Showing 66001 words to 69000 words out of 121650 words

Chapter 23 - MACE A YAU by Shatuuu

Shatuuu   

12 May 2026

150

da Salim ne?

Tabe Baki Khairi tayi tace

Rabu da yan iska, kinga ta bi Sahun su Maimuna ko?

Sulaim tayi dariya tace

Ke Khairi ina ruwanki? Meye naki haka ta zabarwa kanta, nima fa na gansu a see
sweet am sure ranar da ya bata lift suka hade.

Kai Aimana ta girgixa Cikeda mamakin Khulthum tace

Ban taba kawowa zata iya abinda tayi ba, Allah ya shirya kawai.

Daga haka suka rufe shafinta suka fada hirar idanun Sulaim lokacinda Sagay ya
koreta,

Kinsan yadda na tsorata kuwa? Har cikin kaina Seda naji ihunshi.

Aimana tace

Tambaya ya dinga jero miki Ke kuma se murmushi kike kamar wani yayi proposing.

Dariya suka sakeyi hakan yasa Sulaim jin dadi dadi a ranta, suna isa suka shiga
dukkansu suka gaisheshi ta nuna musu kujerun suka zauna, Inda yake ta nufa ta zauna
kujerar dake facing dinsa tace cikin sanyin murya Tace

Yaya ina yini.

Aje pen din hannunshi yayi yace

Zauna mana.

Zama tayi cikin nutsuwa wanda yake burgeshi yace

Se 4 zaku tashi?

Kanta ta gyada tace
Eh.

Key din motar ya mika mata yace

Gida zan tafi, ki taho kawai.

Kafada ta girgixa tace

Kaje da ita ni zan biyo Aimana.

Sure?

Ya tambaya murmushi kwance a Fuskarshi yau Yana jin shi daban da kowa Yana jin
tamkar babu Wanda ya tashi da saa kamar shi a wannan ranar. Itama ganin yadda yake
ta murmushi yasa ta sake jikinta, ranta fal farin ciki duk wannan fear da take ciki
dazu yanzun babu kuma in dai zata cigaba da ganin tarin farin ciki a Fuskarshi tana
ganin babu abinda zai hana ta kasance tare dashi har abada.

Junaid Suna fita ya shafa kanshi tareda mikewa ya dauki abinda zai dauka ya cewa
messenger dinshi duk wanda yazo yace dashi ya wuce gida. Yana shiga motarshi ya
fice Seda ya biya ya dakko yaran kafin ya nufi gida haka kurum yake jin something
is not in place Amma ya kasa figuring me Nene. Haka suka isa gida sunata tsalle
shikuma Yana dariya, yaran kansu are happy Amma a haka Subay'a ke son tafiya ta
Barsu.

Bai tarar da ita a parlor ba, se kawai ya wuce daki, Dama suna shigowa Laraba ta
karbesu Don Yi musu wanka, seda yayi wanka yayi sallah kafin ya nufi dakin subay'a
amma Tun Daga parlor gabanshi ya fadi, ta canza curtain Zuwa wanda idan zata yi
tafiya take sawa, sofas dinta ta rufe da ledojinsu, da sauri ya shiga bedroom dinta
not wanting to believe abinda zuciyarshi ke fada mishi, babu bedsheet kan gadon,
wardrobe ya bude important kayanta duka basu gurin, Dayan bedroom din ya tafi nanma
same case. Da sauri ya fito ya nufi kitchen for the first time, Atika na hada salad
taji kamshin turare hakan yasa ta juo da sauri se ganin Junaid tayi, gaba daya ta
duburburce don Bata taba ganinshi a kitchen ba,

Me zaa baka?

Ta tambaya gabanta na faduwa, kallonta yayi yace

Ina Subay'a taje?

Kanta ta girgixa tace

Nima bansani ba amma sun fita da kaya itada yayarta amma gashi.

Ta ciro paper daga Apron din jikinta ta mika mishi, cikin hanzari ya karba sannan
ya fice Zuwa parlor, Baki daya yasan raini kam subay'a ta gama ko bai karanta
abinda Ke cikin paper ba yasan ta tafi Tunda yaga dakinta a haka.

_Dear, I'm sorry da Abinda zaka tarar amma babu yadda zanyi tafiyar ta zama dole.
Ka yafe min zan kula maka da kaina sannan zan dawo gareka. I missed you. Subay'a_

Daga haka ya dafe kanshi wanda ke barazanar tsagewa saboda yadda kwakwalwar shi ta
cunkushe, hannunsa ya saka ya rufe fuskarsa wadda tayi jawur saboda tsananin bacin
rai. Yana nan Zaune Muhammad yazo yana kukan Mimi. Wannan ya kara daga mishi
hankali ga har lokancin uku batayi ba Balle yasa ran dawowar Sulaim. Atika ce Taxo
ta daukeshi Cikeda mamakin halin da ta samu Junaid.
Shima dakinshi ya koma ya kwanta bayan ya samu Muhammad yayi shiru Ahmad kuma yayi
bacci, ya dade yana tunanin abinda zaiyi Amma ya kasa tuno Abinda ya dace yayi
saboda baya son yanke hukunci cikin fushi amma Wallahi yasan har Subay'a ta koma ga
Allah bazata manta wannan abin da zai mata ba.

