Showing 117001 words to 120000 words out of 121650 words

Chapter 40 - MACE A YAU by Shatuuu

Shatuuu   

12 May 2026

153

pain din mutuwar mata ba, amma nasan pain din rasa 'ya Dan a gidan
aure kaine sirikina Imratu ce 'yata don haka dole a bawa kowa hakuri don munyi
babban rashi, Allah ya jikanta ya bamu hakurin juriya, ya kyautata namu zuwan,
Allah ya Raya mana babyn"

Baki daya suka amsa da Amin hawaye na bin kuncin Jabir wanda baisan har Yaushe ne
zai fita daga kuncin rashin matarshi ba, yayinda Sulaim ke kuka sosae tana rikeda
babyn wadda Ke baccinta hankali kwance.

"Babban yaya a kullum bana son nida Maminku mu zama mun saka idanu akan rayuwar
gidanka amma halayen uwargidan ka Yana bani mamaki, kasan bata zo tayi mana
ta'aziyya ba balle ta duba abokiyar zamanta dake jinya, Anya kuwa muna kan hanyar
daidai? "

Maganar Baba tasa Junaid sunkuyar da kanshi kasa saboda azababben kunya da ta
lullube shi baisan har wani Lokaci ne Subay'a zata shiryu ba don dazun da ya kirata
ce mishi tayi Hajiya zata koma gidan Alhajinsu shi ne suke shirye shiryen tarewar
he couldn't say a word Don takaici amma yanzun zuciyarshi ta Fara wasiwasin Anya
zai iya jurewa halayen Subay'a da da yanzun akwai banbanci matuka.

"Baba........"

Katse shi Baba yayi da fadin

"Tuni nake maka akan gyaran gidanka to me ba dole Se tazo ba dubanta sunzo, Jabir
wannan baiwar Allah wani hukunci ka yanke a kanta, she needs a mother"

Hawayen dake bin kuncinshi ya goge, Junaid ya dafa kafadarshi don ya samu karfin
gwiwa hakan kuwa ya karfafa mishi gwiwa yace

"Munyi magana da Babanta yace na barta anan gurinmu Tunda shi baisan waye zai kula
da ita ba, kayi mata huduba da Nafisa Sunan Mami haka Imratu tace sannan na Mika ta
gaba daya hannun Sulaim ita ce uwarta! "

Idan nace kowa yaji dadin hukuncin Jabir understatement kenan, sosae Sulaim ta Kara
kuka yayinda Junaid ke tayi mishi godiya, haka familyn nan suka yini Cikeda farin
ciki da kuma alhini da yamma aka sallamesu suka koma gida nan Jabir ya tattaro
komai na Nafisa Su'ad ya kawowa Sulaim inda ta dauki shawarwarin Nurses din don
kula da yarinyar.

Washegarin Ranar sadakar bakwai ranar gidan ya koma daidai kowa ya koma bakin
aikinshi har shi Jabir din wanda aka mishi transfer ya koma Kano hakan yasa yaji
dadi don Yana tunanin komawa Delta ya rayu babu Imratu, Junaid da Sulaim Harda
Subay'a wadda tazo ranar sadakar bakwai suka juya kano, babu alamar rashin jin
dadin Abinda tayi don gani take ai babu dole ace se ta zo Tun ranar da akai
rasuwar, Junaid kam baice mata komai ba se kallonta da yake Yana tunanin yadda
zaiyi da ita.

Sulaim suka Fara saukewa wadda ta gaji sosae, Tana zuwa ta Kwantar da Su'ad
yarinyar me hakuri Sede tasa yatsanta cikin baki tana tsotsa, seda tayi wanka
sannan tazo tayi mata ta goya ta ta Fara gyaran gidan, tana kammalawa ta janyo
kayan Su'ad ta shirya cikin abin kayanta wanda shima lokacin ta hada, wayarta ta
bude nan text na gaisuwa da tambayar lafiya ba tazo makaranta ba Daga gurinsu
khairi, zama tayi ta dinga bi tana replying har tazo kan Aimana anan ta kirata tana
fada mata Abinda ya faru sosae Aimana mutuwar Imratu ta dake ta don sunyi sabo
sosae lokacin bikin Sulaim din. Hakan yasa mutuwar ta bigeta sosae, suna kashewa ta
kira Mami ta sanar mata ta iso nan ta Kara mata nasiha sosae sannan sukai sallama.

