Showing 69001 words to 72000 words out of 121650 words
safe jirginsu ya sauka Don haka suna zuwa suka Yi 'yan gyare gyare suka
kwanta dan huce gajiya amma Subay'a se juyi kawai take ta kasa baccin, hankalinta
ya tafi akan Junaid, ko me zai yi bayan ya tarar ta tafi, ko ina yaranta suke. Haka
dai tayi tayi har bacci ya samu ya dauketa. Se dare suka fita dan ganin gari, to a
Wannan ne ma zamu ce ta saki jikinta Don garin ya burgeta Sosae da sosae, se eleven
suka dawo nan suka baje a parlor suka ci abincin kowacce ta kira mijinta ganin haka
yasa Subay'a sulalaewa zuwa dakinta Don nufin kiran Junaid sede tsoro ya hanata yin
hakan.
Washegari suka shirya kowacce ta nufi department dinta don Fara daukar lectures
amma Subay'a babu Abinda take ganewa bata fahimtar komai dukkan hankalinta yana
Nigeria, ga wani ciwon mara da takeyi me tsananin gaske wanda iya shi kadai ya isa
hana mata nutsuwarta. Kafin suyi Kwana uku a garin ta rame tayi fari, tayi xuruxuru
se idanuwa a warwaje. Abinda ya daga mata hankali Tunda Yaya Suhaila ta tambayeta
Abinda Ke damunta Tace babu basu Kara komawa ta kanta ba, suka cigaba da sha'anin
gabansu. Hakan yasa ta kulle kanta a daki ranar ta dinga kuka saboda ta riga ta
gano kuskurenta, tasan da Junaid ne bazai taba barinta a Wannan halin ba amma gashi
yan uwanta da suke bata da kamarsu sun manta da rayuwar ta, basu damu da ita ba a
cewarsu ta dagawa kanta hankali saboda namiji kilan yana can ya manta da ita gaba
daya gwara ta saki jikinta kawai.
Duk ganin hakan da take Kara daga mata hankali yake yasa tayi wanka a daddafe ta
shirya cikin abaya baka tayi rolling ta fito inda ta tarar Suhaila na waya da
Fannah, Tana fitowa taji Suhaila tace
Ga Mimin nan ma.
Mika mata wayar tayi, Subay'a ta karba suka gaisa da Fannah tana ta bata Sautin
abubuwan da take so, Subay'a ta mata alkawari sannan ta kashe wayar tace da
Suhaila.
Zanje gurin Sulma.
Me yake damunki ne, kinga yadda kika rame kuwa?
Salima wadda fitowar ta kenan daga daki ta iskesu tsaye. Baki Samiha ta tabe tace
Tace Sulma zata fadawa damuwarta, Kinsan ita kadai ce me hankali cikin mu.
Salima ta ja hannunta suka koma kujera tace
Fada min Menene.
Hawaye a hankali ya fara gangaro mata Daga idanu, se kuka me Cikeda nadama me
tsanani, me yasa tabi son zuciyarta ta taho gashi ta kasa samun farin ciki Koda na
awanni ne. Sosae ta dinga kuka hakan yasa Suhaila jikinta yayi sanyi ta dawo ta
zauna Itama suna lallashinta. Amma ta kasa daina kuka ana haka sukaji sallamar
Sulma hannunta na rikeda na Amna yar Kimanin shekara da wani abun.
Tunda suka amsa tasan babu lapiya, hakan yasa ta shigo da sauri sede ganin 'yar
uwar da tafi soyuwa cikin zuciyar ta na kuka yasa Gaba daya taji hankalinta ya
tashi, gefenta ta zauna ta kasa furta komai se patting bayanta da take a haka har
tayi shiru, Salima tace
Kuje daki ta fada miki abinda yake faruwa.
Tare suka shiga daki su kuma suka koma dakunansu zuciyoyinsu babu dadi, haushin
kansu sosae sukeji na barinta da sukai cikin damuwa for almost 3 days kenan, Anya
su din sisters dinne kamar yadda take daukarsu. A daki Subay'a ta gyara zama ta
kwashe duk yadda sukai da Junaid ta fadawa Sulma tana kuka Marar dadin saurare,
gaba daya wuta ta daukewa Sulma don Bata taba tunanin wautar Subay'a ta Kai wannan
extent din ba, Amma yanzun ba lokacin putting blames bane mafita shi ne Abinda zasu
nema. Cikin nitsuwa Sulma tace
Sister bakya neman shawara, Tunda yace ki hakura me yasa zaki taho? Kinsan fushin
Allah kuwa akan kin bin miji, he said all this to you and you left without his
consent? Ya salam!
