Showing 114001 words to 117000 words out of 121650 words
dawo aiki Sede kowa yasan ba'a bari a kwashe
daidai amma babu laifi lafiya ta samu!!!
Shatuuu ♥️
[9/13, 9:11 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
58
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
*This page is entirely, wholly dedicated to my ghost readers, those who read and go
without voting or commenting, shatuuu ♥️still appreciate and she loves Evey single
one of you*
_Oh yeah... It was revealed in the Qur'an that every soul must surely taste the
bitterness of death..... Allah baya barin wani don wani yaji dadi, this is life
nothing is permanent, everyone of us is waiting for his time..... Kui hakuri nasan
kunnuwana se sun gaji da jin complains, don't mind me... I love you_
A hankali ta Mike ta nufi toilet din dake cikin dakin da suke, Babu laifi jiki yayi
kwari sosae sede dukda haka ba'a sallame su ba don ana mata sphincter training hade
da treating wasu infections din da suka samu matsugunni a cikin jikinta. Alwala
tayi ta fito inda carpet din sallah yake a shimfide, hijab ta zura tareda kai
dubanta gefen da Gwoggo take takure, gabaki daya Matar ta rame tayi xuruxuru kana
kallonta kasan akwai abu me girma dake hanata sukuni a zuciya, Tunda suka zo kasar
Abu biyu take banda ibada da tarairayar Khulthum babu Abinda take, hakan yasa
Khulthum din hankalinta ya kwanta kafin wani Lokaci ta Fara maida jikinta tana
murmurewa gashi babu inda take zuwa banda ta sakko daga gado taci abinci Se sallah
ko wanka kafin wani Lokaci me tsawo AC tayi aikinta, skin din Nata ya zama flawless
tayi shar se daukar idanu take. Abu daya ne cikin zuciyarta damuwar past dinta
Wanda suke hunting dinta babu dare babu Rana har ta kan zauna Tasha kuka kamar
ranta zai fita, ko sau daya bata ga laifin Musbahu ba, bata kuma ji haushin Abinda
yake mata ba saboda whatever life be ita ce ta saka kudinta ta siya, ita ta kai
kanta har gidan Musbahu ta kuma dauki kafafunta ta kai dakinshi, inda hakane meye
laifin Musbahu wanda Allah ya aiko shi don tayi realising mistakes dinta through
him? Ita kanta a rayuwarta tasan she deserves abinda Yafi haka, tasan ta wulakanta
mutane ta ketare iyakar da Allah ya gindaya mata to ta yaya zata ga daidai?
A bangaren TitαΦ kam abin ya wuce gaban magana, Tunda suka hada idanu da gwoggo ta
zare nutsuwa, farin ciki da dukkan komai ta wuce dashi. Gaba daya ya koma tamkar
mahaukaci ya lalace ya daina fita ko ina sede gida se kuma massallaci, hakan ya
tada hankalin Kabir sosae don dama Irin su Musbahu basu iya tashin hankali ba Tunda
ba magana suke ba Balle su fadi wani abun suji sanyi a zuciyarsu, Wata ranar
alhamis Anty daddafe ya samu ya isa office saboda korafi da yake samu daga gurin
board members dinshi akan shafe wata daya da yayi baya Zuwa office kuma bai nada
kowa ba hakan yasa babu yadda ya iya ya koma, sede kallo daya zakai masa kasan Maza
suna wani hali.
Ya dade rikeda Biro hannunshi ga tarin papers cikin files da suke jiran signature
dinsa amma ya gagara nutsuwa ya karanta content din ciki Balle har ya saka hannu.