Junaid na isa gida kowannensu ya wuce dakinshi don yin wanka, zuciyarshi Sam babu
dadi a yanzun kam dole ya aiwatar da abinda ke ranshi, fitowa yayi ya shirya cikin
kanan kaya sannan ya fito parlour, Subay'a na fitowa ta shirya cikin bakin high
waist skirt ta daura farar top akan blue din skirt din, kanta ta daura blue din
scarf wanda ya kayatar da ita tayi kyau sosae kamar matashiyar budurwa, ga kamshi
dake tashi Daga jikinta me sanyaya zuciya da nutsuwa. Tana fitowa Atika na kokarin
jera abinci a dining gaisheta tayi cike da girmamawa tareda Yi mata gaisuwa don ita
kanta rasuwar ta bige ta ba kadan ba, samasama ta amsa daidai shigowar su Muhammad
wanda ta kaisu gidan Suhaila, hannunta tasa a bakinta alamun suyi shiru sannan ta
bisu daidai ta manna musu peck a goshi tace

"Welcome home boys din Mimi? Ina Amma (Suhaila)"

A tare suka Fara bata labarin Kwana Dayan da sukai gidan Suhaila gaba daya ta
tattara hankalinta Zuwa kansu tana ta murmushi a wannan lokacin taji wayar ta ta
Fara ringing tana dagowa taga My Everything tasan nemanta yake amma a haka tayi
picking tace

"Na'am "

"Ina jiranki a bedroom dina yanzun"

Bai jira amsarta ba yayi hanging wayar, tsaki tayi ta cigaba da sauraron 'ya'yanta,
shikam Yana daki Ya zubawa kofar shigowa ido yaga ta inda zata shigo amma shiru har
ya dauki waya zai sake kira se ya fasa ya janyo wayarshi ya fara surfing internet a
haka har ya gama amma babu ko keyar Subay'a, me son kuka se aka jefashi da kashin
awaki inaga Ya samu dalilin kukan, haka zuciyarshi ta Kara baci se huci kawai yake
amma Junaid been Junaid a lokacin yayi calming kanshi se gashi ta shigo fuskarta a
hade ita a dole batasan raini, zama tayi gefen kafafunshi tace

"Muna tareda su Muhammad Shiyasa ban zo ba"

Kallonta yayi a tsanake wanda har Seda ta zama uncomfortable sannan ya daga pillow
din da yake kwance akai ya zaro wata farar takarda ya mika mata, Lokaci daya jikin
Subay'a ya fara karkawa ta kasa dago hannun balle ta karba, kallonta yayi yace
"Ki karba mana!"

Ya fada Yana buga mata tsawa, hannunta, bakinta Kai ilahirin jikinta rawa yake
tsabar yadda ta tsorata take cikin tsoro, wata tsawa ya daka mata batasan lokacinda
tasa hannu ta karba paper ba Sede tuni hawaye ya wanke mata fuska ta kasa bude
paper shikam yadda ranshi yake a matukar bace ce mata yayi

"You can't read right? Lemme help you "

Ya karba takardar ya bude tareda kafe ta da idanu kamar yadda take kallonshi cikin
wani yanayi Wanda bai taba ganin Irinshi ba, he's sure da idanu na iya yin magana
to tabbas nata zasuyi, all he saw was ban hakuri, roko da Dana sani amma a wannan
lokacin bazasu taba tasiri cikin zuciyarshi a wannan lokacin sede next time

*NI MUHAMMAD JUNAID LUKMAN na saki Matata SUBAY'A YUNUS saki biyu bisa wasu
dalilai*

Tamkar jini ya daina gudu a jikinta haka taji, take fuskarta tayi wani Irin
Fari ,Mika mata takardar yayi tareda mikewa Don bar mata dakin saboda wani kuka da
ta saki Don wannan shi ne last thing da ta taba tunanin Junaid zaiyi mata, da sauri
ta sakko kasa tareda rike kafafunshi tace

"Papa na tuba nabi Allah na bika, Kada kayi min haka, kada ka wulakanta soyayyar
mu, nasan I was never good amma give me another chance"

Baiso yin magana ba amma dole yayi saboda yaga she needs clarification akan abin

"Da Nayi hakuri lokacin ke daya ce amma yanzun bazan iya ba, ke idan banda butulu
irinki har Imratu zata rasu kiki Zuwa gaisuwa ai ko banda ni taci albarkacin
'ya'yanki da ta rike miki, sannan har yanzun baki san me ake nufi da aure ba har
yanxu Bakiyi hanakali ba, kije me tsautsayi ya dauka! "


