Showing 42001 words to 45000 words out of 121650 words
kawai idan na ganta gabana faduwa yake, Wallahi tsoro take
bani.
Wata ashar Samina tayi tace
Haba Yaya Subay'a Kada ki badamu dan Allah wannan yarinyar? Da Ummin Yaya Safina
I'm sure ta gurmeta zata na fadar miki gaba, idan ta kawo miki raini Kici ubanta
shi ne kawai.
Haka sukai ta zugata ita kuma baki daya ta duburburce taki fada musu ainahin signs
din data gani saboda gaskiya hankalinta ya kasa kwanciya da Junaid.
A waje kuwa Hu ya fara isowa suka gaisa sannan ya dauki gimbiya da khairi se BUK,
suna nan tsaye Aimana tana Bata labari Nu'uman ya iso, yana parking ya fito ya zo
inda suke tsaye suka gaisheshi ya amsa kafin yace
Sulaim nace ina sonki kawar ki ta Hana ta kankane ko ina.
Dariya sukai saboda yadda yayi maganar tamkar irin kana son Abu an hanaka, Sulaim
tace
Kayi hakuri I'm already taken!
Aimana ta kalleta da sauri amma se ta kawar da kanta saboda tasan karya tayi amma a
yanxun tana ganin har Yaushe zata cigaba da Tara samari kuma batajin son su a
ranta, don ita tana ganin zuciyarta..... Se kuma tayi shiru yayinda Nu'uman yayi
murmushi me ciwo yace
Ban fidda rai ba, ban hakura ba amma inason na zama admirer from the side, in karba
number ki?
Kanta ta gyada kawai she can't say no, yayan Aimana ne dole tace
Babu damuwa, Aimana ki bashi.
Murmushi sukayi sannan sukai sallama suka barta a gurin har kewarsu ta Fara
damunta. Tadan jima a tsaye kafin ta shiga ciki bata bi takan kowa ba ta wuce
dakinta ta gyara sannan ta yi tilawa.
Karfe Sha daya da Rabi na dare daidai lokacin Sulaim ta dade da yin bacci wayarta
ta Fara ringing, da kyar ta janyo wayar ta kara a kunnenta Sede muryar Salim tasa
ta bude idonta da kyau
Princess Nayi laifi ne?
A hankali cikin bacci tace
Bacci nake fa!
Seda muryar ta ratsashi hakan yasa yace
Ooops sorry Yi baccinki.
Bata jira ba kuwan ta koma ta kwanta se bacci abinta. Washegari akai last paper
kuma babu laifi tayi dadi, suna fitowa Khairi ta wuce Jalingo itama Aimana ta wuce
gida ya rage se Sulaim da Khulthum the bussoms kenan.
Yawwa Khulthum akan maganar Ashir ne ya kuke ciki.
Tsaki Khulthum tayi tace
Rabu da wawa, wai yaki hakura
Kince ya hakura ne?
Eh mana, baya cikin type dina Sulaim so kike na yaudareshi? Na fada mishi gaskiya
ni bazan aureshi ba.
Haba Khulthum yace yakai kudin me kuke cewa abin?
Sulaim ta fada Tana son taunawa
Na gani ina so, Twenty thousand ce fa! Yazo ya karba abarahi .
Khulthum ni kawar ki ce, ke kinfi karfin kawa gurina you the sister I never had, ki
nutsu ki Daidaita kanki rayuwar duniya batada tabbas a wannan zamanin har kika samu
kamar Ashir kike wulakantawa mutum me bright future ahead? A'a fa ki guji dana
sani.
Bazan taba yi ba, Dan Allah Sulaim ki kyaleni da zancen Ashir hakanan kodai asiri
yayi miki ne?
Dariya sosae Sulaim tayi tace
Ina ganin kamar ya cancanci ya zama mijinki ne Shiyasa na dameki, to ki fitar da
Yusuf kui aure mana
Tsaki Khulthum tayi tace
Baida arzikin mijin da nake burin aura, wayeshi? Wa ya sani? Waye ya sanshi? Kin
gane kuma ni yanzun babu aure a tsarina.
Kai Sulaim ta girgixa tace
Wanne irin miji kike so
Murmushi me kyau tayi tace
Me kudi, shekarunshi kamar talatin bai taba aure ba haka bayada yan mata, bayason
mata ma baki daya, kyakyawa wanda yan uwanshi basa zaman kasar Balle su saka mana
ido, me hadadden gida da mota. In takaice miki Handsome in a flashy car and a top
rich Man..... Shi ne burina.
