Showing 51001 words to 54000 words out of 121650 words
zakai tunanin Auren Amra?
Then Jeka fadawa gwoggo me kakeyi mana.
To ya zanyi Kabir? Gwoggo is insisting!
Ya fada Yana dafe kanshi, shi ya rasa Wannan masifar na se yayi aure? Shi yace baya
so to me ye ne matsalar mutane.
Maslaha mu nemi Yarinya Marar gata wadda ko tayi kuka babu me damuwa ka aura, amma
Amra Tana da gata bazata taba jurar zama da kai ba.
To fa! Kunji wata sabuwar. Wanene Musbahu? Meye yake boyewa? Me yasa bayason aure?
Lokaci daya Junaid da Subay'a suka dawo gida, kowannensu basai yayi maka bayanin
gajiyar da yayi ba a kwance take a saman fuskarsu. Suna shigowa kowa ya shige part
dinshi se takwas sannan suka hadu duka parlor, Junaid na koyawa Ahmad homework ita
kuma Subay'a Tana surfing internet a system dinta. Sulaim dama bata fito ba Tunda
ta dawo Tana dakinta dukda taji hayaniyar sun amma tana ganin Lokaci yayi da zata
nisanta kanta daga Junaid Tunda har zuciyarta tayi gangancin sonshi. Ganganci ne
mana Tunda tana son abinda bazata samu ba, Abinda is beyond level dinta. Da hanzari
Junaid ya Mike jin sallamar Jabir da Imratu, Jabir a gaba Imratu na bayanshi suka
shigo har cikin parlon sede fuskar Junaid kamar zata yage saboda murmushi Yana son
a kawo mishi ziyara sosae yake jin dadi amma yasan halin Subay'a ke sawa yan
uwanshi Suki Zuwa.
Kan 2 seater suka zauna Ahmad tuni ya bar homework din yayiwa kansa mazauni cinyar
Daddy (kamar yadda suke cema Jabir) shi kuma Muhammad ya sauka Daga cinyar Subay'a
ya koma kan Imratu wadda se caressing dinshi take a ranta tana addu'ar samun nata
na kanta. Imratu ce ta Fara fadin
Yaya ina yini.
Da murmushi ya amsa sannan suka gaisa da Subay'a suna tambayar juna aiki kafin kuma
Jabir suka Fara hira dukansu, Subay'a ta kwalla kiran
Atika
Bata karasa fada ba ta fito dauke da plate da bowls, seda ta aje Kan dining sannan
ta iso ta gaisheda su Jabir kafin tace
Gani
Bakiji anyi baki ba, kiyi setting table mana.
Dan Dukar da kanta tayi Cikeda ladabi tace
Ina shirin fito da abincin kuma naji shigowarsu shi ne muke kara wani dish din amma
yanzu zan kawo.
Tsaki tayi ta cigaba da Abinda take itakuma Atika ta koma kitchen ranta a bace
kwatakwata Subay'a batada dadin zama sudai adduar su daya Abinda suke tunani
tsakanin Sulaim Da Junaid ya kasance. Imratu ta dubi Subay'a Tace
Maman Ahmad ina Sulaim ko bata dawo ba.
Dagowa tayi tace
Bansani ba ko ta dawo, ban dai ganta ba.
Kanshi ya girgixa Jabir sannan Junaid yace
Ahmad kirawo Anty a daki.
A guje ya nufi dakinta lokacin ta gama sallar ishai amma bata tashi akan carpet din
ba Ahmad ya shigo yace
Papa yace....
Kafin ya karasa tace
Kace ina zuwa.
Seda ta bata Mintina kafin ta Mike ta nade Sallayar ta cire Hijabin da abayar
sallar sannan ta yafo mayafi Kan baggy skirt din jikinta da faffadar top, kanta
cikin hula ta saka kalar skirt din ta fito bakinta dauke da sallama wadda take a
ciki ciki. Kamshin turaren ta na Zahrat Banafsat ya fara mishi sallama, aikuwan shi
ya fara juyawa ya bita da ido har ta shigo parlour fuskarta babu annuri ko digo,
sede idanunta sun kasa jurar rashin kallonshi, zuciya Tana tuhumarta why zata yi
shakalatun Bangaro ma abinda zuciyar ke so
_I love you... Please say you love me too... This three words they could change our
lives forever and I promise you that we'll always be together. Till the end of
time!_
Dagowa tayi ta dubi inda ya kafe ta da idanu ya manta da kowa a gurin, kawai se
taji kamar ana zare mata damuwar dake cikin zuciyarta, har batasan ta sakar mishi
murmushi ba seda ya mayar mata martani, se Jabir yayi gyaran murya wanda ya dawo
dasu hayyacinsu. Jabir ya kwashe da dariya tareda kallon Subay'a wadda take deep a
abinda take.
