Showing 78001 words to 81000 words out of 121650 words

Chapter 27 - MACE A YAU by Shatuuu

Shatuuu   

12 May 2026

135

is he truly dead? How is he? Tell me he's waiting for me inside.

Gaba daya gurin yayi tsit ana jiran amsar bakinshi.

Your husband is OK, yana jiranki kije gareshi.

Babu jira ta kutsa ciki lokacin nurses biyu na kanshi, daya yana sa mishi blood
daya kuma yana daidai ta dakin. Baki daya tsayawa sukai suna kallonta babu Wanda
yayi mata magana har ta dira gwiwarta a kasa ta ruko hannunshi hakan yasa ya saki
karamar kara, da sauri ta sake shi hawaye na bin idanunta, ta kalli Fuskarshi babu
ciwo a jikinta amma tana iya hango jini Yana fitowa daga kunnenshi da hancinshi.
Kifar da kanta tayi tana wani Irin kuka me zafi wadda yake Marar dadi ga kunnuwan
me saurare.

A station na nurses doctor ya zauna shi da Baba don yi mishi bayanin halin da
Junaid din yake ciki.

Sir! Bayan accident din da yayi bamu samu ganin karaya ko daya ba sede ya bugu
wanda ya taba kanshi shi ne muke kira "Head injury" shima mild ne saboda gashi yana
bleeding ba ta ciki yake ba. Se dislocation a hannunsa da karan hancinsa. To
matsalar he's unconscious amma Inshaaa Allah Zamu ga Duk yadda zamui da izinin
Allah ya dawo hayyacinsa.

Kai Baba ya gyada yace

Nagode kwarai, Allah ya Baku saa.

Daga haka suka tattauna da nurses din akan bills da zai yi depositing a account
office dinsu. Daga haka ya wuce dakin da Junaid lokacin kowa ya shiga ya ganshi
kuma koke koken ya ragu sosae don hatta Sulaim tayi shiru sede bata magana haka
Mami wadda ta kasa daina blaming kanta as cause of everything. Tunda Ridwan yace
Accident yayi Bayan ya shigo Kano dayake shi ne last call dinshi yasa bayan abin ya
faru shi aka Fara kira shi kuma ya kira Baba Wanda bai iso gida ba Yana hanyarshi
ta dawowa daga Abuja. Yadda ya shigo gidan hankali a tashe yasa Mami tayi tunanin
mutuwa Junaid din yayi!!!

Basufi awa a gurin ba Imratu da Jabir Harda Jawad suka iso hankalinsu a matukar
tashe Amma ganin yana raye yasa suka nutsu aka Fara jajantawa. Kafin isha'i labarin
accident din ya kai Birnin kudu, Jega, Kebbi da Birnin Kebbi se kira suke a waya
don jin jikin na Junaid amma magana daya ce he's still unconscious.

Karfe goma Baba ya tattara Mami, Ahmad, Muhammad, Imratu, Jawad da Sulaim don su
tafi, aka bar Ja'afar da Jabir a gurin shi, Sulaim kuka akan ita bazata tafi ba a
gurinshi zata Kwana, seda lallashi kafin ta yadda ta bisu shima ta dinga kuka
tamkar ranta zai fita saboda gani take idan bata kusa dashi mutuwa zaiyi.

A gidan Junaid driver din Baba ya ajesu Sulaim, Baba yana tayiwa Imratu kashedin ta
kula da Sulaim, su kuma suka wuce zuwa hotel don su Kwana. Daren ranar ba sai na
fada ba babu Wanda yayi baccin arziki Balle Sulaim me gayya me aiki!

Washegari tun da sassafe ta shirya amma Baba da yazo yace mata ai basu Bari aje
gurin patient se karfe uku na yamma.... Hey pipu tamkar sokuwa haka ta dinga kuka
tamkar don shi Allah ya halicce ta, babu Wanda ya lalashe ta don bazatayi shiru ba,
Baki daya tausayi Take bawa Baba, ji yake idan yana da halin tashin Junaid da se ya
tashe shi kodan Sulaim kodan hankalinta ya kwanta amma bashida wannan halin.

Wajen karfe biyu Mami ta karaso ita dasu Mama Sauda, Umma Fatima, Neneh ta birnin
kudu da Hajiya ta Jega, suka saka Sulaim a gaba Sunata mata nasiha amma ina a ranta
fada take bazaku gane ba, dukkanku da aurenku, iyayenku na da rai Nikam banida kowa
ban kama komi ba. Haka suka dunguma Zuwa Dala sede Alhamdulillah yau ya fara
responding ba dai kamar jiya ba. Hakan ya kwantar musu da hankali suka kara samun
hope.

