Showing 18001 words to 21000 words out of 121650 words
taga Junaid a tsaye Yana kallonta, kanta ta
dauke tareda pouting face dinta, se yaga tayi mishi wani kyau yaji if to say it's
okay he'll hug definitely hug her dan fuskarta ta nuna ranta a bace yake amma babu
dama hakan yasa yace
Shopping zamuje kiyi min text din abinda kike so kinji?
Unconsciously ta buga mishi Harara wadda tayi cikin sa'a ya gani hakan yasa ya zaro
ido da mamaki amma se ta dauke kanta tamkar ba ita tayi ba tace
Tohm.
Tana fadar haka ta tura kofar ta shige, kanshi ya shafa saboda ba haka zuciyarshi
ta aiko shi yayi ba, ta aiko shi yaji damuwar abinda take so sannan ya fada mata
abu me dadi, who knows he will mess up but he couldn't! Bazai iya ba he lacks
wannan courage din.
Fita yayi suka tafi Yana ta mamakin shi Sulaim ta harara, yayinda take kwance har
aka kusa kiran maghrib sannan tayi wanka ta bada farali, Tana idarwa wayarta ta
Fara ringing, Bro ta gani hakan ya tabbatar mata Junaid ne se ta samu kanta da kin
picking, sau biyu yana kira Tana kin dauka shima se ya hakura. Can Sega kiran
Ja'afar ya shigo, Kwana biu nan se taji yau tana daukin jin muryarshi, cikin
silvery voice dinsa yace
Ina gate gidanku fito mu gaisa.
Da gaske!
Ta tambaya Tana jin wani nishadi from no where
Come and see for your eyes.
Kit! Ya yanke call din, Cikeda zumudi ta Mike ta zaro wani plain lace peach zani da
riga, se kuma ta mayar ,ta janyo Abaya ash da silver stones se off white lace da
aka saka a edge din hannun da kasan Riga... Rolling tayi da veil din kayan ta fesa
turare sannna ta dauki wayarta ta fito anan sukaci Karo da Atika
Uwardakina Kinyi kyau, ina zuwa haka?
Sa ido yanxu zan dawo
Har ta tafi ta isa bakin parlour Se ta tsaya da gaske Ja'afar take wa wannan
zumudin ko kuwa? What if idan Junaid ya dawo suka hadu Don ta dan Lura baisan
tarrayar su? Tayi kusan 7 minutes kafin zuciyarta tace mata go shi matarsa Ya dauka
suka fita, se ke xa'ayi caging a hanaki. Da Wannan ta samu karfin gwiwa ta fita,
megadi na zaune Tace dashi
Baba Bari na karba sako
Bata jira me zaice mata ba ta fice, Itakanta bata taba ganin motar ba tana tunanin
ya sake mota ne, Tana isa inda yake ya bude mata ta fada Ciki ,tana rufewa ya ja
motar with full speed ya bar layin. Da mamaki tace
Yaya Ja'afar what are you doing?
Dariya yayi mata yace
Kin manta a kd kika ki bina kisha ice cream shi zan kaiki kisha yanzu.
Dan Allah don't do this kaga yaya bai sani ba Kada ya dawo bananan.
Bai kara kulata ba itakuma Bata fasa Yi masa magiya ba amma yayi iskar kare da ita,
hakan ya tayar mata da hankali.
A gida Junaid da Subay'a sun dawo, yana gama parking megadi ya sanar mishi Sulaim
anzo an dauke ta a mota kuma baisan waye ba.
Bakasan waye ba? Ni Kake cewa baka san waye ba?
Ya fada Yana nuna kanshi tareda nuna kanshi wanda hakan seda yasa megadin firgita,
hatta Subay'a mamaki tayi yadda ya Daga murya ashe basuga komai ba.
Gidan ubanwa ka barta ta fita? Wayace ka barta ta fita?
Subay'a ta matso zata rike hannunshi ya juya kanta
Don't you dare touch me.
Se taja baya saboda yadda ta tsorata da yanayinshi, Ya dinga masifa wadda tasa baki
daya veins din kanshi suka tashi, yayi yayi se kuma yayi shiru ya dinga safa da
marwa yana karkada kanshi, baki daya kwakwalwar kanshi ta cushe waye ya fita da
ita? Ina kuma taje?
Ganin yanayinsa yasa na aje wayar haka kada nima yar rahoto ya make ni! Lol......
