Showing 48001 words to 51000 words out of 121650 words

Chapter 17 - MACE A YAU by Shatuuu

Shatuuu   

12 May 2026

136

nata kamar yadda ya saba, she can even
cry a sanin da yayiwa Sulaim na shagwaba amma shi so yake tayi smiling wannan
brightest smile din Nata da zai bayyanar da wushiryar ta yasa two sided dimples
dinta su lotsa.... Se yayi murmushi tamkar abin ya faru ya fara jin tamkar yana
yawo cikin cloud ne, ya fara jin wani nishadi Yana ziyartar shi.... That's love!
Wayarshi dake kan dash board ce ta Fara ringing, Da sauri ya dakko ta don ya manta
a gurin ya aje ga rana. Cikeda girmamawa yace

Baba barka da rana

Barka ka dai Dan Aminu (shi ne sunan da Baba ke kiranshi kasancewar shi din ya rike
shi har rasuwar shi, Baban Sulaim kenan)

Baban ya fada Daga Dayan bangaren, kafin ya cigaba da fadin

Yanzun na dawo Maminku ke bani daddan labari, mashaa Allah long awaited day has
come, Allah yasa ayi a sa'a Seka hanzarta kayi registration ko?

Da murmushi Junaid yayi yace

Nayi tuntuni yanzun flight nake son booking da Nigerian Airways nida Subay'a.

Cikeda gamsuwa yace

Hakan yayi kyau, Allah ya jikan Aminu da Fatima.

Shi kanshi Junaid yakan tuna inda Daddy Aminu na raye Irin farin cikin da zaiyi
saboda kullum zancenshi "Son make me proud inada high expectations a kanka" here
he's sede ya bishi da addu'ar kam sannan ya rike amanar Sulaim din, Shiyasa yake
ganin auren Sulaim din shi ne Abinda yafi komai muhimmanci.

Ya zakuyi da yaran to?

Muryar Baba ta katse mishi tunanin da yake, a hankali yace

Gobe Sulaim zata dawo jibi ta tafi birnin kudu, idan mukaje daurin Auren se ta dawo
ta zauna dasu Ahmad itama lokacin ta koma school kafin mu dawo. Amman Baba ya ka
gani?

Murmushi Baba yayi yace

Hakan yayi, is better ta Fara sabo dasu Tun yanzun.

Junaid bai fahimci inda maganar Baba ta dosa ba amma Mami dake gefenshi ta fahimta
hakan yasa bayan ya aje wayar sunyi sallama da Junaid tace

Baba me last sentence dinka yake nufi?

Kallonta yayi yace

Zan aurawa Dan Aminu 'yar Aminu!

Kanta ta girgixa da tsananin mamakin Baban tace

Tace Tana sonshi ne? Ko yace yana sonta ne?

Kafada ya dage yace

We wait for the time.

Ja'afar fa?

Ta tambaya Tana karewa Baba kallo

Who's more submissive to her love?



**********

Tashin shi kenan daga bacci ya sakko kafafunshi Daga gadon shi na alfarma, ya kusan
minti biyar a zaune kafin ya Mike tareda Fara rage short din dake jikinshi ya daura
towel a kugunshi hakan ya fito da aihnahin structure dinshi, by mere looking
kakkarfa ne kuma yana gyming saboda yadda biceps and triceps dinsa suka murde, ga
packs dinshi sun fito sosae very prominent, namiji har namiji wanda ko a fuska ka
kalleshi Seka kara dubanshi saboda tamkar mace yake don kyau. *Musbahu* kenan dan
gwoggo. Yafi awa a toilet kafin ya fito Sanye da blue din bathrobe ya shiga
dressing room dinsa inda wani tafkeken wardrobe yake a jibga kaya wanda mutum zai
iya shekara ba tareda ya maimaita ba. Wando Baki ya saka da bakar top sannan ya
feshe jikinsa da daddan turare kafin ya fito inda ya samu komai in place. Wayarshi
ya dauka ya fito parlonshi inda nanma aljannar duniya ce, haka ya zauna kan cushion
yana jiran aka kawo mishi breakfast, Yana nan Zaune yayi shiru deep in thought bai
kuma san tunanin me yake yiba yaji an turo kofar, cook dinshi ne Hannunsa wayam
babu komai. Kasa ya tsugunna ya gaisheshi kafin yace

Gwoggo Tace Kaje part dinta, kaida ita zaku yi breakfast.

