Showing 24001 words to 27000 words out of 121650 words
ta gani cikin idanun shi, sauke kanta
tayi ta kasa motasawa Daga gurin Ja'afar dake tsaye bai lura ba Yana mata dariya
yace
Sweetm idan ba zaki shiga ciki ba zo muje kisha ice cream.
Kawai zuciyarta ta Raya mata kibi Ja'afar haka kuwa tasa kafarta a nutse a kuma
sanyaye ta fada motarshi, Junaid da yaji kamar ya Kurma ihu haka yaja dogon huci
tareda lumshe idonsa.
To fa one word for the page, for Junaid, for Ja'afar, for Sulaim and for Subay'a da
danginta.
Shatuuu ♥️
[6/28, 7:40 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
9
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣shatuuu095@wattpad
Yana bude idanunsa wanda suka kusan Mintina biyar a lumshe, se ganin shigowarta
yayi hakan ya bashi mamaki Don a iya saninshi tabi Bayan Ja'afar ne su fita. Itama
Sulaim din bata kuma dubar inda Junaid yake ba ta shige cikin parlour, Mami ce
kadai a zaune se Muhammad da Ahmad, suna jin muryar ta suka taho a guje suka
rungume ta, itama rungumarsu tayi tana ta murmushi, kwanaki biyar kawai da zuwana
kaduna take jin tayi missing dinsu sosae. Hannunsu taja suka samu guri kan carpet
suka zube suna tayi mata surutu wanda Seka rasa inda suka gadoshi kasancewar
iyayensu kaf babu me surutun sede ko idan Jawad da Ja'afar sukai wa Kara.
Auta kin dawo?
Dagowa tayi ta dubi Mamin tace
Na dawo Mami, Tace Tana gaisheki sannan da zarar kayan sun iso zakiji sakonta.
Kai Mami ta gyada tace
Yayi kyau, Allah ya miki albarka, Junaid Yana tambayarki kun hadu?
Take yanayinta ya canza dama dalilin da yasa Mami yin maganar kenan tana zargin
akwae Abinda Ke aukuwa between the two.
Bamu hadu ba, tare yazo dasu Ahmad?
Eh
Kawai Mami tace ta cigaba da Abinda take itakuma tana wasa da yaran.
Wani ihu Subay'a ta saka lokacinda mukhtar ya mika mata key din motarta hade da
farar takarda cikin farar envelope,
Yaya Suhaila na shiga uku ya sake ni, Abban Fannah kaje ka bashi hakuri , na shiga
uku!
Baki daya babu wanda ya samu courage din tunkarar ta, hatta shi mukhtar wanda Tunda
Sabi'u driver ya bashi takaddar yake murna cikin ransa Don Yana son su koyi hankali
baki dayansu. Amma yadda Subay'a ke yin abu se yaji baki daya tausayinta ya
kamashi, itakam Suhaila ba karamin rudani ta shiga ba saboda tasan duk inda aka je
tanada kamasho cikin wannan abin. Subay'a kam bazata ma iya fadar yadda take ji ba
se kawai ta rabe su ta shiga dakin da ta Kwana ita bata bude takardar ba saboda
tsoron content din ciki haka kuma Bata daina kukan da takeyi ba har Seda ya tashi
Fannah yarinyar Suhaila, ganin halin da uwarsu Ke ciki yasa ta Mike ta fito parlour
Don jin Karin bayani, a parlor babanta kawai ta tarar da Suhaila ta koma dakinta
saka kaya gwara su tafi Asibiti ko gidan hajiya. Abayar da tasaka jiya ta sake
mayarwa ko brush ba tayi ba ta fito hawaye Yana mata zarya, ita bata taba tunanin
Junaid zai iya makamancin haka ba, ko sau daya bata taba kawowa dan abinda ya faru
jiya can lead to such commotion. Tare suka fito da Suhaila wadda lokacin tace
Abban Fannah Bari muje gidan hajiya, Fannah do the right thing.
Bata jira amsar daya daga cikinsu ba tayi hanyar waje, ita ta karbi motar tana
driving bayan Sulma ta tabbatar musu kowa na asibitin, don haka can suka nufa.
Kiyi hakuri Subay'a ban kawo abin zai zama haka ba, amma kema tunda Kinsan halin
mijinki ai you shouldn't have followed me.
Kunji fa bayan seda tace bazata je ba ta tursasa mata amma yanzu take dora mata
blame din itadai jinta kawai take amma gaba daya hankalinta ya tafi Irin rayuwar da
zatayi idan Junaid ya saketa, kenan ta kaishi bango? Kenan ta kure hakurinshi? Dama
idan bakaji bari ba kaji Hoho.
