Showing 36001 words to 39000 words out of 121650 words
Meye tsakaninta da Junaid da take jin zuciyarta
nayi mata nauyi Duk lokacin da ta ganshi da matarshi, ko dai sonshi take? Se kuma
ta Fara fadin No! No it's not possible, it's never gonna happen, to amma Koda tayi
denying it obvious abinda takeji game da Junaid so ne, runtse idonta tayi tana
girgiza kanta Tana fadin No! Never!! It will never ever and will never happen.
Kifar da kanta tayi tana ta tunani wanda ta rasa na Menene Sede babu me bata amsa.
Shatuuu ♥️
[7/17, 5:42 PM] Asma'u Madugu: *MACE A YAU*
16
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
A firgice ta Mike Daga gadon saboda jin har an shiga sallah, da sauri ta shiga
toilet tayi Alwala tazo tayi sallah, qurani ta janyo tayi karatu na thirty minutes
kafin tayi azhkar se wanka. Tana fitowa ta shirya cikin skirt da riga na atamfa
sannan ta zauna gefen gado ta Fara revising book dinta. Nanma she took almost an
hour tana abu daya kafin ta aje littafin saboda kiran Mami daya shigo
Mamina
Ta fada lokacinda ta Kara wayar a kunnenta , da murmushi Mami tace
Auta kin tashi lapiya?
Lapiya lau Mami ya gida, Ina Baba?
Ga Babanki
Ta mika mishi,
Baba
Ummu_Sulaim ya shirin exams?
Alhamdulillah Baba.
Allah ya bada sa'a, focus ok
Inshaaa Allah I'll.
Yawwa Allah yayi muku albarka.
Amin Amin ga Mamin.
Mami ma addu'a tayi mata sannan sukai sallama. Tana aje wayar taga message din
Ja'afar
Exams are near
Subject are not clear
Question appear
And answers disappear
Oh! My dear
Don't be fear
Bcoz im here 2 wish u,
All clear!
Have a great exam fest all the best!
Itakam Ja'afar ta rasa yadda zatayi dashi, kullum text uku ne morning, afternoon
and night. Da karfinahi ya dawo to ita bata san yadda zasui ba. Tsaki tayi ta Mike
tayi ta saka hijab sannan ta dauki Jakarta ta fito, kusan duka tare suka fito,
Anty ina Kwana?
Babu yabo babu fallasa tace
Lapiya
Daga haka ta wuce kitchen dan su Atika basu kai ga fito da breakfast ba, Ahmad ne
ya nufo inda take Sanye cikin uniform na school tas dashi, dukda bawai Subay'a ke
mishi wanki ba amma tanada tsafta dan bazaka taba ganin wani abun kazanta a tattare
da ita ba ko yaranta na kullum they appear neat. Cinyar Sulaim ya zauna Yana fadin
Anty morning
Murmushi tayi tana shafa kanshi tareda sake gyara mishi collar Riga tace
How was your night?
Fine
Ya fada Yana grinning ear to ear, kafin ta kuma wata maganar se ga me gayya me aiki
Junaid ya fito waya a kunnenshi ya rike da kafadarshi, Dayan kafadar Yana rataye da
briefcase dinshi se daya hannunshi Yana saka link jikin Orange long sleeve Shirt
dinsa ta kamfanin marks and Spencer, se black trouser na kamfanin tummy Hilfiger,
yayi kyau sosae kamar kada ka barshi ya fita. Yana Zuwa tsakiyar parlon, ya aje
wayar kafin Sulaim ta gaisheshi Subay'a ta fito bayanta Atika na binta da Jeren
warmers, inda yake ta iso tace
Har ka fito?
Kanshi ya gyada yace Yana sake duban wrist watch dinsa baki kirar Penurai, takwas
saura kadan shi kanshi yayi mamakin yadda suka makara, ba akai Ahmad school ba, ita
bata fita aiki ba sannan exams din Sulaim nine ne
Wucewa Zamuyi mun makara.
Kallonshi tayi tace
Kaine ka makara yau bazanje ba saboda open day dinsu Ahmad ne se nine Za'a Fara.
Kanshi ya dan daka yace
It skipped my mind baki daya, Allah ya kiyaye mu zamu tafi , banga Muhammad ba
Ya fada Yana juyawa alamun nema kafin ya maida dubansa ka Sulaim wadda tayi shiru
deep in her own thoughts.
Still on bed, Abincin fa?
Kanshi ya girgixa yace
Zubawa Sulaim taci kafin ta shiga hall.
