Showing 99001 words to 102000 words out of 121650 words

Chapter 34 - MACE A YAU by Shatuuu

Shatuuu   

12 May 2026

750

na wuya ya bayyana. Tana zaune tayi wanka tayi kyau cikin wata
Holland wax purple me kyau da tsari, dinkin plain zani da riga wanda yayi mata kyau
da cifcif a jikinta, ko dankwali bata daura ba haka take Zaune tana tunanin yadda
komai ya juye mata, aure kusan sati hudu amma sau biyu kadai tasa miji a idonta,
ranar da aka kawo ta da ranar da taje gurin shi a part din shi.

Kwanciyarta ta gyara ta janyo wayar ta dake jikin socket tana caji ta Fara kiran
Sulaim saboda tana bukatar wanda zatayi magana dashi Amma ta buga tafi a irga amsa
daya ce a kashe se lokacin ta tuna Ashe lokacin kanta yana rawar aure ta fada mata
zataje Malta. Kawai se ta Fara kiran Maimuna wadda kamar jira take ta dauka. Seda
ta gama tsokananta

"Matar Manya amaryar TitαΦ uwar Magajin TitαΦoils, foods and flours!"
Da idan Maimuna tayi mata wannan kirarin Jinta take tamkar a saman gajimare amma
yanzun se take jin wani banbarakwai kwatakwata Bata fitting da abin ba.

"Ki Bari kawae Maimuna, ina cikin matsala!"


"Wacce Irin matsala kuma? Haba dai mu a cikin matsala kuma a ciki"

A ranta cewa tayi nima haka na dauka amma gashi ba hakan bace ta kasance, ta dauka
cewar idan ka auri me kudi ka gama dacewa cikin duniya, to gashi babu inda akaje
abubuwa sun lalace! Cikin nitsuwa ta warwarewa Maimuna dukkan abinda yake damunta,
dariya Maimuna tayi tace

"Amma kin bani Mamaki uwar Magaji, Karki manta lokutan da kike saka Maza dripping
Amma gashi mijinki kin kasa juyashi, ni har ina tunanin gobe inzo da PT strip nayi
gwaji. Yanzun har wata daya babu wani abu, ina tactics dinki suke? Kije kiyi
seducing dinshi idan yaki zan kawo miki tablet kiyi mishi amfani dashi. Kiyi amfani
da damar ki kafin ta kubce miki sannan ki yi amfani da damar ki ta mace ki janyo
hankalinshi. "

Wannan magana ta shiga kunnuwan Khulthum hakan yasa ta Mike Bayan sunyi sallama ta
nufi kitchen inda ta bada order plantain, porched egg da coffee, komawa tayi ta
sake wanka ta shirya tsaf tayi barin turare sannan ta dora katon hijabi ta dauki
tray din zuwa part dinshi.

Tana zuwa tsakiyar parlon Sega wani hadadden saurayi ya fito Daga wancan bedroom
din da taga sauran sun shiga wancan karan, kallonta yayi Baice mata uffan ba ya
fice abinshi. Jikinta a sanyaye ta nufi bedroom din gabanta Yana mugugun faduwa
tare da fara tunanin Meye Musbahu yakeyi da Maza har haka???

Ku biyoni a next page dan jin yadda zata kaya tsakanin Musbahu Dan Gwoggo da
Amaryarshi Ummu_Khulthum uwar magaji.


Shatuuu ♥️
[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
50 to 51

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad



*Its a long journey I know, yeah! I'm concluding the novel Inshaaa Allah on or
before 1st September. So from now on Inshaaa Allah double in one page zamu Nayi.
Thank you very much for all the support, prayers, love and comment..... That's what
kept me going, that's what makes me update daily, I'm so much grateful for
everything*


_My heart goes out to Salma Hassan Kwalam, Tee Zarewa, Anty yaya (Sadiya Lawan),
Anty Fatima sadi, Yaya Baby, Anty Asma'u, A'isha, A'isha imam, Aisha kaagu, Aisha
Akko, Aisha Ahmad, Aisha sheikh, Yaya Umma, Farida S maina, Abida Suleiman,
Ammasheikh, Anty Hijja, Daughter Farida, Oum Annur, Maman Zarah, Amaryar yaya
Mousa, my Najeeyba, Maman Hanif, leiymahs delicia, Sister Sadiya, Sister deejah,
Sister Ummin D/batta , Fatima idris, Nanah ganuwa, Fatima ummi, Yaya Nana, Pyaule,
heedaya Bunu, Aisha major, Jidda Hamisu, Fatyn zulayha, Hanifa, Khadeeyja
DRB....including all and all the ghost readers in the SHATUUU's
KINGDOM .....without you many things won't be possible thank you!_



