Showing 33001 words to 36000 words out of 121650 words

Chapter 12 - MACE A YAU by Shatuuu

Shatuuu   

12 May 2026

145

bag taji vibration dinta hakan yasa ta ciro ta ganin sunan Beloved Hajiya yasa
tayi murmushi yau Baki daya bata kirata ba, seda ta Bari ta katse kafin ta kirata

Hajiya barka da yamma

Barka ka dai Subay'a

Hajiya ta fada Daga Dayan bangaren,

Ya aiki ko har kun tashi?

Kai subay'a ta girgixa tace
Muna kokarin tashin dai.

Allah ubangiji ya taimaka ya muku albarka Baki daya.

Cikeda jin dadi Subay'a tace

Amin Amin Hajiyata.

Itama Hajiyar taji dadi Don tanason yadda Subay'a ke yi mata.

Dama nace idan kin samu dama zuwa anjima ko zaki shigo akwai muhimmin abu da Zamu
tattauna.

Dan zaro ido Subay'a tayi tace

Ba dai wani abunne ya faru ba ko hajiya?

Murmushi hajiya tayi don haka sauran ma sukai

Babu komai, kawai dai bazan iya jira bane har Zuwa Sunday.

To shikenan Bari yanxu zanzo.

Tana kashe wayar ta Mike da kayanta tayiwa colleagues dinta sallama Don suma shirin
tafiya suke , seda ta shiga mota sannna ta nemi number Junaid ita Baki daya ta
manta warning din da yayi mata akan se ta zartar da abu kafin ta sanar mishi.
Lokacin Sulaim da Junaid sun manta sun fita saboda dadewar da sukai da komawa gida,
yana parlonshi Yana reviewing questions da aka mishi sending a matsayinshi na exam
officer call din Subay'a ya shigo, agogon dake kafe a jikin bangon ya kalla karfe
shida har ta gota, picking call din yayi

Dear ka koma gida?

Na koma tun 3pm.

Dama zanje gidan Hajiya ne

Murmushi ya danyi don yasan kiran kenan dole wani gurin Zata biya,

Allah ya kiyaye!

Bai jira amsarta ba ya kashe wayar tare da mikewa Don shirin sallar maghrib.
Jallabiya yasa blue black sannan ya dauki farar hula ya saka ya aje wayoyinshi ya
fito, Yana Zuwa parlourn Sulaim na fitowa daga dakinta, da dukkan alamu aiki take a
kitchen, Tana ganinsa ta tsaya tace

Yaya massallaci?

Kanshi ya gyada mata yace

Eh! Ko zamu tafi tare kiyi acan?

Dan dariya tayi tare da rufe fuskarta tace

Ni?

Shima dariyar yayi Cikeda jin dadi yace

Inasu Muhammad kirasu muje tare.
Komawa daki tayi ta fito dasu dama sunyi Alwala tace

Allah ya kiyaye.

Har ya kai kofa ya juyo yaga tana tsaye inda ya barta tana ta murmushi har
wushiryar ta siririya ta bayyana, shima murmushin yayi mata tareda saka hannun shi
ya mata alaman Taxo, babu musu ta isa inda yake tsaye tareda barin space kuma har
lokancin murmushin take,

Addu'ar me zanyi miki idan nayi sallah.

Dan rolling idonta tayi tace

Naci exams.

Se ya bata fuska yace

Shikenan? Ni kuma fa

Cikin rashin fahimtar inda zancenshi ya dosa tace

Bansan me kake so ba ai.

Kanshi ya gyada yace

Shikenan

Daga haka ya fice abinshi, dariya tayi ta sauke ajiyar zuciya ta nufi kitchen bayan
ta cire Hijabin jikinta dama ba sallah zatayi ba , hakan yasa ta shiga suka karasa
girkin itada su Atika dukda yawancin girkin su keyi ita supervising kawai takeyi se
murmushi wanda yaki daukewa Daga fuskarta har Atika Tace

Saurayinki kike tunawa ne haka?

Hararar ta Sulaim tayi ta cigaba da aikinta seda suka gama sannan ta koma daki ta
janyo wayarta da books dinta se kawai taga message din Ja'afar

_If at all I can turn the clock, I'll never have done what I did, I'm very sorry
Susu for that day. Allah shi ne shaida ta I never intended to harm you..... Please
sweetm I'm sorry and I love you! Another chance dear_


Iska me zafi ta furzar, tareda kife wayar tayi shiru Tana tunani yadda zatayi, to
ya zatayi da Ja'afar hakura zatayi? Ko kuma me? Gashi yadda words din suka fita are
so sincere Amma Kwana biyunnan ita kanta hankalinta ya kwanta amma matsawar Ja'afar
ya dawo yanzun zai sake dagula mata lissafi. Se taji inama Za'a canza mata Ja'afar
da Junaid, Junaid to her yanada komai da take burin samu inama inama.... Kawai se
ta kwanta saman tiles din Tana ta juye juye abinta ta rasa yadda zata hada abin.