Kanta ta kawar tace
Tazo ta diba da kanta mana.
Kallon Sulaim yayi wadda take ta kallon Subay'a yace
Tashi ki zuba abinci kyaci a hanya.
Kanta ta girgixa Tana zumbura Baki tace
Na koshi
Kallonta yayi ya tamke fuska yace
Bazaki tashi ki dauka ba se ranki ya baci?
Subay'a tayi murmushi Irin haka take son yana ma wannan yarinyar me shegen tsaurin
ido, Kallonshi Sulaim tayi yadda taga Fuskarshi yasa ta Mike Don babu wargi Balle
tayi musu, kitchen ta shiga ta dakko silver tea flask karami ta tsiyaya plain tea,
Dan karamin flask ta zuba Fried yam da egg sauce sannan ta zuba cikin karamin
basket tabi bayanshi. Seda yayi warming motar kafin ta shiga suka bar gidan
Nayi lefi ne
Ya fada Yana kallon titi.
Ina Kwana
Don tasan shi ne dalilin tambayar , tabe bakinshi yayi yace
Bazan amsa ba, ni kwata kwata baki damu Dani ba, Mintina nawa Nayi saman kanki amma
ko second glance baki bani ba.
Maganar tazo wa Sulaim a bazata hakan yasa ta dago idonta tana kallonshi wani Irin
abu taji Yana fuzgar ta like a magnetic attraction, sauke idonta tayi ta kasa
fassara abinda yake nufi _bata damu dashi ba ita kuwa ita ta damu dashi_ a
hankali taji zuciyrta tana budewa wani Irin unimaginable feeling taji ya baibayeta
har ta kasa boye murmushin din da takeyi. Kanshi ya girgixa ya kara fadin
Allah sarki kuma gata na, bazaa bani amsa ba kenan?
Bakinta ta turo kadan tace
Nima bakace ya shirin exams ba.
Dariya yayi yace
OK ramawa kikayi kenan? To we're even yanzun. Have you read well? Ko yanzun akawo
paper?
Kanta ta gyada tace
Ready for the battle.
Kallonta yayi a ranshi Yana tunanin har wanne Lokaci ya dauka kafin ya sanar da
Sulaimi halin da yake ciki? Karfa wani Daga gefe yazo ya dauke abinda yake ta
tattalawa kanshi. A kofar Faculty yayi parking, kallonshi tayi shima kallonta yake
cikin ido yana murmushi itama se ta samu kanta da sakar mishi tattausan murmushi
kafin ta bude kofar se yace
Sulaim
Juyowa tayi har lokancin bakinta a bude yake ga wushiryar ta a bayyane haka dimples
dinta dake both sides sun lotsa, tamkar ana fuzgarshi haka ya daga hannunshi se
yayi saurin saukewa don yasan hakan ba girmanshi bane. Kallonshi take ta langwabar
da Kai tace
Yaya
Tamkar ruwan sanyi haka kiran da tayi mishi ya isa gareshi, dagowa yayi yace
All the best, idan kin fito Kada ki tafi se five Zamu je gida, kizo office ki huta
sannan ki karanta na gobe OK?
Kanta ta gyada daga haka ta rufe mishi kofar cikin nitsuwa ta taka kofar venue din
tana jinta tamkar tana shawagi ne cikin gajimare, wani Irin farin ciki taji da
nishadi wanda ta dade bata ji makamancin irinsa ba. Shima hakan ce a bangarenashi
Don seda yaga ta zauna kafin ya shafa kanshi ya wuce murmushi fal Fuskarshi.
Tana nan Zaune Khulthum ta iso ta zauna gefenta amma saboda yadda Sulaim hankalinta
ya tafi akan maganganun Junaid yasa ko daya Bata fahimci zuwan Khulthum ba harseda
ta dafa ta kafin ta kalleta, itama Khulthum din kallonta tayi tace
Ke tunanin me kike
Ita kanta bata san ta saki wani Irin murmushi ba seda ta kalla facial expression
din Khulthum kafin ta saki murmushi tace
Sannunki, ina Mama?
Tabe bakinta tayi tace
Mama na gida, Ina Yaya?
Wani smile ta saki wanda yake straight deep down from the ventricle tace
Office.
Sosae Khulthum ta ke kallonta kafin tace
Anya Yaya ne kuwa?
Me fa?
Kanta ta girgixa tace
Back to real business muyi revising.
