Showing 63001 words to 66000 words out of 121650 words
kaya Tana mayarwa a
karshe ta samu wani Lace off white an mishi ratsin pink dinkin gown me kyau ta
saka. Ita yanzun ta Riga ta sawa ranta Duk yadda za'ai Duk me zai faru da izinin
Allah se ta karkato hankalin Junaid kanta Koda kuwa duniya zata zageta amma a
ganinta Lokaci yayi da zata kwatar wa kanta 'yanci, ta gaji da yadda kullum
zuciyarta take wahalar tuwa akan maza a karshe ta tashi da heartbreak, wannan karan
tabbas kida zai canza.
Kusan Lokaci guda suka fito, shi yayi changing Zuwa mark and Spencer trousers Baki
se tummy Hilfiger top ash, hannunsa ya daura bakin agogo wanda ya zauna daidai akan
hannun nashi. Yayi kyau na fitina har Khulthum taji inama shi din nata ne da sun
fasa fitar nan don tasan dole Za'a kalleshi, ita kuma Abinda bazata iya
withstanding ba kenan.
Are you set?
Ya fada Yana kare mata kallo, a ranshi Yana tasbihi ga Allah saboda kyakykyawar
halittar da yayiwa abu mafi soyuwa cikin zuciyar shi, son sulaim ya mishi shigar ba
zata, ya kainanye shi bashida katabis se yadda tayi dashi. murmushi tayi tace
Eh.
Martani ya mayar mata wanda seda ta lumshe idonta saboda yadda murmushin ya wanke
mata zuciya.
Je ki tayar da motar gani nan.
Kanta ta gyada ta fice yayinda ya nufi parlour Subay'a don yaji shigowarta yana
dakinshi. Tana zaune ta zabga tagumi deep in thought, kana kallon ta kasan akwai
abinda take so amma ta kasa furtawa. Sallamarshi yasa tayi firgigit tare da
dubanshi ta ganshi da alamun fita zaiyi saboda shigar jikinshi.
Zan kai Sulaim Asibiti.
Bata da lapiya?
Ta tambaya Tana tsatsare shi da ido tana ganin hakan zai girgiza shi, murmushi yayi
yace
Eh.
Banga alama ba
Ta bashi amsa Tana duban idanunshi, shima kallonta yayi yace
Ke baki gani ba, ni na gani.
Daga haka ya juya ya fice ya barta a gurin Tana bacin rai, ita yanzun Sulaim Bata
gabanta abinda yake gabanta gobe shi ne damuwarta a hankali zata dawo kanta.
Tana hangoshi ta matsa mishi drivers side ya shiga sannan suka fita, zuciyoyinsu
cike da farin ciki da nishadi, suna jin tamkar su biyu kadai suka rage cikin
duniyar. Dukda bawai magana suke ba amma yanayin kawai ya isa ya nutsar da zuciya,
balle su da suka kusan shafe wata basu tare ai wannan ranar is memorable. Duk
tunaninta asibiti zasuje Amma se taga sunyi hanyar grand square, dagowa tayi ta
dubeshi, kallonta yake yace
Ba kan ya daina ciwo ba? Dama ba kukan an ganni bane?
Dagowa tayi ta turo Baki Cikeda shagwaba ta Harare shi. Daidai lokacin yayi parking
kawai se ya tsaya Yana murmushi yace
Sulaim like serious harara ta kikayi?
Da sauri ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana murmushi. Kallonta ya kuma Yi
yana ganin inama kada ta Kara kuka saboda yadda sanyi ke ratsa shi ganin dariyar da
takeyi.
Muje.
Ya furta cikin wata husky voice wadda ta ratsa ta har cikin kanta, ta bude side
dinta ta fito Tana sake gyara zaman Veil dinta.
Tamkar couples haka suka jera ciki fuskokinsu kawai ka kalla will tell you how
happy they are been by each others company.
*We could build up a universe, right here all the world could disappear would it
notice*
Ice-cream kawai yayi mata order, triple treat chocolate, vanilla da strawberry
kowanne scoop dinshi cikin cup, Mika mata yayi sannan ya zauna opposite dinta
tareda tsare ta da ido wanda suke Kara ninka soyayyar shi cikin zuciyar ta.
Hannunshi ya mata alaman ta sha. Babu musu tasa spoon din Cikeda nutsuwa ta fara
kaiwa bakinta, Duk wani move dinta akan idanunshi amma a zahiri wayarshi yake
dubawa kafin kuma ya shiga amsa call. Yana dawowa ta mika mishi cup din da sauran
ice-cream a ciki tace
Gashi Kasha.