Shatuuu ♥️
[7/17, 10:44 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
20
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
*Where are all the fantastic, fabulous, awesome and gorgeous Damsels of SHATUUU's
KINGDOM and Damsels of Maman Mama novels..... Take This page as a token of
appreciation.... Thank you very much ladies for always having my back, for always
being there for me..... You're such a darlings*
Idanunshi a kulle tamkar wanda yake bacci amma kwatakwata ba baccin bane cikin
idanunshi hasalima baya tunanin a Wannan Daren akwai possibility shi din yayi bacci
saboda yana cikin mawuyacin hali, Yana cikin tsananin tsukun rayuwa wanda soyayya
ta jefashi a ciki, soyayya me zafi wadda take neman tayyar mishi da hankalinshi
take neman wargatsa mishi Duk wani karfi da a da yake tunanin yana dashi to Amma
soyayyar Sulaim ta nuna mishi shidin ba kowa bane ba kuma komai bane. Idan zai iya
tunawa jibi ne Sulaim zata cika eighteen years da haihuwa he remember vividly
lokacinda aka haifeta lokacin baifi lokacin shekarunsa wajen sha shida don ya Kare
secondary school dinshi, through out rayuwarshi yayi tane akan bata kulawa ta kanwa
bai ko taba tunanin zai rikeda ya zama wannan zazzafan son ba, gashi wadda yake dan
ita bata masan halinda yake ciki ba sha'aninta kawai take abinta babu wata damuwa a
tattare da ita amma shi gashi nan walwala da sukuninshi gaba daya soyayyar Sulaim
tayi tafiyar ruwa dasu. Kwanciya ya gyara ya kalli agogon dake jikin bango karfe
takwas da rabi ba wani Dare bane yayi hakan yasa ya janyo wayarshi ya fara kiran
Mami, lokacin Mami tana zaune itada Imratu wanda suka dawo jiya daga Saudia,
likitoci sun tabbatar musu lokacin haihuwa ne baiyi ba amma babu wani abu dake
damunsu dukda haka se suka basu guidelines da zai boosting fertility din nasu, to
Sede ayi fatan Allah ya sa a dace.
Mami barka da dare
Barka dae Uban Sulaim
Dama Duk lokacinda ta yanke abu akan Sulaim din shikuma ya nuna rashin amincewar
shi haka take ce masa, kowa yasan Mami tace ayiwa Sulaim booking jirgi ta tafi
Kebbi to yau ya kamata a gama komai se aiki ya rike Junaid bai samu yaje ba ya
kirata akan ta tafi wani satin Tace dashi ya Bari ta turo Ja'afar ya kaita a mota,
aikuwa Junaid yayi tsalle ya dire yace babu Wannan maganar zai bar Duk Abinda yake
ya kaita da kanshi, to kafin su gama magana tayi Baki tayi mishi sallama akan zasui
magana da daddare. Murmushi yayi kayatacce yace
Kai Mami wai Baban Sulaim
Baban Sulaim mana, yanzun ni na rigada na turo Ja'afar Don Tun shida na yamma ya
iso kano, gobe da safe zasu wuce.
Kanshi ya dafe yana tunanin me zaiyi kuma shifa tafiyar ce baki daya baya so Sulaim
tayi ita da Ja'afar amma Mami ta kasa fahimta bai sani ba Mamin tun dadewa ta harbo
jirginsu ta rigada tasan cewar akwai kakkarfar soyayya tsakanin Junaid da Sulaim
dukda a farko Junaid ne kadai amma daga baya se ta fahimci Sulaim ta afka, tayi
farin ciki sosae tunda tasan waye Junaid ita ta haifeshi Duk cikin 'ya'yanta babu
mutum me tsananin hakuri, kauda kai da juriya Irin Junaid tasan idan har ace Jabir
Ke auren Subay'a da tuni gayyar ta watse amma daidai da rana daya bai taba mata
complain akan zamansu da ita ba dukda tasan cewar a takure yake sede tayi alkawari
kwaya daya duk ranar da ya kawo wata zai aura zata Goya mishi baya Sede a yanzun
tana tantamar idan zata yarda da wannan abin kasancewar su biyu Junaid da Ja'afar
sunyi tarayya akan son Sulaim
To Mami Allah ya kaimu goben.
Sanyin halin Junaid na Kara masa matsayi cikin zuciyar ta Mamin, tasan baya so amma
bazai mata musu ba.
Ina sulaim din take.
Dan dariya yayi yace
Mami tana dakinta ina nawa sede ko idan za'akai mata wayar ne?
Itama murmushin tayi tace
Zan kirata kawai a gaida Subay'a da yara.
