Showing 39001 words to 42000 words out of 121650 words
sannan ta kifa kanta ta Fara rera
sabon kuka, ita ba tsawar da yayi mata bace damuwarta a'a fushin da taga yayi shi
ne matsalar ta.
Cikin mota Junaid na zaune yayi clutching fist dinsa kamar wanda yake naushin wani,
why zai dinga tufka and wasu suna warware masa? Se yaji zuciyarshi na fadin you're
selfish Junaid, Kace kana sonta ne? Tanada magic ne da zata karanta abinda Ke
zuciyarka? Wani dogon ajiyar zuciya yaja sannnan ya bude motar ya fito ba tareda ya
koma takan Pizza dake Bayan seat ba.
Misalin karfe takwas da rabi na Daren wannan ranar Sulaim ta fito don tasan tabbas
an gama abinci kuma tunda tayi masa laifi is better ta fita basai ya tura kiranta
ba saboda gaba daya ta dauki alhakin komai ta daura akanta dukda batasan takamaimai
Abinda tayi mishi ba amma yadda yayi dazu tasan tabbas ita taja komai.
Gefen Ahmad ta zauna Bata kalli inda suke ba dukda yana ta taba ta amma bata biye
mishi ba saboda Junaid baya kan table din kuma yaranshi da matarshi har sun Fara
cin abinci hakan ya bata clue din he's not eating. Plate ta janyo ta dauki slice
din Pizza daya ta saka sannan ta tsiyaya tea ta Fara sha amma hankalinta sam baya
kan abincin don taste din ma Bata jin dadinshi, hankalinta Baki daya yana kofar
parlour Junaid. Har kowa ya tashi tana nan Zaune kuma bata cinye slice daya ba. Har
Tara da rabi tana nan Zaune Bata san jiran me takeyi ba tadai San ta kasa tashi ta
tafi, Baki daya tana jinta a takure Tana jin akwai Abinda is not in place, it
doesn't supposed to be.
Yana kwance yayi nisa da aikin da yake cikin system Subay'a ta shigo ta zauna gefen
shi tareda kai hannunta saman kanshi tana shafawa a hankali sannan tace
Dinner is set.
Dago kanshi yayi ya kalleta tayi kyau sosae saboda Dama ita ma'abociyar kwalliya
ce, hannunta ya rike yace
Inada aiki sosae se Zuwa anjima kawai kije kuci, zan ci nawa
Shikuma ya fadi hakan saboda yana avoiding haduwarsu shi da Sulaim ne amma yunwa
yake ji, kanta ta gyada batareda ta ce komai ba ta Mike Don ficewa yace
Dear, kice Sulaim ta fita taci abinci kada ta kwanta haka.
Da sauri Subay'a ta jiyo jin Abinda ya fada, tsira mishi idanu tayi ta koma inda ta
tashi ta xauna tace
Junaid meye tsakaninka da yarinyar nan.
Kallonta shima yayi baiji komai ba kuma Abu daya ne zai hanashi ba ta amsa for
Sulaim's well-being idan ba haka ba da se ya bata amsa daidai tambayarta.
Me kike cewa?
Ya fada Yana kallonta straight cikin idanu
Kaji abinda na fada ai, Meye tsakaninku kake mata wannan extraordinary kulawar,
Junaid sonta kake?
Tsaki kawai yayi ya cigaba da aikinshi dukda tambayar tata tazo mishi a bazata
saboda bai taba expecting zata dago shi ba amma akwai Abinda Junaid bai sani ba ko
minti daya sukai tareda Sulaim a gurin mutane definitely se an dago su to balle
Subay'a wadda Ke tare dasu kullum dukda batada fahimtar abu sosae sannan ba ta
cikin mata masu saka ido akan mazajensu. A fusace ta fice shi kuma ya dafe kanshi
Yana sauke ajiyar zuciya a gaggauce kamar wanda yayi kuka, ya dade kafin zuciyarshi
ta nutsa sannan ya cigaba da aikin da yake daidai da Lokaci daya Sulaim Bata bar
zuciyar shi ba, fuskarta kawai yake hangowa tana kallonshi lokacin da yayi mata
tsawa, sannan kunnuwanshi nayi mishi amsa kuwwar kukanta kamar an tsikare shi ya
Mike bai ma duba time ba ya fito Zuwa parlourn ga mamakinshi tana zaune kan dining
din tana ta juya tea din dake cikin mug kana kallonta kasan itadai tana gurin amma
tunaninta da hankalinta duka suna wani wajen, har ya zauna batasan yazo gurin ba
seda kamshin turaren shi yayi awaking dinta.