Tamkar wanda aka tsikara haka ya Mike ya dauki key din motarshi bai ko amsa maganar
da secretary dinsa ke mishi ba ya biyo lift Cikeda hanzari ya wuce zuwa motarshi ya
tayar tareda buga wani uban horn take securities din dake gurin suka Mike afijajan,
Allah kadai ya tsare zuwan shi gida, ko gate bai shiga ba ya yi wani mugun parking
sannan ya fito ya shigo cikin compound din a hargitse wanda yasa securities din
dake gurin maida dukkan Hankalinsu kanshi sede ko kallon inda suke ya durfafi part
din Khulthum, da kafarshi ya hankada main kofar dake ba a rufe take ba yasa ta budi
Sede wani Irin yanayi na sanyin jiki ne ya mishi rubdugu Lokaci daya saboda yadda
parlon yayi kura alamar babu mutane a gurin, wannan sassanyan kamshin da se yau
yake jin ina zai sake jin irinshi, jiki a sanyaye ya nufi dakinta Sede wayam ya
gani babu kowa a ciki, kaya ya hango a tukunkune akan gado hakan yasa ya isa gurin
tareda saka hannunshi ya bude amma wani wari ne ya dake shi hakan yasa ya ja da
baya yana kallon yadda kashi ya bata mishi hannunshi, runtse idonshi yayi da karfi
don yasan Khulthum ta samu wannan matsalar ta dalilinshi ne, don ana ya gobe zasu
hade da gwoggo ya iske ta a dakin kwance a wannan halin hakan yasa yayi ficewrshi,
yanzun ma tunawa yayi bafa Gwoggo kadai ya zalinta ba hatta Khulthum ya zalinta
kuma idan bata yafe ba bazai taba samun kwanciyar hankali ba.
Wasawasa Musbahu haka ya koma kamar wanda ya zare kwatakwata nutsuwa babu ita a
rayuwarshi hakan yasa Kabir yanke shawarar fada mishi inda Gwoggo take ko Za'a samu
ya daidaita saboda ba karamar asara ake tafkawa a oil, flour da food company din
saboda rashin shi. Wannan yasa Kabir kammala mishi komai ya rakashi airport yana
tsaye har jirgin ya daga sede a wannan lokacin Musbahu yaji Anya Yana son ganin
Gwoggo? Wani hukunci zata yanke mishi.
Misalin bakwai na safe a agogon dake kasar ta India, an kammala bawa Khulthum
maganinta na safe hakan yasa ta shiga tayi wanka sannan ta fito jikinta daure da
towel wanda ko gwiwa bai Kai ba, Gwoggo ta fita karbo wani sako hakan yasa Ita daya
kawai ta rage a dakin, a hankali taji an turo kofar an shigo amma ba'ayi sallama ba
amma kamshin turaren da ko a kabari taji shi zata gane maishi, kafin wani Lokaci
jikinta ya fara rawa tamkar mazari ko wadda ake kada mata wani abu haka ta jiyo
amma se me shi dinne! Musbahu ne tsaye helplessly, idanunshi sunyi jawur ga wata
uwar kasumbar da ya Tara ta cika Fuskarshi tamkar wani Tsoho haka ya koma, a
hankali ta dinga ja da baya tana girgiza mishi kanta yayinda shima yake takowa
cikin nutsuwar da ya rasa Yaushe ta dawo jikinshi, wani kuka ta saki jin ta kai
karshen bango, runtse idonta tayi jin ya riko hannunta cikin nashi tamkar Marar
lapiya ya bude bakinshi karo na farka ya kira sunanta wanda yasa ta bude idonta da
sauri suka sauka cikin nashi kwayar idanun, Khulthum ta sha hada idanu eye ball
into eyeball amma se ta tsinci kanta cikin wani yanayi me wuyar fassarawa ta manta
rabon taji Irin wannan tun akan Ashir, a hankali ta lumshe idonta saboda kallon is
so intense ga effect dinsa sosae yake ratsa jikinta. Shi dinma hakan ce ta kasance
bai taba tsayawa da mace so close haka ba, bai taba kallon mace cikin idanu ba,
Ashe haka abin yake, is this how it feels se yaji tamkar zuciyarshi na budewa ne
yaji wani bakon yanayi me nauyin gaske yana shigarshi and that's *LOVE*
Hannunta na cikin nashi yace
"Ban canci second glance daga gareki ba, I know I was bad I was never good amma
dukda haka ina Baki hakuri ki yafe min, kilan Allah ya sassauta min laifukan da
nayi mishi"
Kuka sosae Khulthum take lokacin ta zura wata bakar abaya wanda tun zuwanta ire
iren su take sawa kawai a jikinta, hannunta tasa ta kara rufe fuskarta zuciyarta
wani Irin sanyi take ji, tasan ko babu komai Allah ya yafe mata Tunda har ya
kaddaro shiryuwar Musbahu to ta yaya zatace bata yafe mishi ba, Bayan itama wasu
sunyi overlooking kurakuranta sun yafe mata kuma jikinta yana Bata Allah ya gafarta
mata sannan Hajiya Shatuuu ta yafe mata hakan yasa ta sauke hannunta tareda kallon
inda yake Zaune ya tsira mata idanu tace
"Allah ya gafarta mana duka,.... "
Bai barta ta kammalla statement dinta ba ya iso inda take ya rungume ta so close,
so tight and so romantic. For the first time Musbahu yaji sanyi a zuciyarshi yaji
wani abu ya darsu cikin zuciyar shi. A wannan halin Gwoggon shi ta shigo bakinta
dauke da sallama sede bata iya karasawa ba ganin Musbahu shima a rikice ya Mike se
kuma ya sunkuyar da kanshi saboda wata kunya da ta lullubeshi, Khulthum kwatakwata
Bata san Abinda Ke faruwa ba, amma kallonsu da tayi tasan they need privacy hakan
yasa ta dauki siririn mayafi ta yane kanta dashi ta fice tareda janyo musu kofar ta
samu wani guri ta zauna Tana jin tamkar tayi completing wani mission ne.
