Showing 93001 words to 96000 words out of 121650 words
tsinci kanta da juyawa ba tareda tayi mishi
musu ba ta wuce dakinta kamar sokuwa ta tattaro keys din Baki daya ta kawo mishi.
Yana karba ya wuce abinshi babu wani bayani ko wata magana hakan ba karamin tayar
mata da hankali yayi ba.
What's Alhaji up to?
Rana bata karya sede uwar diya taji kunya wannan shine popular Hausa proverb da
muka sani, tabbas ya tabbata Ummu_Khulthum Suleiman Malumfashi ta zama mallakin
Musbahu Suleiman Jimeta akan sadaki zunzurutun kudi naira dubu Dari bakwai. Mutane
sun halarci wannan daurin Auren duniya ta shaida saboda yadda Musbahu ya daukaka a
duniyar business da Entrepreneurship, the young billionaire kenan, Musbahu me TitαΦ
Dan Gwoggo na Khulthum!
Anyi biki na Kece raini ba Daga bangaren Amarya Ba ba Daga bangaren Gwoggo ba, anyi
harkar girma don kuwa Khulthum ta sakar ma Mama kudi Don ta fitarda da ita kunya
aikuwa babu karya ta fitar da itan. Parties iri iri seda tayi kala biyar babu Wanda
Ango ya halarta se wata English dinner da business partners dinshi suka hada mishi
anan garin Abuja, haka yasa aka mishi booking flight ita dashi suka tafi karfe
shida na yamma, anan aka shirya ta tayi kyau tamkar ba ita ba sannan driver yaxo ya
dauketa ya kaita inda Musbahu yake, yayi kyau shima cikin grey tuxedo suit hannunsa
daure da bakin agogo na kamfanin Boss, yayi kyau sosae kana kallonshi kaga fulanin
usul, lokacinda ta isa gareshi waya yake, ya juya bayanshi a hankali ta kare mishi
kallo Tana Kara godewa Allah mijin da ya bata wanda ko daya bata taba tunanin zata
samu kamarshi ba. Amma here she's with mijin da duk duniya tasan ta auri mijin
nunawa saa. Juyowa yayi Don Tun shigowarta yaji a jikinshi saboda turarenta da ya
ziyarci kofofin hancinsa, kallonta yayi he has to admit the fact that Khulthum
kyakyawa ce wadda bazai yi shayin shiga da ita kowanne guri ba, Sede yasan babu
digon son shi cikin zuciyar ta, kudin shi take yiwa zai cika mata burinta kamar
yadda zata zama protector ga rayuwarshi.
Kanshi ya dauke ganin sun hada idanu kar tayi tunanin ta burgeshi ne, itama kanta
ta dauke a ranta tana fadin duk wannan girman kan naka se na sauke maka shi! Tare
suka fito Zuwa wata lambhorgini baka wuluk da take tsaye Tana jiransu. Kunsan abin
wayayyu, Manya wanda kudi ya zauna musu, dinner was great karfe Tara aka tashi
Khulthum ta tafi da kyaututtuka iri iri.
A Daren suka dawo kano, Washegari ranar ta kasance lahadi tun safe yan uwa,
munafukai, abokan arziki, Kawaye sukaje ganin daki kowa idan ya dawo banda zancen
gidan babu Abinda suke, gida ne da suke ganin tamkar drawing ko kuma a film saboda
yadda ya hadu.
Da daddare Misalin Tara Gwoggo da kanta tazo ta tafi da Khulthum, babu wata nasiha
da akai mata don kowa tsoron magana yake ganin gidan da Khulthum din ke ciki waye
zaiyi gigin barar da kujerarshi, hatta Mama bata wani Yi mata fada ba kawai tace
mata tayi abinda ya dace.
Har daki Gwoggo ta kaita tazo itada Musbahu wanda gaba daya jikinshi a matsanancin
sanyaye yake gefen ta ta sanya su ta shiga tsakiyarsu tare da kamo hannunsu cikin
nata fuskarta kadai zaka kalla kasan tana cikin farin ciki Marar misaltuwa,
furucinta kadai seda ya kara jefa zuciyar Musbahu cikin Anya kuwa?