Sosae Subay'a ke kuka tace
Na gane kuskure na sister, Nayi dana sanin abinda nayi don haka Nigeria zan......
Bata karasa ba saboda wani sharp pain da ya turnuke mata mara, hakan yasa ta rike
cikin tana fitarda wata Irin Kara da ta jawo hankalin su Salima dake dakunansu, a
guje har suna Karo da juna suka nufi dakin Subay'a wadda Ke durkushe jini yace a
bashi guri ya nuna nashi basirar, suna bude kofar sukai karo da Sulma wadda Ke
kokarin fita kiran su, ba wanda yayi magana saboda firgici, Sulma ta Fara kiran
Daddyn Amna, Salima ta kira ambulance, Suhaila kuwa tana kokarin hada kaya. Kuka
Sulma take sosae saboda yadda Subay'a ke axabtuwa. Within wani Lokaci Daddyn Amna
ya iso kusan tareda ambulance din akai Asibiti da ita. Anfi two hours kafin aka
basu izinin shiga gurinta, Tana kwance idanunta na digar da hawaye, jini da aka
karbo daga Lab Yana jikinta haka suka sameta suna mata sannu don nurse din ta
tabbatar musu idanunta biyu.
Fita Daddyn Amna da Sulma sukai Don zuwa enquiring akan maganar subay'a. Seda suka
zauna doctor yayi musu bayanin ciki ne da ita na wata daya da kwanaki ya samu
zubewa, sunyi mata wankin ciki sannan yayi directing dinsu inda zasu biya bill din.
Suna fitowa Sulma ta sauke ajiyar zuciya saboda dadin da taji cikin ya fita kada
yazo ya shiga gararin rayuwa kamar yadda uwarshi zata jefa shi a ciki, itama uwar
batasan halin da take ciki ba Balle dan da bai zo duniya ba ma.
Honey ka kira Yaya Junaid ka fada mishi halinda ake ciki.
Wayarshi ya fito da ita ya fara neman layin Junaid lokacin yana zaune a office yana
magana da Ridwan akan case din auren dan duk yadda Junaid yake tsamannin maganar ta
wuce haka, Duk yadda yaso Mami ta fahimci inda ya dosa Amma taki hakan yasa duk
hankalinsa baya jikinsa, ya rasa abinda Ke mishi dadi, the only moment dayake samun
nutsuwa shi ne idan yana tare da Sulaim din to yakan manta da cewar rabasu ake son
Yi, kullum tamkar son ta ake Kara mishi cikin zuciyarshi, abubuwan da a da suka fi
karfin shi yanzun a saukake yake samun shi, hakan yasa sonta ya mishi mugun kamu,
in har ya dawo gida to damuwa ya gama samunta Sede idan kebewa yayi a daki Amma
Sulaim da gaske take ta kwace shi, Ta shiga rayuwar shi ta bashi yadda yake so,
Mami ce kawai matsalar a Wannan lokacin itama ya rasa ta inda zai shawo kanta kuma
baisan saka wani cikin maganar yafi son sui ita dashi. Jabir ne ma ya shiga amma ta
ce ya fita ba huruminshi bane hakan yasa ya hakura.
Seda Daddyn Amna ya kira sau biyu sannan Junaid yayi picking, jin muryarshi yasa ya
saki jikinshi sukai magana anan yake sanar dashi halinda Subay'a take ciki,
Yanzun ya zaayi kenan?
Ya tambaya bai masan abinda yake ji akan abinda yaji ba
Tana kwance amma jikin da sauki yanzun.
Kanshi ya gyada yace
Ka Turomin account details dinka, zan tura maka bill din asibitin se sako da zaka
bata.
Inshaaa Allah zan turo maka. Bari akai mata wayar.
Bai amsa shi ba ya kashe wayar, me zaice mata ko ita me zatace mata. Bai tashi a
gurin ba seda ya tura komai, Tunda ciyarwar ta akanshi take dole ko ina taje Tunda
da aurenta akanshi dole ya bata abinci.
Kwanaki uku tayi a Asibiti sukai discharging dinta ta warke garau se tarin damuwar
da take ciki don ta samu sakon Junaid a hannun Daddyn Amna, Tana dawowa Tace da
Sulma Nigeria zata koma amma hajiya tace Allah ya bata saa, daga Wannan kuwa se ta
hakura abinta ta dangana ta Fara fafutukar kiran Junaid amma Tunda yayi picking sau
daya yaji muryarta, yayi blocking contact dinta don har yanzun fushi yakeyi da ita
kuma bai zo gabar yanke mata hukunci ba.