Wata Irin faduwar gaba ta ziyarce shi, Innalillahi wa Inna ilahil rajiun! Me kuma
ya kunno kai shidai yasan wa'adin da aka daukar mishi na fito da mata akwai
kwakwaran watanni hudu da suka rage. Cikin hanzari Fuskarshi na nuna tashin
hankalin da yake ciki ya Mike ya zura wani Gucci slippers ya fita Baki daya Daga
sashen. Baison Zuwa part din gwoggo ya dade saboda yawancin cousins dinsa Daga
wannan ta tafi wannan tazo suna binshi da admiration look wanda baya so. Ga tsoron
gwoggo da yake tun yarinta. Har yanzun tsoronta yake most of the times Yana
contemplating ko ita ta haifeshi amma yasan ita ce haka zuciyarta take, a cikin
idanun akwai soyayyar amma bazata nuna mishi ba.

Mintina biyar suka kaishi part din Nata, dayake he's strict yasa masu musu hidima
da hannu yake amsa gaisuwar su. Tana zaune kan sofa wadda take tata ita daya by
mistake bazaka taba ganin wani ya zauna a gurin ba se ita daya, gabanta fresh milk
ce me dumi cikin mug se yan mata biyu akan kujera suna hira. Gefen kafarta yaje ya
zauna Cikeda girmamawa yace

Gwoggo barka da safe.

Kallonshi tayi sonshi na tsarga mata tace

Barka dae, muje muci abinci.

Anan yan matan da suka hadu karshe amma ko second glance bai basu ba hasalima a
ciki ciki ya amsa musu gaisuwar shima don alfarmar idanun gwoggo ne. Varieties ne
kan table din haka cook din gwoggo tazo tayi musu serving kafin suka Fara cin
abinci. Shiru har suka gama sannan gwoggo tace

Amra zata je booking flight zata koma Indonesia next week ka fita da ita.

Tamkar ya daura hannunshi yayi ihu haka yaji amma babu hali, calmly yace

Tayi sauri inada board meeting da shareholders dinmu na *TitαΦ Oils*

Da sauri Amra ta Mike yarinyar very calm and gentle gata kyakyawa Duk cikin cousins
dinsa tana da babban matsayi a gurin shi, na farko 'yar favorite uncle dinshi ce
kuma sunan gwoggonshi gare ta, yasan tana sonshi amma bai taba kamata da wani
kallonshi ko nuna mishi ba, hasalima Bata Zuwa gidansu se on special occasions ko
gwoggo ta matsa. Da zai iya da ya aureta amma idan ya aureta wannan secret din zai
bude kowa ya sani is better ya hakura.

Ina fata TitαΦ Flours babu matsala don board directors sun kawo min korafi.

Kanshi ya gyada yace

Akwai gwoggo amma Nayi sorting abin shi yasa ban miki zancen ba.

Kanta ta gyada ta kurbi madarar dake gabanta daidai fitowar Amra cikin kyakyawar
shiga very decent tayiwa gwoggo sallama sannan tabi bayansa wanda tuni ya fice
bayan yayiwa gwoggo sallama.

A mota ta tarar dashi gefenshi ta zauna ya tada motar ba tareda ya kalli inda Take
ba Balle ta saka ran zai mata magana. Duk yadda zuciyata Ke azalzalata akan tayi
mishi magana haka ta danne har suka isa sannan ya ciro kudi daga pocket din motar
ya mika mata a dakile kamar bayaso yace

When you done Kimin text.

Karba tayi don tasan ba'a musu dashi tace

Jazakalllahu khairan. Allah ya kyautata rayuwar gwoggo.
Baisan ya juyo ya wanke ta da murmushi ba saboda har cikin zuciyarshi tsananin
farin ciki yaji ya mamaye shi. Itama yau kam ta tashi da dama murmushin is OK for
her haka ta fice daga motar ta barshi Yana mamakin kanshi!



****

Takwas daidai na safe jirginsu Sulaim ya sauka kan runway dake cikin international
airport of Aminu kano dake cikin birnin Kano ta dabo ci gari! Cikin nitsuwa ta
sakko idanunta suna ta zagaye don hango abinda ya addabe ta, ya hanata sakat
kwanaki bakwai kadai ba karamar axabtuwa zuciya tayi da rashin ganinshi ba, yanzun
ta yadda bawai Yaya ne Junaid ba ta gama concluding cewar sonshi take kuma so me
wahalarwa a jiya ta tabbatar da hakan amma taki yadda da hakan tana ganin wani
laifin tayi zuciyarta zata hukunta ta da mafi tsaurin laifi shi ne son Junaid tana
ganin zuciyarta ta zalunce ta, ta kaita inda zata wulakanta amma tasan Rayuwarta
inhar da gaske sonshi take will definitely be shattered.