Shatuuu ♥️
[7/29, 6:16 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU*
25
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
Dariyar da Jabir yayi yasa Junaid ya kalleshi da sauri, Subay'a ta dago, Imratu ta
dubi mijinta tana mishi kallon kaima ka gani? don kuwa Tunda Sulaim ta fito take
Lura dasu har wannan flashy smile din da sukayiwa juna. Sulaim kam tuni ta isa
jikin Imratu ta rungume ta tana fadin
Fushi nakeyi daku har Yayan ma.
Dagota Imratu tayi tace
Kya yi mu bamuyi fushi ba se ke?
Bakinta ta turo Irin nayi fushi ta dubi Junaid
Yaya kace su bani hakuri.
Baki sake Subay'a take kallon shagwabar da yarinyar ke yiwa mijinta. Gyara zamanshi
yayi yace
Ku bata hakuri yanzunnan.
Me Jabir zaiyi idan ba dariya ba, tabbas ana abu cikin gidannan. Subay'a mikewa
tayi kamar zata tashi sama ta wuce kitchen nan da nan suka hada baki wajen fadin
Afuwan!
Are you OK?
Ya fada Yana mata kallo me Cikeda kulawa, kanta ta gyada Imratu ta bugi bayanta
mamaki fal fuskarta.
A table kowa maida hankali yayi kan cin abinci dukda ana exchanging glance Lokaci
Lokaci tsakanin Junaid da Sulaim. Tabbas kafin ka samu careless wife irin Subay'a
zaka dade Duk Wannan Abinda ake hankalinta baya kansu tana can tana tunanin maganar
da hajiya tayi mata dazun dasuka hadu da safe. Ta rasa ta ina zata bullowa
ala'lamarin gashi bata san dago maganar Tunda har yayi mata maganar zuwa Estonia
tana ganin zata Bari su dawo se ta tunkareshi taji!
Parlon Junaid Jabir dashi suka kebe don zantawa kasancewar sun jima basu hadu ba,
yayinda Subay'a ta koma dakinta, Imratu da Sulaim suka wuce dakin Sulaim din. Hira
sosae suke tsakanin su kasancewar ba karamin sabo bane tsakanin biyun. Suna hira
Sulaim na harhada kayan da zatayi amfani dashi a Birnin kudu Don Junaid ya sanar
mata tareda su Yaya Jabir zata wuce suma can din zasuje , wata katon gift ta dakko
anyi wrapping da farin sheet se kyalli yake, Imratu tace
Wannan fa?
Jujjuya shi tayi tace
Sakon Yaya Ja'afar ne, Yaya Hanan ta bayar a bashi.
Kai ta gyada ta bi Sulaim din da kallo a ranta tana tunanin Sulaim batasan tsakanin
Hanan da Ja'afar ba kenan? Kasancewar ita ba mai shiga abinda babu ruwanta bane
yasa ta kauda tunanin da take dole wata Rana komai Zai bayyana amma bata taba yiwa
Sulaim shaawar auren Ja'afar ba, kwatakwata he's not a Man, idanunshi baya zama Kan
mace daya. Idan banda zalama da kuma iskancin Ja'afar Tunda har hankalinta yana
kanshi Bata tunanin ta cancanci hakan. Sede bata sani ba yau Abinda idanunta suka
hango yana faruwa tsakanin Junaid da Sulaim ko idanunta ne ko kuma gaske ne? Abu
daya ta sani time will tell!
Da murmushi saman fuskar Jabir ya dubi Junaid wanda hankalinshi na kan Jabir din
yace
Bros Kana son Sulaim ne?
Baiyi mamaki ba saboda yanzun son Sulaim nema yake ya maida shi rago, nema yake
yasashi ya zama desperate and Babban abin Yana ganin idan ya cigaba da kauran baki
to zai iya furtawa gaban Subay'a ba kuma zai taba son hakan ya faru ba at least
Subay'a matarshi ce, first love dinshi bazai taba wulakanta ta ba Sede idan ita ta
wulakanta kanta kamar yadda suke yanzun.
Kana son sani ne ko confirming Kake son Yi?
Junaid ya tambaya Fuskarshi dauke da murmushi, shima murmushi yayi yace
Confirmation ne.
Then is true, I love her!