Da daddare Bayan Mami sun kwanta itada Baba ta matso jikinshi ta daura hannunta a
Fuskarshi tace

General!

Dagowa yayi yace

Nafisatou!

Haka yake fada idan soyayyar ta motsa.

Nasan ban kyauta ba Abinda nayiwa Junaid amma Allah ya sani inada dalili na....

Hannunta ya riqo gam yace

I know and I understand you Shiyasa kikaga ban saka baki ba kwata kwata nasan duk
Abinda kikayi kina da dalili. Rest well please.

Hawayenta ta goge tace

Inada abu daya da zan rokeka kuma Dan Allah gobe juma'a ka daura auren Sulaim da
Junaid!

Da sauri ya kalleta yace

No! Nafisatou mu Bari ya tashi tukunna.
Kanta ta girgixa Tana kuka a hankali tace

Dan Allah Baba just do this for me please !

Ta fada hawaye na Kara wanke mata fuska, hannunta ya Kama yace

Is ok gobe kike so right?

Kanta ta gyada yace

Inshaaa Allah .

Daga haka ya sauka a gadon ya dauki wayarshi ya koma can gefe yana waya, ya jima
yanayi ba da mutum daya ba sannan ya dawo ya kwanta.


[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤:
Shatuuu ♥️ *MACE A YAU*
39

✍️Shatuuu ♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad


Ranar ta kasance juma'a, jumaatu babbar rana, Tunda Junaid ya fara rashin lapiya
wannan shi ne Karo na farko da Sulaim ta samu tayi bacci shima bawai niyya tayi ba
a'a taci bashi da yawa dole ta biya, hakan yasa bayan ta Idar da sallar Asuba tana
zaune kan praying mat wadda tun ranar da ta iso gidan ta shimfida ta, wanka da
Alwala kawai ke tada ita se idan zasu tafi Asibiti amma dama abinci ta dade da
daina ci, yoghurt kadai take iya sha shima se wani na tsaye a kanta. Ta rame ta
lalace tayi baki tamkar ba Sulaim ba, babu komai ya rage fuskarta banda kwalakwalan
idanu da suke a warwaje kamar na owl. Suna zaune Bayan sunyi sallar Imratu ta dube
ta tace

Sulaim bazaki sawa zuciyarki salama ba ki rungumi kaddarar da Allah ya aiko miki
ba. Duk wannan damuwar da kike ciki bazata Hana Kun Fayakun aiki ba. Ki kwantar da
hankalinki kiyi mishi addu'a gwargwado iko.

Hannunta tasa ta share hawayenta tace

Anty Imratu, kina ganin Yaya zai tashi? Kina ganin zai samu sauki bazai mutu ba?
Wallahi ya mutu mutuwa zanyi.

Ta fada Tana fashewa da matsanancin kuka me cin rai, me taba zuciya. Rungumota
Imratu tayi tana bubbuga bayanta alamun rarrashi Don gaba daya tausayin Sulaim din
take sosae, yarinyar tana cikin mawuyacin hali tana bukatar dauki. To daga nan ne
bacci me nauyi ya dauketa wanda Bata farka ba se karfe goma da rabi shima hayaniyar
da ta cika gidan ita ta farkar da ita. Gabanta na wani Irin bugawa, tsoro Yana kara
shigarta ta mike jikinta a matukar sanyaye tamkar an watsa mata ruwa haka ta fito
amma se ranta yayi matukar baci saboda at first tayi tunanin Junaid ne ya rasu Amma
tana fitowa se tayi kicibis da su Mami anata hada Hada tamkar wanda suke shirin yin
biki. Fasa fitowar tayi ta koma daki ta kwanta tareda kifa kanta ta saki kuka me
ban tausayi, bakin ciki sosae takeji cikin zuciyar ta, wato yaya Yana can a kwance
unconscious su kuma saboda basu damu ba yasa suka zo Harda hada Hadar biki lallai
ma!

Yaya Maryam wadda ta kasance first born din Umma Fatima ta shigo don duba ko Sulaim
ta tashi ta ganta a wannan halin. Gefenta taje ta dago ta, tare da fadim

Haba Sulaim kin dinga kuka kenan? Se Yaushe zaki hutawa zuciyarki, Allah zai yayewa
Junaid ko.