"Allah ubangiji yau ya cika min burina da ya dade cikin zuciya ta, Allah yasa yau
naga matar ka Musbahu, ina fata zaku zauna da junanku lapiya, zaku sauke dukkan
hakkokin da ubangiji ya daura muku. Ina fatan kunsan cewar shi aure is for two
parties babu yadda za'ai ace na mutum daya ne, kowannenku Yana da nashi role din
dayake playing. Dukkanku babu yaro ina fatan zaku zauna lapiya!..... "
Ta dade tana tuna musu hakkonkinsu kafin ta hada hannayen su guri daya ta fice baki
daya daga gidan, ta koma nata. Sun dade a haka kowannen su da Irin tunanin da yake
har wasu mintuna suka shude kafin Musbahu ya cire lallausan Hannunsa Daga nata, ba
tare da ya furta komai ba ya fice daga dakin.
Mikewa tayi itama, ta Fara kallon dakin da yake mallakinta, duriyar da aka dankara
a ciki don ko cokali ba Taxo dashi ba anan ta samu. Touring part din Nata tayi,
kana shigowa zakaga karamin parlor me dauke da cushions guda biyu se center table
da carpet, ta gefe jikin bango akwai wani hadadden console a manne. Daga nan se
siririn corridor wanda yasha ado da manyan frames da akai painting a jiki na
flowers masu kyau, a karshen corridor akwai tafkeken parlor wanda ya kunshe kujeru
set uku kowanne da kalarshi da kuma design dinshi. Parlon kadai abin kallo ne, anan
wawakeken kitchen wanda ya kunshi kayan alatu na idon duniya electronics iri iri
kusan duka ma batasan yadda zatayi amfani dasu ba. Bedrooms biyar ne, uku nata biyu
na Baki. Gidan yayi kyau.
Dakinta ta koma ta shiga wanka zuciyarta Fara kal kamar shinkafar tuwo, shiryawa
tayi cikin wata sexy sleeping wear iya gwiwa baka tayi kyau kamar ba ita ba Balle
yadda Tasha gyara don ta durzu a wajen masu gyaran jiki Shiyasa ta Kara kyau sosae
kamar ka tabata jini ya fito, kwanciya tayi idanunta a lumshe tana planning yadda
abubuwa zasu tafar mata. Tun tana zuba idon ganin ta inda Musbahu zai bullo har
wani nannauyan baccin gajiya yayi tafiyar ruwa da ita.
Washegari Bata tashi ba Se sha daya na safe, seda ta tsala wanka kafin ta fito tayi
kyau cikin wani dankareren bakin lace wanda aka mishi ado da manyan flowers fuschia
pink, parlor ta fito inda ta tarar komai in place, dining an shake shi da different
dishes na gida dana waje. Can ta wuce tana bubbudewa amma ko abinci kwaya daya Bata
san sunanshi ba. Tana kokarin zama Sega wata matashiyar budurwa Sanye da uniform
tazo ta gaisheta cikin Pigin English, ta gabatar da kanta matsayin Linda Itace me
kula da abinci.
Zama Khulthum tayi Cikeda isa Tana karkada kafa ta dubi Linda tace
"you're welcome here, inason duk lokacinda aka gama abinci kafin ayi serving dina
se an fada min sunanshi da asalin dish din wanne kasa ne "
Da sauri Linda ta gyada Kai tareda fadin
"Noted Ma'am"
A hankali ta Fara bubbudewa tana mata bayanin komai, Khulthum tana saurare saboda
ta rike don babu girma ace Bata san wannan abubuwan ba. Bata jima da kammalla cin
abincin ba Maimuna da Safiyya wanda suka zama sababbin kawayenta suka zo gidan,
Bedroom dinta suka baje ana tashan shafta Bayan ta saka an cika musu gaba da
abubuwan tabawa. Maimuna tace
"Hajiya gidannan yayi kyau babu karya se Munji kin Fara laulayi "
Dariya tayi tana jin yadda sanyi ke zagaye ilahirin jikinta, tana jin burinta ya
kammalla cika bata da sauran matsala kuma. Seda sukai La'asar sannan suka tafi,
dake an ware mata driver da me kaita da kuma na bakinta, haka tasa ya kaisu har
gida, suna ta fasa mata kai ita kuma tana Kara girman kai. Dama Tun kafin a kawo ta
Tace da Mama kada wadda tazo mata gida Washegari Tunda duk sunga gidan to hakan ma
yayi, Shiyasa yau Batayi Baki ba se zagayen gidan da ta karayi.