Daga haka sukai sallama ya kifar da wayar shima ya kifar da kanshi, Baki daya yau
ranar Bata masa dadi ba ya yini cikin aiki a office ga wannan ya kunno kai, ya
zaiyi kenan? Zuwa zaiyi ya tunkare ta da zancen? What if it happens tanason
Ja'afar? Se ya zama me son kanshi bayan yasan idan Ja'afar ne zai iya dedicating
mishi ba Sulaim ba ko Abinda yafi Sulaim dinne? To shi Yana babba me yasa yake son
kanshi da Yawa? Tambayoyi barkatai wanda babu amsarsu kuma suke neman tarwatsa
kwakwalwar kanshi saboda kanshi ya fara Sara mishi, Sede wata zuciyar tace babu
yadda xa'ayi ta sadaukarwa da Ja'afar abar kaunarta idan kuma hakan ta kasance
bazata taba hutawa ba kuma bazata yafewa Junaid din ba kuma se Allah yayi musu
hisabi on the resurrection day!
Cikin hakane Subay'a ta shigo tayi kwaliyya bawai iya ta fuska ba har a jikinta,
tayi kyau har ta gaji da yinshi, babu Abinda Ke tashi jikinta banda kamshi me
mutsar da kwantar da zuciya Sede a yau babu Abinda Ke bakanta ma Junaid rai Irin
ganin Subay'a saboda yana ganin rashin kulawar ta gareshi yasa shi cikin wani hali,
saboda lokacin ai son baiyi karfi ba Tunda har idan yana tareda Subay'a yakan manta
da Sulaim amma saboda rashin bashi muhimmanci se Wannan implantation na kaunar
Sulaim wanda aka dasa shi can kan Septum na zuciyarshi seda yayi yado ya taba
Ventricles, Atrium, bundle of hiss, inferior and superior Vena cava, Aorta da
dukkan wasu jijiyoyin dake zuciyarshi har yakan ga Subay'a ta rikide mishi ta koma
Sulaim.
Gefenshi ta zauna ta Daura hannunta Kan hannunshi ta zuba idanunta cikin nashi tana
karanto halinda idanun ke ciki, taga So me karfi wanda ba mallakin ta ba, taga fear
na kar na rasa Wannan abin, taga haushi na wannan ta watsar dani, idanunshi masu
haske sunyi ja alamar yana cikin wani hali.
Better half!
Ta kira cikin wani salo wanda duk karfin zuciyarka se ka jishi har kwakwalwar ka,
Balle Junaid that's helpless wanda bashida makoma soyayyar Yarinya mitsitiya tana
neman maida shi rago. Ya kalli Subay'a wadda idanunta suka Fara maiko alamun
taruwar kwalla
Better half Meye ke damunka? Meye matsalar ka? Yaushe rabon naga kayimim murmushi?
Baka nemana, ka daena cin abinci. Dan Allah ka fadamin ni matarka ce Bakada kamata.
Sosae yake kallonta saboda yaso abinda take fada gaskiya ne, amma karya take, ina
ya zama better half dinta ta ina? Da ta bashi muhimmanci da bazai shiga Wannan
halin ba. Baice ko uffan ya Mike ya fada bayi kamar five minutes ya fito Fuskarshi
da kanshi na digar da ruwa, seda ya goge kafin yace
Abinci kikazo ki kirani mu ci ko? Let's go
Haka ya fice ya barta a gurin, hawayen suka samu damar sakkowa daga idanunta. Waye
ya maida mata miji haka? Wayake so har haka? Ko dai waccan yarinyar yake so? Da
Wallahi ko ta tsiya ko ta arziki se ta bar gidan. Hawayen ta goge tabi Bayan Junaid
wanda har ya zauna yayi serving yaran dashi kanshi, Sulaim Bata gurin bai kirata ba
bai kuma damu ba a cewarshi kenan amma baki daya hankalinshi Yana kan me takeyi?!