Kanshi ya girgixa yace
A'a wannan maganin Ciwon Kai ne, kinga ni kuma lapiyata kalau ko?
Ya fada Yana kashe mata ido wanda yasa zuciyar ta harbawa da sauri, a ranta tana
tunanin me Junaid ke nufi da ita ne? So yake ya fasa mata zuciya?.
Seda ta gama sannan ya kaita wani Pizza joint dake kan new hospital road ya kaita
yayi mata order pizza slice biyu, Dakyar ta cinye Daga nan yace mata
Ina kike son Zuwa kuma?
Shiru tayi tana tunani kafin tace
Cinema!
Kanshi ya shafa yace
Shi ne inda kike son Zuwa?
Kanta ta gyada tana murmushi, agogon hannunsa ya kalla lokacin hudu tayi hakan yasa
ya tsaya yayi sallah batace zatayi ba shima bai ce mata ba don Abinda yayi
believing ba yadda za'ai ka cewa mace tayi sallah kilan tana off.
A cinema shoprite sukaje ya tambayeta na wanne kasa tace India. Can sukaje bayan ya
karba mata popcorn se tace
Kai kuma fa?
A'a na Ciwon Kai ne wannan ai, Ke kadai zaki ci abinki.
Murmushi tayi ta cigaba da bin bayanshi har suka karba ticket ana shooting
Goliyinka Ram Leela Ras Leela. Bata taba kallon film din ba amma tasan famous wakar
film din, suna ta kallo ko ita kadai takeyi don shi hankalinshi Yana kan wayarshi
seda aka kusa yaji alamar sheahekar kuka, da sauri yace
Oh God! Meye kuma na kukan?
Hannunta tasa ta goge fuskarta tace
Sun kashe kansu fa?
Su waye?
Ram da Leela na film din.
Tsaki yayi yace
Tashi mu tafi.
Mikewa tayi ta bi bayanshi ba tareda ta ce komai ba, gaba daya se yaji ranshi ya
baci if at all yasan cewar ranta zai baci Wallahi bazata kalla film din ba. Duk
kokarin ganin ya faranta mata rai haka kurum wani fiction yazo ya bata mishi komai.
Basu suka koma gida ba se bayan sallar ishai seda ya tabbatar ta samu farin cikin
da yake son ganinta a ciki, babu ko digon damuwa cikin kwayar idanunta kafin suka
nufi gida amma abin mamaki duk wannan abin ya kasa Furta "L" word din.
A parlor Subay'a na zaune da Ahmad se Muhammad da ya sata a gaba yana kukan shi
Anty zaije, Tun tana lallashinshi har ranta ya baci ta daddake shi, nan Kuwa ya
kara Sautin kukanshi, abin ya dameta ga Junaid bai dawo ba, ga tsanar sulaim dake
kara nunkuwa cikin zuciyar ta, ga tsoron yadda zata tunkareshi da maganar nan. A
haka suka shigo gidan, rigerigen taro Sulaim Ahmad da Muhammad sukai, ta tsugunna
ta rungumesu jikinta tareda daga Muhammad sama ya fara dariya sannan ta riko hannun
Ahmad zuwa cikin parlour. Zama tayi ta dubi Subay'a dake kallonta tace
Kun dawo lapiya?
Lapiya.
Ta bata amsa Tana bin bayan Junaid, tabe Baki tayi ta dauki yaran zuwa dakinta,
seda ta shirya su tsaf kafin ta shirya itama don bacci amma taji an turo kofar,
fitila ta kunna da mamakim ganin Subay'a tsaye Tana kallonta, itama kallanta tayi
batace mata uffan ba, se dan kanta tace
Yarana fa.
Gasu
Sulaim ta bata amsa, aikuwa ta karaso da nufin daukar Muhammad Yana bude ido ya
fara ihun shi gurin Anty zai Kwana haka Ahmad dole ta hakura ta koma gurin Junaid
wanda tuni yana gado yana aiki da system gefenshi ruwa ne kan table Yana Sha time
to time tareda murmushin tuno Outing dinsu, se yakejin tamkar they went for a date.
Gefenshi ta zauna tareda mika mishi envelope tace
Papa gashi.
Ture system din yayi ya bude envelope din, visa dinta ce ta zuwa Cyprus se wasu
takaddu na makarantar da zataje masters din. Glasses dinshi ya cire yace......