A cikin daki kuwa dukkansu shiru sukai kowanne Ya kasa magana se Musbahu ne ya isa
inda Gwoggon Ke zaune ya Dukar da kanshi tareda dira gwiwarshi a kasa yace
"Gwoggo ki dake ni, Kiyi min fada amma your silence is killing me... Nasan
kwatakwata banyi daidai ba, nasan Allah ya hana amma nakeyi, na cutar musu yarsu
banida wani uzuri gwoggo Dan Allah ki yanke min hukunci"
Gwoggo ita ta haifi Musbahu amma ta manta lokacin da taga yana kuka hakan yasa ta
janyo kanshi ta Dora a cinyarta Hakan ya tsananta kukan da yake itama ta Nayi a
haka suka shafe lokuta kafin Gwoggo tace
"Na yafe maka, kayi Istighfar ka nemi yafiyar Khulthum, ka rike sallah Tana Hana
alfasha sannna kayi Tuba sahihan kada ka komawa laifinka ka gyara tsakaninka da
matarka, ka dage da ibada Allah zai lamuranmu sannan ka manta na ganka ka dauka
hakan bai faru ba, let's move on"
Wata nannauyar ajiyar zuciya Musbahu ya sauke hawaye na Kara mishi sintiri, is the
thing he never expect, dukkan tunaninshi ya tafi a wahalar da zaisha kafin Gwoggon
ta saurareshi Amma Allahu Akbar gashi ta karbeshi ta yafe mishi.
Kwanaki biyu suka Kara aka sallami Khulthum suka wuce saudiyya Don yin umara,
Khulthum da Musbahu dukkansu masu laifi ne hakan yasa suka dage da addu'a ibada don
har gwoggo na musu fada akan rashin hutawa da suke sede akwai wata shakuwa a
hankali da ta Fara samun matsugunni cikin zuciyar kowannensu, a hankali suka Fara
damuwa da Al'amuran juna wanda gwoggo ke Lura dasu a haka sukayiwa Nigeria tsinke.
Hannunshi dake jike da ruwan da yayi Alwala yasa ya shafa fuskar subay'a wadda Ke
baccinta hani'an, a hankali ta gyara kwanciyarta hakan yasa ya dan bubbuga pilon da
take kwance se ta bude idonta Wanda bacci ne fal cikinsu ta kalleshi, shima
kallonta yayi yace
"Babe time for prayers! "
Kwabe fuskarta tayi kamar zatayi kuka saboda yadda bacci yake dadi kuma tasan nacin
Junaid dole Se ta tashi haka ta mike ganin ta tashi yasa ya fice abinshi, yana zuwa
yayi raka'atanul fajr sannan aka shiga sallah Yana idarwa kamar yadda ya saba idan
Subay'a keda girki to ana Idar da sallah zai wuce gidan Sulaim, haka idan Sulaim
dince Keda girki haka zaije gidan Subay'a hakan ba karamin kwantar musu da hankali
yake ba don sosae yake kwatanta adalci don idan Yana tareda Sulaim tana jin tamkar
ita kadai ce a duniyarshi haka idan Subay'a ce Wannan yasa kowaccensu take Zaune
lafiya.