Kanta ta girgixa tace

Amma kuna kallo Yaya Yana Asibiti unconscious, shi ne zakuzo kui ta hayaniya.

Murmushi Maryam tayi tace

Kiyi shiru mun daina, taso muje Umma na kiranki.

Babu musu ta Mike tabi bayanta, parlon daya kasance na Junaid anan Mami da 'yan
uwanta suke da kuma 'yan uwan Baba, Tana shiga ta tsugunna ta gaeshesu Sede farin
cikin da take hangowa akan fuskarsu yasa ta Fara tunanin kodai Junaid ya farka ne
amma ai da Za'a Fada mata. Zama tayi inda Amma ta nuna mata. Wata budurwa me
Kimanin shekaru ashirin ta dubi Amma tace

A fara?

Kanta Amma ta gyada tare da duban Sulaim tace

Duk Abinda yazo cikin rayuwarki, ki karbeshi hannu bibibyu kinji?

Hawaye na zuba daga idanunta ta gyada Kai, zuciyarta na son sanin dalilin da yasa
ake mata wannan Mulken mulken Amma ba Wannan ne a gabanta ba, karfe uku kawai take
jira tayi ta tsallake koma Menene taje ga yayanta.

Tamkar an dade da sanar da mutane wannan daurin Auren haka massalacin na Alfurqan
dake cikin Alu avenue ya cika da dumbin mutanen dake zaune don shaida auren na
Junaid da Sulaim. Ja'afar shi ne Wanda ya wakilci Junaid, yasha manyan kaya tamkar
aurenshi, Fuskarshi babu yabo babu fallasa cikin zuciyar shi Yana gwada Irin asarar
da yayi amma ko babu komai dan uwanshi ya samu, yasan it was all his fault ba
laifin kowa.

Karfe daya da Rabi, Bayan an kammalla sallar juma'a babban Limamin massalacin Wanda
Baba ya bashi wallicin Junaid don abokinshi ne Tun school days, Baba Abdul Aziz
wanda abokin Daddyn Sulaim ne shi Baba ya bawa wallicin Sulaim. Babu bata Lokaci
dubban jama'ar dake ciki da harabar massalacin suka shaida daurin Auren Muhammad
Junaid Lukman Birnin kudu da Ummu_Sulaim Aminu Birnin kudu akan sadaki Dubu Dari
Biyu. A take aka shafa fatiha kafin aka ja doguwar addu'ar rokawa Junaid lapiya.

A gidan Junaid kam Sulaim Tasha gyara na gani na fada, within hours ta canza Baki
daya tamkar ba ita ba, tayi kyau sosae tamkar an Bare ta sabuwa. Ga wani kamshi da
takeyi kamar an mata barin turare. Seda suka gama pampering jikinta kafin suka Fara
zana mata lalle ja. Lokacin daga ita se Najaatu wadda Ke kunshin, sauran biyun
Aliyah wadda gyaran Kai tayi mata se Mamaaa wadda Itace head din ita tayi gyaran
jiki.

Cikin sanyin murya Sulaim tace

Me yasa ake min wannan abin, Yayana yana Asibiti amma har nake da lokacin kunshi.

Murmushi tayi tace

Kede ki Bari na karasa miki kinji.

Kanta ta gyada kawai, ta cigaba da ambaton sunan Allah tareda lumshe idonta Wanda
ya fara washewa Daga jan da yayi. A hankali taji tamkar ana zubawa zuciyarta ruwan
sanyi, Lokaci daya taji wata nutsuwa Tana shigarta, taji wani bakon yanayi me dadi
wanda ta manta rabon da ta shiga Irinshi, ajiyar zuciya ta dinga saukewa har
lokancin idanunta a lumshe suke. Seda Najaatu ta kammalla kafin ta bude idonta tace

Dan Allah idan kin fita ki tambaya Wace Imratu ki Turon ita.

Inshaaa Allah ta fada haka kurum take jin tausayin Sulaim din a zuciyara saboda
kana kallonta zakaga tana cikin damuwa. . Kafin Imratu ta shigo taji gidan ya kuma
kacamewa da guda da ihun murna a'a nanma kanta ya kara shiga duhu tana tunanin
abinda yake faruwa?

Tun tana zuba idon ganin Imratu har ta hakura ta cigaba da zama, can Sega Najaatu
Taxo ta cire kunshin, subhannalllah! Kwaai zaka iya fada saboda masifar kyau da
yayi. Wasu abubuwa ta shafa mata sannan ta hada bakin lalle ta Fara mata shima me
kyau. Shi bai dade ba aka cire kuma har lokancin babu Wanda ya shigo gurinta hakan
yasa taji Duk ta damu tana son sanin abinda yake faruwa da ita, don tasan ko Meye
dole it has to do with her, amma ko a ranta bata kawo ta auri Junaid bane.