Yau kam Khulthum ba takai dare Ba, karfe hudu ta isa gida, Tana shiga ta samu se
Mama kawai sauran duka basu nan. Seda ta gaida ta kafin ta shige daki tayi wanka ta
shirya cikin wata atamfa tazo ta zauna kan daddumar data shimfida. Kallon Mama tayi
tace

Mama jarabawa zamu Fara ranar litinin me Zuwa.

With lot of concern Mama tace
Allah ubangiji ya bada sa'a, yasa a dace

Amin Mama, Amira sun tafi makaranta ne?

Eh yanzu nasan suna hanya.

Kanta ta gyada ta Fara revising books dinta, Kwana biu cikin kudi take jin kanta
don Huzaifa Yana sakar mata kudi daidai yadda ya dace ga Yusuf da ta hadu dashi
yau, Architect ne a wani construction company gashi yana taking private contract
wannan yasa yake da kudi shi ne abinda ya fada mata. Kallon Mama tayi tace

Anyi abinci ne?

Kai Mama ta girgixa tace

A'a yace Se ya dawo zai bada kudin cefane.

Allah ya kaimu

Ta fada Tana cigaba da karatunta. Tafi awa tana karatu sannan su A'isha suka dawo,
Amira da kananan suka gaisheta, Ta kalli Amira tace

Duba cikin jakar da na fita da ita ki kawo min purse dita.

Tashi tayi ta dakko ta kawo mata,

Amir!

Meye ke kuma zaki ishi mutane?

Harara ta maka masa tace

Siyo mana macaroni uku da nama da kayan miya.

Ta fada Tana mika masa 1500.

Kowa Seda ya kalleta Cikeda mamaki itama kuma tasan haka zata faru amma tasan
hakanne kadai zaisa abinda take shirin aikatawa. Mama kam farin ciki sosae ta dinga
sawa Khulthum albarka, Aisha ana kawowa ta Fara aikin girki yaran se murna suke yau
zasu ci nama wanda aka dade ba a hadu ba. Ana Idar da sallar maghrib Amir ya shigo

Khulthum tashi kije Ashir yana nemanki fa.

Tsaki tayi ta Mike don Tana son bin komai a sannu don Kada ta kwafsa. Bata wani
canja kaya ba kamar yadda take duk lokacinda Yazo ta nufi waje, yana tsaye gefen
Lifan dinshi wanda a yanzu take ganin shida gurgu basuda maraba. Ko gaisuwa bai
samu ba ta tsaya tana jiran taji abinda zai fara fada, shima kallonta yake yana
mamakin Khulthum wai wannan Khulthum dinsa ce yarinyar nan Itace idanunta suka bude
har haka lallai yarinyar nan shi mamaki take bashi, Ashe mamaki yana gaba

Idan Bakada abin fada zan koma ciki.

Ta fada Tana nufar zaurensu, seda ta shige ciki sannan Amir ya fito ya tarar da
Ashir wanda mamaki yake neman kasheshi a tsaye yace

Har kun gama?

Kanshi ya girgixa yace
Kayi min magana da Mama Dan Allah

Lapiya dai?

Kayi mata magana

Haka kawai yace dashi, haka ya wuce ciki ya tarar mama na tsaye kan Khulthum tana
tambayarta dalilin da yasa ta dawo

......dama kwana biyu Naga take takenki baki daya tunda kika shiga makaranta
halayenki ya canza kin koma wata iri........

Mama wai Ashir yana son magana dake .

Wani harara ta dallawa Khulthum sannan tace

Amira dakko min mayafi na.

Ana miko mata ta nufi gurin shi Khulthum tamkar zatayi bindiga a ranta tace

Lallai Ashir kana ganin wannan ce hanyar bullewa kada ka damu Dani kake magana.

Mama gefe guda ta zauna cikin mutunci da mutunta juna suka gaisa itada Ashir, nan
ya fara fadin

Mama kiyi hakuri kila kina wani abun na katse miki aikinki

Babu komai dannan, inajinka

Dama akan Khulthum ne Mama, Dan Allah Inaso ki tambayeta ko akwai abinda nayi mata
kwatakwata Kwana biu nan taki dadi kuma ni naga Tunda manya sun shigo ya kamata na
sanar dake halinda ake ciki.