Har aka Idar da sallar isha'i bata ji shigowar Musbahu ba, mikewa tayi ta dauki
wayarta da niyyar kiranshi ta tuna bata da contact din shi, abinma se ya bata
dariya don ko a labari bata taba jin hakan ba. Duba kanta tayi tana cikin wata
Indonesian Abaya beige color, Abayar tayi mata kyau sosae abinka da farar mace,
kanta na cikin wani milk scarf wanda ya zauna daidai da tsarin jikinta. Flat milk
vine ta zura ta fito bayan ta feshe jikinta da sassanyan Arabian turaren ta. Tana
fitowa Linda na kokarin setting table, kallonta tayi tace
"Ina ne part din Musbahu? "
"Ma'am ta gefen naki yake"
Kanta ta gyada ta nufi kofa zuwa nashi haka kurum gabanta ya dinga faduwa, amma ta
cigaba da nufar part din, babu kowa a parlorn se sanyi da kamshi dake tashi, parlon
ya hadu ba iyaka don haduwar shi will put her own into shame! Rarraba idanu ta
tsaya yi se taji bude kofar bedroom din dake fuskantar ta, hankalinta ta mayar
kofar take wani charming guy wanda shekarunsa bazasu dara 23 ba ya fito bayansa
Musbahu ne Fuskarshi a wani yalwataccen murmushi ne wanda ake gani kamar sau daya a
shekara!... Lol.... Ko kallon inda take baiyi ba sema guy dinne ya gaisheta ta amsa
Tana nemarwa kanta masauki cikin daya daga cikin Royal Cushions din dake cikin
parlour.
Tafi Mintina talatin zaune kafin Musbahu ya shigo Yana binta da kallo Marar ma'ana,
kasa tayi da kanta har ya sami guri ya zauna sannan yace
"Me ya faru? "
Da sauri ta dago idonta tana kallonshi don ba haka ta Zata zaice ba, ta yaya ma zai
mata wannan maganar Bayan yasan ba hakan ya kamata yayi ba.
"Naga baka shigo bane, nazo naga lapiya"
Tana rufe bakinta yace
"Lafiyata kalau, bana san sake ganinki a part dina, duk Abinda kike so zaki iya
kirana, idan kuma ina bukatar abu zaki ganni. Ina fata zaki kiyaye saboda gudun
mummunan gani"
Cikin rashin fahimtar furucinshi na karshe ta dago Amma har ya nufi dakinshi, kanta
ta dafe a ranta tana fadin Khulthum me kika siyawa kanki? Tana nan Zaune tana jiran
ya fito ta fada mishi batada contact dinsa amma shiru, har ta Mike zata fita Sega
wani matashi wanda shekarun shi bazai wuce 19 ba ya shigo kuma straight dakin da
Musbahu ya shiga nan shima ya fada ko kallonta baiyi ba.
Kwadayi mabudin..........
Shatuuu ♥️
[8/26, 5:03 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
47
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
*Where are you my best friend, beloved and my other half, the first person I know
_Salma Hassan Kwalam_ take this page please! My everything.... The person that
always brags I'm not missing you but keeps on calling asking se Yaushe zaki dawo?
That's my sister for me*
_VALLETTA_
Sulaim na tsaye gaban water dispenser hannunta rike da Tea mug, ruwan zafi ta
tsiyayo sannan ta dawo cikin parlon dake suite din nasu, tea bag ta jefa ciki
tareda cube din sugar. Seda ta juyo kafin na samu damar kare mata kallo, tayi kyau
kamar ba gobe dukda babu Abinda ta shafa a fuskar Amma kana kallonta kasan Hutu,
Jin dadi da kwanciyar hankali sun samu guri. Ta kara haske fatarta se glowing Take
tare da murmurewa. Tana Sanye da mini skirt fari me ditson gold, rigarta wadda ko
cibiyarta bata rufe ba gold da fari farin lacy design a jiki, kanta babu dankwali
se parking da tayi in a ponytail design. Transparent golden jacket ta daura saman
kayan wadda akaiwa ado da gashi me laushi a jiki.
Single bedroom din dake cikin suite din ta nufa, Junaid na tsaye jikinshi Sanye da
bathrobe wanda ya tabbatar mata da fitowarshi kenan daga wanka, tea din ta Ajiye
Kan dan table din dake gefen gadon wanda Junaid ya maida gurin wajen aikinshi
system dinshi a gurin take dindin da papers yana aiki, gurin no go area ne ga
Sulaim don ya hana ta saboda yace aikin school yake bai son ta gani Tunda she's
still thier student.