Haka sukai ta brainstorming har invigilators suka shigo aka Fara, tunda aka ce
start Sulaim ta dukufa abinta tana ta rubutu se time to time Tana sakin murmushi,
can tana last question taji sassanyan kamshin Fierce cologne by Abercrombie and
Fitch ko bata dago ba tasan duk duniya mutum daya take jin wannan kamshin a
jikinshi kuma shi ne _Junaid_ a hankali tamkar me tsoro ta dago idonta shi ne kuwa
yana tsaye kyem a kanta sede Fuskarshi babu walwala he's not the Junaid she left a
mota wannan examination officer ne kuma senior lecturer dinta. A hankali ya motsa
bakinsa ya furta
Stop staring, kiyi rubutu.
Bakinta ta turo mishi ta maida kanta kasa amma ta kasa cigaba da rubutun saboda
yadda taji ya cika gurin gashi bugun zuciyarta is increasing its pace. Ganin haka
yasa ya bar gurin kafin daga bisani ya fice a hall din baki daya. Ana cewa pens up
ta aje nata akai tattara suka fito baki dayansu, su hudu suka tsaya gefen hall din
kowa na fadar albarkacin bakinsa, exams dai babu laifi ta yi dadi sede addu'a.
Khairi da Khulthum suka tafi hostel don Khulthum zata shiga toilet yayinda Aimana
da Sulaim suka nufi office din Junaid, baya nan se messenger dinsa ne ya bude mata,
Kan sofas din suka zauna Aimana tana tabin office din da kallo tace
Office din waye?
Gira ta daga tace
Easy mana, office din Yaya ne
Yaya dai Yaya dai every time, dama nan yake aiki?
Dariya Sulaim tayi wai Yaya dai all the time itafa bata jin wani fadar Junaid da
take amma se suce wai common saying dinta kenan.
Eh he's a lecturer here
Kai ta gyada tana admiring gurin kafin kuma ta gyara zama tace
Sulaim
Kallonta Sulaim tayi ta tsaya da danna wayarta tace
Yaya?
Ina wannan brother nawa da ya taba Zuwa daukarmu Yaya Nu'uman?
Ta fada Tana nuna mata hoton Nu'uman a wayarta, karba tayi ta kalleshi, yes she
remembers him, wannan shiru shirun shi ne kadai abinda zata fada a kanshi.
Na tuna shi.
Ya min maganar Yana sonki.....
So?!
Sulaim ta fada Tana zaro ido waje, dariya Aimana tayi tace
Keep calm and chill, nace mishi Kinada Yaya.
Da confusion tace
Yaya kuma?
Kafadar ta ta rike tace
Sulaim kenan, wannan Yayan da kike fada is not just an ordinary Yaya akwai wani abu
karkashin zuciyarki, tell me kina sonshi ne.
Shiru Sulaim tayi ta kurawa Aimana idanu tamkar amsar tamabayar tana Kan fuskarta
ne, baki daya se ta shiga cikin dilemma she's confuse ba kadan ba, ta yaya zaace
tana son Yaya Junaid, Yaya fa mijin Subay'a no way he's just an important person
cikin Rayuwarta.
Yaya, is an important mutum a rayuwata, Mummy da Daddy suka rikeshi har ya fara
aiki, Kinsan ni am an orphan banda uwa banda uba, gidansu ake riko na. Yanzun Yaya
shi ne komi nawa kinga dole Nayi maganarshi. Kinyi misunderstanding abin.
With a pity face tace
Ayya sorry for the loss, Allah ya jikansu Amma zancen Yaya ki tuhumu kanki.
Kafin ta bata amsa Sega Yaya ya shigo shida Ridwan. Mikewa tayi ta nufi inda yake
yayinda Aimana take mamakin dama Dr Junaid shi ne Yaya? Haba no wonder Sulaim ta
falling. Gaisheshi Aimana tayi fuska a sake ya amsa Yana tambayarta exams, itama ta
bashi amsa kafin ya maida dukkan hankalinshi kan sarauniyar tashi dake gaisawa da
Ridwan
Amarya na tambayarki Bakixo kin ganmu ba.
Dan murmushi tayi tace
Yaya bai kawo ni ba.
Da sauri Junaid ya daga hannunshi sama in surrender yace
Count me out of maganar nan, Ke Yaushe kika ce zakije tsakaninki da Allah?
Turo bakinta tayi tare da jujjuyawa hakan yasa Junaid dafe kanshi tace
Ka manta ranar.
Baki bude Junaid yace
Yaushe kika koyi sharri ke kuwa.