Har dakinta Mamaaa ta kaita lokacin babu mutane da yawa a gidan ya dan sarara, kowa
ta kalla Fuskarshi annuri ne kawai ke fita amma da idan ta nufesu se taga babu
fuakar ta Tambayesu. Ita ta hada mata ruwan wanka me hade haden kamshi da stuffs
dinsu wanda Bata San meye ba, tayi wanka da kyau dama tana son Ruwa hakan yasa duk
dadewar da tayi a ciki bai dameta ba. Amma hankalinta gaba daya yana kan Junaid don
har hudu tayi tasan yanzun Duk anje an ganshi ita daya ce kawai.

Tana fitowa aka barta tayi sallah Sega Mami ta shigo hakan yasa duka suka fita,
Mami ta zauna Tana ta kallon Sulaim din wadda tayi kasa da kanta, gabanta na tsanan
ta faduwa don batasan me Mami zatace da ita ba. Sun kusa Mintina talatin in awkward
silence kafin Mami tayi breaking silence din da fadin

Ummu_Sulaim!

A hankali Cikeda nutsuwa ta dago idanunta da sukai haske kamar an diga zaiba a ciki
ta kalli Mami kafin ta dauke kanta don haka kurum taji kunyarta take ji.

Yau Friday, juma'a kenan babbar rana ga Dukkanmu. Wani barin na zuciyarta yana fada
min Nayi shishigi amma wani barin na fadamin daidai kenan. Bayan mun rabu jiya mun
yanke shawarar aura miki junai......

Da sauri Sulaim ta dago Tana kallon Mami wadda kallon yasa ta kasa karasawa, wasu
Irin mixed emotions ne cikin idanunta da kan fuskarta, lokaci daya madaukakin farin
ciki ya mamaye mata zuciya da dukkan jikinta! Amaryar Junaid! Oh Allah ta ayyana
cikin ranta kafin kuma ta saki kuka a hankali wanda yasa Mami tace

Bakya murna ne?

Da sauri ta girgixa kanta Tana share hawayenta kuma ta kasa furta komai banda
hailala da kirari da take yiwa Allah daya cika mata barinta ko tace burinsu, Allah
ya tayar mata kafadun Junaid ta gaya mishi ta zama mallakinshi, inama yana nan
tasan murmushin nan zaiyi wanda ko fushi take yayi se taji ya tarwatsa fushin, ta
tuno idanunshi masu kaifi da Hana mutum sakat! Kuka ta dinga Yi tana Shesheka wanda
Mami ta tabbatar na tunanin halinda Junaid yake ciki don tasan Sulaim ko abinda
tayi a wannan jinyar tashi ya isa ya tabbatar wa da kowa son da take mishi.

Bayan sallar isha'i Mami da Umma da Amma suka shirya Sulaim cikin zani na soft
cotton material Baki da long sleeve top Fara kal, kanta da Aliyah tayi mata parking
gashinta in an assemble bun ya tashi yayi kyau aka saka mata bakar hula me kyau,
sannan amma ta ciro wata lafaya me tsananin kyau Fara tas da sequence bakake a jiki
se edge dinta wani black lacy ne aka mishi ado. Haka suka shirya ta tayi kyau Tana
fitarda kamshi na musamman me kwantar da zuciya. Flat Takalmi bakake Mami ta sata
tasa sannan suka kama hannunta se mota inda Jawad ke mazaunin driver, suna shiga ya
cillar mota zuwa orthopedic dake Dala!

Gabanta babu Abinda yake banda faduwa lokacin da Amma ta tura dakin suka shiga
kanta na kasa ta kasa dagowa don batasan ganin Junaid a halinda ta barshi. Gefen
gadon Amma ta aje ta sannan ta Ajiye mata wata jaka batareda tace da ita komai ba
tasa kai ta fice, ta jima tana zaune yadda ta barta gashi ta kasa dago idanunta
Balle ta kalli dakin dukda tasan gurin Junaid aka kawo ta, kenan ta zama matarshi
da gaske an daura auren kenan! Allah kenan yana amsa addu'a ya bawa Bawa Abu
lokacin da ya debe tsammani.