Seda ta kwantar da yaranta kafin ta kwanta gefensu ita ba kullum take Kwana dakin
miji ba ranar da abin nata ya motsa zataje shima se ya zuba mata ido, wayarta ta
janyo ta Fara neman layin Sulma cikin sa'a ta shiga kuwa amma har ta katse Batayi
picking ba hakan yasa ta kara kiranta wannan karan tayi picking
Sister Kin duba agogo kuwa goma tayi fa, ina fata lapiya?
Sulma ta tambaya
Inafa lapiya sister?
Me ya faru ni uwar Amna
Dan tsaki Subay'a tayi tace
Ina yarinyar da nake gaya miki tana karatu a gidanmu?
Shiru Sulma tayi tana son tunawa kafin can tace
Yarinyar nan wadda iyayenta suka rike Papa?
Da sauri Subay'a Tace
Ita fa, sister Junaid sonta yake!
So!? Haba dai Sister wanne irin so kuma?
Wallahi ba wasa nake miki ba, walahil azim sonta yake.
A'a dai Sister sede idan baki lura ba ta yaya Papa zaiso wannan yarinyar? Kede
kawai insecurities ke damunki amma da Papa zaiyi aure ai da tuni yayi, Dan Allah ki
fitar da hakan daga zuciyarki babu wani abu. Amma ke how sure are you?
Hawayenta ta goge tana jin haka ne kuma tabbas insecurities Ke damunta Tunda tasan
Junaid ba tsoronta yake ba idan har yana son yarinyar da da ta tambayeshi se ya
fada mata koda zatai Meye ne.
Yana bata kulawa wadda ta wuce gaban misali
Shikenan? Karki manta yarinyar marainiya ce kuma batada kowa se su idan basu kula
da ita ba yakike so suyi. Kiyi hakuri sister ki kwantar da hankalinki Zamuyi magana
da safe Abban Amna Yana jirana.
Babu yadda Subay'a zatai haka sukai sallama ta koma ta kwanta zuciyarta kamar zata
fito ga wani kululun abu da ya tokare mata makoshi amma ta kasa Miqewa ta sameshi.
Yana zama ta Mike Don komawa daki Amma cikin gaggawa yace
Koma ki zauna
Babu yadda zatayi haka ta zauna Tana jujjuya fork din data dauka, bai kara ce mata
komai ba ya dauki tea ya kai bakinshi Yana Sha yana dubanta se lokacin ya fahimci
kuka take. Tsaki yayi Wanda yasa ta dago idonta tana kallonshi tareda fadin
Yaya kayi hakuri
Shuru yayi ya aje mug din hannunshi tareda runtse idonshi, Sulaim is not helping
matters kara tabarbara komai take idan ba haka inhar tasan yadda kukanta yake
dukanshi baya tunanin zata yi Koda fushi balle takai ga yin kuka.
Is ok, tashi kije ki kwanta.
Kanta ta girgixa Tana share hawayenta Tace
Kuma fushi kakeyi fa, ni bansan Meye nayi maka ba
Kinsan bana son musu ki tafi daki.
Haka ta Mike ina mamakin kukan me takeyi, seda ta shiga daki kafin ya dafe kanshi,
inhar ya cigaba da haka tabbas zuciyarshi ta gaji da boyewa, he's tired ya kamata
yayi uncaging zuciyarshi ya sanar mata amma yana ganin kamar Lokaci baiyi ba, Yana
ganin is too early hakan ya kasance.
Washegari karfe bakwai Sulaim ta fito da books dinta tayi bak yard din gidan inda
nan ne window din Junaid yake ta zauna kan kujera dake aje a gurin ta Fara karatu
Tunda jiya Bata samu tayi ba batasan se su Khulthum sunzo ana karatu tayi kirikiri.
Tayi zurfi sosae cikin karatun taji muryar Junaid Daga dakinshi Yana fadin
Ya zanyi Ridwan na rasa tattaro karfina Naje, ina ganin kamar Lokaci baiyi ba.
Tsaki tayi ta cigaba da Abinda take, se can wayarta ta Fara ringing tana dagowa
taga Junaid dinne, Seda gabanta ya fadi kafin ta tattara courage din ta dauka kafin
ta gaisheshi yace
Ina kika je
Kallon gurin tayi tace
Ina backyard karatu nake
A hankali ya sauke ajiyar zuciya yace
Ki dawo ciki.
Bai jira amsarta ba ya kashe wayar sannan ta tattare books dinta ta nufi cikin
gidan, suna zaune a parlour suna kallo, ta zauna a gefe tace
Yaya ina Kwana, Anty an tashi lapiya?