Sulaim na cikin daki ta Idar da sallah gabanta bowl ne Cikeda custard wanda Seda ta
dama tukun ta tada sallah tsabar yadda yawunta Ke tsinkewa ko addu'a batayi ba ta
janyo bowl din ta Fara sha babu kakautawa, turarenshi ne ya fara isar mata da sakon
zuwanshi dake idan yazo key dinshi yake sawa kawai ya bude ya shigo. Kallonta ya
tsaya yi baki bude ganin yadda ta zage tsakaninta da Allah, shigowa yayi ya karba
spoon din hannunta yace
"Wai Dove meye sirrin custard ne? Ke yanzun da asuba ma sha kike"
Bakinta ta turo mishi tace
"Shiyasa nake sauri Karka shigo ka sameni, Barka da Asuba Heartthrob"
Zama yayi a gabanta tareda debo custard din ya kai mata bakinta sannan yace
"I'm fine baby sede missing din wannan shagwabar"
Rufe fuskarta tayi tana murmushi tace
"Kai Yaya na"
Bai bata amsa ba sakamaakon ringing din da wayarshi dake cikin Aljihun jallabiyar
jikinshi ta Fara ringing ya ciro, haka kurum yaji gabanshi yayi mugun faduwa Amma
haka yayi picking
"Mami barka da asuba"
Jin an ambaci sunan Mami yasa ta dago da sauri ta Kalli Junaid lokaci guda taga
yanayinshi gaba daya ya canja damuwa kwance saman fuskarsa, ga kuma saurin mikewa
da yayi Sannan ya fara ambaton
"Innalillahi wa Inna ilahil rajiun!!! Ya hayyu ya kayyum"
Cire wayar yayi Daga kunnenshi Cikeda tashin hankali yake kallon Sulaim wadda itama
take kallonshi gabanta se faduwa yake, hannunta ya Kama Yana jin yadda harshenshi
yayi nauyin abinda zai fada mata, haka kurum taji gabanta yayi mugun faduwa cikinta
yayi wani Irin hautsinawa, a hankali kamar me rada tace
"Yaya waye.....? "
Se hawaye Sharrrrrrr ya fara zubar mata daga idanunta tsabar tsoron me zai fada,
matsota yayi Zuwa jikinshi ya rungume hakan yasa ta kara fashewa da kuka, shima
jiki a sanyaye yace
"Kiyi hakuri Allah yayiwa Imratun Ja'afar rasuwa! "
Kallonshi ta tsaya yi kamar wata doluwa saboda son comprehending abinda ya fada
take, rungumeta yayi Tsam a jikinshi saboda yasan she's in shock ko ba'a fada ba,
hakanan dai tayi shiru har ya kira Subay'a yace ta shirya yanzun zaizo su wuce
kaduna don acan ta rasu Amma ga mamakinshi se cewa tayi
"Allah ya jikanta amma kui gaba na taho inda uzurirrika"
Baice mata komai ba ya kashe wayar tare da rike Sulaim ya zaunar da ita akan gado
shi kuma ya nufi wardrobe dinta ya janyo trolley ya zuba musu kaya zuciyarshi a
cunkushe tareda tunanin halin da Jabir yake ciki. Tunda Khulthum ta zauna Bata kuma
magana ba har driver din da zai kaisu yazo, haka ya janyo hannunta suka shiga mota
inda ta kwantar da kanta kan kafadarshi tareda runtse idonta, babu Abinda take iya
ji se wani azababben Ciwon Mara dake damunta a Wannan lokacin idanunta ta runtse
tareda matse hannun Junaid. Ita batayi kuka ba ba kuma tayi magana ba ta kuma kasa
tantance Abinda take ji banda Ciwon mara.
A haka suka isa Kaduna babu Wanda yake magana har suka isa gidan inda tuni Imratu
ta dade a makwancinta, saboda yadda gidan yake a cike haka babu yadda Junaid zaiyi
ya bar Sulaim ta shiga ita daya, idanunta sunyi ja saboda azaba da kuma tashin
hnkli, a parlor kasa ta tarar da mutane dankam inda ta hango Mami wadda kallo daya
zai fada maka tashin hankalin da take ciki ga idanunta sunyi luhuluhu tsabar kukan
da Tasha, cikin nitsuwa ta taka har gaban Mami sede kafin tayi magana wata mata
dake kusa da Mamin tace
"Meye wannan yake bin jikinki? "
Da sauri Mami ta dubi Sulaim din, jini ne ya bata mata zaninta hakan yasa Mami
janyota jikinta amma kafin wani Lokaci jini ya Balle mata ga azababben Ciwon mara
kamar zata mutu, tuni hankalin kowa ya kara tashi, Mami ta rasa yadda zatai se kuka
se Maman su Yaya Hanan ce ta kira Junaid a waya aikuwa se gashi shida Ja'afar
hankali a tashe akai Asibiti da ita amma cikin dake jikinta na watanni uku ya fice
Wanda babu Wanda ya san da zamanshi. Gashi ta zubar da jini sosae wanda dole Se an
kara mata!
