Showing 96001 words to 99000 words out of 121650 words

Chapter 33 - MACE A YAU by Shatuuu

Shatuuu   

12 May 2026

472

a kanta
sun sauka da kansu ba ita ta sauke su ba. Hajiya kam bata wani koma ta kanta ba don
itama tata ce ta same ta, kwata kwata ta rasa direction din Alhaji ya saka gaba, ta
kasa fahimtar ina ya nufa, ita karan kanta Tana iya Kwana biu bata saka shi
idanunta ba, da sassafe yake fita as early as six am sanann bazai shigo gida ba se
ta twelve am, hakan seda ya tayarwa da Hajiya hawan jininta wanda ta dade da
mantawa cewar Tana dashi saboda yadda take bin doka tareda kaffa kaffa.

Hankalinta a tashe ta nufi dakinshi bayan taci kwalliya kai kace sabuwar Amarya ce
amma har dare ya raba gida biu babu alamar Alhaji, Karo na farko da Hajiya ta samu
kanta da zubar da hawaye don tasan komai ya lalace kenan! Ita babu Abinda bata
yadda ta aikata ba Irin neman taimako hannun wanin Allah, a ganinta Allah kamar
yadda yayi alkawari bazai yafe shirka ba, Tasan bin malaman tsibbu manyan shirka ne
hakan yasa as much as she can take kokarin ganin ta kaucewa hakan. Amma haduwa da
hatsabiban Kawaye seda suka gama mata dukkan hudubiobin tsiya suka jefata hanyar
malamai hakan yasa ta dage a tsaye wajen ganin 'ya'yanta imanunsu ya tsaru kuma
tayi wannan nasarar don kuwa kowanne abu ya lalace ita kanje gurin malaminta ya
gyara abubuwan Sede bai taba nasara akan Junaid ba hasalima baya kwatanta aiki
akanshi don se ya rushe saboda tsananin adduar da rike Allah da yayi.

Wayarta ta janyo a hankali tana jin Lokaci yayi da zata bi Abinda zuciyarta Ke raya
mata, ya kamata ta Fara gyara mistakes din da tayi kusan shekaru bakwai tana yi.
Lokacinda Subay'a ta Fara dialing number Mami gabaki daya wata iriyar kunya ta
mamaye ta hade da tsoro me firgitarwa saboda bata san wanne irin karba Mami zatayi
mata, zuciyarta taji tana bugawa da karfi saboda jin call din ya fara ringing, ga
mamakinta se jin muryar Mami tayi tana fadin

Subay'a!

Baki daya se ta duburburce ta Fara kame kame words din bakinta dukka suka dauke har
Mamin ta Kara fadin

Subay'a Kina jina?

Ma...Ma.... Mi ina yini iiii

Ta fada Tana stammering, murmushi Mami tayi tace

Lapiya lau Subay'a kin dawo lapiya? Yasu Hajiya

Se kawai hawaye ya Balle mata, dama haka rayuwar take kayiwa mutum sharri ya saka
maka da alkhairi, gashi ta gani taga wanda suka gaji arziki suke Daga gidan girma
Wanda jira kawai suke mutum yayi nadama sui embracing dinshi.

Three weeks kenan Mami.

Bude Baki tayi Cikeda Al'ajabi tace

Amma babu labari, kina ina yanzun?

Ina gidanmu

Shiru Mami tayi don ta rasa me zatace, what if idan Subay'a bata san yayi aure ba
taji a bakinta? Hakan babu dadi amma se tace

Ai Junaid din yayi tafiya zuwa Malta amma cikin week dinnan muke expecting dinshi,
yaran kuma suna Delta wajen Imratu.

Wata ajiyar zuciya ta sauke jin inda yaranta suke in a safe hand, tasan wacece
Imratu bazata cutar da yaran ba amma ita abu daya kawai take jira Mami tayi
testifying auren Sulaim da Junaid don gani take karya ne Duk dare gani take kamar
idan ta tashi zata ganta gefen mijinta amma ina ta riga tayi sake da damarta, Dama
Anty Takori tace A BARI YA HUCE shi ke kawo rabon wani....