Yana tsaye gefen motarshi, yayi pocketing Hannunsa wani Irin farin ciki yake ji
Marar misaltuwa, ji yake tamkar yayi ta dariya kowa yazo yasan halinda yake ciki,
it's been long bai sata cikin idanunshi ba. Seda ta gama komai sannan ta fito inda
ta hango shi tsaye cikin daruruwan mutane amma ta ganeshi, ga mamakinta wani Irin
farin ciki from no where wanda tun kafin barinta kano rabon da ta tsinci kanta a
haka, zuciyarta ta bude wani sanyi ya dinga ratsa ta, wata nutsuwa Tana shigarta.
Shikenan ta faru ta Kare, zuciyarta is cruel ta cuceta.

Inda yake tsaye ya bada baya ta tsaya kamar me koyon magana tace

Ya.. Ya.

Da sauri ya juyo saboda muryar da yaji ta ratsa shi da yawa, idanunshi ya sauke Kan
fuskar ta dake sunkuye yace

Auta sannu da zuwa

Wai Auta? Karo na farko taji haushin sunan at least he should address her with
Sulaim amma auta is so casual Haba. Ranta a bace tace

Yawwa.

Daga haka ta zagaya gefenshi ta shiga yafi five minutes Yana kallonta tareda
mamakin me ya bata mata rai suddenly haka? Ko ganinshi ne ya bata mata ranta.
Kanshi ya gyada rai a jagule ya tada motar. Suka bar premises din gurin shirun da
yayi yawa yasa yayi turning radio station suna shirin Barka da Hantsi a Freedom
radio. Se time to time yakan tambayeta yadda ta Baro kowa shima answers dinta a
takaice suke hakan yasa ya kyaleta ko missing can din take.

Suna isa gida yana parking ta fito tare da dubanshi tace

Thank you.

Kallonta kawai yayi a ranshi Yana mamakin wannan halittar. Tunda ta shiga daki bata
kara fitowa ba ko abinci bata bi ta kanshi ba shikam ya fice yana ta kokarin
kammalla shirin tafiya Estonia.

_Anytime you lonely can I be the one you calling? I hope you understand? Please
take my hands and go with me my love_
**

Kwanaki takwas cif Tunda aka samu matsala tsakanin Khulthum da Yusuf, guess what?
Idan akace Kai kwadayye ne an gama, the worst thing a duniya shi ne ka Bari
makiyinka yasan weaknesses dinka Khulthum ta bari Yusuf ya sani don haka kwanakin
ya karar dasu wajen kashe mata kudi, wajen nuna mata ita din masoyiyarshi ce kuma
ya nuna mata jikinta ba shi ne a gabanshi ba kafin wani Lokaci sun dinke Duk Wannan
nadamar tayi evaporating into the clouds. Ta koma sabuwar Khulthum wadda take jin
da ba rayuwa take ba yanzun takeyi.

La'asar sakaliya, yamma har ta Fara yi suka iso cikin motar Yusuf ta mishi rakiya
wani guri, tayi kyau cikin pencil skirt da long sleeve top matching da takalminta.
Tayi kyau taji ta tayi fitting da mutanen da ta samu a gurin saboda yawancinsu Irin
shigar ce a jikinsu se wanda tasu tafi nata watsewa, kanta scarf ne me Dan girma ta
daura wrap me kyau akanta, Yana parking ta wareshi tayi rolling amma dukda haka
nayi tunanin ya akai Mama ta barta ta fito a haka? Hannunta ya Kama yayi kissing
wanda yasa taji electrons suna passing jikinta. Dagowa tayi bata hanashi ba se
murmushi da ta sakar mishi. Hannunta ya saki yace

Se gobe kenan?

Kanta ta gyada tace

I'll miss you

Ko?

Ya fada Yana kashe mata ido, murmushin tayi na assurance ta fito rikeda nylon da
karamar handbag dinta, yadda take tafiya kamar chameleon tana Kada jiki kamar wadda
take fadawa mazan gurin look at me. Tana ji suna ihun da suka saba amma ko
kallonsuu Batayi ba. Sede me tana zuwa ta tarar Ashir yana tsaye tamkar jiranta
yake. Gabanta seda ya fadi Amma ta dake taci mazu zata wuce ta gaban shi kawai taga
yayi blocking hanyar, dago idonta tayi ta watsa mishi kallo me Cikeda kaskanci Tace

Bani hanya!