Shatuuu ♥️
*MACE A YAU*
31 nd 32
Double page
✍Shatuuu♥
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
Zare glasses din idonsa yayi ya aje papers din kan table din sannan ya dago ya aje
maida hankalinshi kanta, ya kusan minti biyar Yana kallonta tareda nazarin yanayin
da take ciki wanda hakan Ke Kara mata uneasiness a tattare da ita, kafin yace
Explain yourself
Dago idonta tayi rashin gaskiya da tsoro karara a idonta, tamkar ba Subay'a ba haka
ta koma.
Hajiya ta aiko min jiya akan gobe da safe zamu wuce Abuja mu tashi zuwa Cyprus. Two
years ne program din, zan na dawowa every six months. Kuma ni, Sulma, ya Suhaila da
Yaya Salima Zamu tafi.
Ta fada Tana kawar da kanta , kanshi ya girgixa yana Kara mamakin Subay'a, da gaske
ita hankalinta ya bata ta tafi ta barsu kenan. Ya dade bakinshi a rufe yana harhado
kalamun da suka fi sauki ya mata magana dasu domin already cikin ranshi ya fara
baci, baisan me Subay'a ke nufi dashi ba, baisan me ta dauki aure ba gaba daya.
Idan kika tafi, a hannun wa kika barwa ni da su Ahmad? Ko marayu kike son mu zama?
Ya fada Yana kara kallonta, inda baisan wacece Subay'a ba da zaice tana da gaskiya
Amma Subay'a crook ce, kasa bashi amsa tayi ita dama Abinda bata so kenan a Junaid
tambaya, idan ya tsareka da ido ko kana da gaskiya se ka duburburce hakan yasa
indai zasui irin wannan maganar tafi son se ta shirya kafin ta sameshi. To Amma yau
abin is different and seems difficult, kuma tun safe take harhada abubuwa da zata
fada mishi.
Bakida amsa right? Kinsan dalilin da yasa nake daga miki kafa akan abubuwan da
kikeyi?
Bai jira amsarta ba ya cigaba da fadin
Saboda wasu lokutan tursasa ki ake akan Kiyi abu, ke kuma babu yadda zakiyi tunda
haka kika tashi kika tarar anayi a gidanku. Wannan karan nasan kin raina ni Baki
dauke ni a bakin komai ba don ina tantamar idan kinsan me kalmar aure take nufi, me
kuma ta kunsa.......
Da sauri ta katse shi da fadin
Nace maka fa yau suka kawo min, bansan da maganar ba kwatakwata.
Dago kanshi yayi yana dubanta Cikeda mamaki yace
Se Yaushe xaki daina karya a rayuwarki? Duk Abinda kike babu Wanda bansani ba,
maganar masters dinku ke kika Fara bawa Hajiya shawara akan kuje Cyprus ko ba haka
akai ba? itama ta biyeku tayi. Saboda kin raina ni for more than four months da
maganar se ana gobe zaku tashi sannan zaki fada min? Kece mijin ko ni?
Shiru yayi ya dafe kanshi saboda zuwa lokacin ranshi ya gama baci, mijin Sulma ya
kirashi ya sanar dashi abinda ya faru, tun lokacin yake jiran ta fada mishi don
yayi niyyar barinta inda ta fada mishi a lokacin amma serves her right, don yana
son nuna mata wannan karan tayi karya shike aurenta ba ita ba.
Papa Dan Allah na amshi laifi na, amma kar ka hanani tafiya asarar kudi zaayi kuma
hajiya.....
Shi yasa bazaku taba zama gidan miji ba, ni Nake aurenki ba hajiya ba, a yanzun
I've every right over hajiya a kanki, zancen asara I promise to refund abinda ta
kashe buri na kawai ki zauna a gidanki.
Kanta ta girgixa tace
Papa please
Murmushin takaici yayi ya zame Daga Zaunen da yake ya kwanta tare da juya mata baya
yace
Idan kin tashi fita Kunna min AC, ki sani in har nine mijin, ni na aureki, ni Allah
yace na shygabance ki ban amince ba amma zaki iya tafiya sede.....
Bai karasa ba ya saki murmushi. Itama Ta sani Tunda ya fadi haka to bazai sake
magana ba, to zaman me zatayi? Ita tana cikin tsaka me wuya Don kuwa Hajiya tayi
rantsuwa akan kowa se Yaje yanzun ita kadai ce matsala haka ta mike jikinta a
sanyaye ta fita zuwa dakinta. Ta dade a tsaye Tana kallon kayan da tayi parking
cikin trolleys, kayansu Ahmad da ta hada musu. Zama tayi gefen kujera tana tunano
zancen su itada Junaid tasan gaskiya ya fada bata taba zama matar kirki ba ko uwar
arziki, ita a duniya aikinta shi ne priority dinta not her family amma tasan
tafiyar ta Zuwa Cyprus dole ce, tasan halinshi da ta tafi zuciyarshi zata huce babu
Abinda zai iya mata Don sabonta ne ya hanata Abu ta tsallake amma wani bari na
zuciyar ta gargadi yake mata da babbar murya akan Kada ta tafi.