Cikin dakiya da jarumta Uwar magaji ta Kai hannunta Kan handle din kofar, gabanta a
lokacin ya kara bugun da yake amma haka ta murda kofar ta shiga, sanann ta maida
kofar ta rufe tareda murda key din da yake jiki.... Kunji karfin Hali kamar
dakinta. Zare key din tayi ta daura saman tray din dan yau ko Wacce aljana ce ta
aure mata miji as they said, ko da bashi da lafiya yau se tayi yadda tayi. Tana
juyowa idonta bai sauka a ko ina ba se makeken Italian bed din Musbahu, kafin cikar
seconds jikinta ya fara bari tamkar mazari, idanunta Manya ta Kara ware su kirjinta
tamkar zai balle, tamkar an ingiza hannunta tray din dake hannunta ya kubce jikake
Tas! Tas! Ceramic plates, cups da bowls din dake kan tray din Baki daya sun fashe
wanda a take yayi awakening Musbahu da partner dinshi Daga abinda idanun Khulthum
dani na kaina suka gane min...... Khulthum kidimewa tayi ta juya da sauri ganin
yadda Musbahu ya sauka Daga kan gayen dake kwance malale akan gado tamkar ruwa Don
ya kasa katabus gara Musbahun ya samu courage din mikewa.

Gaba daya Khulthum ta manta ta rufe kofar hakan yasa ta dinga jijjiga kofar tamkar
zata balla kofar amma ko gezau kofar baiyi ba a haka Musbahu ya iske ta, hannunshi
ya daura akan kafadar ta, tamkar garwashi haka taji ga wani masifar tsoro da ya
kara turnuke ta, juyo da ita yayi Fuskarshi tamkar ta zaki wanda ya shekara bai ci
ba gashi kuma ya hadu da abincin shi, babu ko imani digo a Fuskarshi ya fuzge
Hijabin dake jikinta, take jikinta ya bayyana cikin wata riga wadda Baki daya net
ne fari tas wanda in har Namijin da yake lafiyayye ne to tabbas sai hankalinshi ya
tashi amma ko a jikinshi se wani mugun kallo da yake bin ta da shi na bakida Abinda
zaki birgeni dashi.

Tsugunnawa yayi don tun sakkowarshi daga gado yaga key din bedroom din, kofar ya
bude, Khulthum dake gefe ta taho cikin wani azababben sauri zata fita ya rike
hannunta tamau yadda duk wannan tirjiyar da take ta gagara kwace hannunta, juyawa
yayi Yana duban wannan gayen da tuni ya Mike ya maida kayanshi jikinshi ya fito ya
wuce ba tareda yace uffan ba, yana fita Musbahu ya maida kofar ya rufe tareda zare
key din daga kofar ya cigaba da jan hannun Khulthum wadda ilahirin jikinta rawa
yake, tasan tayi iskanci a waje amma ko sau daya a Rayuwarta bata taba tunanin haka
daga Musbahu ba, Gay! Neman Maza yake! Hannunta ta kara kokarin kwacewa amma ya
mata rikon tsauri, ganin tana neman wahalar da shi yasa ya hankada ta kan gadon,
kafin tayi wani yunkurin kubcewa har ya hayo gadon, idanunta ta Kara budewa tareda
bude bakinta tana fadin

"Dan Allah...... "

Muryarshi ya bude wanda Tunda take bata taba jin Irin wannan Amon ba, shikanshi ya
isa firgitata

"Ba hakkinki kika zo karba ba? Fine"

Wajen Mintina ashirin babu Abinda yake tashi cikin part din na Musbahu banda ihu da
kururuwar Khulthum tamkar wadda ake zare mata ranta, Tana kwance babu komai jikinta
se rizgar kuka take tamkar an bata sakon mutuwa, a hankali kofar da nake tunanin
Itace ta toilet ta bude, the Charming Musbahu ya bayyana cikin wata farar bathrobe,
kanshi ruwa Yana ta diga, kamar kullum fuskarnan babu digon annuri akai, daidai
inda take ya tsaya Yana Kare mata kallo tareda jin ihunta na kokarin tarwatsa mishi
kwakwalwar kanshi bawai don tausayinta ba a'a se Don naturally baya son hayaniya.