Waye zai bawa Junaid ansa NE? Ya haduwar Sulaim da Junaid zata kasance? Me Ja'afar
ke planning yi kadafa yayi!
Shatuuu♥️
[6/23, 5:20 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
6
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
LLB1 yayi shiru saboda wata zazzafar test da akeyi ta philosophy, gaba daya kowa
hankalinshi yana kan paper dayake rubuta test dinshi, inda Sulaim take naje abin
mamaki Tana zaune gefen Khulthum wadda itama dukkan hankalinta ya ta'alaka wajen
test din. Baifi minti goma ba daya daga cikin malamin yace
Pens up.
Aje pen din Sulaim tayi tareda sakin ajiyar zuciya, yayinda ta gefenta ma hakance
ta kasance, a hankali suka dinga bi suna tattara papers din kafin suka fice.
Khulthum ce ta Fara kallon inda Sulaim take wadda hankalinta yana kan wayarta tana
karanta text din Junaid akan idan ta tashi ta sameshi a office dinshi, se ta
tsinkayi muryar Khulthum tace
Ya test din?
Murmushi tayi Wanda ya fito da gapped teeth dinta ta dago tace
Alhamdulillah, tayi sauki not as expected.
Yadda tayi magana shi ya fara jan hankalin Sulaim, itama martanin murmushin ta
mayar mata tace
Gaskiya kam amma......
Kafin ta karasa class rep dinsu ya bayyana gaban class inda ya bada announcement
din Logic class baxaiyi taking place ba don haka kowa is free now. Kowa murna yayi
mussaman yan nesa da suke son barin kano ranar don an tafi mid semester break, tare
suka mike suka jero har wajen class, Sulaim tace
Bari na tafi ana jirana se Bayan break.
Murmushi Khulthum tayi tace
Allah ya kiyaye nima na tafi ayi Hutu lapiya.
Kanta ta gyada mata kafin kuma tace
Bansan sunanki ba fa.
Nima haka, Sunana Ummu_Khulthum
Ido Sulaim ta dan zaro kafin tace
Ummu_Sulaim
Tare da mika mata hannu sukai musabaha, basu bar gurin ba seda sukai exchanging
phone digits, Khulthum na fito da wayarta wata Infinix note ce hannunta ta zama
babbar yarinya don a cewarta dole a dama dasu, shi kanshi kayan dake jikinta ba
karamin amsar ta sukai ba, hardly ka hasaso cewar ga daga gidan data fito, yadda
take tafiya a hankali kamar bazata taka kasa ba shi ya fara janyo hankalin Huzaifa
dake tsaye gaban motarsu da dukkan alamu wani abun yake jira, ita bata Lura da shi
ba hankalinta Baki daya ya tafi tunanin Sulaim, yarinyar ta burge ta she's simple
yet classy, kuma kana kallon yanayinta kasan Daga gidan data fito don wani zobe na
gold data lura dashi hannun Sulaim din, fatarta ma is flawless. Tana ta wannan
tunanin taji alamar anyi parking gefenta, amma da yake Khulthum is Khulthum ko daga
idonta Batayi ba balle ta kalli gefenta inda motar take haka ta cigaba da
tafiyarta, Huzaifa dake ciki yayi murmushi sannan ya bude motar ya iso inda ta
tsaya ita a dole napep take nema nan kuwa addu'a take a ranta Kada ya tafi. Abinda
ya fara futawa shi ne
Kin burge ni.... Kizo Nayi dropping dinki dan kyakyawa kamarki bai dace rana ta
doke ta ba.
A hankali ta juyo da fuskarta ta sauke Kan tashi, bashida tsayi don idan ya fita da
kadan zai fita, kana kallonshi kasan dan Hutu ne kuma dan gayu, naira tana kuka
hannunsu.
Nagode
Ta bashi amsa kafin ta kara matsawa gefe don tarar napep, shima juyawa yayi ya Daga
kafada alamar Kinyi missing yaja motarshi ya barta a gurin Cikeda mamaki Don bata
taba tunanin hakan zai faru ba, tabbas ta bar opportunity dinnan ya wuce ta, a haka
a kufule ta samu napep shima ya dinga raina mata hankali dayake ya sameta a Bagas
se bata kulashi ba, haka ta isa gida abin Yana ta damunta.
Sulaim na zuwa kofar office din Junaid tasa hannunta tayi knocking, cikin deep
voice din nan tashi yace
Come in.
Hannu tasa ta bude kofar, bakinta dauke da sallama ta shiga, yana zaune kan
kujerar, yayinda wani wanda ta saba ganinsu tare kuma take tunanin shima lecturer
ne Yana zaune opposite him.