Lokaci daya suka amsa mata, Subay'a Tana ta binta da ido tamkar tana son gano wani
abu a tattare da ita, haka ta wuce daki tayi wanka ta shirya cikin gown ta material
sannan ta zauna gefen gado ta dauki wani picture dake jikin wani kyakyawan frame ta
kalla tana shafawa idanunta sun cicciko da kwalla, hoton Daddy da mummy ne suna
murmushi sosae, da na kalli hoton tabbas Junaid da Baban Sukam yake kama tamkar
yayi kaki haka suke. A hankali ta furta
Allah ya jikanku ya rahmushe ku.
Kafin ta aje ta dauki wayarta ta turawa su Khulthum address din. Tana nan Zaune ta
dauki wayarta ta kunna data ta shiga Wattpad don debewa kanta kewa, dake bata iya
karatun Hausa ba yasa yawancin novels din library dinta are English. Wani a ciki ta
Fara karantawa kafin wani Lokacin har hankalinta ya kau Daga tunane tunanen da
take. Atika ce tayi sallama ta shigo tace
Anty Sulaim Kinyi baki a parlour.
Da sauri Sulaim ta Mike ta fito fuskarta kamar gonar auduga Don murna she can't
believe cewar su Khulthum ne, ai kuwa su dinne suna Zazzaune Khulthum tana ta kalle
kalle, kujera ta samu ta xauna Tana fadin
Sannunku da zuwa har nayi fushi.
Khairi ta maka mata harara tace
Ke kika sani dai
Dariya sukai sannan suka gaisa tace
Muje ku gaisa da Anty Subay'a.
Tashi sukai suka bi bayanta har parlon Subay'a Tana zaune itada su Ahmad tana koya
mishi two letter words, dago idonta tayi tana kallonsu fuskarta kamar kullum har
suka zauna suka gaisheta ta amsa musu sannan suka Mike suka koma dakin Sulaim inda
Atika ta cika musu gaba da abinci da drinks seda suka ci suka sha ana hira sannan
suka Fara karatu. Se Azahar sukai sallah sannan Khulthum ta bude Jakarta ta ciro
hadadden lallai da cone na kunshi tace kowa ya zauna ta mishi kunshi, gaba daya
suka tsaya kallanta Irin kada kiyi mana jagwalgwalo fa, dariya sosae Khulthum tayi
for the first time ever ta Fara basu labarinta tanayi tana musu kunshin da suke
gani a Temple of Hennah. A karshe tace
Don haka gaba daya rayuwata na tsara ta a Auren me kudi don yadda na tashi a
talauci bazan dawwama a talauci ba.
Khairi for the first time ta fadi abin hankali tace
Bake zakiyi deciding haka ba Allah shi zai tsara miki yadda zakiyi, kuma akwai masu
kudin da kwatakwata hankalinsu ba a kwance yake ba.
Sulaim tace
Hakane Wallahi, Kede Kiyi addu'a kuma kinga Ashir dinnan Allah ki daina wulakanta
shi.
Dariya Khulthum tayi tace
Ku bazaku gane ba, ki kalla dakin da kike ciki fa Bana aurenki ba na gidanku,
kingani da banbanci sosae.
Kai Sulaim ta girgixa tace
Ke kuwa ki godewa Allah wasu basu da gida gaba daya fa, kuma kina zancen me kudi
kince Marar aure, to at that tender age ina kike tunanin zai samu kudin da kike
mafarkin Kiyi?
Akwai su Bakiga Huzaifa ba, ba kiga Yusuf ba?
Se lokacin Aimana tayi magana tace
Ki daina wannan zancen Huzaifa ba kudinshi bane na iyayenshi ne kuma ko yau suka
fadi suka mutu dole a raba gado, yusuf is too young ace yanada kudin da yake dashi
Kinsan sana'ar da yake? Kimsamshi waye? Baki sani ba kun hadu a titi kawai ya gaya
miki kin zauna akai, Bari in fada miki bawai zagi ne ba amma yanzu rayuwar da ake
Bani gishiri na baka Manda, Dan wane se dan wancan kin taba jin dan Dangote ya auri
yar Malam Ayubah? Baki taba ba Sede dan Mangal da dan Ndimi, dangote da 'yar
yaradua! Ina ma zaki gansu ke balle suce sun kyasa is better ki zauna daidai inda
Allah ya ajeki ina ganin burin ki zaifi saurin cika amma idan kika matsa zakiyi da
na sani nan gaba.
