta kawo tuwon da miyar ogun wadda a ido ma kawai cewa take "eat
me" ajewa tayi ta juya yayinda ya dawo da dukkan hankalinshi kanta hakan yasa ta ji
duk ya takurata se ta turo Baki, kanshi ya dauke Yana shafawa a ranshi yace "Sulaim
case" ita dama haka take rasuwar su Daddy yasa ta rage shagwabar amma Bayan ta gama
secondary se abun ya fara dawowa kuma indai tanayi dole Se ta dauki hankalinka wasu
lokutan ko magana take se Junaid yaji kamar don tasan tana rikitashi Shiyasa take
amma ina haka take normalcy dinta kenan.

Seda ta koshi ta tattare Kwanukan kafin yace

Babu Abinda kike so kuma?

Kanta ta gyada tana murmushi, shima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login