Shatuuu ♥️
[9/12, 10:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A
YAU*
59
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
*Halo people of Wattpad Wallahi page din naku ne, you guys are Muah.... I can't
stop loving you exactly like the way I can't stop thanking you for always
supporting me and gingering me Up!*
Mami na Zaune gefen gadon da Sulaim ke zaune ta hada kanta da gwiwarta tana kuka
kamar ranta zai fita, yau Kwananta hudu a asibitin an samu anyi mata wankin ciki
sannan Tasha jini Leda uku, yanxun ta dawo hayyacinta sosae don haka ita yanzun
take kukan mutuwar Imratu, kuka sosae take Tun Mami na lallashinta har ta share ta
itama tana matsar kwallar saboda yadda take tuna wacece Imratu a rayuwarta, tasan
bata haifi mace ba amma Sulaim da Imratu sun mantar da ita wannan rashin da tayi.
Babyn dake kwance cikin peach Cot ta Fara kuka alamar ta farka, da sauri Mami ta
cirota Daga Cot din ta Fara jijjigata har yarinyar tayi shiru, tsaida kukan Sulaim
tayi ta miko hannunta babu musu Mami ta mika mata babyn, karbar ta tayi ta rungume
a jikinta wani Irin son babyn na ratsa zuciyarta rayuwa kenan duk yadda ake dokin
cikin Imratu ashe ajali ne don ita kanta batasan abinda ta Haifa ba tasan ta haihu
Daga nan jikinta ya rikice duk wani taemakon da ya dace an bata amma Allah yayi
lokaci yayi haka ta rasu ana kallo. Jabir kowa yasan yadda yake son Imratu babu
Wanda yafi shi shiga tashin hankali haka ya rungume Mami Yana kuka kamar karamin
yaro tamkar ba soja ba. Sede muce Allah yasa ta huta!
Mami da ta gama hada mata Madarar da akai musu prescribing ta mikowa Sulaim wadda
ta Fara bata tana jin tausayin yarinyar a zuciyarta, tasan me ake kiran maraici
tasan zafinshi dukda babu Abinda ta rasa amma iyaye daban suke ko me ka samu a
rayuwa kuma ko mai ka zama dole iyaye daban suke amma tasan wannan ba zata rasa
gata ba, bazata taba maraici ba kamar yadda itama ba tayi ba tasan wannan family
bazasu barta haka ba, ita kanta she's covered with love, tasan Abinda suke mata ko
Daddy da Mummy na raye ba Lallae suyi mata hakan ba.
"Sulaim ba zaki daina kuka ba, Imratu ta tafi addu'a kawai take bukata amma wannan
kukan naki yayi yawa, Kema kinga yadda kike bazai helping condition dinki ba"
Haka ta tsinkayi muryar Mami a kanta, hakan yasa ta goge hawayen fuskarta tareda
daura babyn akan kafadar ta don tayi gyatsa sannan tace
"Mami tausayin Baby nake ji, zata tashi batada uwa"
Karo na farko tun bayan rasuwar Imratu da Mami tayi murmushi tareda kama hannunta
tace
"Kina nan zatayi rashin uwa? Nasan idan kina raye ba zata taba kukan maraici ba,
inason ki rungume ta ki zame mata uwa kinji Auta ta? "
Da sauri Sulaim ta gyada kanta tare da kara kankame babyn daidai shigowar Baba da
dukkan yaranshi. Idanunta cikin na Junaid wanda ya dan fada Balle kuma Baban baby
idanunshi sunyi jawur ya rame sosae se ido da karan hanci. Kana kallonshi dole
tausayinshi ya kama ka saboda yana cikin mawuyacin hali wanda shi kadai yasan yadda
yake axabtuwa da rashin Imratu.
Dukkansu kan carpet din da Mami ta shimfida suka zazzauna, seda suka gaggaisa aka
Kara jajantawa juna rashin Imratu da barin da Sulaim tayi kafin Baba yace
"Jabir bansan