Se yayi shiru, itakuma tayi zugum seda ta tabbatar yakai aya tace

Da farko zan baka hakuri, yaran yanzu ka haifesu baka haifi halunsu ba, Inshaaa
Allah zan zauna naji matsalarta idan yaso se asan abinyi. Kadai yi hakuri.

Babu komai Mama kada dai kiyi fushi.

Dan murmushi tayi amma Lokaci guda ya dauke saboda jiyo takun Khulthum da tayi,
kamar Aljannah saboda yadda tayi dolling fuskarta, Tana cikin wani royal blue paper
lace da farin mayafi iya kafada tayi kyau har ta gaji abinta.

Ke gidan ubanwa zakije?

Mama ta tambaya a fusace, Nikam ina tunanin Wannan ne Karo na farko da Mama ta Fara
fito na fito itada Khulthum, shima Ashir kallonta yake Baki daya idanunsa sun Kada
sunyi jawur dayake ya haska gurin da wayarshi kirar Tecno hakan ya haska gurin Kake
ganin komai daidai. Harara ta watsa mishi idanunta Cikeda tsana Tace

Mama bako Nayi fa

Ubanki Keda bakon kinji ubanki nace Marar mutunci yarinyar nan.

Baki ta turo tareda bubbuga kafarta a kasa, sannan ta ficewarta Mama na kwalla mata
kira amma ko Waiwaye!

Turkashi!
Seda Subay'a tayi sallar isha'i sannan ta nufo gida dama kiran Ba wani abu bane wai
kawai son ganinsu take. Seda taci abinci cikin yan uwanta kafin ta tuko motar ta
hankalinta a kwance don tasan babu Abinda Junaid zaiyi mata Tunda da tace zataje
bai musa ba. Tana parking a gefen motarshi ta nufo cikin gidan kafadarta rataye da
jaka, se jakar system dinta a hannunta, Tana yin sallama taji Sulaim ta amsa mata
karo na farko taji jin muryar Junaid ya fadar mata gaba, sosae gabanta ya tsananta
bugawa tamkar wadda tayi bugun marathon haka taji, se kawai ta tsaya a gurin,
Sulaim din na Sanye da wani shiny silk material dark purple da pattern na light
purple a jiki, dinkin simple gown se mini veil da tayi rolling dashi dan Bata taba
zama babu mayafi jikinta saboda wannan tarbiyyar mummy ce hade da Mami, ta rigada
ta san akwai aure tsakaninta da Junaid so bata taba zama babu lullubi jikinta
that's the rule. Tana dining tana jera plates da spoons yadda kasan Itace matar
gidan, shikuma me gayya me aiki yana zaune kan carpet da books din Khulthum din
Yana sake highlighting mata abubuwan da suka shige mata duhu, Sede Tunda ta tashi
gaba daya yaji ya daina fahimtar Abinda yake karantawa, sukam su Ahmad suna ta wasa
abinsu suna jin muryar Mamansu sukai kanta. Shigowa tayi idanunta sun canza kala
baki daya taji Anya ba akwai Abinda yake Zaune ba a muhallinsa ba? Anya ba akwai
Abinda yayi breaking along the line ba amma ta rasa Meye, taga kwata kwata Junaid
baya damuwa da alamuranta kamar da, ko bata nan bai taba damuwa sannan Hana fitar
da yake duka ya barta tana tambaya zaice Allah ya kiyaye to abin ya fara damunta,
ta Fara zargin kanta da yin sake data bar Sulaim zama mata a gida.


The game is about to start..... Kowa Yana rike da hurdle let's see wanda zai cimma
burinsa.


[7/17, 5:39 PM] Asma'u Madugu: *MACE A YAU*
15

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad

Mama kasa fadin komai tayi ga matsanancin bacin rai da yake taso mata, Tamkar an
dasa Mama haka ta tsaya ta kasa gaba Kuma ita Bata koma ciki ba, gashi Baki daya
kunyar Ashir dinma takeji, mikewa yayi ba tareda ya sake furta komai ba ya wuce
abinshi, to me zaice? Duk yadda yayi tunanin saiyawar khulthum ashe tunaninsa ya
wuce hakan. Yana fitowa ya same ta tsaye gefen Yusuf se murmushi take tamkar
bakinta zai yage, shima hakan ce gareshi Yusuf din, Bai Kara kallon inda suke ba
dan surely zuciyarshi zata iya fashewa.