"Kinzo ki karbi hakkinki sanann kinzo kiga me nake aikatawa, ban so kika ga hakan
ba saboda kada zuciyarki ta buga, Amma duk Abinda na fada miki kada ki cika bincike
amma kika saka kafa kikai fatali da hakan. Ina fatan you're satisfied, idan kina
bukatar Kari zan baki saboda ban taba kawowa Anal sex haka take da dadi ba se yau"

Yana gama fadar haka ya wuce cikin walk in closet dinsa ko Mintina ashirin bai kara
ba ya fito ya shirya cikin sweat pants black da Top maroon , kallon ta ya kuma Yi
har lokancin Bata motsa Daga gurin ba amma kukan ya dauke sakamaakon dusashewar da
muryar ta yayi saboda yadda ta bude murya da makogaro tana kwarara ihu.

"Tashi ki fitar min a daki"

Ya fada cikin kakkausar murya, jikinta na rawa ta Mike tare da daukar Hijabin da ta
zo dashi tayi waje a million, sosae hakan ya bashi dariya, ya dauke kanshi babu ko
dar na tsoro cikin zuciyarshi, ta hutar dashi da tazo ta ganewa idanunta komai, ba
se yayi bayani ba.

Khulthum Seda ta taka kafarta cikin part din sannan ta ji wani Irin azababben
radadi ta gurin Bayan gidanta, kafafunta sunyi mummunan sagewa ga tarin gajiya da
tayi mata rubdugu, da kyar tana Jan kafa ta isa dakinta ko gado kasa hawa tayi haka
ta kwanta kan carpet idanunta na zubar da hawaye.

A hankali ta samu damar tuno Irin mugun ganin da tayiwa Mijinta, hade da wani katon
namiji ba ma mace ba, babban laifun da Allah ya hallaka mutanen Annabi Lut AS Amma
ita mijinta kenan, ga wani haramci da ya tafka wato Anal sex, saduwa ta dubura
wadda Allah da manzonshi sukai Hani akan hakan, Kaddara ta kenan! Auren GAY!!!

Karfe daya na ranar litinin motar da ta taso Daga Kano zuwa kaduna ta sauke
passengers dinta a Tashar DIT dake alheri radio. A hankali Subay'a ta sakko daga
motar janye da trolley, hannunta da handbag yar karama, tana Kallon mutane yadda
suke ta kai kawo, Bata kalla kowa ba duk yadda 'yan union suke tambayarta inda
zataje amma bata kula kowa ba, hankalinta yana ga Irin tarbar da zata samu daga
inda zataje. Napep ta tare tare dayi bashi address din gidan, ya yanko kudi daidai
suturar jikinta ya fada mata ta shiga suka wuce zuwa gidan da ta manta rabon da
kafafunta su taka.

Kofar gidan Rtd Gen. Lukman Birnin kudu Subay'a ta tsaya tana tunanin ta inda zata
Fara, ta jima a tsaye ba tareda sanin inda ta kama ba, ga kuma Anxiety.... The fear
of Unknown, ta isa bakin kofar dan fara kwankwasawa taga an bude tangamemen Gate
dinsu. Jawad ne ciki wanda ke kokarin fita zuwa Aiken Mami, kamar yasan tana tsaye
ya juyo idanunsa gurin karaf suka hade. Fitowa yayi tare da nufo inda take tsaye
kanta a kasa saboda tsabar kunya, ta tuna lokutan da Jawad ke zuwa gidan ta tayi
mishi banza.

"Maman Ahmad Yaushe kika zo? "

Kanta ta dago tace

"Yanzun. Mami na ciki? "

Kanshi ya gyada yace

"Tana ciki Ki shiga"

Kanta ta gyada ya koma mota itakuma ta shiga, dake sojojin dake gate din sun Santa,
hakan yasa suka gaida ta, Smith har kokarin karbar trolley din hannunta yayi amma
ta mishi godiya ta wuce ciki. Tunda ta zura kafarta tasan akwai wani muhimmin abu
da zai faru a gidan saboda yadda gidan ya hargitse bawai datti ba a'a very neat and
tidy ga kamshin turaren wuta da nasu fresheners na lavender flavor da ya cika
gurin, Amma duka masu aikin se kai kawo suke ko Lura da ita basui ba Seda Imratu ta
sakko hannunta cikin na Muhammad wanda ya sha wanka an shirya shi cikin kaya masu
kyau. Kallon kallo sukayi da Imratu kafin Imratun ta dan saki fuskarta tare da
karasowa inda take tsaye, Muhammad bai lura da Subay'a ba wasanshi kawai yake har
Seda suka zo gaf da juna kafin yace

"Mimi"

Lumshe idonta tayi don wata kwalla ce ta cika mata idonta, tsugunnawa tayi ta
rungume shi Tsam cikin kirjinta tana sakin ajiyar zuciya, kanshi ta dinga shafawa
tana jin abubuwa da dama suna taba mata zuciya, a hankali ta furta