Mami ce ta katse mata tunaninta da fadin

Ki gaishe min da Hajiyar da 'yan uwanki.

Kanta ta gyada tace

Inshaaa Allah Mami nagode!

Daga haka sukai sallama ta kwanta tare da sakin kuka don tayi hakan saboda Mami ta
shiga lamarin amma poor her Mami bata bata Koda number Junaid din ba.

Ta dade a kwance se ta jiyo muryar da ta Sata saurin mikewa don if she's not
mistaken Suhaila Tajiyo, da sauri ta fito Zuwa parlourn amma mamakinta ya girmama
saiamakon ganin sauran yan uwanta su bakwai gata ta takwas, kowaccensu ka kalla
jikinta babu wani kwari haka suka samu guri cikin kujerun suka zauna, itama gefen
sister ta zauna Tana fadin

Meye haka kamar wanda akai mutuwa zakuzo dukkanku jiki a sanyaye.

Babu Wanda ya bata amsa don babu me bakin amsar, hakan ya kara daga mata hankali se
ta Mike Tsam ta nufi bedroom din Hajiya ta sameta hankalinta a matukar tashe tana
amsa waya, gefe ta zauna Tana jiran hajiyar ta kammalla wayar wadda ta fahimci da
Anty Kubra take wayar hakan ya kara bata mata ranta don ta tsani Anty Kubrar saboda
ta hannun daman Hajiya ce, babbar aminiyarta ce wadda dukkan wani abun hajiya babu
Wanda bata sani ba akan hajiyar dasu su Subay'a duk Abinda Hajiya keyi wannan matar
ke daura ta akan hanya, hakan yasa Subay'a ta tsane ta itama Matar ta sani Shiyasa
basa shiri kuma Subay'a ta zama koma baya a tallafin da Anty Kubra ke kawowa
sauran.

Ya akai Subay'a?

Hajiya ta tambayeta bayan ta aje wayar don hankalinta yadan dawo jikinta saboda
Antyn tayi mata alkawarin yau dinnan Za'a sabunta aiki, Nawa Alhajin yake da har
zai zauna Yana daga mata hankali ita kuma ta wani tsaya har kwanakin nan tana
kunsar bakin cikinshi.

Hajiya bazaki rabu da Anty Kubra ba? Hajiya kina kallon Abinda ya fara kunnowa
cikin rayuwar mu, Duk yadda kike tsaye kanmu amma haka Junaid yayi aurenshi! Inace
hakan ya zame mana izina gaba daya......

Da sauri Hajiya ta katse ta da fadin

Ke gidan ubanwa kika ji Junaid yayi aure? Waye ya fada miki?

Itafa Hajiya bata san dalilin dawowar Subay'a ba don Bata bi ta kanta ba kasancewar
itama tana cikin matsalar Ashe....

Ba wanda ya fada min Hajiya, a social media na gani Shiyasa na dawo na daidaita
rayuwar aurena kafin wankin hula ya kaini dare.

Hajiya ta bude Baki ta bata amsa Subay'a ta tari numfashinta da fadin.

Kizo parlour Kinyi baki!

Tana fadar haka ta fito jikinta a matukar sanyaye, tabbas basui Saar uwa ba don
kaso mafi girma ita ce ta watsa musu rayuwar gidan mazajensu, ita ta dora musu
halin cewar mace ita ce shugaba gidan aure ba miji ba hakanan ta sakasu suka dinga
zuba iskancin su wanda duk a cikinsu Sulma ce kadai ta fita zakka.