Kice dazun da muka hadu banga komai ba kenan?

Yusuf ya fada Yana sake Kare mata kallo, murmushi tayi tace

A hakan?

Ta fada tana masa wink, dan dariya yayi yace

Kice kada nayi underestimating dinki?

Bata kuma fadar komai ba hakan yasa ya canza topic da fadin

So kina ganin ban takura miki ba idan na turo iyayena, saboda gaskiya ni da gaske
nake Kuma aure nake son yi I'm not getting any younger kullum girma Kara kamamu
yake.

Gabanta taji ya Fadi,wani irin aure daga zuwanshi, gaskiya itadai she's not ready
bata gama fahimtar halayenshi ba kawai se a fara zancen aure ita duk ba wannan ba
bata shirya aure ba a wannan lokacin, Bata gama kashe kurar Ashir ba ita Bata San
abinda zata tarar a gida ba don tasan dole Mama ranta zai baci.

Kinyi shiru ko Baki shirya ba?

Ya fada yana assessing fuskarta , Dan murmushi ta Kuma saki tace

Haba dai, kasan first semester nake level one so bazai yiwu ace daga fara karatu se
aure ba, if you can be a little more patient na shiga level two Ina ganin Babu
matsala.

Shima murmushi yayi bayan ya gama saurarnta se yace

Abinda Kika fada is in place, sede Ina ganin aure baya hana karatu kowanne Yana da
matsayinshi what matters Shi ne Zan barki ki karasa idan munyi aure.

Wata dariya ta saki, a ranta tace

Lallai Kai har kana tunanin zaka barni ko aa ai ni ba irin wannan matan bace

Amma a fili se tace

A'a bana jinka zaka barni nayi Amma sede hakan Shi ne burina Dana iyayena.

Ganin ta dage yasa yace ya amince amma bawai yakai zuciya ba don ya fahimci auren
ne baya gabanta Baki daya Kuma idanunta a bude suke. Sun Dan Kara taba Hira ya ciro
katuwar ppaer bag daga back seat dinsa ya Mika mata, se farar leda, karba tayi ta
mishi godiya daga haka ta mishi sallama se gida. Ko dar bataji ba don tasan Babu
abinda zaayi mata.
A nutse ta shiga cikin gidan Mama na zaune Kan sallaya ta idar da sallar ishai
baki daya abin duniya ya iaheta ta rasa yadda zatayi. Kada khulthum ta watsa musu
kasa fa a ido? Saboda taga take takenta abinda take niyyar yi kenan. Tana shigowa
daki ta nufa tana jin Mama Tana kiranta bata amsa se cewa tayi

Mama kada ki damu indai maganar Ashir ce kada ki saka baki.

Ni kaina nayi tunanin Mama zatace wani abu amma se cewa tayi

Khulthum idan zaka rabu da mutum ba ta haka ake ba, a hankali ake bin komai.

Aisha ce tace

Mama haka kawai Zaki fada? Mama bakwa kyautawa abinda kuke, Ashir Bai canci haka ba
wallahi.

Khulthum dake daki ta leko tace

To uwata munafuka ke idan kina sonshi kije Zaki zauna kina gutsiri tsoma.

Aisha batace Mata komai ba ta mike don harhada kwanukan da akai amfani dashi. Mama
shiru tayi Don tasan tabbas abinda Aisha ta fada gaskiya ne, is not in place bai
dace ta fada haka ba Amma Babu yadda zatayi sede idon kawai.

***
Agogon dake daure kan tsintsiyar hannunshi ta Rolex ya kai duba, Tara na dare ta
gota gashi goma daidai ya kamata ya tafi gurin da ya kamata Amma Babu yadda zaiyi
wane Shi Gwoggo nasan ganinshi yaki zuwa, hakanan ya ja motar ya nufi asalin
gidansu dake cikin unguwar kuntau a Kano. Makeken gida ne na alfarma tun daga gate
din zai tabbatar maka da kudi ya zaunawa masu gidan. Bude mishi gate akayi ya shiga
ciki yayi parking sannan ya fito Yana amsa gaisuwar masu gadin gidan. Tamkar rana
haka yake saboda yadda ko Ina yake a haskake, parlon ya nufa tana zauna kan kujera
gabanta an aje mata mug cikeda tea Akan saucer, matar ta manyanta sosae sede yadda
take cikin Jin dadi bazai nuna manyanta tata ba. Gefenta daga kasa ya zauna cikeda
girmamawa yace

Gwoggo barka da dare

Seda ta gama kallonshi a tsanake ta kurba tea din sannan tace

Barka ka dai Musbahu.