Bai taba mata kaskantaccen kallo ba me Cikeda tsantsani ba se ranar yace

Nayi da na sanin furta kalmar so gareki, naji kunyar tunanin Baki matsayin uwar
'ya'yana, Nayi asarar Bata Lokaci na gurinki......

Dakata Ashiru ko whatever your name is! Kayi kadan ka cimin mutunci saboda wata
useless 20,000 dinka da kake tunanin ta siya maka ni! Allah ya kiyaye. Nima na fika
bakin cikin tarayya da kai abun kunya na tsaya da bai not knowing dubannin mazan
dake waje suna jirana.... Hopeless element kawai!!

Tana gama fadar haka ta balle Jakarta............


Shatuuu ♥️
[7/29, 6:16 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU*
24

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad
.....Ta Balle Jakarta wadda a ciki kudi ne da ya tasarwa 50k, cikin fushi ta irgo
20k ta zura mishi cikin aljihun gaban shaddar dake jikinshi sannan tace

Ga tsiyar ka nan, ga kudinka da Kake tunanin ka siye ni dashi, aje can me tsautsayi
ta dauka amma banda ni Ummu_Khulthum na wuce ajinka Wallahi.

Tana gama fadar haka ta buga mishi kallon wulakanci sannan ta wuce ciki abinta,
kallonta yake tayi bakinshi a bude tamkar statue haka ya zama a tsayen yana tunanin
da gaske Khulthum ce? Da gaske? Shi ne abinda ya samu bayan shekarun da ya dauka
zaman jiranta, Yana dakon sayayyarta. Tabbas kowa ka kalleshi ka barshi kawae.

Zan iya ce muku Wannan shi ne mafarin lalacewar rayuwar Khulthum, that's what makes
Khulthum what she was a halin yanzu amma ko yaya kuma kome Khulthum ta zama ita ce
sanadi.

Cikin gida ta shiga tana jin tamkar ta taka Arfa tana jin ta yakice kwallon
mangwaro, Tana jin Duk duniya she's free. Kowa harkarshi yake hakan yasa ta shige
daki ta Adana kudaden sannan ta cire kayanta ta zauna itada zani se vest Tana
kallon film cikin system.... Ni dai nasan Khulthum batada system amma bansan inda
ta samu ba. Tana nan kwance ta jiyo muryar Baba yana kwallawa Mama kira. Tsaki tayi
a ranta tana fadin na tsani gidannan kayi aurenka babu ruwanka da hayaniyar nan.
Bata Kara jin duriyar Baba ba se bayan 10 minutes sannan taji salatin Mama tana
fadin

Amma yarinyar nan anyi 'yar banza. Khulthum! Khulthum!! Khulthum!!!

A hankali ta Mike Tana mitar kiran da ake mata kamar wadda tayi sata kuma Bama haka
ba ita batai tunanin cewar abinda ya faru tsakaninta da Ashir zai iya shigowa gidan
da wuri har hakaba. Fitowa tayi ta yafa dan karamin mayafin abaya Tunda taji muryar
Baba, suna tsaye tamkar zakaru itama taje ta tsaya tana binsu da kallo

Dan ubanki me kika yiwa yaron can Ashiru?

Kallon Mama tayi ta kalli Baba Wanda fuskar ta kasa boye damuwar da yake ciki tace

Shi ne ake ta kwalla min kira kamar nayi wani laifin.

Mama wadda zuciyarta na wuya tasa hannunta ta bige bakin Khulthum tace

Mu sa'anunki ne kike mayar mana da magana? Uban me kika yiwa bawan Allah nan.

Tsaki tayi a ranta tace ni kuma bawan shedan kenan? Dauke kanta tayi hakan yasa
Mama tayo kanta zata buge ta Baba yace

Karki taba ta, khaltume zauna.

Babu musu ta zauna kamar yadda yasa Mama ta zauna shima hakan yayi kafin ya gyara
muryarshi yace

Ina saurareki

Baba bana son shi, nace mishi ya rabu dani yaki saboda kamar zargina yake kuma yayi
tayimin gori......

Shi ne kika maida masa Dubu ashirin dinshi?

Mama ta katse ta, Baba ne yace
Maman Aisha Kada ki Kara magana se na baki izinin yin hakan, ke khaltume kikace
bakya son shi?

Kanta ta gyada batareda ta furta komai ba, kai Baba ya jinjina yace

Lokacinda kika kawo Ashiru a matsayin me nemanki, ke Kika karbi kudinshi ko ni?