Inda yake ta isa fuskarta dauke da madaukakiyar fara'a wanda ya bayyanar da
hakoranta, wushiryar ta da kuma dimples dinta da suka lotsa baki daya, shima wani
kwantaccen murmushin ya dinga binta dashi wanda yake sa takan manta har kanta,
murmushin nan ba karamin kwantar mata da hankali yake ba, tana jin duk duniya in
har zata cigaba da ganin Wannan murmushin Fuskarshi to she need nothing again in
her life, he's everything he needs, har ta isa inda yake bai daina murmushin ba,
zagaye hannunta a jikinshi tayi tareda kwantar da kanta kan kafadarshi ta na mishi
kallo cikin idanu. Hannunsa yasa ya shafa kanta yace
Kinyi kyau Dove.
Thank you....
Se tayi shiru bata karasa ba saboda yadda ya tsareta da idanunshi Yana jiran tace
Yaya, sakinshi tayi ta isa kan gadon ta zauna tareda fadin
Hearthrob!
Gurarshi guda ya daga tareda karasowa inda take ya zauna Yana rike hannunta tareda
fadin
I'm I as sweet as that?
Dariya ta saki tana rufe fuskarta, janye hannunta yayi tareda matso da ita jikinshi
yace
Comeon Dove tell me mana!
Ya fada kamar yaro a shagwabe, turo bakinta tayi tace
Kafi haka ma.
He was stunned saboda yadda tayi maganar Daga karkashin zuciyarta yake, wani farin
ciki Marar misaltuwa ya kara mamaye ilahirin jikinshi, tashi yayi Daga gefenta bata
tsammata ba ya daga ta sama yana rocking dinta tamkar baby, se dariya takeyi tana
jin kamar duk duniyar nan su biyu kadai suka rage kuma babu Wanda ya kaisu farin
ciki
"Hearthrob Kaga I'm feeling dizzy"
Jin hakan yasa ya sauketa tareda danneta suna maida numfashi kafin kuma Sulaim ta
Fara ihu
"Ka daga ni "
Kafada ya maqe alamun No, hannunta tasa ta Fara tutture shi har ta samu ya zame
zuwa gefenta ya kwanta Yana sakin ajiyar zuciya, wannan shi ne babbar dacewa auren
abinda kake so yake sonka don shi yasan yasha Kwana!
Tare suka shirya Don yace mata zasuje restaurant din dake cikin hotel din suyi
breakfast, jeans ta saka wanda ta cikashi tayi dam revealing dukkan wasu curves
dake jikinta, Top ta zura wadda ta sha rubutu masu yawan gaske with different
colors, wata lallausan kimono baka ta daura tareda rolling karamin veil daya sakko
ya rufe mata kirjinta, tare suka nufi kofa se Lokacin ta tuna da ashe tea zata sha,
dariya tayi Wanda yasa shi dubanta amma baiyi magana ba, haka abin yake lokuta da
dama takan manta abubuwa da yawa, Junaid ya zama babban jigo cikin rayuwarta.
Simple abinci na breakfast aka musu serving, Cikeda nutsuwa suka ci sannan suka
fita don yin walk, garin badai dadi ba ga weather dinsu itama is favourable, a
yanzun Satinsu biyu kenan da isowa kasar, Seda sukai kwanaki hudu ko kofar suite
dinsu basu leka ba suna ciki suna honeymoon dinsu me kyau, hakan yasa suka shaku
sosae har Sulaim ta zama 'yar gari a fannin, wannan zaman ta kara fahimtar abubuwan
da Junaid yake so da wanda baya so, shima kuma da Wannan damar ya daura mata mugun
sabo dashi wanda an inch suka kasance basu kusa se jikinsu ya fada musu, haka Kuma
yayi nasarar kawar da 60% na kunyarshi a kanta. A Kwana na biyar suka samu cab ta
dinga kaisu gurare cikin Valletta basu suka dawo suite dinsu ba se yamma likis
Wanda gajiya take neman ruguza su. Kwana biu suka huta sannan suka dora da gurare
cikin kasar ta Malta.