Sorry for d little page.... We meet later Inshaaa Allah!
Shatuuu ♥️
*MACE A YAU*
35
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
Gabaki daya yau dinnan jinta take tamkar tafi kowacce mace sa'a a Wannan ranar,
jinta take tamkar something great awaits her, hakan yasa ta Mike ta daura towel don
yin wanka ta Ajiye wayar ta, ta nufi bayi. Ta jima tana wanka tayi sitbath don yau
dinnan jinta take samasama gwara ta kalkale ko ina.
Tana fitowa ta Fara gyara jinkinta da sababbin mayukan da ta Fara amfani dasu, tayi
kyau se sheki take tana daukar ido, ta daina bleaching ta zama babbar yarinya wadda
zamani ke yayi, Dama tana bleaching saboda rashin kudi yanzun kam kudi Sede ka
kalla amman ba dai ta kalla naka ba haka abin yake.
Saffa saffa tayi kwalliyar tata saboda yanzun ta Fara blending da 'yan gayu ta
yarda da abinda Aimana tace mata yan gayu basu kwaliyya ta hauka ta gani duk
lokacin da zasu fita se on special occasions. Trolley ta bude ta Nemo wani
dandatsatsen lace na idon duniya dinkin fitted gown me kyau, ta saka a jikinta.
takalmi da jaka ta saka bayan ta kalli katon mirror data kafe a dakin. Tana fitowa
call din Haris ya shigo, wani abokin Ashir ne wanda ta biya shi Yana fada mata move
din Ashir don kome zatayi tafi son tayi Abinda yafi nashi, tafi son taji wanne step
yake takawa hakan yasa ta bashi wannan aikin
Haris ya ake ciki?
Ta tambaya kanta tsaye Bayan tayi picking, Seda ya gama mata kirarin da ya saba
sannan yace mata
Wani satin zai wuce Texas, wani abokin babanshi yayi sponsoring dinsa yaje yayi
Chemical Engineering.
Idanu ta bude tace
How genuine labarin nan yake?
Murmushi yayi yace
100%.
Kanta ta gyada zuciyarta Cikeda hassada tace
Karka damu, nagode.
Daga haka bata jira cewar shi ba tayi cutting layin, tareda kaiwa iska naushi cikin
takaici don Abinda take tsananin son gani shi ne Ashir ya kaskanta ita kuma tayi
gaba amma babu komai jikinta na Bata akwai babban abu dake jiranta. Hakan yasa ta
daidaita kanta ta fito Zuwa tsakar gida, Mama na Zaune tana yiwa Amira tsifa, Aisha
na girki se Amir dake gefe yana duba books dinshi dake ya fara zuwa school shima.
Kuma Tunda abin ya faru Baba Ke iya bakin kokari wajen ganin ya kawo abinda zasu
saka cikin bakinsu, yasan barin Khulthum da yayi tana ciyar dasu shi ne Abinda ya
kashe shi, ya zubar mishi da kima da darajar shi, ya Jawa yaron kunne akan ko me
zata kawo Kada wani ya ci, su barta da tsiyar ta akwai ranar nadama. Sede akwai abu
daya dake hunting dinsa yana ganin ko yaya ne akwai gazawar shi wajen lalacewar
rayuwar Khulthum Tunda shi yayi alkawarin kula da ita Tunda ita din marainiya ce
amma here she's ya tabbatar abinda yake zargi akan yarinyar kusan gaske ne amma ya
kasa samunta da maganar.
A pounded yam joint dake lodge road anan ne inda Khulthum ta hada AP dinta da Salim
don tuntuni tafi karfin kwanyar Huzaifa ta wuce class din Yusuf wanda Zamu iya
cewar shi ne ya fara bude mata idanu to such life amman yanzun Khulthum tafi
karfinshi, ta girmi tunaninshi ta Riga ta zama abinda bai taba tunani ba.
Juice kawai tayi order saboda tana jiran Salim yazo se suyi lunch tare, a hankali
take sipping cikin yanga da class na mussaman da take Kara, wayarta take daddanawa
tana duba latest fashion trends saboda tana son tana tafiya daidai da zamani. Tun
tana enjoying abin har ta Fara gajiya da zaman baki daya ta Fara neman layin Salim
Amma network ya hana communication din haka tana gani ta hakura ta cigaba da
surfing cikin wayarta.