Tana isa parlon ta koma inda ta tashi babu Abinda ya canza, gurin is so tensed and
not favorable kwatakwata hakan yasa taji ta gundura har Seda Hajiya ta iso idanunta
a warwaje ganin Suhaila, Sulma da Kuma Salima mutanen Cyprus, ga kuma Surayya,
Samina, Samiha da Sakina. Gabanta Yana bugawa da sauri sauri tamkar zai fito tazo
ta zauna Tana fadin

Meye ne kuka dawo kuma? Meye kukazo kuka zazzauna kamar marasa......

A makogaro maganar ta makale ganin Abinda idanunta Ke hangowa, Alhaji ne Sanye da
trouser na kamfanin Zara se top wadda ta amshe shi, kanshi anyi masa saisaye hatta
Fuskarshi an rage kasumbar da ta cikata, yayi kyau tamkar lokacin yana ganiyar 20s
dinsa, Baki daya tsufan ya wuce se yarinta karara da ta bayyana a tare dashi. Duk
wannan bashi bane damuwar Hajiya ba a'a kyakyawar Yarinyar da shekarunta bazasu
wuce sha Tara ba tana Sanye da pencil trouser Baki da top ja kanta babu dankwali ta
zubar da gashin kanta Wanda ya sauka har ya dan wuce dokin wuyanta Baki sidik Yana
sheki, ita kanta yarinyar tamkar anyi barin perf jikinta saboda tsabar yadda take
fitar da fitinannen kamshi, kyakyawa ce ta gasken gaske don kallo daya zakai mata
ka gaskata hakan. Fuskarta ta nuna tsantsar yarinta ga kuma kyabe fuska da tayi
kamar me shirin yin kuka, se kara shigewa jikinshi take. Surayya ce ta Fara mikewa
idanunta tamkar xasu fado kasa ta bude bakinta Dan magana Alhaji yace

Duk Wacce tayi magana se nayi mugun saba mata.

Jagwab ta koma ta zauna, Sulma hawaye ta Fara itada Subay'a Bayan sun kankame
hannayen junansu, Samina kuwa kana kallonta itada Suhaila kasan a cike suke taf da
masifa don fuskarsu har tayi jawur saboda tsabar Abinda yake cinsu basu fitar dashi
ba. Salima tafin hannayenta tasa ta rufe fuskarta, yayinda Samiha da Salima suka
kurawa Alhaji da yarinyar idanu tamkar basu taba ganin Alhajin ba ko kuma ya zama
wani bako, Surayya ta Mike tareda kamo Hajiya wadda ta rigada ta daskare a wajen
saboda tsabar yadda ta fita a hayyacinta ta zama tamkar statue wadda aka dasa ta a
gurin! Tsoron Surayya kada hajiyar ta fadi ta samu stroke su shiga ukunsu!

Na Tara ku anan saboda na gabatar muku da Matata, amaryata, sabuwar uwarku Asiya!
Ina.......

Alhaji....

Hajiya ta katse shi mid sentence shima ya katse ta da fadin

Mistakenly kika Kara saka min baki Se na sauke igiyar aurenki.

Jin wannan furucin ba karamin dukansu yayi baki daya ba, itakam Asiya ba su bane a
gabanta don ko kallon arziki babu wadda ta yiwa hasalima tana jin an takurata Zuwa
gurin nan hakan yasa ta dubeshi a shagwabe tace

Honey mu tafi mana.

Mikewa yayi ya kama hannunta baice dasu komai ba ya nufi wajen part din zuwa na
gefen inda anan ne zata zauna. Kamar hadin baki gabaki daya Suka fashe da
matsanancin kuka saboda a ganinsu an tozarta su, sun manta tozarcin da saukai yiwa
wasu, sun manta rashin arzikin da sukai a nasu gidajen. Hajiya kam tamkar fool haka
ta koma Ta rasa me zatace se binsu take da ido tana jin inama ita ke kukan da suke
at least ta samu sassauci. Basu gama wannan tunanin ba Alhaji ya dawo shi daya, ya
hadasu ya wanke su tas har uwarsu, yace yayi cancelling Cyprus kowacce ta koma
dakinta, kada su sake Zuwa mishi gida weekly kamar yadda suke sede Bayan wata dai
dai, sanann ya basu awa daya suci abinci kada ya samu mutum daya a gidan!