A asibiti kamar jiya haka suke zaune kowacce tayi shiga ta alfarma, kayan wannan
yana cewa na wannan bani waje Don a su takwas babu wadda Ke Auren talaka dukkansu
masu kudi ne tamkar policy haka abin yake. Tundaga sallamar Suhaila Salina tace
Lapiyarku?
Hajiya da sauran suna binsu da kallo har Subayaa ta fada jikinta tare da fadin
Hajiya Junaid ya sake ni na shiga uku.
Gaba daya salati suka saka saboda yadda abin yaxo musu a bazata.
Me ya faru?
Hajiya ta tambayeta Tana dagota Daga jikinta. Ba karya ta zayyane mata komai
tareda mika mata envelope din. Karba tayi itama jikinta yayi balain sanyi ta buda
sede content differs from Abinda kowa Ke tunani.... It says
Ki zauna a gida ki Bari har se ranar da babyn yayi Kwana arbain se ki dawo.
Wani sigh of relief ta saki tareda bawa Surayya wadda ta karanto a fili nan take
jikin kowa yayi dadi se kuma suka Fara zaginshi shi uban waye da zai musu gatse
Wallahi ba zata koma ba se ranar da ya yanka mata kuma se Sun gwada mishi tana da
gata. Itakam Subay'a batace uffan ba se godewa Allah da take, anan tayi wanka dake
seminar bank dinsu ya turata Hakan yasa Bata fita Tunda online ne seminar kuma se
wajen laasar ake Farawa. Baki daya suka tafi suna kara lallashinta akwai solidarity
sosae a tsakaninsu. Daga ita se Sulma suka rage a dakin Bayan kowa ya fita tace
Sister dama Papa bai yarda ba jiya kika fito?
Dago kanta tayi fuskarta Cikeda alhini tace
Seda naki zuwa tunda yaki bari amma tace Wallahi se naje.
Haba Sister kina me ita Yaya Suhaila ita take aurenki ko Papa ke aurenki. Kin ganni
da ne nayi sokanci nake bin duk Abinda suka gindaya min amma ki sani tun ranar da
na fahimci cewar ina dauke da cikin nan naji tabbas bazan iya sake yiwa Umman D
iskanci ba haka darajar D ta sake karuwa a idona. Yanzu akan D babu Abinda bazan
iya ba kuma na yadda na Bata da kowa Don duk ranar da aurena ya mutu babu Wanda zai
jajanta min cikinsu kin tuna yadda Yaya Safina tayi. Tunda na haihu nasan darajar
da kuma naji idan ace Dana yayi aure matarshi take neman rabani dashi Se inda
karfina ya kare, Umma tayi hakuri don haka I'll make it up Kema ki yadda komai ki
fuskanci aurenki Sister.
Share hawayenta tayi tace
Ki bani shawara ya zanyi
Ki jira ayi suna Seki koma kafinnan kiyi mishi text ki bashi hakuri sannan kiyi
addu'a ki kuma gyara kurakuranki is never late.
Haka Sulma ta dinga bata shawarwari kafin kuma suka fada wasu hirar abinsu na yan
uwantaka hakan yasa ta ware abinta.
Mami yau dinner amaryar Ridwan inason Sulaim ta rakani.
Junaid ya fada suna zaune lokacin shida Mami, Sulaim dake gefe tayi saurin dagowaa
Sede suna hada ido da Mami tayi saurin dauke kanta. Murmushi Mami tayi tace
Babban Yaya ni na amince ita zaka fadawa.
Wani fari tas yaji ranshi yayi mishi hakan yasa ya dubeta yace
Auta ki shirya 8pm Zamu je.
Se taji bazata iya missing opportunity din ba hakan yasa tace
Tom.
Tunda ta Idar da sallar isha'i ta bude wardrobe dinta tana assessing kayanta,
tunani take tayi me zata saka a jikinta, haka kurum take son fitar dashi kunya, so
take tayi kyau. Tana tsaye taji ringing din wayarta da sauri ta isa gurin amma
maikmakon ganin kiran Junaid as expected se kiran Ja'afar, karamin tsaki tayi ta
aje wayar can ta hango wani lace har ta kai hannu zata ciro se ga Mami ta shigo, da
murmushi saman fuskarta tace
Troubled?
