Showing 120001 words to 121650 words out of 121650 words
tayi seda ya shiga kafin ta rike
marfin motar tana kallonshi kamar yadda yake kallonta yace
"Ki fita da wuri ki dawo da wuri bansan na dawo bakya gida "
Salute tayi mishi tace
"Angama Yallabai"
Murmushi yayi sannan yaja hancinta suka saki dariya gaba daya Cikeda farin ciki da
nishadi, rufe motar tayi ta daga mishi hannu sannan ta wuce cikin gida Bayan ta ga
ficewarsu Daga gate din. Tana shiga ta tarar komai an gyara hakan yasa ta wuce
dakinta ta shirya cikin milk din Voile lace da red flowers tayi kyau sannan ta
harhada abinda take bukata ta fito Tana jin sanyi cikin zuciyarta, gaba daya
rayuwar tayi mata rangwami Allah Yana sonta da ya hukuntata kuma ya maida ta akan
hanya, gashi ta fahimci kudi ba komai bane farin ciki da kwanciyar hankali shi ne
jigon rayuwa wanda yanzun haka ta samu batada matsala da kowa don a yanzun
renovating gidansu Mama take wanda Musbahu ya bata kudin duk wanann rowar ta daina
Don ta rigada ta samu kawa ya rabeta se ya jiku.
Tana fitowa driver dake kaita Duk inda zataje ya taso dama tuni ta sanar dashi inda
zataje, aikuwa bai sauke ta ko ina ba se gidan Aminiyarta Sulaimi, Sulaim ta
kammalla dukkan abinda zatayi na tarbar su tana kwance kan carpet se Su'ad da ta
Fara wayo tana gefenta tana mata wasa yarinyar kamar an ciro fuskar Jabir an saka
mata saboda yadda take masifar Kama dashi. Sallamar Khulthum yasa Sulaim tashi ta
zauna fuskarta dauke da murmushi, shigowa Khulthum tayi ta zauna suka gaisa tana
rikeda Su'ad
"Allah sarki Sulaim wayo Su'ad take karawa kullum"
Murmushi Sulaim tayi tace
"Gata nan kam, Matar nan kin ganki kuwa Musbahu ya dage fa"
Dariya sosae Khulthum tayi suka Fara hira yawancin Khulthum ce ma me maganar Tana
Kara bata labarin yadda komai ya koma normal tsakaninsu a lokacin ma ciki gareta na
watanni biyu, Sulaim murna tayi sosae a haka su Aimana suka karaso kafin wani
Lokacin tuni hira ta barke ta Yaushe gamo.
Karfe hudu na yamma Jabir yayi parking kofar gidan su Junaid, dake yawanci nan yake
wuni idan bashida aiki hakan na kara kwantar mishi da hankali, Tundaga kofar parlon
yaga takalma yasan tayi Baki amma haka ya shigo da sallama bakinshi lokacin Su'ad
na hannun Aimana tana canja mata diaper da kaya, Sulaim na gefenta tana waya da
Junaid wanda ya tafi Kwara attending wani conference. Sulaim ce ta Fara amsawa
sannan Aimana dake Khairi da Khulthum sun fita wani guri zasu karbo sako, zama yayi
kujerar dake gefen Sulaim tana facing Aimana, seda suka gaisa da Sulaim kafin
Aimana ta gaisheshi haka kurum ya kura mata idanu ba tareda ya amsa gaisuwar ba har
Seda Sulaim ta buga handle din kujerar sannan ya ja numfashi tareda dauke kanshi ba
tareda ya amsa ba, itama mikewa tayi ta nufi bedroom din Sulaim hannunta rikeda
Su'ad ga idanun Jabir da sukai mata rakiya har ta kule cikin corridor din, zamanshi
ya gyara tareda kallon bangaren Sulaim ashe kallonshi take hakan yasa ya saki
dariya tareda daga hannun, itama dariyar tayi tace
"Zaka shiga ne? "
Murmushi kawai yayi yace
"Zan samu abinci? "
Kanta ta gyada Bata Kara cewa komai ba ta hada mishi a dining sannan ta dawo
parlour tana lissafi cikin ranta, yana gamawa ya kalli corridor da Aimana tabi
sannan ya dubi Sulaim wadda ta tsareshi da idanunta masu kaifi
"Yaushe kika zama yar sa ido ne wai? "
Kanta ta girgixa tace