Tabbas abinda Aimana ta fada is in place, daidai ne daidai kudinka iya shagalinka
ki tsaya inda kike kada rudin social media ya fitsare miki kanki, *MACE A YAU* ta
dauki buri ta daurawa kanta se tayi abinda waccen tayi is not right ki zauna inda
kike rabon kwado baya Hawa sama ko yaje se ya sakko haka bahaushe yace kuma haka
yake. Most charming guys masu kudi at a young age are arm robbers, thieves, gays ko
wani abun ina ganin guntun gatarinka yafi sari ka bani. Is high time we change that
fact na cewar mijin da zan aura se ready made not sugar daddy, single ta yiwu
babanki at that age baya da komai to meyasa zakice se Kinyi, *KALUBALEN MU* wannan
Itace *RAYUWARMU A YAU* sannan komai *MUQQADARI NE* daga Allah shi zai tsara maka
komai Amma rashin yadda da hakan yana daya daga cikin *MATSALARMU A YAU* kuma ita
mace Allura ce cikin ruwa *ME RABO KA DAUKA* Shiyasa *GIDAJENMU* bazasu taba rabo
da matsala ba saboda hakan ya kamata mu gyara rayuwarmu.
Shatuuu ♥️
[7/15, 10:32 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
19
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣shatuuu095@wattpad
Duk wanda aka yiwa maganar da Aimana ta fadawa Khulthum idan har zai dauka yaci ace
ko da na wannan lokacin ne ya dauka amma khulthum gani take to idan ta tsaya a
wannan gurin me ta samu? Wacce ribar zatace ta samu? Babu! Tunda har yanzu cikin
samarinta babu Irin Wanda idan ta tsaya sukai hoto dashi tayi posting zataji ana
comments da irin "oh Allah ina kika hadu dashi? Awwnnn Dama kinsanshi ne? I'm
envying you? Wannan crush dina ne" words of such haka take so to wanne ne a ciki?
babu shi. Tana gama yiwa Khairi ta aje cone din tayi mika sannnan ta koma gefen
gado ta zauna Tana ta kallonsu kamar yadda suma suke kallonta, se tayi murmushi
tace
Dangin babana basu nema na, sun Kori Mamata da ni basu kuma nemeni ba, so inason na
auri me kudi wanda aurena se ya girgixa ilahirin Nigeria, se sunyi Dana sanin
abinda sukai.
Tana yin shiru Khairi da Aimana suka kwashe da dariya, Harda rike ciki saboda
maganarta ta basu dariya, a yanxun ka kyautata rayuwarka ma kaga ba daidai ba Balle
ka rike wani shirme, yadda sukeyi babu kakautawa itakam Sulaim tambayar kanta take
shi aure ba bautar ubangiji bane ko kuma shi source din yanke talauci ne?
Kinsan ni ban taba mafarkin auren me kudi ba, ni akaran kaina nake son Nayi kudin.
I want to be my own boss naci gashin kaina ba under umbrella wani ba.
Khairi ta bata amsa Bayan ta gama dariyar.
Kinga wannan ra'ayinki ne, so nima hakane ra'ayina Duk inda me kudi yake ko
saurayin waye inhar yayi min I'll definitely make him mine.
Baki bude Sulaim tace
Muyi kaffa kaffa kenan.?
Gaskiya kam yadda nake ji da baby tsaf zan miki duka akanshi
Khairi ta fada suna kara kwashewa da dariya Don su duk tunaninsu wasa take, abinka
da wayayyu take aka bar maganar aka cigaba da zancen wani Korean movie da Sulaim ta
samo musu lokacinda taje kaduna daga gurin Jawad Kings woman. Sunata hira Aimana
tace
Nifa babu jaki a film dinnan irin Min Feng yana sonta amma shi dole gadinta yake a
karshe ya tashi a tutar babu se Kisa da akai mishi
Dariya Sulaim tayi tace
The useless brat ba kuma bata taba recognizing halin da yake ciki ba.
Khairi tace
Hakane fa, gwara mashi fa yana ganinta amma kinga Jin Ke dinnan Allah kadai yasan
yadda na tsaneshi naji dadin kasheshi da akai Wallahi.
Khulthum tace
Ni kuma baki daya Yin Zheng din na tsana
Ido a waje Khairi tace
King baki daya? Gaskiya kin zake.
Kafin a Bata amsa sukaji ana kwankwasa kofa, Khulthum ce ta Mike ta nufi kofar ta
bude gaban Sulaim ya dinga faduwa tamkar wadda Abu ya biyo ta, a ranta addu'a take
ubangiji yasa ba Junaid bane Don maganar Khulthum ta tsaya mata a rai so se taji
batason su hadu. Fortunately sega Atika ta shigo hannunta rike da fararen envelope
guda uku, Tana shigowa ta Kara gaishe dasu Aimana kafin ta mikawa Sulaim tace
Alhaji yace a Baki, wai ina Wayarki?