Kuka sosae Subay'a take amma ko kallon inda take baiyi ba yayi wucewarshi Zuwa
Dakinsu Ahmad inda ya tarar dasu suna cin pringles suna tsomawa cikin mayonnaise
wadda aka hada da Venigar, suna ganinshi suka rungumeahi, shafa kansu yayi sannan
ya zauna kan Mini cushion din dake aje a dakin yace

"Waye zaije gurin Ammiey"

In chorus sukace

"Ni! "

Kanshi ya gyada yace

"Kowa zaije"

Mikewa yayi ya hada musu kayan da ya zama basic yasa a katuwar trolley sannan yace
suje su jirashi a mota, dakinshi ya koma har lokancin tana durkushe inda ya barta
ko kallonta baiyi ba ya shige dressing room dinshi ya hado kayan da zai bukata ya
fito lokacin hawaye kawai take don tasan ta makara lallai Junaid ya shammace ta don
Bata taba kawowa zai iya rabuwa da ita ba se gashi ya bata unexpected blow!

Tana kallo ya fice ya barta a gurin ganin haka yasa taji karfi yazo mata ta fito a
daki ta nufi nata, ta tsaya tsakiyar dakin tana tunano Irin halin da ta shiga
wancan komawarta gidan amma me yasa tayi repeating same mistakes gashi ta kare a
babu, sosae ta shiga kuka babu kakautawa haka ta shirya kayanta ta fito bayan ta
daura Abaya saman kayan sede har lokancin kuka take sannan tayi clutching takardar
sakin Tana jin yadda zuciyarta Ke zafi da radadi anma Lokaci ya kure.


Hajiya na Zaune Kan sofa gefenta Fannah ce wadda tazo Hutu, kanta babu dankwali
Tana ta bawa Hajiya labari suka ji shigowar Subay'a, seda gaban hajiya ya fadi
saboda ko ba'a fada ba tasan aure ya Kare, Fannah daki ta wuce ranta babu dadi,
Hajiya ta ruko Subay'a wadda ta sake wani kukan tace

"Hajiya ya sakeni, na kashe auren na cuci kaina, na shiga uku! "

Wani wawan mari taji da Bayan hannu Wanda yasa ta gigice hatta Hajiya batasan
Alhaji ya shigo ba se saukar Marin ne ya sanar mata da zuwanshi,

"Se kizo mu zauna Tunda haka kika zaba jaka Marar hankali, kuma Wallahi Keda farin
ciki har abada "

Alhaji ya fada sannan ya fara kiran sauran yaranshi akan a Daren yau suje su kwashe
kayanta kada su bar komai, hajiya ta dinga rokonshi akan ya bari a sasanta wani
mugun kallo yayi mata yace

"Kin cuci Rayuwar yaranki haka zasui ta fitowa daya bayan daya, kuma Wallahi
Subay'a se kinyi dana sanin kashe aurenki se na nuna miki ni ne ubanki! "

Kuka sosae take haka ya fice kuma kamar yadda ya fada haka aka kwaso kayanta
kowannensu mamaki yake don sunyi tunanin a cikinsu babu Wanda zai kuma wannan saken
se gashi Subay'a tayi. Sulma da tazo kasa magana tayi jin Abinda ya faru tace

"Dama nasan hankalinki bazai taba kwanciya ba har se kin kashe auren,
congratulations Sister kinyi kokari you've succeeded se ki jira hukuncin Alhaji"

Sosae Subay'a Tun ba a je ko ina ba ta fara nadama wadda Lokaci ya riga ya wuce!


Sulaim na kitchen ta kammalla hada miyar kifi se farar shinkafa da ta dafa, gefe ta
hada salad sannan ta samu guri a kitchen din ta kunce su'ad Daga bayanta ta Fara
bata Madarar dake cikin feeding bottle din, Seda ta koshi kafin ta sabo ta a kafada
ta shiga daki inda ta gyara kanta sosae kamar tasan mijinta na hanya, pencil skirt
tasa Wanda ya wuce gwiwa amma bai Kai idon sawunta ba baki me wasu glitters da suke
ta haskawa, tasa top gold wanda kamata kadan sannan ta bude wani dan kit ta ciro
chain na gold da dan karamin pendant ta daura a wayanta tasa dan kunnenshi tareda
shafa maroon paint lip, kafin wani Lokaci tayi kyau kamar Mamie water.... Beautiful
Oyinye. Bakar ribbon tasa ta hade kanta in a Bun sannan tasa hula baka da golden
ribbon a gaban, turarruka masu sanyi tasa ta dakko karamin Cot din Su'ad ta kaita
parlo ta kwantar sannan ta dakko system dinta ta Fara karatu wasu slides da Aimana
ta turo mata na lecture din da tayi missing.