"Ni na isa baka dauki Su'ad ba"
Tsaki yayi don yasan Jan magana take ya fice baice mata komai ba. Wasawasa se
karamar magana ta zama babba tun Jabir Yana dauke idanu amma picture Aimana da akai
storing a kanshi ya kasa barin kanshi hakan yasa ranar wata Thursday da daddare
kamar yadda ya saba ya shiryo ya taho gidan. Suna parlor suna kallo yayi sallama
inda Ahmad ya taroshi suka shigo ciki, Seda suka gaisa kafin suka ci abinci sannan
Sulaim ta kwashi yaran suka tafi Dakinsu don tayasu homework anan ta bar Su'ad
hannun Junaid suna hira shida Jabir. Har ta gama yaran suka kwanta ta dawo ta tarar
Jabir bai tafi ba, gefen Junaid ta zauna tareda daura kanta a kafadarshi ta kalli
Junaid tace
"Bacci nake ji fa! "
Ya gane me take nufi hakan yasa ya saki dariya tareda kallon Jabir yace
"Gwauro Zamu rufe kofa dare yayi"
Fuskarshi ya yamutsa yace
"Ni Abu ne ya kawoni kuma specifically gurinki Ammin Su'ad"
Kanta ta dago tace
"Ni kuma?"
Kanshi ya gyada tareda gyara zama yana shafa kanshi yace
"Wannan friend din taki, kina ganin zan iya aurenta? "
Gaba daya mamaki ya daskarar dasu don babu Wanda yayi tunanin Jabir Zai nemi aure a
Kwana kusa Amma se gashi ya basu mamaki, sun kansu basu sha wahala ba Aimana ta
amince a hankali abubuwa suna tafiya har iyaye suka shiga cikin abin suna shiga
level 4 akai Auren se ya rage Khairi ce kawai batai aure ba itama kuma wanda zai
aureta dan jaligon ne yana jira ta kammalla sannan ayi abin.
A hankali kwanaki suka shude kowacce dakika na zama Mintina haka mintina na zama
awanni har cikin Khulthum ya tsufa Gwoggo ta takura dole Musbahu ya maida ita can
shima kuma ya tare acan din, ko sati bata rufa ba ta haihu danta namiji me kama da
Musbahu, ranar suna aka Sakawa yaron Muhammad anyi shagali Irin na gasken gaske
kuwa, Tana arbain ta wuce gidansu inda suka samu afuwar rayuwa suka zama tamkar
basu ba yadda haihuwa tayi rana ba Daga Khulthum ba, ba Daga A'isha ba haka Amir
kowanne na iya bakin kokarinshi. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Musbahu ya
nema mata admission a wata university dake Michigan State inda take Law din Don ya
wanke kanshi ya kafata ta kamu kafu sosae.
Bangaren uwar dakin su walida Hajiya Subay'a kam ta yadda ubanta shi ne Alhaji don
seda taji tamkar ta bar gidan ya muzgunawa rayuwarta yasa ta bar aikin bank din da
take ya hanata fita ko ina Tana gida kullum tsamannin ganin anzo bikonta take amma
shiru gashi hajiyar ma bawani dadi takeji Daga gurin ta ba haka yan uwan, Seda tayi
shekara daya cif a gida ta gane batada wayo, ta gane Junaid shi ne rufin asirin ta
sannan ya maida aurensu inda ta zage damtse sosae ta zage ta shiga taitayinta
yaranta duka suka dawo gurinta. Watanta biyar da dawowa ta samu ciki lokacin ita
kuma Sulaim ta yaye Su'ad yarinyar ta girma sosae tana yawonta amma ciki shiru babu
labari tun abin bai dameta ba har ya fara damunta amma bata taba nunawa ba haka
Subay'a ta haihu Sede babyn kwananshi biyu ya rasu, a wannan haihuwar anan Hulda ta
Fara hada Subay'a da Sulaim kullum se taje gidan an gyara gidan ta wuce school ana
gama lectures ta dawo se dare ta koma gidanta haka har akai Kwana bakwai sannan ta
daina Zuwa. Bayan sati biyu Subay'a ta Fara fita tazo tayiwa Sulaim godiya shikenan
zaman lafiya ya kara wanxuwa cikin rayuwarsu har Su'ad na Zuwa tayi weekend abinta.