Who saw this coming? Ina Subay'a zataje? How will everything be? Let's continue d
journey to its end!!!

[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
Shatuuu ♥️

49

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣shatuuu095@wattpad
*Of course, today is a special day, my beautiful, elegant favorite sister has
clicked 12 years today. Maman moon, Oum Abdallah are all a year older... I pray
Allah continue to shower his endless blessings, mercies and support upon them. Be
blessed dearies!*


Kowanne ka kalla cikin su takwas din kasan ba karamin duka maganar Alhaji tayi musu
ba, tamkar saukar aradu haka Maganganunshi suka isa kunnuwansu, Baki daya ba kansu
suke tausayawa ba Illa Hajiyarsu da zata kwashi bakin ciki cikin gidan, gaba daya
Asiyar Nawa take ba zata wuce shekaru goma Sha Tara ba, to Samina ita ce autarsu
wadda ta dade da bawa shekaru ashirin baya, yanzun haka shekarar ta ashirin da uku.
Amma Alhaji ya rasa wadda zai aura matsayin matarshi se wannan mitsitsiyar yarinyar
da Fannah 'yar Suhaila kadan ne Bata girme mata ba. Yanzun duk wannan cika bakin da
suke na su basu zama da kishiya, nasu su kadai ne mata gidajensu se gashi Anyiwa
uwarsu da jikarta. Kuka sosae suke wannan karan har ita kanta Hajiyar, gaba ki daya
jinta take tamkar ba ita ba, Tunda take bata taba jin Irin wannan wulakncin ba ko a
labari se gashi ya faru a karan kanta.

Samina ce ta Fara mikewa tayi hanyar fita ko dankwali babu a kanta, cikin sauri
Surayya ta Mike tareda fadin

"Ke samina ina zaki je? "

Juyowa Samina tayi idanunta sunyi jawur, ga hawaye da yayi mata kacakaca a fuskarta
tace

"Zanje gurin waccan yarinyar da Alhaji ke kiranta Uwarmu, Wallahi se na targada
mata kashin ta"

"Idan baki targada ta ba, ni na karairaya ki shashashar wofi! "

Haka ta tsinkayi muryar Alhaji Yana fada a bayanta da yake ya dawo Dan ganin ko sun
tafi, da sauri jiki na rawa Samina ta shigo tayi Bayan Hajiya jikinta na rawa
saboda tsabar tsoro, ita dama haihuwarta an gama asirce Alhajin don haka a
laushinshi tubus ta sameshi amma dukda haka basa kawo mishi wargi, bar su dai da
basu bin takanshi idan zasui abu idan hajiya ta amince shi kenan. Su Surayya su
suka san waye Alhaji Alkasim, su suka san true definition dinsa, Shiyasa suka hango
wautar Samina da take tunanin ketare umarnin shi.

"Uban me kuke har yanzun Baku tafi ba? Kun manta Abinda na fada kenan? "

A rikice duka suka Mike kowacce ta Fara maida mayafinta da tazo dashi, Hajiya ganin
hakan yasa tayi ta maza tareda kallon Alhajin tace

"Babu inda zasu je Kasimu, babu inda zasuje nace, ku koma ku zauna nace gidan
ubanku ne babu Wanda ya isa ya koreku Daga ciki. Idan banda asara da lalacewa Irin
taka tsofe tsofe da Kai Kaje ka auro yarinya Saar jikarka, ai Wallahi kaji kunya ka
bani mamaki, kuma tsakani na da kai Allah ya isa! 'ya'ya babu inda zasuje na fada"

Maimakon yayi fada se yayi murmushi tareda fadin

"Kika ce babu inda zasuje?"