Junaid Na kwance idanunshi rub a rufe amma ba bacci yake ba, haushin kanshi yake ji
yana jin duk Abinda Subay'a takeyi kamar dukka laifinshi ne, ya tuna yadda Tun yana
nemanta Mami ta nuna kin amincewa saboda ance uwarta tana juya ubanta Amma lokacin
ba karamin so yake ma Subay'a ba haka Daddy Aminu yayi fadi tashin ganin kowa ya
amince sunyi aure saboda yana yawan fadawa Junaid "Tarbiyyar da nayi maka, inason
ka zama tsayayyen namiji wanda son mace bazai Kada shi ba, ya zamana kai ke ruling
gidanka ba matarka ba" amma gashi yayi failing to the extreme kuwa. Yasan Matar da
ya aura, mutane ne dukkansu masu son duniya hakan yasa duk tafiyar da zaiyi zai
tafi da ita don ta kashe kishirwar da takeji amma bai tsira ba, shi kuma in har ta
tafi se yayi mata hukuncin da yasan har ta mutu bazata taba mantawa ba.
Washegari, babu Wanda ya fito a cikin su biyun, Sulaim ce kadai take ta kokarin
shirya su Ahmad da kanta zuwa makaranta. Tana gama shiryasu tace
Kuje ku gaida Mimi da Papa.
Suka fice ita kuma ta karasa gyara dakin ta fitar da kayan wanki sannan ta hada
abinci Se Gasu sun fito dukkansu har Junaid da Subay'a, gaisheku tayi sannan suka
Fara cin abincin. Suna gamawa Junaid ya koma daki don ya dakko key da briefcase su
tafi, itakam Subay'a zama tayi ta janyo yaran ta rungume wannan tayi kissing wancan
idanunta taf da kwalla. Sulaim ce ta Fara fitowa suka hada ido da Subay'a kowacce
seda gabanta ya fadi, sulaim ta Fara dauke kanta yayinda Subay'a ta kura mata ido
zuciyarta na fada mata tafiya zatayi ta bar mijinta da yarinyar nan? Bayan Abinda
take zargi tsakaninsu. Se tayi murmushi kawai saboda ta tuna waye Junaid, meye
matsayinta a zuciyarshi.
Yana fitowa ya mikawa Sulaim briefcase dinshi da key din motar yace
Ku jirani gani nan Zuwa.
Amsa tayi ta ja yaran waje yayinda ya dubi Subay'a yace mata
Zan wuce office, na bar miki kudi akan decoder na cefane, bazaki je office ba?
Kanta ta girgixa ta taso ta rungumeshi tare da furta
I'm so sorry and I love you.
Shima rungumeta yayi Yana murmushi yace
Is ok ya wuce, I've to go.
Sakinshi tayi Bayan ta bashi peck a kumatu ya fice saboda kukanta na karyar mishi
da zuciya. Yana Zuwa suka wuce, kamar ko da Yaushe seda suka kai su Ahmad school
kafin suka wuce,
Sulaim
Ya fada cikin muryar daukar hankali, Dago kanta tayi ta dubeshi tace
Na'am.
Kallonta yayi Yana tantamar Abinda zai fada mata amma yana ganin is high time ya
kamata ya fada mata. Jin yayi shiru yasa ta maida kanta gefe Sede abinda kunnuwanta
suka jiyo mata yasa cikin hanzari ta dubeshi daidai lokacin da yayi parking don
tabbatar da furucin daga bakinshi ne ko kuwa, kallonshi take kamar yadda yake
kallonta, Sede kowa da Irin wanda ke cikin idanunshi. idanunta sunyi haske gashi ta
bude su wanda hakan yasa yaji ilahirin jikinshi ya mutu, a hankali ya bude Baki
yace
Ba se kin amsa ni yanzun ba, I want to you to think over it. Amma ki dauke
kasancewa ta cousin dinki ki dauka ni Baki sanni ba kawai na ganki ne nace *INA
SONKI, ZAKI AURENI?*
Da sauri ta kalleshi mamaki fal fuskarta, a take wani murmushi ya kwace mata,
idanunta cikin nashi tana jin wani nishadi na daukarta se kuma ta sauke idonta a
hankali kafin ta lalubi murfin motar ta bude ta fice dukkan jikinta a sanyaye. Yaya
Yana sonta? Tambayarta yake zata aureshi? Yana son ta completing puzzle din da ya
kasa? farin ciki se take jin tsoro Yana shigar ta, Me yasa bata amsa mishi ba.