Five Years Leap
A wannan lokacin tuni su Sulaim sun Gama Law har Law school inda a shekarar da suka
shiga suka kammala anan ta zama cikakiyyar Barrister, buri ya cika se lokacin
hankalinta ya dawo jikinta ta dawo gida ta gina sabuwar rayuwa itada mijinta da
yarta Su'ad wadda a lokacin Aimana ta Haifa Namiji me sunan Baba ana kiranshi Abid,
itama Subay'a ta kara haifar namiji Mahmud.
Tun Sulaim na damuwa akan ciki har ta hakura saboda yadda Junaid dasu Mami ke
Kwantar mata da hankali akan ai Mummynta ma Seda tayi shekara bakwai da aure kafin
ta haihu hakan yasa ta hakura bawai Dan bata son haihuwar ba sedan kwantarwa
mijinta hankali.
Ranar ta kasance Monday Tun sassafe ta tashi ta shirya breakfast Don a ranar Haulat
matar Ja'afar zata koma kaduna tazo tayi Kwana biu kuma da sassafe zata tafi ga
Junaid zaije office haka Su'ad dake primary one zataje school. Seda ta kammalla
komai sannan ta nufi dakin Junaid tabar Su'ad Haulat zata shirya mata ita, wanda
dawawarshi kenan daga massalacin asuba inda ya biya gidan Subay'a sannan ya dawo.
Zama tayi gefenshi tareda fadin
"Heartthrob Ina Kwana? "
Kanta ya shafa yace
"Lafiya lau Dove dita, how was your night baby "
Murmushi tayi tace
"It was...... "
Ta fada kusada kunnenshi, mikewa tayi ganin yana son rama cizon da tayi mishi a
kunne ta fada toilet ya biyota suka kammalla wanka anata watsin ruwa sannan ta fito
mishi da kayan da zaisa Itama ta shirya cikin plain material baki me kyau dinkin
Bubu style yayi mata cif sakamaakon cikowar da jikinta yayi, turare ya dauka nashi
na kullum fierce cologne by Abercrombie and Fitch, hancinta tayi saurin toshewa jin
yadda zuciyarta ta tashi lokaci daya ga hautsinawar da cikinta yayi, kafin tayi
yunkurin wani abu se amai hakan yasa ya nufo ta da sauri amma yana karasowa ta Kara
rikicewa ta dinga amai wanda ya tayar mishi da hankali, kafin wani Lokaci ko
tsayuwa kirki bata iyawa dole ya kira Jabir akan ya hada yaran duka ya kaisu school
akan zaikai ta Asibiti. Kafin suje wani Asibiti dake kusa dasu private akan gwarzo
road har zazzabi ya rufeta tana ta surutai, Junaid iya rikicewa kam yayi a haka
suka isa aka Fara bata taemakon gaggawa har bacci ya dauke ta sannnan aka tura
jininta screening, result din na fitowa ya nuna tana dauke da ciki, murna
understatement ce, farin ciki kamar zasu hadiye junansu, kafin wani Lokaci Mami ta
iso inda ta tarar Aimana da Subay'a suna gurinta ana ta Faman pampering dinta.
Da daddare Junaid ya shigo lokacin ita daya ce tana Zaune Akan carpet ta Idar da
sallah saboda jikin nata yayi sauki sosae Alhamdulillah, gefenta ya zauna tareda
janyo wani farin flask wanda ya shigo dashi, yana budewa yawunta ya tsinke dama
zaman da tayi so take ta Kira Mami taji abincin ba a kawo ba, plate ya janyo ya
fara xuba mata pepper chicken wanda akai garnishing da Irish potatoes, sosae ta
nutsu taci dukda akwai yaji amma ko a jikinta haka ta gama ci ta goge bakinta da
hannunta Tasha zobo sannan ta kwantar da kanta kan kafadarshi, a hankali yasa
hannunshi Yana shafa fuskarta yace
"Precious babynmu na hanya, I can't wait to hold the baby in my arms"
Murmushi tayi tareda sake shigewa jikinshi tace
"Thank you for the love, thank you for everything and thank you for the baby
and..... "
Bai bata damar karasa maganar ba ya shiga bata wani sassanyan kiss me tsayawa a
zuciya wanda yasa suka manta cewar a asibiti suke!!!
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!
Shatuuu ♥️