Kanta ta gyada ta kallesu dukkansu sunyi tsaye kamar zakaru tace

"Babu inda zakuje, gidan ubanku ne"

Bai ce mata komai ba ya ficewarshi , dariya tayi tana tunanin aiki ya fara dawowa,
dukkansu suka zauna amma a tsorace banda Sulma da tace
"Hajiya ki Bari mu tafi kawai, wannan fadi in fada da kuke ke da Alhaji, bashi da
amfani, aure ya riga yayi, hakuri ne kawai namu. Dama ai munsan ranar nan dole Se
tazo ranar da komai zai kwabe mana"

"To Muslim Sister, Assheikh, Malama. Naji nace naji idan ke bazaki zauna ki tayani
kukan abinda ubanku yayi min ba, kije Allah ya kiyaye dadin abin ba ke daya bace
'yata da tuni takaicin ki ya kasheni"

Sumsum Sulma ta samu guri ta zauna tunda ta rasa Wanda zai Goya mata baya, dukkansu
sunyi shiru masu sharar hawaye Nayi, Masu kulle kulle cikin zuciya sunai dukda
sunji maganganun Sulma kuma gaskiya ta fada amma furucin Hajiya bazaisa su Goya
mata baya ba, don idan aka bi salsala duk saboda su waye ta shiga wannan halin?
Saboda su dinne, don su samu soyayyar uba ba tareda an raba ta zuwa ga wasu yaran
ba amma a karshe abinda ake gudun shi ya faru!

Dawowa alhajin yayi, mamaki kwance a Fuskarshi ganin yaran suna zaune, a ranshi ya
Raya dole ne ma yayi abinda yayi niyyar, Seda ya tsaya gaban Hajiya kafin ya ciro
farar takarda Daga aljihunshi ya Mika mata tareda fadin

"kije na sake ki! "

Dif parlon yayi saboda wani abu da ya ratsa dukkansu, Subay'a ta lumshe idonta a
hankali tana jin ita ce next person da hakan zata faru a kanta, Hajiya was dazed
and confused ta kasa Koda kwakwaran numfashi me tsawo, tunaninta Baki daya ya dauke
se harbawa da zuciyarta Ke yi tsabar firgici. Juyawa Alhaji yayi Bayan yace

"Duk tsawon rayuwar ku Baku taba kallona a matsayin uba mahaifi ba, se shashasha da
kuke daukata. Mahaifiyar ku ita ce mutum a idonku Don haka nake son ku tattara har
ita ku tafi duk inda zakuje amma ku manta na haifeku"

Yana gama fada ya juya don ficewa amma ya gagara hakan sakamaakon Sulma da ta
tsugunna ta rike mishi kafafunsa kamar zata balla su, kuka take wanda me saurarenta
ma dole zuciyarshi ta karye, kallonta yayi a ranshi Yana jin tausayin ta da ta
kasance Yarinyar Hajiya, Yarinya me hankali da hangen nesa wadda ita daya take
binshi bata manta cewar shi din uba ne a gareta ba, yana sonta a kaf cikin yaranshi
babu Wanda ya ke da gurbin da take dashi, Amma bazai bari ta karya masa Abinda yayi
niyya ba, hakan yasa ya janye kafafunshi ya fice baki daya. Ta jima tana kuka kafin
ta Mike ta koma ciki inda ta samesu suna hadawa Hajiya kayan ta wadda ko uhm ta
kasa furtawa se hawaye da take tana binsu da idanun ta.