Kai ne

Yayi kyau, me yasa yanzun kika bashi Bayan Baki sanar dani ba, karamin mutum kike
son maidani?

Bakinta ta turo a ranta tace wai karamin mutum? Shi babba ne Dama? Talaka futuk se
shegen policy na banza da na wofi!

Ganin haka yasa Baba ya gyada Kai tareda ciro sababbin 1000 naira notes guda
ashirin ya mikawa Khulthum yace

Ga kudinki nan na mayar mishi da nashi, Amma ki sani kin nuna min ni ba ubanki bane
kuma duk Abinda zai faru dake hannuna bazan kuma sawa a ciki ba. Ke kuma Maman
Aisha

Ya juya kan Mama Ya cigaba da fadin

'yar ki ce na tsame hannuna daga kanta, Duk wani abinta kukai wa dangin mahaifinta.

Haba Malam! Haba

Kanshi ya girgixa yace

Ki bar maganar kawai. Aisha!

Dama tana kusa se gata ta fito ta tsugunna gefen Khulthum wadda Tana ta Harare
Harare a ranta tana ayyana taji dadi da me yake mata zai zo Yana kumfar baki kamar
ubanta, ita Wallahi tun tuni take son komawa dangin ubanta me take tsinta anan?
Banda wahalarsu da aka daura mata. Zancen da Baba yake Yi ne ya saka ta dawo
hayyacinta

.......Daga yau inhar kin daukeni mahaifi inason duk lokacinda Ashiru ya shirya ki
aureshi, don na Karba kudin 'yar uwarki na maida kanki.

Mama ce tayi saurin fadin

Haba Malam, ya zaayi haka? Idan Khulthum a bacin rai ne fa tana son abinta fa?

Mamaki kwance saman fuskar Baba yace

Dama na dade da sanin haka, khaltume a gurinki ita kadai ce 'Ya , na miki uzuri
saboda haka dan fari yake amma son kan naki yayi yawa. Ki sani na Bata dama don
haka A'isha ki sawa ranki bakida miji se Ashir sede idan wani cikinku ne ya mutu ko
kaddarar rayuwa!

Mikewa yayi Don ficewa Khulthum tayi saurin mikewa tace

Basai an nuna min cewar banida uba ba, basai an nuna ni agola bace Aisha ita ce yar
masu gida, idan da kara kwarton uwa ai uba ne, naki abu sannan abawa Aisha shi ba?
Da idan kunsan yar ku kuke son ya aura meye abin labe......

Ke amma 'yar iska ce, Baban kike fadawa haka saboda bakida mutunci?
Amir ya fada wanda Shigowarshi kenan yaji diban albarkan da Khulthum take musu.
Juyowa tayi ta kalleshi tace

Nayi din kuyi abinda zakui, Dan rashin mutunci.....

Bata karasa ba saboda yadda Amir yayo kanta tamkar zaki sede bai Kai ga yin abinda
yayi niyya ba Baba ya dakatar dashi tareda fadin

Kyaleta, batada laifi. Uwarku ce me laifi don haka ko na fita kada wanda ya kulata.
Allah yayi muku albarka.

Yana fadar haka ya sa kanshi ya fito, Mama daki ta wuce tunda ba Abinda zatace kuma
a ganinta Baba yaso kanshi ne da yawa.


Cikin makeken office dinshi na Managing Director of TitαΦ Flours Yana zaune kan
kujerar yana rocking kanshi, Kwana biu nan bashida nutsuwa sosae ya rasa inda zai
saka ranshi yaji dadi. Knocking yaji yasan bazai wuce secretary dinshi ba hakan
yasa ya bada izinin shigowa,

Sir, Kabir is here

Let him in

Ya fada batareda ya dago ba, ba'a fi 3 minutes ba Sega Kabir ya turo kofar ya
shigo, Yana ganinshi ya Mike suka dawo kan cushion din office Bayan sun gaisa aka
kawo musu coffee, Seda suka shanye tas kafin Kabir yace

Akwai wani move ne? Naga Kwana biu kamar kana da damuwa.

Tsaki Musbahu yayi yace

Ba kamar bane ina da ita, kana ji ko Amra zan aura ne?

Cikin rashin fahimta Kabir yace

Amra? Kada Kace min 'yar Baba Balarabe

Ita dai!

Cikeda mamaki da kuma takaicin maganar Musbahu Kabir yace

Amma me TitαΦ ka samu matsala, ina tunanin ka yaje har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login