Dariya sosae sukai Harda Aimana dake gefe, Ridwan ya dauki abinda ya shigo dashi ya
fice yana ta dariya shi kawai yana ganin Sulaim ma tana son Junaid din, shi kanshi
ya rasa dalilin Junaid na kin fadawa yarinyar yana sonta amma zai kara tuntubar shi
akan inda aka Kwana.
Kan sofar ya zauna Yana facing dinsu yana ma Aimana tambayoyi kafin ya maida
dubansa kan Sulaim wadda ta bata rai kamar ba ita take dariya ba, a hankali ya
dubeta yace
Me nayi kuma?
Bakace ya exams ba
A'a sau nawa zan fada ne? Ya exams din to
Cikin nitsuwa tace
Alhamdulillah!
Tashi yayi yace
Kin Faye damuwa Walhi, Bari nayi aikin gabana, Bari kuci abinci ko?
Kanta ta gyada mishi ya koma seat dinshi ya fara aiki Bayan ya bada order. Aimana
ta kalli Sulaimi tayi kasa da murya Tace
What a perfect match!
Me?
Keda Yaya mana, Kuna son junanku Amma is like kamar baku fahimta ba.
Dan Allah Kiyi shiru Kada yaji, nace miki he's very important cikin rayuwata!
Waye ya yadda da sulaim?
Shatuuu ♥️
*MACE A YAU*
17 nd 18
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
A Kwana a tashi babu wuya gurin ubangiji, ranaku gudu suke suna shudewa tare da
kara kusanta mu da kabarinmu, fata daya Allah ya sa mu cika da imani. Exams ana
tayi har yaxo saura daya su gama , ranar Friday sun fito Daga Logic and philosophy
paper, paper rana ce hakan yasa suna fitowa Junaid Yana jiranta a mota. Ciki ta
shiga fuskarta babu annuri ko digo dama kuma yaji a bakin invigilators suna fadin
exams din tayi wuya. Tana zama ya fara driving kafin ya kalleta don har lokancin ba
tayi mishi magana ba yace
Ya exams din?
Dama abinda take jira kenan ta Fara kuka se yayi shiru Yana Dana sanin yin magana,
ta kusan minti biyar tanayi bai hanata ba Sede bawai yana jin dadin sauraran kukan
nata bane, seda ta share hawayenta kafin yace
Kiyi hakuri kinji, you will make it.
Kanta ta gyada se taji tsoron ta kusan kashi hamsin ya wuce taji ta samu hope da
courage.
Yaya
Na'am
Ya fada ba tareda ya kalleta ba.
Gobe Inshaaa Allah wajen nine zamuje karatu ni da friends dina.
Juyowa yayi ya dubeta idonta har yayi Dan ja saboda kukan da tayi,
A'a
Kai Yaya
Kice musu su zo nan gida kuyi tare hankalina zaifi kwanciya.
Kanta ta gyada tace
Tohm.
Daga haka sukai shiru ya cigaba da tukin shi Yana tunanin sakon Mami da safe akan
ranar laraba yayiwa Sulaim booking flight ta tafi Kebbi gurin dangin Mami da Anty
zahra. Shi a so samunshi ne tayi zamanta Tunda hutun Baifi 2 weeks ba amma Tunda
Mami tace haka zaayi bai isa canjawa ba. A wani Pizza joint yayi parking ya shiga
ciki ya batta a mota, da Wannan ta kirasu Khulthum ta fada musu yadda Yaya yace
Dama Aimana ce suke tunanin ba Za'a barta ba to itama ba'a samu matsala ba. Tana
aje wayar daga kiran Khairi call din Ja'afar ya shigo.... Dam! Taji gabanta ya fadi
Yaushe rabon taga wannan sunan ya kirata har ta manta, kamar bazata dauka ba se
kawai taga bari taji me zaice mata. Tana picking wannan muryar tashi me dadi yace
Susu!
Se ta lumshe idonta saboda yadda sunan ya ratsa ilahirin jikinta, its been a while
da aka kirata da hakan, so she missed been addressed as Susu.
Nasan kina jina, nasan kinga messages dina Baki daya, this time around I'm ready
Sulaim, bazan Kara miki wasa da zuciyarki ba, I promise you only one more chance
_Baby give me one more chance to be the one to hold your hands, may be we could
learn to love again...._
Shiru tayi words suna sinking cikin jikinta tareda sake auna su cikin kwakwalwar
kanta, for how many times Ja'afar zaina mata fake promises, kullum maganarshi one
more chance. Anya ba wasa take da rayuwar ta ba? Anya Ja'afar is the right person?