Tana kwance ta tasa system a gabanta tana kallo, ita bata kallon Korean dramas Amma
Tunda ta dawo Nigeria Jawad ya kwadaita mata su gashi yanzu batada abin kalla se
su, yanzun ma wani Empresski take kalla ko nace maimaici Don ta jima da kallonshi
amma yadda yayi kyau yasa take maimatawa, ta Gama shirinta tsaf gobe kawai take
jira ga dokin ganin dangin uwa ga dadin sun shirya da Ja'afar zaayi tafiya tare
Sede acan kasan zuciyarta akwai wani abu da take ji Marar dadi, Ta rasa ko meye
abin amma Lokaci guda har yana son yayi overcoming baki daya farincikin da take
ciki, lokuta da dama takanji inama ace itada Babban yaya zasu tafi, wannan
murmushin nashi, wannan muryar very deep amma me dadin saurare, me kuma mutsar da
Mai laifi, wannan idanun masu haske tamkar an disa musu abu a ciki, wannnan sharp
and piercing looks din nashi masu maidata jin she's helpless! Kai everything about
Junaid is just perfect.... Ta jima tana mafarkin inama ace shi ne Ja'afar, Ja'afar
ne shi, Tasha ayyana idan ace Itace Subay'a she will never ever mess up kamar yadda
Subay'a ke barin damarta. Tamkar karfe da magnet haka Sulaim taji mummunan force of
attraction haka cilak ta Mike ta doshi kofa sede Allah ya taimaka tayi assessing
kanta Ashe half gown ce jikinta da sauri ta dawo ta cire rigar ta dauki abaya ash
ta saka ta yafa mayafin ta fito batareda sanin meye dalilin fitowar ba ashe she
wants to see him, she wants to see all Abinda ta lissafa akanshi. Almighty Allah so
kind, da idanun ta Fara tozali Bata jira ba ta sakar mishi tattausan murmushi wanda
for life ba zai taba manta wannan murmushin ba, shima bai bata lokaci ba ya mayar
mata da wanda ya fiahi Lokaci daya suka runtse idanunsu gam! Wani Irin chemical
reactions, chemical bondings ya fara taking place, within seconds magnesium ya hadu
da sulphate, hydrogen da oxygen, sodium da chlorine and many more. Ina Subay'a? Ta
tafi daki amsa call din hajiya!...... Sorry kawata Kinyi missing.... Lokaci daya
suka bude idanunsu wanda suka sauke akan junansu Sede lokaci daya kunya ta lullube
Sulaim meye haka takeyi? Meye ke damunta? Juyawa tayi zata koma daki tamkar an
fisgo Junaid yace
Sulaimi!
Cak ta tsaya tana kokawa da numfashinta sboda yadda Sautin muryarshi ya illata mata
oxygen supply dinta Baki daya, a hankali ta juyo ta dubi inda yake bai tashi ba
Sede dukkan hankalinshi na kanta, da ido ya mata alaman taje gareshi haka ta tafi
cikin nitsuwa ta zauna inda ta Saba zama, idanunta a kasa idanunshi masu huda mata
jiki da tarwatsa dukkan kuzarinta suna kanta hakan yasa ta takura matuka shi kuma
kallonta yake yana mamakin kanshi, shifa ko Subay'a ya rantse da Rabbul Ka'aba
lokacinda yake sonta baiji Rabin Abinda yake ji akan Sulaim ba, yarinyar ta
shammace shi da yawa, ta shiga rayuwar shi tayi masa karan tsaye, tayi ma
zuciyarshi shigar ba zata....... Abincin da ya Fara ci ya tura Mata yace cikin
sassanyar murya
Kici!
Wannan muryar ba wadda xaayiwa musu bace hakan yasa ta dauka ta Fara ci shi kuma ya
maida kanshi kan call din Ja'afar da ya shigo masa daidai wannan lokacin. Farin
cikin da ta tsinci kanta a wannan Daren ba shida na biyu, Rana ta farko ta Fara
tuhumar kanta me take ji game da Junaid? Kada ya kasance zancen su Aimana su
Khulthum su khairi ya tabbata, tabbas da zuciyarta ta zalunce ta Tunda babu
possibility shidin zai so ta...... Amma fa wannan tunanin Sulaimi ne...... To
bangaren Junaid Wannan Daren matarshi ta kasance Tate dashi an Raya Daren,
sayayyarta da ta kwanta ta dan kankaro wani potion daga ciki, Tana bacci ya Mike
yayo Alwala ya fara kai kukanshi ga Rabbul Izzati! Baice Allah bani Sulaim ba a'a
yayi addu'ar Allah ya bashi alkhairi idan ita ce, idan kuma babu alkhairi Allah
yasa zuciyarshi ta dangana!
Washegari karfe bakwai Ja'afar ya iso, Junaid ya takura masa seda sukai breakfast
tare, Karo na farko cikin mutunci suka gaisa shi da Subay'a daga nan Sulaim ta fito
sede jikinta dukka yayi sanyi se satar kallon Uban Ahmad take, shima hankalinshi na
kanta Yana kallon duk Abinda take amma bai nuna ba. Takwas daidai suka rakosu har
bakin mota an zuba kaya da komai, Junaid ya miko mata envelope wadda bandir din
sababbin 200 naira notes ne sannan yace
Wannan naki ne, ki Turon account details dinki zan turo miki kudin da zaki bawa
mutane, Kai kuma
Ya juya kan Ja'afar
Be careful as you drive, Bana son Wannan gudun please.