Babu mamaki a Fuskarshi se wani farin ciki da at once ya lullubeshi yace
Amma naji dadi, Baban Sulaim zai auri Sulaim itama Naga kamar tana ciki, a ina
kuke?
Kanshi ya shafa Lokaci daya murmushin ya dauke dif se kamar fear da wani abu da shi
Jabir din ya kasa karatowa Junaid yace
Ba ta sani ba, ban fada mata ba.
Why? Waiting for what?
I dunno Jabir, banda courage din.
Haba Bro, Sulaim ce fa, your Sulaim ita ce Kake tsoro? Ni zan fada mata da kaina
Da sauri ya girgixa kanshi yace
No please! I promise ina dawowa daga Estonia I'll let the word out Inshaaa Allah.
Yasan Junaid baya magana biyu su kuma bazasu taba barin such a golden opportunity
ya wucesu ba, dama bai kamata ace bare ya auri Sulaimi ba Tunda basu san wani
hannun zasu mika ta ba. Hira cikin nishadi sukai dukda Jabir se zolayar Junaid yake
akaan Sulaim. Abin gwanin shaawa don bazakai tunanin cewar brothers bane sunfi Kama
da abokai. Wajen goma Jabir ya dubi Junaid yace
Bari mu wuce ko room bamui booking ba.
Cikin rashin fahimta Junaid yace
Kana nufin hotel zakuje, already an gyara wancan dakunan, idan baiyi maka ba se ku
zauna anan.
Babu yadda Jabir ya iya haka suka koma part din dake gefe don dama don haka aka
tanadi gurin.
Wallahi yau ba se gobe ba Seka fada min Abinda Ke tsakaninka da waccen yarinyar.
Subay'a ta fada idanunta taf da hawaye, Haba ta gaji bazata iya ba, kowa daukarta
yake shashasha a gidanta mijinta na son wata. Kallonta yayi yaga yadda take tada
jijiyoyin wuya amma tausayinta yakeji kuma for Sulaims safety yasa bai kulata ba ya
cigaba da Abinda yake cikin system. Gefenshi ta matso tareda kawar da system din
daga gabanshi ta Maye gurbin tace
Wallahi se ka fada min Junaid kaji na rantse.
Idanunta na digar da hawaye da Lokaci daya sukai nasarar wanke mata fuska, abin ya
fara kaishi Anty bango amma baisan bacin rai yasa yayi Abinda zai yi Dana sani daga
baya yasa ya Mike don zuwa cikin bedroom dinshi, Sede kamar wata zakanya ta rigashi
isa gurin tareda blocking hanyar tace
Ai kaji abinda nace, babu inda xakaje se ka fadamin.
Dagowa yayi ya dubeta, se kuka take kamar wadda akaiwa mutuwa Amma yadda take abin
ransa ya baci hakan yasa yace
You want to know right? OK! Son ta nake kamar yadda kike zargi kuma aurenta zanyi.
Is that all?
Lokaci daya numfashinta ya fara fita cikin sauri sauri tamkar wadda tayi gudun
marathon. A gigice Subay'a ta farka daga wannan mummunan mafarkin, hannunta ta kai
ta kunna bedside lamp din Lokaci daya haske ya gauraye dakin, idanunta suka sauka
kan Junaid dake zaune kan carpet ya kura mata idanu, itama kallonshi take hawaye
wani na bin wani dukkan jikinta na rawa wanda hakan ya tabbatar masa mummunan
mafarki tayi! Hannunshi ya mika mata babu musu ta zura nata tareda sakkowa ta lafe
jikinshi kukanta na Kara karuwa jinta jikinshi, Baki daya tashin hankali da tsoro
suka addabe ta, Tana son tambayarshi ko Abinda ya fada mata cikin mafarki gaske ne
sede tana gujewa kunnenta mugun ji.
Cikin sassanyar murya yace Yana shafa gashinta wanda ya bayyana sakamaakon hular da
tayi nata gurin har Zuwa bayanta
You had a nightmare?
Kanta ta gyada tana sake bawa hawayen idanunta damar zuba freely. Gogesu yayi da
tafukan hannayenshi yace
Ya isa haka, Bakiji you're safe ba kina arms dina just pray ko zaki fadamin?
Da sauri ta girgixa mishi kanta hakan yasa ya rabu da ita, daga karshe da kukan ya
lafa ya jata suka koma gado batareda ya karasa tsayuwarshi ba. Da kyar bacci ya
dauki Subay'a saboda ta kasa manta mafarkin.