Kamar daga sama ta Fara jiyo kamshi me sanyi me kuma sanyaya zuciya Yana shiga
kofofin hancinta, karku manta Khulthum din da data yanxun akwai banbancin, dukda
urge da take ji na sanin me turaren haka ta danne ta cigaba da Abinda take har Seda
sukai wajen Mintina goma kafin Kabir yayi clearing throat dinsa yace
Kinada class!
A hankali ta dago fararen idanunta wanda suke rikita Maza ta aje Kan fuskar Kabir
wanda ya bude hanci, baki, kunne yana kallonta ya shagala sosae.
Mutane da yawa sun fadi hakan.
Ta fada Tana maida kanta Kan wayarta, cikin Mintina uku Kabir ya gama assessing
dinta, balle da ta kalli idanunshi ya gama hango tsantsar zulama a ciki. Murmushi
ya saki yace
Bari Naje Naga kamar I'm not welcomed here kamar Kina jiran wani ne.
Kanta ta dago tareda kallon shi tace
Ina jiran wani amma ya gaza cika alkawari bai zo ba, Kaga kenan I'm waiting for no
one.
A hankali yaji Tana dada fitting gurin da yake son sakata hakan yasa yace
Then, ni kike jira dama, bari muyi order ko.
Murmushi tayi tace
Hakan ma yayi.
Cikin nitsuwa suka ci abinci suka gama babu Wanda ke magana dukkansu har suka
kammalla, kafin ya dubeta yace
Muje ko?
Kanta ta gyada tareda mikewa tabi bayanshi yayi settling musu bill sannan suka nufi
wata golden Benz dake Parke a gefe, seda ta shiga kafin ya bude shima ya shigo ya
fara driving Yana ta harhada kalaman da zai fada mata, Amma se yaga tamkar abin
yayi wuri ya kamata ya fara tuntubar me gayya me aiki kafin.
Seda ya rakata har gida, Tun daga unguwar, layin har Zuwa gidansu ya tabbatar
khulthum ce kadai zata iya wannan aikin ita kadai tayi soothing abinsu, Tana da
kyau na shiga taro, zamansu ya fahimci akwai turanci a bakinta, kuma babu damuwa ta
waye dukda ya Lura ba wayayyiya bace tayi forcing kanta tayi blending da rayuwar da
take ciki!
Bayan sun rabu yayi mata alkawarin kiranta yayi mata bayanin dalilinshi, da haka
suka rabu tana ta anticipation na Abinda zai kasance kuma. Yana barin gurin
Khulthum ya wuce gaida don secretary Musbahu ya tabbatar mishi Musbahu na gida.
Haka akai mishi iso ya shiga suka gaisa da Musbahu dake zaune yayi zurfi akan aikin
shi, Seda ya kammalla kafin ya dawo kujerar dake facing Kabir yace
Akwai wani move ne?
Dauke da murmushi Kabir yace
Babba ma kuwa, yau ka gama damuwar gwoggo sede wani abin.
Wa ka samu? A ina?
Cikin nitsuwa ya fayyace mishi komai ya kara da fadin
Idanunta na fada maka cewar kwadayyayi ce, kuma she's no one don ta Fara Law an
anguwarsu ance ta bari ta fada tarkon shedan , kaga tayi daidai da taste dinmu.
Murmushi me kyau Musbahu yayi yace
Abokina.......
Se kuma yayi shiru hakan ya tabbatar mawa Kabir ya rasa wanne word zai mishi
godiya. Sun tsara duk steps din da zasu dauka akan maganar sannan suka rabu.
Ranar ta kasance Monday, karfe shida na safe Junaid, Sulaim, Ahmad da Muhammad suka
dauki hanyar Kaduna, ko Sulaim Bata fada ba murna farin ciki ne fal cikin zuciyata
har ta gaza boyeahi ya fito karara kowa na gani. Junaid farin cikin da ya gani yasa
shima yaji duk duniya kuncinshi ya yaye, farin cikin rayuwarshi, sanyin idaniyarshi
na farin ciki shi waye da zai yi bakin ciki amma dukda haka deep down inside him
Yana jin tsoron approaching Mami, yana jin yau yakai karshe in har Bata amince ba
to tabbas komai zai iya faruwa. Sunyi nisa sosae motar shiru babu me magana yaran
duk sunyi bacci, Sulaim tayi breaking silence din da fadin
Yaya
Juyowa yayi ya dubeta sannan ya kara dafe steering tare dage girarshi daya yace
Yaya..... Yaya.. Yaya! Shi ne kadai abinda bakinki ya iya fada, come on nothing
sweet ko?