Yaya barka da Rana
Ta furta lokacinda ta iso tsakiyar office din, kafin ya amsa ta dubi bakon nashi
shima ta gaisheshi maimakon amsawa se yace
Sulaim right?
Kanta ta gyada, shi kuma Junaid ya zabga mishi harara wanda yasa ya kwashe da
dariya cikin kankan da murya yadda Sulaim ba zataji ba yace
Se na fada mata Wallahi.
Itadai tana tsaye ta dauke kanta daga kallonsuu taji Junaid yace
Auta koma kan cushion ki zauna kafin na gama.
Babu musu tayiwa kanta masauki tareda tunanin Yaushe rabon da yace mata auta ita
kanta ta manta last time din. Wayarta ta ciro ta Fara abubuwa da bansan me takeyi
ba, wajen Mintina talatin ta dago idonta cikin sa'a shima kallonta yake se suka
hade cikin na juna, dauke kanta tayi shi kuma ya bata rai Wanda kadan ne Ridwan
dake gefe baiyi dariya ba haka suka karayi wajen sau uku sannan Junaid ya gyara
murya yace
Ya akai ne?
Bakinta ta turo tace
Tafiyan fa?
Idonshi ya kura mata yace
Zuwa ina kenan?
Kaduna mana, yau fa an tafi mid semester break.
Kanshi ya dauke don kwatakwata bayada niyyar ta tafi wani gurin better ta zauna don
shi se yanzu yake ganin Tun tuni me ye dalilin da Tunda su Daddy suka rasu bai
dakko ta ba ya bari su Mami suka dauketa. Ganin yayi shiru yasa tace
Yaya flight din fa 6pm zai tashi
Da sauri ya dago Cikeda mamaki yace
Waye yayi miki booking, you didn't even let me know.
Tun last week Ja'afar yayi mata booking ko Mami bata sani ba, to yanxu tasan inhar
yasan Ja'afar ne tafiyar sede a fasa,
Mami tayi booking fa,
Junaid baice komai ba ya mike shida Ridwan suka fita, suna fita ta Mike
kafafuwanta. Acan Ridwan yace
Ka kyaleta ta tafi, kada kana takura mata idan ba haka ba Abinda muke nema bazamu
samu ba.
dafa kanshi Junaid yayi ya sake jinginar da jikinshi a jikin mota yace
I don't want her to go, nafi son kullum ina ganinta by my side.
Kallonshi Ridwan yayi yace
Kada ka zama me son kanka, to me yasa bazaka fada mata ba.
Da sauri Junaid ya dubeshi Yana zaro ido kafin kuma ya fara girgiza kanshi yace
Is not yet time and kasan yanzun haka tare suke da Ja'afar, ni ina tunanin shi yayi
booking flight dinnan Don there's no way Mami zatayi batareda sani na ba.
Tabdi! Ja'afar Yana son ta?
Ridwan ya fada Yana kara jinjina abin kafin yace
Abokina ka hakura mana.
Murmushin takaici yayi yace
Da zan iya da tuni na hakura, bazan iya bane na kasa dangana.
To idan bazaka iya hakura ba is better you let her know, yarinyar da alama bazatayi
wahalar shawo Kai ba.
Dariya Junaid yayi yace
Ba haka bane, shi ne kawai Abinda mutane Ke gani a tattare da ita amma ni nasan
taurin kan Sulaim se addu'a.
Sun dade suna tsaye har Sulaim ta gaji da jiranshi zata kirashi ya turo kofar ya
shigo, tashi tayi ta zauna Tana kallonshi, shima kallonta yake har ya zauna inda
Ridwan ya tashi yace
Kinyi sallah?
Kanta ta gyada yace
Mu tafi kenan?
Take wani murmushi ya subuce mata, bai kulata ba suka fito Zuwa mota, lokacin awa
daya ta rage flight dinsu, kallonshi tayi yadda yake tuki kamar bayaso tace
Yaya zanyi missing flight din fa
Baice da ita komai ba ya cigaba da takunshi itama tayi iskar kare dashi tareda
daukar wayarta tana ta danne danne taji muryar shi yace
Zaki dauki abu a gida ne?
Dago kanta tayi tace
A'a na saka a booth Tun safe
Seriously? Kin gaji da ganina ne har haka?