Washegari Tunda suka tashi ta Fara bashi wata care wadda ko lokacin farkon aurenshi
ban tunanin an bashi, haka shima saboda Kwana tayi da zazzabi Shiyasa tausayinta
kawai yakeji. Tare sukai wanka ta shirya shi sannan ta shirya kanta kafin ta fito
don ganin yaranta. Tana fitowa sukai kicibis da Sulaim wadda take kokarin komawa
dakinta. Kallo ta bita dashi gabanta na faduwa kamar zai balla kirjinta Don
fargaba, tsana Sulaim ta mata dirar mikiya Sede ita Sulaim din bata ma lura da
halinda Subay'a ke ciki ba hasalima tana gaisheta ta wuce dakinta zuciyarta a
cunkushe tana ganin kamar ita din tsaiko ce tsakaninta da Junaid din.
Tare sukai breakfast gaba dayansu, kasancewar Junaid na ganin har lokancin Subay'a
bata ware daga firgicin mafarkin jiya ba yasa yake nan nan da ita, motsi tayi
kwakwara zaice
Are you OK Dear?
Hohohoho? Hakan da yayi ba karamin Sosa ran Sulaim yayi ba, itakuma Subay'a kamar
ta zuba ruwa kasa Tasha. Can ana tsaka da cin abinci mistakenly Subay'a ta kware
cikin hanzarta Junaid ya balle murfin bottle water dake gefenshi Don ka'idar shi ce
shan ruwa after breakfast, da kanshi ya kafa mata a baki Wanda idanun Sulaim sukai
kir Akansu, zuciyarta ta buga da sauri kuma ta janye idanunta tareda daukar spoon
sede tana dibar abincin hannunta ya kifar dashi saboda rawar da yake, Jabir ne ya
gyara murya yace
Sulaim are you OK?
Se lokacin Junaid ya dubeta idanunta sun cika taf da hawaye kadan suke jira sui
splitting mata a fuska.
Meye ke damunki?
Junaid shima ya tambaya amma se ta dauke kanta daga kallonshi Tace da Jabir
Na koshi.
Then jeki karasa shiri muna gamawa zamu wuce.
Da sauri ta Mike har tana tuntube ta nufi dakinta, baki daya suka bita da ido
Subay'a na mata rakiya da harara, she hate the girl that is just the fact!
Tara na safe suka fito baki dayansu a gefen mota, ita Subay'a tuntuni ta fice itama
yaran dake Muhammad ma an kaishi kingdergaten, Tunda ta fito ya lura fushi take
wanda ya rasa dalilin da yasa Sulaim Keda saurin fushi haka to shi bai masan ko me
akai mata ba amma dukda haka kallonta yayi tana kokarin bude bayan motar yace
Sulaim.
Ko tana so ko bata so dole ne ta juya Don kuwa zuciyar ta bazata yafe mata ba
matsawar taki yin hakan. Cikin ido suke kallon juna kowa nutsuwarsa na dawo mishi,
tayi saurin dauke kanta ta sunkuyar tana mitar abinda yasa take kallonshi, envelope
ya mika mata yace
Se Saturday.
Amsa tayi ta mishi godiya sannan ta shiga ciki Jabir Yana kallonsu yana murmushi
sannan sukai sallama sannan suka dau hanyar.
Awanni biyu cif ya kaisu gurin Birnin kudu, gaba daya Sulaim a gajiye take sosae
kamar dukanta akaI sauki daya ta sha bacci wanda da wannan damar Imratu ta samu
itada Jabir ya tsegunta mata abinda Ke faruwa. Itama farin ciki sosae tayi amma
tana ganin yadda zaayi da Subay'a.
Kwananta uku a Birnin kudu Mami, Baba, Jawad da oga Ja'afar suka iso, wannan
kwanaki uku babu Daren da Batayi kuka ba saboda yadda zuciyarta Ke axabtuwa da
rashin Junaid a Rayuwarta, baki daya tayi mamaki yadda Lokaci daya soyayyar Junaid
take neman farautar farin cikin ta. Duk yadda take cikin dangi anata shirin biki
Amma ita abin baya burgeta ko daya hasalima kullum tana dakin Neneh kamar yadda ake
kiran kakarsu, Mama Sauda da kullum Se taxo gidan tayi fadan har ta gaji, Sulaim ce
kadai tasan Abinda Ke damunta ita kadai tasan kuncin da zuciyar ta ke ciki. Ranar
Sulaim murna gata ga Mami duk inda Mami zataje Sulaim Tana bayanta Mama Sauda ta
dinga mata tsiya wai makon uwa ne da ita itakam sede dariya.