Tafiya take a hankali Cikeda nutsuwa ta isa class zuciyarta cunkushe haka kanta
yayi mata nauyi Tana son tayi tunanin dalilin da zaice yana sonta.
Can bayan class ta zauna ita daya saboda yau bata da raayin jin lecture din gaba
daya, Tana nan Zaune taga shigowar Aimana hakan yasa tayi saurin Dukar da kanta dan
kar ta ganta, Seda ta zauna sannan ta dago kanta Sega Khairi sun shigo itada
roommate dinta wata Amina, bata ga shigowar Khulthum ba kawai ta hango ta acan gefe
itada wata Maimuna suna hira. Hakan ya tabbatar mata Khulthum tayi nisa Tunda ta
Fara ma'amula da yarinyar saboda tayi kaurin suna cikin faculty akan iskanci kuma
yarinyar ta samu kyakyawan backing na lecturers din da take bi, to dama idan Khairi
na basu labarin yadda yarinyar take abu a hostel se Khulthum tana kareta OK gashi
yanzun tayi joining dinsu.
Sagay ne dasu kuma very strict mutumin yake Tunda ya shigo class din yayi tsit,
itama shiru tayi hankalinta Baki daya baya cikin class din tayi nisa sosae gurin
tunani tabbas Tasan tana son Junaid so kwaya daya tak nashi ne amma bata taba
tunanin he feels the same way ba, bata taba wannan tunanin ba. Ji tayi an buga
table din dake gabanta hakan yasa ta dago da sauri, Sagay ne a gabanta ita bata san
yazo ba ma kwatakwata ba she was deep in thought. Cikin karaji yace
Stand up and get out of my class !
Babu musu ta mike bata ma ce mishi ko yayi hakuri ba saboda tasan shi office din
Junaid, suna yawan haduwa. Jakarta ta dauka ta fice baki daya daga class din sede
tana fitowa sukai kicibis da Junaid wanda yake kokarin wucewa. Tsayawa tayi kanta a
kasa gabanta nata faduwa, shima kallonta yayi yace
Ina zakije?
Kanta ta girgixa tace
Koro ni yayi?
Me kika Yi?
To anan tayi shiru don batasan me zatace mishi ba, bata concentrating ko kuwa? Ajin
ya nufa hakan yasa tabi bayanshi suna zuwa yayi knocking dan ya Riga ya kulle
kofar. Budewa Junaid yayi ya tako har gaban Me Sagay, da sauri ya sakko ya mikawa
Junaid hannu suka gaisa Cikeda girmamawa don he seniors him. Kallon kofar yayi ya
yiwa Sulaim alamar ta shigo, aikuwa ta shigo tayi kicinkicin da fuska, kallonta
Junaid yayi yace
I'm sorry na shigar maka abin class dinka.
Kanshi ya girgixa yace
Ba damuwa sir, she wasn't concentrating that's why na Kore ta amma taje ta zauna.
Kallon Sulaim yayi yace
Go and sit down.
Kanta ta gyada tace
Thank you sir
Batareda ta kalli Junaid ba ta wuce gefen Aimana ta zauna amma da ta Fara kokarin
concentrating se ta koma tunanin Junaid haka period din ta kare bata tsinci komai
ba. Ita a karan kanta tayi tunanin idan Junaid yace yana sonta wanne irin farin
ciki zata shiga amma se gashi tsoro ya hanata sakat, ta kuma rasa tsoron da take
amma tana jin kada shima ayi irin ta sauran mazan. Babu yadda Aimana batayi ba akan
taji abinda Ke damun Sulaim din amma fir taki, suna nan Zaune junairu ya kirata,
seda taji gabanta ya fadi kamar bazata dauka ba se ta dauka ta kasa magana se shi
ne yace
Kizo office Ina jiranki.
Sauke wayar tayi tace da
Kuzo muje office din Yaya.
Mikewa sukai dama tuntuni Khairi ke mitar dama Dr Junaid ne Yayan amma ita ba'a
fada mata ba. Dariya kawai Sulaim tayi tace
Gashi yanzun kin sani.
Suna tafe Aimana tace
Wai ni Khairi ya akai kika san tsakanin Khulthum