Kanta ta gyada hakan yasa Mami tazo ta tsaya tana scrutinizing kayan har takai kan
wani kyakyawan code net wanda ta dinka mata a wani biki kuma aka fasa Baki daya,
gold ne material din me dinkin skirt da Riga se ta dakko wani black scarf ta daura
mata bayan tayi touching mata fuska da light make up, take sulaim ta fito tayi kyau
kamar ka saceta. Seda ta gama komai sannan suka fito tare har kasa, Junaid ta Fara
hangowa cikin milk tuxedo suit se tie Baki da leather covered baki da matching
wrist watch. Yayi kyau sosae shima tamkar ka sace su. Baba yana zaune ganin sun
fito yace
Is like an wareni fa, se ina haka?
Dariya duka sukayi Mami tace
Ridwan ke kara aure shi ne zasuje dinner.
Kallonsu yayi sosae bai kara cewa komai ba Mami tace
Allah ya kiyaye, Junaid Kada kui dare.
Inshaaa Allah Mami, Baba se min dawo.
Kamshi ya gyada musu yayinda Sulaim tayi waving dinsu suka fita, zama Mami tayi ta
fuskanci Baba Don taga akwai magana bakinshi, aikuwa tana zama yace
Kin kusa hada wani auren ne?
Me ka gani?
Ta bashi amsa da tambaya ,
Yaranki is like they're in love amma ko nayi mistake ne?
Kanta ta girgixa tace
I'm not sure, so Kaga bazan ce maka komai ba amma from yadda suke exhibiting wasu
signs ina tunanin kamar .......
Is not kamar they're deeply in love with each other, kawai dai ina tunanin basu
fahimta bane.
Kai Mami ta rike tace
Amma Ja'afar fa?
Dariya Baba yayi yace
Keda yaranki ni nawa ido kawai.
Shiru Mami tana nazarin maganganun Baba.
A cikin mota babu me magana baki dayansu sunyi shiru se karar ababben Hawa dake
yawo kan titin. Junior ne ya fara breaking silence din yace
Yaushe zaki koma Kano?
Saturday
Ta bashi amsa, ita ta rasa dalilin da idan suna tare se tana jin bugun zuciyata
yana karuwa sosae, ga wani uneasiness da take ji ko kuma da yayi mata magana se
taji dukkan ilahirin jikinta ya amsa, ko kuma ta zama short of words gwara ma idan
waya suke.
Basu kuma magana ba har suka isa event center din, cike gurin yake da motoci Nawa
Kece raini, guri ya samu yayi parking sannan ya dubeta yace
Shall we?
Murmushin nan nata me kyau tayi masa sannan ta bude kofar suka fito a tare, seda ya
rufe kofar da kyau sannan suka shiga shoulder to shoulder. Dake gurin yan Boko ne
masu kudi kuma komai a tsare hakan yasa kowa Yana zaune dake Baifi Mintina biyar da
Fara event din, suna shigowa idanun MC ya sauka kansu kawai se ya fara fadin
Kaga wasu couples wanda Bayan Amarya da ango Bana tunanin akwai wasu perfect match
kamarsu, kallesu fa
Gaba daya wani nishadi ya mamaye Junaid ya dago idanunshi lucky enough ya hade
cikin na Sulaim take wani covolent bonding yayi taking place dukkansu seda
zuciyoyinsu ta tsaya cak kafin kuma sauke idanunsu hakan yasa hanaklin kowa ya koma
kansu Sega Amarya da Ango sun sakko daga inda suke Zaune dan karrama su, hakan yasa
duk inda suka gifta kallonsu ake a haka suka zauna, se taga yawancin abokansu in
one way or the other tasansu a Faculty yawanci lecturers dinsu ne. Suna ta zuwa
suna gaisawa har wani da bakinshi baya shiru yace
Ashe mun kusa zuwa wani bikin, da farko nayi tunanin uwargida ce ai.
Dan murmushi Junaid yayi yace
Bakaga muna kama ba autarmu ce banaso zuwa ni daya.
Autarmu ta maimaita cikin ranta, shikenan matsayinta no any other special matsayi
only a sister. Baki daya se taji ta gundura da zaman garin duk yadda ake abubuwa na
ban dariya saboda MC akwai barkwanci Amma se taji gaba daya haushin gurin takeji.
Duk Abinda take yana Lura da ita amma bazaice ga takaimaiman abinda ya bata ranta
ba ganin haka yasa yace
Kin gaji mu tafi ne?
Da sauri ta gyada kanta, se ya Mike itama tabi bayanshi sukayiwa Ridwan sallama
wanda se tsokanarshi yake ba tareda ya Bari Sulaim din taji ba.