Wasu cikinsu kuka suke, wasu kuma sun shiga taitayin su kamar Subay'a, Salima da
Sakina. Suna gamawa Surayya ta dafo Hajiya suka fito tareda kulle sashen gaba daya
Bayan Subay'a ta fito da nata kayan zuciyar ta Cikeda zulumin inda zata nufa.
Dukkansu da motarsu suka zo hakan yasa kowacce ta shiga tata se Subay'a ta shiga ta
Sulma. Surayya ce a gaba hakan yasa suka mara mata baya zuwa Darmanawa inda anan
gidan aurenta yake. Ita kadai ta shiga da motarta dukkansu a waje sukai parking
sannan suka shiga kayataccen parlon gidan Wanda ya sha gyara ga dukiya da aka
narkar a ciki. Yaran ta basu nan sunje gidan su mijinta suna Family meeting hakan
yasa gidan masu aikinta kadai suka rage. Dakin dayake spare cikin gidan ta bude ta
kai wa Hajiya kayanta se a sannan Hajiyar ta dinga kuka Tana karawa, a ganinta bata
cancanci hakan Daga gurin Alhajin ba. Yaran dukka suka saka ta a gaba suna kuka
wasu na lallashinta.

"Kaico ni! Haka Alhaji ya zaba yayi min, hakan ya ga yayi mishi daidai? Seda na
gama mishi aiki na bauta mishi sannan zai sakeni? "

Kuka yaci karfinta, su kansu sunsan fada kawai take amma Babu abu guda daya da take
yi cikin abinda ta lissafa, su a karan kansu sukan manta cewar wai suna da Uba, se
suje gidan su yini amma ko sashen da yake basu kalla kasan ba. Gashi nan karshensu
dukka yazo Allah se ya fara daga kan uwarsu wadda ta dorasu a hanyar!

"Surayya miko min wayata na kira Kubra dole a gaggauta aikin"

"Wacce Kubrar? "

Suka hada baki, Suhaila tace

"Hajiya Baki daddara ba, har tunanin sake komawa ga laifinka kike? Haba Hajiya ko
ni nan na bar komai na tuba nabi Allah don ya nuna mana iyakarmu, ya nuna mana shi
ya halicce mu"

Surayya tace

"Mufa tsakanin mu da Anty Kubra Allah ya isa! Saboda ita ta jefa mu cikin wannan
rayuwar, Hajiya ki manta da komai ki rungumi Allah kilan hakan yasa Alhaji ya maida
ki dakinki Amma ni dai yau na girgiza matuka "

Samina wadda se lokacin tayi magana tace

"Nufinku yarinyar can taci bulus? Shi kenan ta Kori Uwarmu Daga gidan ta, Wallahi
ni nan se nasan yadda na Kwata mana 'yancin mu"

Hajiya wadda jikinta yayi matukar sanyi, kalaman yaranta suka shige ta farat daya
tace

"Kaiyya auta, babu wata wadda ta koreni ni na Kori kaina, ina fatan hakan ya zame
mana darasi gabaki daya, kowaccenku ta gyara gidan ta kafin Lokaci ya kure mata,
Kawaye basuda amfani Don na gani a karan kaina. Subay'a ki tattara ki tafi Kaduna
ki jira mijinki ya dawo sannan ki zauna da abokiyar zamanki lafiya don munyi sake
babba. Haka nima bazan zauna anan ba akwai gidana dake tarauni can zan koma har
Zuwa yadda Allah ya tsara! "

Tabbas sunga saurin nadamar Hajiya amma basu san Hajiya ta Fara laushi ba tun
zuwansu gidan Junaid da sukaga yayi aure, Tun lokacin jikinta ya bata karshenta
yazo Amma taki aminta da hakan ta cigaba da bin son zuciyarta gashinan ga inda ya
kawota!!!


Amarya Kinsha kamshi Koda kin kashe dan masu gida! Haka abin yake, haka bahaushe
yace Amma ga Khulthum zata iya karyata wannan popular saying din, zata iya Rantsuwa
cewar ba gaske bane Don kuwa ta shaida hakan. Aure de gashi tayi shi, irin wadda
take mafarkin yi kullum, ga dukiya nan ta samu kana kallonta kasan Hutu da jin dadi
Ya samu guri Sede rashin kwanciyar hankalin da take ciki yasa idanunta suka Fada
ciki sosae, kashinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login