Kawai abinda yaji bakinsa ya furta kenan, lumshe idonsa yayi a ransa Yana fadin you
messed up Junaid. Itakam kallonshi tayi tace
A'a Yaya, ina son kawai zuwa ne.
Kanshi ya gyada bai kuma fadar komai ba saboda gudun kwafsawa haka ya kaita airport
seda aka gama komai kafin suka rabu, tana ta murna wadda ta kasa boyuwa shi abin
har mamaki yake bashi ma.
A airport tana sauka ta fito a departure hall ta hangoshi a tsaye ya harde
hannayensa Kan kirjinsa, Yana cikin Kaftan coffee da hula a kanshi yayi kyau har ya
gaji da kyau, Kada Ku manta Duk yaran Mami Ja'afar Yafi kowa kyau, idanunshi Yana
cikin eyeglasses fari tas, sede yana tsaye da wata azabbabiyar kyakyawar Yarinya
Irin lousy kyau dinnan wanda abinda zaka fara hangowa kenan, suna tsaye Sunata
dariya Irin abinda ake fada yayi dadi, gaba daya se Sulaim taji tamkar karta karasa
gurin amma se ta dake ta isa inda suke fuskarta babu walwala ta zagaya Dayan kofar
ta bude ba tareda tace komai ba ta shiga ta zauna amma ko bata fada ba kunsan how
it feels kaga Abinda kake fadi tashi a kanshi, kake fatan ya zama naka na har abada
yake tsaye da wata, abinda taji yace shi ya sake dugunzuma ta
Bari na wuce Kada baby sis tayi ta jira.
Seda ta zagayo inda Sulaim ke Zaune tace
Baby Sis ki kulamin da baby na naga Yana ji dake.
Kamar an buga mata guduma haka taji "Baby sis" like serious, shiru tayi ta sunkuyar
da kanta Tana ta battling da hawayen dake son zubo mata se taji ta wulakanta....
Yes wulakanci ne. Shima jiki a sanyaye ya shigo but being the Ja'afar se cewa yayi
Sweetm se ki bani tsoro yadda kika Bata rai dinnan.
Ko kallonshi Batayi ba ta bata rai Haka ya aje wayar shi saman cinyarta ya fara
driving sede yadda yake driving kawai will tell you cewar baiji dadi ba. Haka suka
tafi shiru kamar anyi rasuwa Duk Surutun Ja'afar kasa magana yayi se can yace
Susu ba fushi zakiyi ba at least let me explain.
Ban tambayeka ba.
Come on Susu why you behaving like this.
Mtsssssssw
Taja tsaki wanda ba Ja'afar ba hatta ni Seda nayi mamaki, yadda take kada kafarta
da kuma fuskarta ya nuna bacin rai sosae. A haka bai sake magana ba har aka bude
gate din gidan, wani sharp breath tayi inhaling at least she's home. Yana gama
parking ta aje masa wayoyinsa ta fice, tana bude parlon Mami ta fito daga kitchen
hannunta rike da katon tray, a guje ta nufe ta itama aje tray din tayi ta rungume
abarta, wani Irin farin ciki ya dinga shigarsu a hankali Mami tace
Haka unexpected Autar Mami?
Murmushinta tayi daidai shigowar Ja'afar, bai kulasu ba ya wuce inda zai kai shi
dakinsu iatakam Mami tabi Zuwa sama rikeda tray din, ganin yanayin ta yasa Mami
tace
Auta kamar ranki a bace yake?
Boye fuskata tayi cikin hannunta tace
Babu komai na gaji ne Mami, Ina Baba ?
Yaje massallaci jekiyi wanka kafin ya dawo.
Babu musu tayi dakinta, se lokacin da ta shiga bayi Abinda ya faru daxu ya fara
dawo mata, wannan shi ne Karo na uku da suna Irin haka itada Yaya Ja'afar se take
ganin kamar ta sake mishi da yawa ne, a haka tayi wanka tana ta tufka da warwara.
Seda ta shirya sannan ta dauki wayarta Don duk expecting dinta Junaid ya kirata
amma ko message babu hakan yasa ta kirashi, yana zaune kan sofa a parlonshi Ahmad
yana ta damunshi akan se sunje siyo chocolate yayinda Subay'a ke dakinta kannenta
sunzo, kiran Sulaim ya shigo, kawai murmushi ne ya kwace masa tareda jin sanyi
cikin zuciyarshi. Shi kanshi mamakin yadda son Sulaim yayi masa Illa har haka yake,
gashi ita bata wani damu dashi ba a yadda take abubuwan ta, a haka dai kiran ya
katse. Kamar tana gabanshi tayi pouting lips dinta Wanda har ya zama jikinta tace
He'll not pick shima.