"I missed you son"

Kwace jikinshi yayi yana fadin

"Mimi kizo kiga yadda Mami ta gyara komai yau da Daddy da Ammiey zasu dawo! "

Dam taji kirjinta ya buga, a hankali ta Mike tsaye Daga tsugunnon da tayi ta saki
Muhammad, shi kuwa bai lura da ita ba ya ruga sama se Imratu ce ta karba trolley
dinta tace

"Muje ko"

Hawayen dake kokarin sakko mata ta shanye tareda sniffing hancinta ta bi bayan
Imratu zuwa sama, tamkar ta juya haka taji inda tasan Abinda zata tarar kenan da
babu yadda zaayi ta dawo gidan. Suna zuwa parlon ta tarar Mami na Zaune gefen ta
Ahmad yana danne danne a system din Mamin. Mamaki sosae Mami tayi ganin Subay'a a
wannan lokacin Kuma Harda trolley, ganin yadda tayi kasa da kanta Mami tace

"A'a Subay'a sannu da zuwa, Ahmad bakaga Mimi ba? "

Zama Subay'a tayi yayinda Ahmad ya taso da murmushi a Fuskarshi ya rungume ta
sanann ya cigaba da Abinda yake, kafin wani Lokaci an cika mata gabanta da lemuka
da abinci, lemo kadai ta iya sha sannan tace da Mami

"Mami zanyi sallah"

Kallon Imratu Mami tayi tace

"Kuje Imratu "

Tare suka nufi dakin da Imratu ke zama idan tazo anan aka sauki Subay'a seda ta
nuna mata inda komai yake kafin ta fice ta barta akan sallaya. Seda ta Idar da
sallah sannan ta hada kanta da gwiwarta ta saki kukan bakin ciki hade wani
masifaffen kishi da ya turnuke ta Lokaci daya, Da gasken kenan da kishiya zata
zauna, da gaske Sulaim ta zama kishiyarta ta kwace mata mijinta, kuka sosae ta
dinga yi har Bata san lokacin da ta dauka a haka ba, amma tasan tafi karfin awa
daya Don har fuskarta seda tayi jawur ga babu Wanda ya kara ko nemanta a gidan.

Ganin haka yasa ta Mike ta cire kayanta ta fada toilet tai wanka ta dauro Alwala
nadama fal cikin Zuciyata babu Abinda take banda inama ace Nayi kaza! Inama ace
banyi kaza ba!! Amma ina Lokaci ya kure tuni sede a tari wani lokacin. Bubu ta wani
cotton lace ta saka ta yafa mayafin kayan sannan ta samu guri gefen gado ta zauna,
tamkar jiran zamanta ake taji ihun Ahmad yana fadin

"Daddy! Ammiey!! Oyoyo!!! "

Idanunta ta runtse da karfi, tareda dafe kirjinta hawaye suka Balle mata duk kuwa
da yadda take kokarin ganin ta Hana su zubar Amma it is natural dole hakan ya
kasance.
A parlor Junaid na gaba ya Saba Ahmad a kafadarshi Fuskarshi murmushi ne kwance
akai me nuni da tsananin kwanciyar hankali da cikar buri, a bayanshi Dove ce
hannunta rike da na Muhammad da yake rigimar se Sulaim ta daukeshi amma taki, tana
ganin Mami ta nufe ta da gudu ta rungume ta wanda hakan ya kusa kada su baki daya,
take parlon ya cika da murnar dawowar Love birds, a tsakiya suka saka Mami kowa na
bata labari, farin cikin da take ciki yasa ta manta da wata Subay'a. Da kyar ta
samu suka tafi wanka kafin su dawo itada Imratu sun gyara gurin sannan sun shimfida
dining mat an Jere warmers din abinci. Junaid ne ya fara hawowa shida Jabir suna
dariya, Junaid ya kara kyau se kyalli fatar jikinshi take, kana kallonshi kasan
bashida wata matsala. Gefe guda suka zauna se sannan Sulaim ta fito tayi kyau cikin
gown ta atamfa ABC wax, tayi kiba ba wai cancan ba amma ta murje ta murmure,
yaranta sun saka ta a tsakiya suna tambayar ta tsarabarsu. Bata zauna ba Mami ta
cigaba da tayawa aiki duk yadda Mamin taki amma se kyaleta yayi, Duk inda tayi
idanun Junaid na binta Yana jin tamkar ranar farko da ya Fara ganinta kenan, tsabar
kallon da yake mata Seda Jabir ya zungureshi yace

"Haba mana"

Dariya Junaid yayi yace

"Bazaka gane ba "

Dariyar Jabir ya sake yi tare fadin

"Really?"