A hankali taji alamar an bude kofa an fito, tasan ba shigowa akai ba Daga toilet
aka fito, to ko dai wani na ciki ne? Amma se kawai taji muryar da ko a ina take ko
me takeyi ta jita tasan ta wacece, wannan karan a hargitse ta dago idonta ta dubi
inda ta jiyo muryar shi, shi dinne her beloved, her everything, her world, her life
yana tsaye jikinshi da jallabiya yayi haske amma akwai rama sosae tamkar bashi bane
wanda ta bari jiya baisan waye a kanshi ba. Hannunsa ya bude mata Fuskarshi tamkar
gonar auduga Don fara'a, babu musu ta Mike Tana sassarfa ta isa gareshi Tare da
fadawa cikin kirjinshi ta saki kuka, a hankali ya zagaye hannuwansa a bayanta, ya
rungumeta Tsam Yana jin wata nutsuwa wadda zai iya rantsewa bai taba jin makamancin
hakan ba!


Shatuuu ♥️
[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
40

✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad



Daga office din Musbahu Bata Kara zuwa ko ina ba ta biyo Kabir don ya kawota gida,
Tunda yanzun ta samu abinda take so Tana ganin kamar yawace yawace ya Kare ya Kuma
kamata ta zauna ta nutsu ta tsara yadda zatayi rayuwa tare da Musbahu.

Suna zuwa gida tayi sallama da Kabir akan se sun zo Washegari sannan ta shigo gida
fuskarta dauke da wani madaukakin murmushi, murmushi ne daga kasan zuciya wanda
yake nuni da burina ya cika. Babu kowa tsakar gida hakan yasa ta shige daki ta cire
kayanta, tare da kurawa kanta ido jikin mudubi, bazata taba gajiya da yiwa Allah
godiyar kyau da diri da yayi mata ba don tasan shi ne Abinda yake jawo hankulan
Maza kanta, juyawa tayi ta shiga karewa kanta kallo tasan tana Hulda da Maza, tayi
Hulda sosae dasu amma ko da wasa batayi Kuskuren bada kanta ba, zaayi romancing,
smooching, fingering da duk wani abu amma bata yarda da penetration ba saboda tana
ganin shi din shi ne pride dinta, shi ne darajarta ta 'Ya mace!

Katifa ta koma ta kwanta, ta janyo wayarta wadda tuni ta kashe da taje office din
Musbahu, kunawa tayi babu tunanin komai ta Fara kiran Aimana, Bata dade tana
ringing ba Aimana wadda mamakin kiran yasa tayi picking tace

Khul......
Katseta Khulthum tayi da fadin

Ba wannan na kiraki kiji ba, na kiraki na fada miki aure zanyi.

Aimana da bata fahimci inda maganar Khulthum ta dosa ba tayi ihun murna tace

Ke amma naji dadi Wallahi, Yusuf ne.

Wata harara Khulthum tayiwa wayar tamkar Aimana na gurin tace

Kina abu tamkar har zuciyarki bayan bakin ciki ne fal, Bari kiji na samu miji Wanda
har ki mutu bazaki taba haduwa da Irinshi ba! Kince masu kudi ba'a haduwa dasu ina
son kisan cewar na samu kuma zan aura.... Kije ki samu rijiyar da tafi kowacce
zurfi cikin kano state ki fada don bakin ciki!!

Bakin cikin Aimana guda daya ne Bata samu ta rama ba, bata fadi Abinda take son
fada ba, ba kuma ta samu ta mayar mata da martani ba ta kashe. Haka ta Bata kusan
Mintina ashirin tana kiran Khulthum amma taki shiga kawai se ta kira Sulaim ita
kuma wayarta a kashe. Tsaki tayi tana addu'ar Allah ya hada su itada Khulthum Koda
cikin mafarki ne Wallahi se ta sha mamaki, ita har ta isa ayi mata bakin ciki,
bakin cikin me talauci ko kuma rashin tarbiyya?

Da daddare wajen karfe Tara tana kwance tana kokarin hada wayarta da power bank,
Amira ta leko tace

Yaya Khulthum kizo Baba yana kiranki.

Kanta ta gyada tace

Kice gani nan.

Amira ta fice ita kuma ta cigaba da Abinda take babu niyyar ma fitar, jin shiru
yasa Baba ya kalli Mama yace

Kije ki Kira min ita Tunda ke Uwarta ce, ni kuwa kinga ba haifar ta Nayi ba.

Kai Mama ta girgixa ranta a bace saboda yadda Khulthum ke jawo mata magana. Tana
zuwa ta sameta a kwance, kunnenta da earpiece ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login