Tana shirin fita taji yayi returning call din, wani murmushi ta saki ta dauki wayar
ta kara a kunnenta Sede kafin tayi magana ta Fara tuhumar kanta dalilin da yasa ta
kirashi, meye take jinta special saboda yayi returning call dinta.......
Sulaim are you there?
Idan tayi Rantsuwa cewar babu mahalukin da duk duniya ya iya kiran sunanta Irin
yadda Junaid ya ke kira Batayi karya ba, Harda gunna, kalkala sufra, madda da komai
yake kira, kowanne harafi se ya bashi hakkinsa.....
Mhm
Mhm
Shima ya furta Yana rike wayar sosae, itakam jikinta duk yayi wani yum hakan yasa
ta kwanta
Talk to me, ya kika je?
A hankali in a whisper tace
Lapiya lau, Mami na gaisheka
Dan murmushi yayi me sauti har tajiyo shi
Ina amsawa, kije Kici abinci.
Pouting bakinta tayi tace
To Yaushe Xaka zo.
Da sauri ya zaro idanunshi amma yaji dif ta kashe wayar saboda cajinta ya dauke
Shit! Ya furta
Shatuuu ♥️
[6/25, 4:12 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
7
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣shatuuu095@wattpad
Tana tsaye gefen titi hannunta yana dauke da Leda baka da tambarin Sahad stores,
Tana Sanye da skirt da riga na atamfa purple da pattern na mint green, yayi mata
kyau, kanta ta yane shi da mint green mini veil, hakan ya bawa surar jikinta fita
dukkan wani shape seda ya bayyana. Tana nan tsaye wata flashy car ta wuce, se kuma
a hankali akayo reverse ya dawo daidai saitin inda Khulthum ke tsaye yayi wining
glass dinshi kasa....Huzaifa ne the rich brat shidin yaron wani senator ne a
Zamfara Yana level 4 a engineering cikin BUK , kana kallonshi kaga kwallo wanda
duniya take damawa dasu. Murmushi yake tayi yace
Abokaina suna kirana lucky Hu saboda I'm always lucky, luck is always by my side.
Gashi mun kara haduwa.
Kallonshi tayi batareda ta canja yanayin fuskarta ba tace
Amma kanada naci
Dariya yayi yace
Wanda ya nace shi zai dace ko ba haka hausawa sukace ba ?
Dauke kanta tayi, shi kuma se ta bashi dariya ita a dole Se ta ja aji ,
Ki shigo bai dace rana tana dukan kyakykyawa kamar ki ba.
Bude gaban motar tayi ta shiga yayinda murmushi ya kwace masa, suna tafe Yana mata
hira a haka har ta dan fara warewa, bai tambayeta inda zataje ba itama sanyin AC da
daddan freshener yasa ta manta, se ganinsu tayi a kofar More and More, dubanshi
tayi tace
Banan zan zo ba.
Irin dariyar shakiyanci yayi yace
Ooops nayi tunanin na dakko ki ne we're on a date, amma dukda haka muje ko abu me
sanyi ne kisha.
Ledar ta aje cikin motar sannan suka jero, mutuniyata ta saki fuskarta dama Irin
rayuwar da take so kenan, rayuwar jin dadi da yawace yawace kamar yadda take ji
take kuma gani idan aka dauke ta gidan yan gayu kunshi.
Tunda suka shiga suka samu guri take ta juye juye hakan ya so bawa Hu dariya amma
instead se ya musu placing order. Yana zama wayarta ta Fara ringing alamun kira na
shigowa, se taji kunyar fito da purse dinta saboda yadda ta kode, dauke kanshi yayi
hakan ya bata damar daukowa Sede take yanayinta ya canza saboda Ashir ne me kiran,
silent ta maida wayar a haka aka kawo musu Burger da chilled Smoov, itadai tasan
tana kallon abubuwan a kofar bakeries haka amma bata taba tasting ba, amma haka ta
danne ta dinga ci da kadan kadan har suka gama sannan ya bada bill dinsu suka fita,
a motar yake ce mata
A level nawa kike ne?
Dagowa tayi tace
Level 1 nake.
Kallonta yayi kafin ya maida titi yace
Shiyasa Naga Baki gama sakin jiki da mutane ba.
Dan dariya tayi a haka har suka iso wani ice cream