Shatuuu ♥️
[6/30, 7:28 PM] Shatuuu😍:
*MACE A YAU*
10
✍️Shatuuu♥️
🌈Kainuwa writers Association
#⃣shatuuu095@wattpad
Let's call it a day! We meet in our next class and hopefully there will be test
then.
Malamin ya fada bayan ya kammalla darasin shi na wannan ranar, haka ya shiga
tattare kayansa cikin briefcase yayinda sauran students din dake cikin ajin kowa Ke
hade nashi dukda bawai sun gama classes din ranar bane Amma akwai interval na zuwa
aje ayi sallar axahar, Wanda zasu ci abinci suje suci. Seda yazo fita kafin yace
class rep dinsu ya bishi.
Sulaim na zaune inda kusan kullum nan take zaune har tana neman maida gurin
permanent seat dinta, hada book din datayi taking note a ciki Ta zura cikin wata
off white back pack, dake ranar talata ce hakan yasa kowa Yana sanye da black and
white, haka tsarin Law school yake a BUK every Tuesdays and Thursdays black and
white ne sede wasu ranakun ko Za'a fita ko kuma zaayi mood trial to dole ne a saka
wannan uniform din, hakan yakan sa su zama elegant and attractive.
Yan mata uku suka taho inda take Zaune tana niyyar mikewa, Khulthum ce ta Fara cewa
Sulaim tashi mu tafi.
Mikewa tayi ta sabi back pack din a shoulder dinta daya wrist watch din hannunta
wanda yake Baki kuma yayi kyau kan shiny caramel skin dinta ta duba. Tare suka fito
su hudun Ummu_Sulaim, Ummu_Khulthum, Ummu_Aimana da Ummul_khairi.....the 4 Ummu's.
Khairi tace
Kuzo mu fara yin sallah kafin muje neman abinci.
Khulthum ta bata rai tace
Gaskiya ni yunwa nakeji, mu fara cin abincin kawai.
Ke kullum yunwa kikeji baki cin abinci daga gidan ku ne?
Harara ta watsa mata Wanda yasa Khairi yin dariya itakuma Aimana tace
To meye abin hararar tawa, ba gaskiya na fada ba, malama sallah zamu Fara yi.
Itakam Sulaim jinsu kawai take don bawai tayi wani sabo bane ita dasu last week
suka dawo Daga mid semester break, ranar da ta dawo ta nemi Khulthum saboda zaman
ita daya baya mata dadi to ita kuma Khulthum already tanada su Aimana hakan yasa
sukai jamming baki dayansu. Amma har yanxu bata fiya sakewa ba sosae. Massalacin
suka Fara zuwa suka bada farali Khulthum tana ta bacin rai wai ba'a girmama opinion
dinta ba. Sulaim kam murmushi kawai take musu. Wani joint sukaje nanma kafin aje
seda aka bata Lokaci kan ayi deciding gurin da Za'a ci abinci Se sulaim taji
tarayyar batada amfani don lokacin tana ita kadai yanxun ta kammalla komai ta koma
class amma ya zatayi Tunda ta Riga ta biyosu. A joint din sukai order fried rice da
salad se Beef akai da drink. Dama se an gama ake biya kuma kana shiga gurin kasan
na manyan yara ne ya'yan masu kudi don hardly kaje baka hadu da wani lecturer ba a
gurin, sunsan takan iya girki. Suna fara cin abincin wayar Khulthum ta Fara ringing
gaba daya suka kalleta itakam tana kokarin picking tana sakin wani lallausan
murmushi
Kina ina ne?
Shi ne tambayar da Hu ya Fara mata, cikin daidaita muryarta ta fada masa joint din
da suke. Tana aje wayar Aimana tace
Wa zaki rakito mana?
Khairi wadda wasu abubuwan nata na shige Dana Khulthum tace
Batta yazo dama yau purse dita babu nauyi, Dan kun nace Keda Sulaim ne amman yau
banyi niyyar Zuwa gurinnan ba.
Dariya Sulaim tayi ta cigaba da cin abincinta saboda itama yau yunwar takeji Don
Junaid Nada class din safe yau hakan yasa ya figo ta bata wani Yi breakfast din
kirki ba. Suna tsaka da cin abinci Hu ya shigo shida abokansa kusan zan ce muku
babu Wanda a gurin bai san lucky Hu ba, har wani kirari ake mishi Kaga yaro me kudi
kana gudu luck na binka, yaro me tashe. Kusan bawai a faculty dinsu yayi suna ba
entire new site ansan Lucky Hu saboda yadda yake da yanmata idan baiyi dating dinki
ba to yayi flirting kawarki haka abin yake Shiyasa ko award night ake shi ke daukan
most popular a cikin faculty. Abokansa uku suna bayanshi, Tunda ya shigo Khulthum
baki daya ta rasa nutsuwarta, ta gyara nan ta matsa can har Aimana tace
Dallah ki nutsu se kace tsutsa kin kasa zama guri daya Bari naga waye wannan
saurayin.