Shareshi yayi ya cigaba da binta da kallo, Yana ganin lokacinda tayi pouting lips
dinta alamar kallon ya isheta hakan. Gaba daya suka zazzauna aka Fara cin abinci
Cikeda nutsuwa da nishadi hadi da soyayya, Mami ce ta aje spoon tareda kallon
Imratu wadda ta tattara dukkan hankalinta Kan chicken Salad din da take ci,

"Imratu kirawo ta taci abinci"

Mikewa Imratu tayi a ranta tana tunanin yadda abubuwa zasu kasance, itakam Mami
tausayin Sulaim take ji yadda ta saki jikinta sosae tana tunanin ta manta Junaid na
da wata matar. Da kyar Imratu ta samu Subay'a ta biyo bayanta don tasan ranta ne
kawai zai baci don yadda ta dinga jiyo muryoyinsu yasa jikinta ya kuma yin La'asar
Don tasan suna cikin farin ciki.

Sulaim ke facing dakin don haka idanunta akan Sulaim din ya fara sauka, haka itama
Sulaim din ita ta Fara ganin Subay'a, idanunta ta dan zaro saboda yadda taji
kirjinta ya buga kusan tare da Subay'a din, gaba daya ji tayi taste din abincin ya
bace, taji gaba daya zaman ya gundure ta, a hankali ta cigaba da taunar abincin
tareda sunkuyar da kanta Tana ambaton Allah saboda wani Irin abu ne ya tokare mata
makoshi, Mami na kallonta amma bata ko kula ta ba ta dubi Subay'a tace

"Kizo ki zauna mu ci abinci mana"

A lokacin Junaid ya dago idanunshi wanda suka sauka tar cikin idanun Subay'a wadda
ta dauke Nata cikin saurin gaske, se ta samu kanta da kasa yiwa Mami musu ta zauna
a gefen Ahmad Wanda suna ta tsakurar abincinsu ba Lallae idan sun San tazo gurin
ba, Aje spoon din hannunshi Junaid yayi ya Mike don barin gurin, Mami ta dubeshi
tace

"Har ka gama? "

Kanshi ya gyada ya tafi abinshi ba tareda ya ko kalli kowa ba, bai taba tunanin
Subay'a batada kunya ba se yau, kenan ta bullo mishi ta bayan gida inda bai isa ya
ja ba, kwanciya yayi Yana jin tamkar an rugurguza mishi wani plan ne. A parlor kam
tunda Subay'a ta fito gurin yayi shiru se karar spoon dake tashi, a hankali daya
Bayan daya suke tashi ya rage daga ita se Mami se Sulaim wadda ta kasa tashi har
Seda Mami tace

"Auta kwashe kayan nan kije ki Kira min Yayanki"

Da sauri ta Mike ta fara tattare kayan jikinta kamar an mata duka, babu wani kuzari
haka ta nufi kitchen ta kai kayan sannan ta nufi dakin Junaid, A kwance ta same shi
yayi zurfi a tunani Amma sassanyan turarenta yasa shi saurin dagowa don bai kawo
ita din ba ce amma se ya ganta a tsaye kana kallon fuskarta kaga me cike da damuwa,
mikewa yayi Yana jin abubuwa suna kara kunce mishi a kanshi, Yana Zuwa inda take ta
fada jikinshi Lokaci daya ta saki kuka Wanda ita kanta bata san me yasa take kukan
ba, tasan dai zuciyar ta bata mata dadi tana jin wani zafi a kirjinta. Janye tayi
daga jikinshi ya shiga share mata hawayen a hankali cikin kunnuwanta ya ce

"Everything will be OK, kinji? "

Kanta ta gyada mishi don ya fahimci kishi ke damunta, ba tun yau yake ayyana zuwan
wannan ranar ba gashi ta zo a lokacinda shi kanshi bai shirya ba, hannunta ya ja
suka fito Yana ta fada mata kallamai wanda yasan suna saka ta farin ciki, a haka
har suka isa parlon Mami da Subay'a na nan inda ta barsu. Kusan tare Mami da
Subay'a suka dubi hannayen Sulaim da Junaid, gaba daya Mami kunyar Subay'a ta kama
ta hakan yasa ta watsawa Junaid harara, Dan chuckling yayi ya saki hannun nata ita
kuwa straight ta nufi dakin Mami gabanta na kara faduwa. Zama yayi Fuskarshi a
murtuke tamkar bashi bane wanda ya gama dariya yanzun ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login