Murmushi Ja'afar yayi yace
An gama babban yaya.
Itakam zuciyarta kunci take so take ko digon hawaye ya zuba mata taji sauki dukda
ta rasa me yasa take jin hakan, Ahmad da Muhammad suka zo sallama aikuwa Ahmad se
kuka zai bita, dama kukan take nema se kuwa ta Fara, Ja'afar yayi tsaki yace
Kin fiye shirme meye abin kukan.
Shikam Junaid kanshi ya girgixa mata yace
Ya isa haka Allah ya tsare .
Bata amsa ba amma tana ta kokarin shanye kukan a haka tana gani ta tafi ta bar
Junaid kewarshi ta mamaye ta har ta kasa sakin jiki sui hira sosae itada Ja'afar
seda Junaid yayi mata text din
_Those tears mean alot, is not every time ya kamata suna zuba. Allah ya kiyaye
hanya_
Wata Irin ajiyar zuciya ta sauke tanajin sabon abu Wanda bata san Meye ba Yana huda
mata jiki yana shiga zuciyarta, Lokaci daya kasala ta mata rubdugu Daga wannan se
bacci me Cikeda farin ciki!
Gbam! Gbam!! Gbam!!! Muuna kallon kowa a 3D screen.... Ehen rate this page on a
scale of 10.....
Shatuuu ♥️
[7/29, 6:16 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU*
21
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
Seda suka zo Funtua kafin Sulaim ta farka Daga baccin da take shima sanyin AC Ke
damunta dukda akwai hijab a jikinta amma bai hana taji sanyin na ratsa ta ba,
daidaita zamanta tayi ta dubi inda Ja'afar yake tirelessly driving, a kirjinshi
yaji ta farka hakan yasa ya dubeta yace
Sweetm kin tashi?
Kanta ta gyada tareda janyo bottle water dake gefenta ta Fara sha, seda Tasha Rabi
kafin tace
Munzo Gusau?
Kanshi ya girgixa yace
Yarinya wasa farin girki muna Funtua.
Bakinta ta turo ta janyo wayarta ta Fara danne danne, ita kanta bawai tasan me
takeyi bane,
Sweetm se Yaushe zanyi making move ne, ya kamata by now ace kowa yasan halinda muke
ciki?
Da sauri ta dago kanta ta dubeshi se murmushi yake, kanta ta girgixa tace
Kai a'a gaskiya!
Kallonta yayi yace
A'a me? Sulaim bafa aure nace muyi ba at least mu sanar dasu Mami yadda Lokaci nayi
dama ansan da maganar.
Kanta ta girgixa tace
Nidai a'a gaskiya
To saboda me?
Yaya yace Se naje level 3 kafin nan
Idanunshi a waje yace
Kice babanki bai amince ba, shikenan yadda kike so haka xa'ayi.
Cikeda jin dadi ta sauke nannauyan ajiyar zuciya har Seda Ja'afar ya dubeta sede ya
cigaba da tukinshi, itama ganin ya bar Wannan zancen yasa ta ware suka Fara hira
dukda karfin hirar shi ne, hira me dadi me tsayawa a rai.
Lokacinda suka isa garin jega sun gaji likis, nanne garinsu Mami asalin mahaifarsu
itada Mummyn Sulaim anan family house dinsu yake cikin Shiyyar Ni'ima, katon gida
ne ginin zamani me part biyar a cikin compound din, Tunda aka bude musu gate din
wani Irin yanayi ya lullube Sulaim ta tuno lokutan da suke zuwa tareda Mummyn ta,
Allah sarki mummy Allah dai ya kara haskaka kabarinsu ,bazata taba daina kewar su
ba, komai zata samu bazata taba daina cewar ina ma Daddy da mummy suna raye.
Cikin parlour kayattace wanda idan ka shiga zakayi tunanin gidan wata Amarya ce
amma ko daya mahaifiyar Mami ce a gurin Hajiya Juwairiyya itada megidanta Alhaji
Alkasim se jikokinsu guda uku da suke Zaune dasu, Hanan yarinyar Kawu Ali wanda ke
bin Mami iyayenta suna birnin kebbi, Amaturrahman diyar Kawu Mamman shi kuma Mummyn
Sulaim ke binshi sa'ar Sulaim dince yan watanni ne tsakaninsu, se Najib shi kuma
Yayan