Me zasuyi banda dariya Don Aimana ita ke maganin rawar kan Khairi da Khulthum.
Gefenta ya tsaya tareda dubansu Sulaim yace musu
Sannunku!
Suma sannu sukai mishi daidai lokacin gama cin abincinsu Aimana wadda tana kallon
Hu ta ganeshi kasancewar faculty dinsu daya da yayanta kuma yana yawan bata
labarinsa, mamaki sosae tayi haka yake kamar me charm indai yace yana so to dole ne
mutum ya amince dukuwa da sanin halinshi da sukai, mikewa sukai Don biyan bill ya
dakatar dasu yace
Paid! Kuna kawayen Her Majesty ta yaya zaku biya kudin abinci.
A'a Khulthum se aka Fara blushing Irin taji kunyar nan, itakam Sulaim shiru tayi
tana jiran jin Abinda sauran zasu fada. Aimana ce tace
No Dan Allah Karka Kara biya mana , zamu biya namu ita se ka dinga biya mata. For
today thank you!
Tana fadin haka taja hannun Sulaim suka fito ita kuma Khairi ta zauna godiya,
yayinda Huzaifa ya bisu da kallo saboda bai taba katari da irinsu ba, kawayen yan
matanshi shishige masa suke amma wannan har akan Fuskarshi take fada masa bata
bukatar payment dinsa.
A class Khulthum ta shigo lokacin already Ridwan was in class, dayake period dinsa
ce yana taking dinsu wani course shima banashi bane mutumin bazai samu Zuwa bane
Shiyasa ya turoshi, so ranar ne ranar farko da ya Fara shiga class dinsu. Tana ta
yauki ta shigo class din itada Khairi, bai ce musu komai ba seda t
Suka zo tsakiyar aji yace
Hey! Get out of my class, irresponsible ones.
Simsim kamar an dakesu haka suka fito Khulthum tana ta Balai yaci musu mutunci, se
bayan La'asar ya fita kowa ya tashi ya fito, tunanin Aimana da Sulaim Khulthum tuni
ta tafi dake Khairi a hostel take su uku suna day. Tana hangosu ta nufo su, Sulaim
ce ta Fara fadin
Me yasa kuka zo late gashi yayi yabbing dinku.
Tsaki Khairi tayi tace
Rabu da shege, ya dauki tsayi kamar Daren bakin ciki.
Dukda maganar batayiwa Sulaim dadi ba ganin laifinsu ne for coming late, banging
into the class without permission seda tayi dariya wai tsayi kamar Daren bakin
ciki. Khulthum ce ta Fara magana ranta a bace tace
Aimana ni banji dadin Abinda kikayiwa Huzaifa ba, har zakice wai ya rike kudinshi,
don kin samu ya kalleki ma.
Baki sake Aimana take kallon Khulthum kafin tace
Ya kalleni? Na rokeshi ne? Ke nifa Bana son wani kato ya biya min abu har idan zan
wuce yana tunanin favor yayimin, kuma Inace cewa nayi ya biya muku nida Sulaim Bama
bukata.... Ke bana son nonsense stuffs kinji.
Ganin ta dauki zafi yasa Sulaim tace
Kai friends basa fada, Dan Allah kui hakuri meye a ciki.
Khulthum dai batace komai ba se juyawa tayi ta nufi inda yake jiranta kullum ta bi
bayanshi ta fada mota suka tafi, Khairi ma sallama tayi musu ta tafi hostel itada
wani gaye dan class dinsu. Se ya rage Aimana da Sulaim wadda har lokancin mitar
abin take, suna tsaye Sega kiran Oga Junaid ya shigo gabanta ya fadi don ta rasa me
ya hanata kiranshi tace ta gama kamar yadda suka Saba bare yau tasan har ta gama
lectures bai tashi ba Balle tace ko Yana gida. A hankali kamar me tsoro ta Kara a
kunne tace
Yaya na gama.
Ki samu napep ya kawoki na wuce Tun dazu, zamuje shopping da Subay'a
Zaro idanta tayi don bai taba barinta ba ko ya tafi se ya dawo ya dauketa hakan ya
kular da ita ba tareda ta amsa ba ta kashe wayar, kallon Aimana tayi tace
Bari na