Sallamarsu Muhammad yasa ta aje System din gefenta tareda nufarsu ta rungumesu tana
jin yadda tayi kewarsu har cikin zuciyar ta, ganin zasu fara ihu yasa tace

"Kui shiru kuzo Ku gani"

Gabaki daya sukai tsit suka biyo bayanta har inda Cot din Su'ad yake tace

"Ga kanwarku nan "

Gaba daya suka tsira mata idanu suka Fara murna hakan yasa ta Fara motsi Sulaim ta
matsar dasu don kada su tashi, tana dagowa ta hangeshi yana tsaye ya harde
hannayensa Kan kirjinsa ya zuba mata ido, murmushi tayi tareda yi mishi wink,
kanshi ya kawar ya bude mata hannayenshi alamar ta rungumeshi, kanta ta girgixa
Tana zumbura Baki, shigowa yayi ya Daga ta sama hakan yasa ta kankameshi tana
dariya Wanda ya kwantar mishi da hankali tareda saukar masa da nutsuwa, juyawa tayi
taga Ashe yaran sun shige ciki, tare suka ci abinci yana ta zolayarta da tsokana
tana dariya, dake bai shigo da kayan ba yasa bata kawo komai a ranta ba tayi
tunanin yaran ya kawo mata Tunda sun jima basu hadu ba, amma ga mamakinta har dare
bai ko Yi alamun tafiya ba, wanka tayi ta gyara su'ad tasa Nighties dinta ta
kwantar da ita sannan ta fito Yana zaune Yana kallon news ta zauna gefenshi tareda
fadin

"Zamu kulle gida fa!"

Juyowa yayi yace

"Kora kuma Dove, anan zamu Kwana ga yaranki sun Fara bacci"

Idanu ta tsura mishi kamar tana son karanto wani abu tace

"Be serious Heartthrob bacci nake ji"

Dariya ya danyi tareda gyara zamanshi yace

"I'm sorry Amma ina sake neman alfarma akan ki rike su Muhammad a gurinki har Zuwa
lokacinda ni bansani ba, nasan Kinyi kankanta da wannan burden din amma inason ki
daure Kimin wannan taemakon"

Kanta ta girgixa tace

"I can't gaskiya su koma gurin Miminsu "

Idonshi ya zaro Don wannan ne Karo na farko da Sulaim tayi mishi musu hakan yasa
yace

"Dove ni ne fa"

Kanta ta gyada tace

"Me yasa zaka yanke hukunci kana cikin fushi, why will you do that, nace maka kayi
hakuri ka zauna da ita ko albarkacin ya'yanta amma ka nuna min banda mukamin baka
shawara, then babu Wanda zan rike I'm sorry!"

Shiru yayi saboda tsabar mamakin furucin Sulaim akan bazata riskesu ba, Daga karshe
tashi tayi ta wuce dakinta bawai don komai ta fadi hakan ba sedan tana son su
Muhammad su tashi suna daraja mahaifinsu amma inhar suka tashi babu uwa lallai zasu
zargeahi akan wulakanta babarsu.

Da kanshi ya kai yaran suka kwanta sannan ya biyo ta daki ya samu tana kwance gefen
yarta, hannunsa yasa ya dauke Su'ad sannan ya matso da uwar wadda ta Fara kokarin
kwacewa ita a dole fushi take dashi Seda ta gama ture turenta kafin ya fara zuba
mata ruwan kisses kamar zai haukata ta daga karshe ya kashe ta da soyayyarshi me
tsada, Seda suka nutsu sukai wanka sannan ya kwanta kan cinyarta tana wasa da
gashinshi tareda kallon Baby Su'ad dake baccinta hankali kwance

"Nayi tunanin a yadda kika sanni bazaki zargeni da rashin adalci ba, Sulaim ya
zanyi this is the last thing da zan iya dauka Daga gurin Subay'a na bata dukkan
chances da take bukata amma har cemin tayi idan na gadama na saketa, to na nuna
mata sakinta is the simplest thing da zan iya nidai kawai I need your support plz
Kada ki barni no matter the hardship kinji"

Sunkuyowa tayi ta manna mishi peck sannan tace
"Allah ya daidaita komai and I will forever remain yours till death do us apart,
I'm sorry for dazun"

Mikewa yayi ya hade bakinsu guri daya........... Tired I need a break...... Gobe
Inshaaa Allah I'll post the final episode fadan karshe kenan!