Sulaim please
Taji ya katse mata tunaninta, hakan yasa ta bude idonta har lokancin Junaid bai
dawo ba tace
Na gaji Yaya Ja'afar bakasan darajar Abinda kake so ba
Sweetm ni ne fa, your Luff ko kin manta?
Dan murmushin takaici tayi wai ta manta, sede ta bude Baki da niyyar magana Junaid
ya bude kofar ya shigo hakan yasa ta kasa magana shi kuma Junaid Yana zama yace
Yi hakuri na barki ke daya, I met an old friend.
Kanta ta gyada tace
Uhm.
Dake hijab ne jikinta daya kalleta baiga wayar ba don haka ya cigaba da fadin
Tare mukai NSUKKA dashi Yana da kirki, se yau Allah yayi muka hadu.
Dama hakane kam
Ta fada Tana zare wayar daga kunnenta saboda ba zata iya cigaba da wayar a gabanshi
ba. Aikuwa Ja'afar ya dinga kira tana katsewa se taji Junaid yace
Waye ke kiranki?
Kallonshi tayi taga hankalinshi Yana kan titi tace
Yaya Ja'afar!
A bazata maganar tazo mishi hakan yasa yayi wani juyi ya kalleta kanta a kasa taki
dago idonta ta kalleshi, se yaji duka ilahirin jikinshi yayi sanyi saboda ya
tabbatar Ja'afar baya tareda Sulaim Yaushe suka hade Yana gefe
Yaya!
Sulaim ta kwalla kara saboda motar dake gabansu amma dukda haka Seda ya buga mishi
kuma bugun ba sosae bane ba inda Allah ya taimaka, Gaba daya ilahirin jikinta rawa
yake tsabar yadda ta tsorata, se ta Fara kuka, bai bi ta kanta ba yayi parking
gefen titi ya fito, shima wanda aka bugawar ya fito mutane har Sun taru, ana maida
yadda akai.
Fuskarta a rufe da tafukan hannayenta taji an kwankwasa mata kofar side din da
take, dago idonta tayi wanda har ya canza kala saboda firgici, da idanun ta bishi
da kallo kana kallonshi basai anyi maka bayani ba ya hada jini da larabawa, fari ne
sosae tamkar ka taba shi jini ya fito, yana da tsayi sede bayada kiba ya hadu
karshe babu karya. Cikin turanci me tsafta babu blonders yace
Ke kyakyawa ce, can I please have your digits.
Yadda ya tsare ta da ido se taji ba zata iya hanashi ba, hakan yasa ta mika mishi
hannunta shi kuma ya bata wayarshi ta saka mishi numbers din ta mika mishi tace
Sulaim
Lumshe idonsa yayi yace
What a nice name baby. I'm Salim
Daidai bude motar da shigowar Junaid idanunshi bai sauka akan kowa ba se akan
Salim, wani Irin mummunar faduwar gaba ce ta ziyarce shi Lokaci guda, bai gama
dawowa daga wancan shock din ba gashi yazo ya tarar da wani, shikam wanne irin abu
ne yake faruwa dashi daga wannan se wannan kada yarinyar nan ta fasa mishi
zuciyarshi.
Sulaim Bata Lura da halin da Junaid yake ciki ba amma gaban ta se faduwa yake,
Salim ya juya ta side din da Junaid yake ya bashi hannu tareda fadin
Barka da Rana.
Batareda ya kalleshi ba yace
Barka ka dai.
Daga haka ya sakar mishi hannu ya bawa motar key, tamkar a bye pass haka ya dinga
sharara gudu Fuskarshi tamau tamkar bai taba dariya ba, itakuma taki dagowa bare
taga yanayinshi. A haka suka isa gida yana parking yace
Get out!
Da sauri ta kalleshi idanunta a waje Tana son tabbatar da Junaid ne ya fadi hakan?
Shi dinne yana kallonta da idanunshi yayi jawur wanda ya Kara tsoratar da ita
Are you deaf? Get out of my car stupid kawai.
Maimakon tayi yadda yace se hawaye ya fara zubar mata Daga idanu, ita me tayi
mishi, ita tace kada ya kalli gabanshi while driving zai zo ya huce a kanta, shima
se ya tsaya Yana kallon ta, gaba daya se yaji duka hankalinshi ya tashi why will he
shout at her? Bakin hijab dinta tasa ta goge fuskarta sannan ta bude murfin motar
ta fito, stupid kwakwalwar ta ta maimaita mata, se hawaye suka kara sakko mata a
kunci. Dama Batayi expecting kowa ba a parlon haka kuwa babu kowa Don haka straight
dakinta ta nufa tana shiga ta maida kofar ta rufe