Daf da Za'a Fara shiga sallar Azahar ta zauna kan wani bench dake gefen titi shi
kuma ya shiga massallaci don yin sallah, wayarta ta dakko ta Fara chatting nan taga
message din Jabir da na Anty Imratu, cikin hanzari ta bude na Imratun it says
"Matar Yaya, Nanda eight months kui expecting baby from me Inshaaa Allah"
Gaba daya se taji tamkar wani awaited burunta ne aka cika mata shi, Anty Imratu
nada ciki, dukda ta kasance a yanayin rashin sallah hakan bai hanata yin sujudus
shukr ba don nuna godiyar ta ga Allah. Tana dagowa ta Fara kiran Jabir Allah ya
taimaka wayar ta shiga aikuwa yana dauka ta Fara fadin
"Alhamdulillah Yaya! I'm so happy for you guys "
Ko ba'a fada ba tasan yana cikin farin ciki Marar iyaka
"Nagode sosae mutanen Valletta, Ina Yaya "
"Yana sallah"
Ta bashi amsa, kanshi ya gyada yana Kara mata godiya bai jira sunyi sallama ba ya
kashe saboda wani call dake shigowa, Jin dadi sosae yasa bakinta kamar zai yage ta
Kira Mami da Imratu Amma amsa daya ce wayarsu is not reachable at the moment. Haka
ta hakura badan taso ba, wani Irin dauki take ji take kamar ta shiga massalacin ta
fada mishi sakon Amma babu Hali, haka Tanan Zaune se murmushi take tana jin tamkar
tayi tsuntsuwa Zuwa Nigeria don taya su Yaya Jabir murna, dama rayuwar hakuri ce
kawai gashi su At longest last gashi sun haihu, Dama haka abin.......
Bata karasa tunanin ba taji tattausan hannaye sun rufe mata idanu, ko baa fada ba
tasan Junaid ne don kuwa turarenshi ya tona asirin shi, dariya ta saki tareda fadin
Heartthrob!
Sakar mata ido yayi, tare da jiyowa ya tsaya a kanta yasa hannunshi ya rankwashi
kanta, kanta ta yi saurin mikewa tare da Dora hannunta daidai inda ya rankwashe
tan, ta zumburo bakinta idanunta sun cika taf da hawaye don taji zafin rankwashin
ba karya! Wuceshi tayi har lokancin Bata daena sosa kan ba, ganin haka yasa yayi
saurin bin bayanta tareda shan gabanta Yana mata Abinda yasan shi ne weakness dinta
wato wannan kayataccen murmushin, Hararshi tayi tana bawa hawayen damar zuba kan
kuncinta, da sauri ya zaunar da ita don rabon da yaga hawaye a fuskarta tun ranar
da zasu zo Malta, yasan wancan ma shagwaba ce amma wannan fa? He's the cause Bayan
alkawarin da Yayi mata da kanshi akan he'll do whatever it takes to see batai kuka
ba. Poor him gashi baaje ko ina ba ya sata kuka.
Itama ganin yadda Fuskarshi Lokaci daya yasa ta share siraran hawayen zafin
rankwashin tace
I'm OK, kawai heartthrob mugunta kamin"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da rungumota jikinshi ya rada mata abu a kunne, dariya
sosae ta dinga yi hakan ya mantar da ita rankwashin da yayi mata. Seda suka koma
suit dinsu ta Fara fada mishi cikin Imratu, sosae yayi murna sannan ya kira Jabir
sun jima suna magana har bacci ya fara fizgarta akan carpet din kafin taji ya matso
da ita jikinshi Yana fadin
"Raguwa kawai, 3 months har yanzun kin kasa conceiving se bar mana babies kike suna
ficewa"
Ya fada Yana murmushi, hannunta tasa ta toshe kunnenta tana jijjiga Kai irin bata
ji ba, dariya yayi yace
"Take your time dear"
A hankali yayi slipping bakinshi cikin nashi, itama cikin bukata ta bashi hanya
suka Fara kissing junansu.........
🎤Zuciya ta da taka abokan juna, da basu rabuwa ko a gun Kwana! Ina a farke ko a
cikin barci na kai nake tunani cikin kwakwalwa ta....
🎶
The page is very small I know.... Just manage OK..... I love you guys! Irin one
love dinnan!
Shatuuu ♥️ *MACE A YAU*
48
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
Ranar ta kasance Lahadi wanda yayi marking Kwanaki ashirin da uku da Subay'a ta
baro garin na Cyprus ta dawo gida zaman jiran gawon shanu, zaman da bata san Meye
makomar ta ba, zaman da wanda take dominshi bai san tanayi ba. Gabaki daya tayi
rama ta kare tamkar kudin guzuri, Duk wannan abubuwan da ta dauka ta aza