Shatuuu ♥️
[9/13, 6:29 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
60
_FINAL CHAPPY_

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad




*I've seen the critics akan sakin Subay'a, of course Subay'a need to go she need to
learn her lesson, Kada Ku manta tayi amfani da son da Junaid ke mata take
iskancinta amma ga page ne se ku gani ko hukuncin yayi muku. This mark the end of
MACE A YAU I hope you guys liked it, ina fatan zaku cire lessons din ciki kui
amfani dasu kubar sauran. I love each and every person who was, is and will be with
me through this journey.... May Allah shower his endless blessings upon
you.....nagode sosae Allah ya bar zumunci da kauna.... One Love💕*


_GODIYA TA MUSSAMAN_

My wattpad follwers
SHATUUU's Kingdom damsels
Ladies of Maman Mama Novels
Kainuwa writers association group
Kainuwa fans club 1 to 12
Zauren Sadeeya novel
Ummu hanash novel group
Mace tauraruwa
Ummu Safwan novel group
Taskar Marubuta group



_My gratitude also goes to Anty Sumayya Takori, Anty Nafisa Tafida, Anty Fauza 'yar
amanah..... You guys are my personal persons♥️
_




Bayan Watanni Uku

Shigowar Musbahu cikin bedroom din Khulthum din yasa ta rufe Wardrobe din da take
sake gyarawa saboda kayanta da aka kawo daga gurin guga, zama yayi gefen gadon
idanunshi na kanta har ta karaso ta zauna a gefenshi tareda fadin
"Yanzun nan zan taho"

Hararar ta yayi yace

"Shiyasa naga kina gyaran wardrobe"

Dariya ta danyi tareda mikewa ta Kama hannunshi Tana fadin

"Oooo gashi na tashi muje na shirya ka"

Kafadarshi ya noke yace

"Goyo nake so"

Baki ta bude tareda sakin dariya tace

"Tabdijam, Too Big fa! "

Rankwashi ya kai mata akanta tayi saurin kaucewa tareda barin gurin Tana yi mishi
gwalo, kanshi ya gyada yace

"Ni ko?"

Dariya tayi mishi ta bude kofar ta fice, hannunshi ya ware ya biyo bayanta a ranshi
Yana Raya present situation dinshi, ko cikin mafarki bai taba kawowa cewar akwai
rana da zai zauna da mace haka ba bai taba kawowa ba, bai ma taba tunanin cewar a
mace akwai abin burgewar da har zaisa yana aiki Yana tunanin dawowar gida, har yana
jin dokin dawowa gida, har yana jin tamkar yafi kowanne saa a rayuwarshi.

A farkon dawowarsu daga India yasha wahala kafin yayi coping da rashin Abinda yake,
ya kasa tunkarar Khulthum don gani yake Yana Zuwa tabbas zai cigaba da Anal sex
dinne da ita amma haka ya kaurace mata sede kira kawai a waya yaji yadda take, ya
jima a Wannan halin idan ya hadu da maza se yaji Yana son komawa ruwa ga yadda suke
kawo mishi attack ta ko ina Seda ya tsaya a tsaye akan addu'a da neman gafarar
Allah sannan ya samu ya dace har ya fara hango abubuwa a tareda Khulthum na burgewa
hakan yasa ya fara shiga jikinta itama ta saki jikinta dashi ta Fara bashi kulawar
da ya kamata shima baya taba wofantar da Al'amuran ta a haka shakuwa da sabo suka
shigesu har basu san soyayya ta samu guri a zukatansu ba a haka rayuwar ta cigaba
da tafiyar musu har ta mallaka mishi kanta Wanda wanann taste din yasa yaji tabbas
ya cuci kanshi da ya zauna Yana biye ma zuciyarshi akan wanda suke jinsi daya,
tundaga ranar suka bude shafin soyayya tayi kiba ta murmure hankalinta a kwance,
Duk Saturday a gidan Gwoggo suke yini.

Iskar bakinta ta hura mishi hakan yasa ya saki murmushi tareda zama ta Fara serving
dinshi ya nutsu yana ci suna hira har ya kammalla ya goge bakinshi tareda mikewa
Yana gyara rigar jikinshi, itama mikewa tayi tana fadin

"Har ka koshi? "

"Cikina kike so ya fashe? "

Dariya ta danyi ta dauki briefcase dinshi tayi gaba yana bayanta har ta iso bakin
motar da driver ke jiranshi, bude mishi back seat

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login