Se lokacin ta tuna wayar ma baki daya a silent take hakan yasa tace
Oh tana silent, ya fita ne?
Eh
Ta bata amsa sannan ta fice, Khulthum da babu kunshi jikinta yasa ta miko mata
wayar Sega missed call na Yaya, ya Ja'afar, Salim da wata unknown number. Ita
basuyi waya da Salim din ba jiya ya Kira tayi bacci gashi yanzun ta Kara missing
call din nashi. Junaid ta Fara kira bai dade yana ringing ba yayi picking
Wayan a silent yake ne
Ko kuma kina ta surutu ba
Ya fada Yana kallon Ahmad dake gefenshi. Murmushi tayi tace
A'a ne fa.
Shima murmushin yayi yace
Anyways, ga sako nan ki basu ki gaishesu ni na fita
Kallon envelope din tayi tace
Mungode Allah ya saka da alkhairi Zasuji, a dawo lapiya.
Kai ya gyada yace
Akwai Abinda kike so na taho miki dashi?
Kai ta girgixa tace
A'a, se kun dawo.
Daga haka sukai sallama ta dauki envelopes din batareda ta buda ba ta mimika musu
tace
Yaya yace a baku
Duka sukai godiya suka zura cikin handbags dinsu nan hirar ta koma kan Junaid wanda
Aimana ce kawai tasan shi amma su basu taba ganin shi ba
To Sulaim ki aureshi mana kiga yadda yake kula dake Yana kaffa kaffa da ke.
Khulthum ta fada , Sulaim Baki bude tace
A gidanshi muke fa matarshi tana nan, wayace muku wai soyayya muke.
Tsaki Khairi tayi tace
Ki cigaba da denying abin ai a bayyane yake, ko tone din muryarki ansan akwai
magana.
Haka sukai ta yi mata se ta sharesu kawai, ana La'asar aka cire kunshi yayi kyau
sosae suka dinga mamakin dama haka Khulthum take dama tanada wannan talent din amma
take neman tsayawa dogara da namiji. Wajen 5pm aka zo daukarsu Khairi zata bi
Khulthum Hu zai sauke ta a BUK, yayinda Nu'uman yazo daukar Aimana. Suna fitowa
tace
Muje kui sallama da Anty.
Parlonta suka nufa Sede Tun kafin su bude kofar muryoyi Ke tashi Wanda ya tabbatar
musu tayi baki, da sallama suka shiga yan uwanta ne dukda wannan ne Karon farko da
Sulaim ta gansu dukkansu Amma tana ganinsu jefi jefi suna Zuwa, mutane ne yan
rainin hankali da suke ganin kowa bai iya ba su kadai suka iya to haka suke, ga
kallon wulakanci. To tunda suka shigo suke binsu da ido suma su Khulthum haka, tare
suka gaishesu Subay'a dake zaune tace
Ya akai?
Sulaim ta kalleta saboda taji haushin tambayar, se ta kyaleta tace
Zasu tafi ne.
To
Kawai tace takaici kamar me haka Sulaim taji suna fitowa Surayya tace
Subay'a wannan yarinyar ce kanwar Junaid din?
Subay'a ta dago tareda fadin
Ita ce fa
Kan babban bala'i! Kika barta take Zaune a gidanki
Sulma tayi saurin fadin
Me yasa kuke haka itada gidan dan uwanta.
Samina tace
Yaya Sulma dan Allah Kiyi shiru, Amma Yaya Subay'a this is carelessness, how sure
are yarinyar ba spy bace.
Tsaki Suhaila tayi tace
Ke ta spy kike, taje tayi ta leken asirinta who cares? What matters kada ta juyawa
Junaid kwakwalwar kanshi, kinga kyau kamar Aljana.
Didim!!! Gaban Subay'a ya fadi kada fa hakan ta kasance, kada fa turo ta akai don a
aura mishi ita!
A'a Kada kui haka, Sister kada ki manta maganar da mukai dake, babu wani alaka
tsakaninsu amma idan kinji shawarata kenan kada ki tada hankalin ki a banza kuma
yazo baida niyya yaga Abinda ake gani a tare da ita.
Samiha tace
Gaskiya kika fada Sulma sede ina ganin kiyi watching yarinyar, saboda kallon da
take miki kadai Irin na baki gabana haka take miki.
Dakyar Subay'a ta hadiyi mugun yawu tace
Kallon da takeyi min kenan Tun zuwanta gidannan, akwai wasu abubuwa tattare da
yarinyar na rasa Meye