Dan murmushi tayi Cikeda kunya ta rasa abinda zata ce mishi, shi kuma dariya yake
kasa kasa don yasan ya kashe mata baki ba zata kara magana ba. Daga nan yace
Dove.
Har cikin zuciyar ta taji Wannan sunan, she loves the name without even knowing me
yake nufi, tasan whatever ya fito Daga bakin Junaid daban yake kuma me ma'ana ne, a
kalla tayi soyayya da mutane kusan uku amma akwai unique abubuwa a tare dashi,
abubuwa da ko bai nanata son da yake mata ba tasan a yanxun Itace a birnin
zuciyarshi kuma ita take Jan ragamar shi Sede bawai ta manta Subay'a bane a'a tana
nan daram cikin ranta, musamman in yayi kwance kwance ya kasheta da daddan kalamai
se taji kada fa Subay'a ta dawo abu ya canxa, Tana kishin Subay'a sosae me zafi ma
kuwa.
Kina ganin soyayyar Dana nuna miki ta sati biyu is sufficient for you ki zauna
Dani?
Kallonshi tayi yana driving cikin kwarewa, ta yaya zatace son da yake gwada mata
bai isheta ba, ko kuma yace Bata yadda Yana sonta ba, kanta ta girgixa Tana ganin
lokaci yayi da zata bude mishi zuciyarta amma tana ganin kamar Lokaci baiyi ba amma
abinda take kallo kadai cikin idanunshi sonta ne me tsananin gasken gaske aciki, ga
kuma tsoro wanda duk yadda taso fahimtar tsoron menene ta kasa hakan yasa ta zame
mishi shoulders da zai kwanta akai lokacin bukata.
*If you in d rain I'll cover u, lost I'll found u my love don't lie, E no dey lie,
don't worry I'll be here and I'll catch you if u fall, I no lie, I no dey lie, give
me ur hands and I'll show u which way to go, lemme be ur guide, hold on don't be
afraid trust me and have some faith u be alright u be fine*
Shatuuu ♥️
*MACE A YAU*
36
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
Lokacinda suka isa gidan, shiru tamkar masu gidan basu tashi ba, se ma'aikata dake
ta aikin gyara gidan. Yana gama parking ya juyo ya dubi Sulaim da take kokarin
tashin Ahmad yace
Ku shiga ciki, zan wuce wajen seminar din. A gaida su Mami.
Murmushi tayi ta gyada Kai tareda fadin
Mami zataji, take care please.
I'll definitely do that Dove.
Murmushinta me kyau tayi daga nan ta tashi su Ahmad suka shiga ciki shi kuma ya
wuce. Da murna dukkansu suka shigo gidan, sojojin dake bakin gate suka kawo musu
kayansu ciki. Tun a tsakiyar parlour Ahmad yake kwalla kiran Mami wadda ke kitchen
tana kokarin hadawa Baba breakfast Don batayi tunanin zasu zo da sassafe haka ba.
Fitowa tayi ta tsaya bakin kitchen tana binsu da kallo fuskarta Cikeda murmushi da
murnar ganinsu.
Mami!
Sulaim ta fada lokacin da ta isa inda take tsaye.
Ummu_Sulaim sannunku da zuwa marhaba..
Murmushi tayi tace
Mami kun tashi lapiya?
Lapiya lau Sulaimi, Me ya samu Muhammad yake cin kunu. Kai fita a gidannan dan
kaniya kawai!
Turo Baki yayi ya nufi Sulaim wadda Ke ta dariya, rungumeta yayi Mami ta kame
hannun Ahmad dake sunfi shiri saboda copy din Baba ne, Muhammad kuma gidansu
Subay'a yayo.
Yi hakuri rabu da Mami ko?
Kanshi ya gyada, Mami ta girgixa kanta Tana jin tsantsar soyayyar Sulaim na kara
ratsa ta, dubi yaran uwarsu ta tsallake su ta tafi wata duniyar ita kuwa gata tana
bauta musu.
Ina shi Yayan naki.
Oh! Ya tafi seminar se anjima zai dawo, yace na fada miki.
Kanta ta gyada tausayin Junaid na shigarta, kallon Sulaim tayi wadda ta maida
hankalinta Kan Ahmad dake nuna mata wata kurjewa da yayi, ganin yadda ta bashi
dukkan hankalinta tare da rarrashin shi dukda Ciwon ya dade ya kara tabbatar wa da
Mami babu macen da ta cancanci zama da Junaid se Sulaim amma ita bata son takura
mata Don tana ganin kamar