Kanshi ya sunkuyar gabanshi Yana faduwa don baisan abinda yasa take nemanashi ba,
itama ta Lura da hakan shiyasa tace

Dama na kiraka naji yadda muka tsaya Akan zancen auren ka, Musbahu wannan karo na
nawa ne Ina yi maka magana?

Kanshi a kasa dama jikanshi ya bashi maganar kenan hakan yasa yayi shiru seda tace

Bakaji tambayar tawa ba ko?

Girgiza kanshi yayi yace

Bazan iya irgawa ba.

Good

Ta fada kafin ta sake kurbar tea tace

Mata nawa na kawo maka ka nuna min you're not interested in them, daga kace wannan
se kace wancan don haka kayi marking date din yau a matsayin Rana ta karshe da zan
Kara daga maka kafa, watanni biyar kawai na baka ka kawo min Mata Shima don na
fitarda hakkin ka ne Amma banda haka wallahi da da kaina Zan baka mace.

Kanshi a kasa har lokancin a ranshi Yana fadin to ai akwai Lokaci kenan, shifa
bawai aure ne bayaso ba kawai dai bai taba ganin akwai abin burgewa a jikin 'ya
mace ba balle har yayi Sha'awar su shi a iya rayuwarsu zai iya counting matan da
yayiwa magana dasu a girman shi yanzun hakan zai iya kirga matan da yayi mu'amula
dasu shima don dole ne don ita kanta Gwoggo Tasha sawa ayi mishi addu'a don
tunaninta ko aljana ce ta aureshi amma shiru babu sauyi.

Inshaaa Allah Gwoggo kafin lokacin zan kawo miki.

Kanta ta gyada tace

Zaka iya tafiya.

Take ya Mike kuwa yayi mata sallama don Dama a takure yake sosae, shikam haka ya
tashi cikin tsananin tsoron mahaifiyarshi kuma har yanzun daya girma Bata canza
zani ba saboda baya mantawa kafin rasuwar mahaifinshi yana yawan mata fada akan ta
daina irin takura mishi.
Musbahu yana fitowa ya sauke nannauyan ajiyar zuciya tareda sake kallon agogon
hannunsa, it's almost time hakan yasa ya figi motar ya fice baki daya daga harabar
gidan, a motar ya Kira babban amininshi na hannun dama Kabir Seda suka gaisa sannan
ya sanar mishi yadda sukai da Gwoggo,

Ina ganin ya kamata kayi hakuri kawai kayi aure Tunda Naga Gwoggo da full force
Taxo

Kabir ya fada, sake dafe steering yayi yace

I thought of that nima, amma ta yaya zan fara neman mace idan naje ya zanyi?

Dariya sosae kabir yayi har ya kusa batawa Musbahu rai, sannan yace

We'll talk about it later, kadai kayi amfani da damar ka ta Daren yau.

Dariya sukai sannan sukai sallama.


***

Cikin tsantsan Subay'a ta karaso parlon yaran sun rike both hands dinta, Tunda ta
shigo idanunta Ke kan Sulaim wadda ta cigaba da Abinda take tamkar bata ga shigowar
Subayan ba, gefen Junaid ta zauna tareda fadin

Papa na dawo.

Ta fada Tana shafa Fuskarshi, Allah ya taimaka shugabar kishin duk duniya wato
Sulaim bata lura ba Don hankalinta yayi nisa kan shirya dining Sede itama a ranta
taji babu dadi tana ganin kamar Subay'a din wata barrier ce tsakaninta da Junaid.
Shikam Junaid hannunta ya rike tareda nuna mata su Ahmad yace

Barka da dawowa.

Se ya Mike ya nufi dining din, yana zama Subay'a ta taso ta zauna gefenshi tareda
janyo plate ta Fara serving dinsa, Sulaim na ganin haka ta zuba nata ta bar gurin
Zuwa dakinta, saboda gani tayi Subay'a ta Fara bashi abincin cikin baki tasan
matsawar ta zauna a gurin zuciyarta fashewa zatayi, da taje dakinma saka abincin
tayi a gaba tana ta kallo Baki daya farin cikin da take ciki ta nemeshi ta rasa, a
hankali ta aje spoon din hannunta ta daidaita zamanta don tuhumar kanta dalilin da
yasa take haka, in the first place

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login