Da daddare babu kowa parlor kowa na dakinshi Sulaim ta fito da gifts din, wayarta a
kunnenta tana kiranshi Ja'afar don ya karba,
Luff ina parlon kasa kazo.
On my way Sweetm.
Baifi 5 minutes ba ya fito cikin 3 quarter jeans da top armless, Baki daya ta
bayyanar da damtsen shi dake a murde saboda gyming. Zama tayi akan carpet shima ya
zauna gefen ta Yana kallonta yace
What do we have.
Me zance tsautsayi? Ko kuma karar Kwana? Sulaim Bata bashi amsa ba ta farke
wrapping sheet din tace
Yaya Hanan tace na kawo maka.
Cikin sauri ya kai hannunshi don kwatar komai Amma it was late don ta riga tayi
tozali da rose flowers biyu, turare amma Abinda yafi daukar hankalinta shi ne wani
kyakyawan frame me rubutu kamar haka
_When you are in love, the heart works faster than the brain, without the brain the
body survives but when the heart fails the body dies! You're my heart and I love
you!-
Dago idonta tayi tana kallonshi kamar yadda shima kallonta yake ba tareda yasan
abin yi ba.........
Shatuuu ♥️
*MACE A YAU*
26
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣shatuuu095@wattpad
Halo people of *SHATUUU's KINGDOM and MAMAN MAMA NOVELS* Double hey! Triple godiya
for the love and everything I'm very happy having u guys as my Buddies 😘
*A broken heart can be pieced back together, it might be a heart again but it's
still a BROKEN HEART*
Shima cikin idanu yake kallonta kamar yadda take kallonshi mamaki karara saman
fuskarta.
Sulaim lemme explain.
Wani kallo ta watsa mishi wanda a take yasa shi rufe bakinshi Wanda DA ya bude da
niyyar sake wani protest din amma kallon da tayi mishi yasa ya hadiye maganar
tashi, mikewa tayi daga zaunen da take har lokacin hannunta na rike da frame din,
kallonshi kawai take da idanunta da suke cike taf da hawaye Wanda by mistake tayi
magana to tabbas zasu zubo, wata Irin bugawa zuciyarta take, wani Irin ciwo take ji
kirjinta nayi mata, frame din ta doka da kasa akan tanganyar tiles babu jira glass
din gaban ya tawarwatse, perf din ta dauka shima ta buga da bangon parlon sannan ta
toshe bakinta da hannunta dan kuka ne ya taho mata tun karfi, then komai ya kare
kenan her only hope ja'afar bai daina kule kule ba bayan ample of chances da ta
bashi, zuciyata data mika mashi that's the pay back daya bata. Ga zuciyarta
mayaudariya, macucia, azzaluma data zalunce ta take son Junaid wanda baisan abinda
take ciki ba, take hawaye ya balle mata babu waiwaye ta nufi staircase a million
don tana bukatar break, me tayi haka da tayi deserving such treatment? Me tayi.
_Call the man who deals in love beyond repair, he can heal the world of heart in
need of care... Shine the light ahead when the next step is unclear....._
Jaafar na tsaye tamkar an dasa shi akan kafafuwanshi haka ya tsaya yana kallonta,
ya kasa furta komai na kare kai saboda yadda idanun sulaim suke ko shi waye bazata
saurareahi ba, to shima bashida abin fada sede idan karyar da ya saba zai mata.
Jagwab ya zauna kan kujera tareda buga tagumi ya rasa abinda yake ji Yafi Mintina
goma kafin Zuciyarshi tace mata nawa ke binka kana dodging? Mata nawa kuke soyayya
dasu?don kwaya daya tace batayi shi ne abin damuwa? Abin daga hankali?kanshi ya
girgiza ya mike yana daga kafadarshi irin ko a kwalar rigarshi but deep down him
yasan he missed an angel Don ko ya yarda ko yayi denying Sulaim is still Sulaim.
Sede yana ganin tayi kadan ta juya shi kuma yasan son da take mishi ba zata jure
been away from him! Se muce tunanin Ja'afar kenan ba namu ba! Ko ba haka ba
Shatuuu's kingdom and Maman mama people?
Mami Zaune Kan kujera a parlonta se Jabir da Imratu dake gefe, Jawad na kan carpet
yana cin abinci Se Subay'a da Junaid wanda zuwansu kenan kasancewar very late ya
tashi a office Shiyasa basu zo da wuri ba kuma Mami tace lallai ya bar Duk Abinda
suke shi har da Subay'a din su taho, yaran babu yadda Junaid bai yi ba akan su taho
tare se cewa tayi wai sauro