Wasa wasa haka Junaid ya zauna a daki shi daya zuciyarshi na tafarfasa a haka akai
sallar laasar ya fita zuwa massallaci kafin ya dawo Sulaim ta dawo, Tana shigowa
Tajiyo kukan Muhammad, da sauri ta nufi kitchen dan can ta jiyo kukan, Tana zuwa ta
karbe shi daga hannun laraba tana girgiza shi tace

Waye ya taba min babyna?

Mimi

Ya fada Yana kara Sautin kukan shi, kallon Atika tayi tace

Ina Mamansu ne?

Atika tace

Tun safe akazo aka dauketa.

Juyawa tayi ta fita tana mamakin Subay'a she's never a good mother neither a good
wife. Komawa tayi parlor tare da Lallashin shi Sega Junaid da Ahmad sun shigo,
kallonshi tayi taga wani tashin hankali kwance a Fuskarshi wai a hakan ma ya ragu
kusan 70cent Bayan yayi sallah tareda kai kukanshi ga Allah, se taji gaba daya
ranta ya baci har Seda ta saki tsaki. Zama tayi shima ya shigo ya zauna ya kalli
Muhammad dake jikinta yace

Kin dawo kenan?

Kanta ta gyada tana patting bayan Muhammad se yaji inama ya zama Muhammad ko ya
samu wannan care din shima.

Na dawo Yaya, ya gidan?

Dan murmushi yayi mata yace

Alhamdulillah, gobe zanje kaduna akwai sako?

Kanta ta dago da sauri tace

Zanje nima

Murmushi yayi a ranshi Yana ganin wannan yarinyar will kill him tamkar bashi bane
dazu ya rasa inda zai tsoma ranshi amma daga ganinta har ya fara dawowa hayyacinsa.

A'a kiyi hakuri next week zan kaiku kinji?

Turo mishi Baki tayi tana bubbuga kafa hakan yasa ya tsira mata ido kamar bazai
dauke idonsa ba, ganin haka yasa tayi saurin daidaita kanta ta Mike zuwa dakinta
tana jin tamkar tafi kowa saa a rayuwarta.

Washegari Seda ya kaisu makaranta kafin yayi mata sallama yace

Gobe Inshaaa Allah zan dawo, kinji?

Kanta ta gyada tace
Tohm Allah kaemu, safest journey a gaida su Mami.

Zasuji dear, kuma haka zan tafi babu ko kallon da zan na tunawa dashi, babu
something sweet?

Hannunta tasa ta rufe fuskar ta tana dariya, a hankali kamar me rada tace

I will miss you.

Matso da kunnenshi yayi saitin bakinta yace

Kikace me?

I'll miss you.....

Wata kayatarciyar dariya ya saki yace

I'll miss you more *my Dove*

Jin yace dove yasa ta kalleshi se yayi dariya yace

Se munyi waya.

Fitowa tayi tana jin farin ciki na ratsa zuciyata tamkar ta tashi sama, Yaya
Junaid!

Karfe goma na safe ya isa kaduna seda ya gama dukkan abinda zaiyi sannan ya nufi
gida, luckily Mami da Baba suna gida. Mami ta kasa boye murnar da take ciki tare
sukai breakfast sannan suka zauna hira dukkansu. Junaid ya rasa ta ina zai fara se
can cikin damuwa ya sanar dasu halin da ake ciki, Baba couldn't say a word se Mami
ce ta Fara salati tace

Wani hukuncin ka yanke?

Sakk


[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
33

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad


Da sauri Ja'afar ya juya don komawa dakinshi saboda maganar da yaji Junaid ya furta
tamkar kibiya haka ta sokar mishi zuciya, bai taba kawowa zaiji Irin wannan
mummunar maganar ba kenan yayi wasa da damarshi, kenan Abinda Sulaim ta dade tana
fada mishi akan Watarana yana gani zata zabi wani over him. Hannunsa ya cusa kanshi
wanda yake Cikeda gashi da ake bashi kulawa tamkar na mace. Me yayiwa rayuwar shi
kenan? Me ya amfana a rayuwarshi. Ya sani yana da 'yanmata amma son gaskiya na
Sulaim ne itakadai take da features da yake bukata Daga gurin matar da zai aura se
gashi ya luza akan fushinshi na banza wanda ya sani laifinshi ne amma yaki waiwayar
ta Yana takamar tana mishi son da bazata jure rashin shi ba.

Kujerar dake kusa dashi ya fada kamar me shirin kuka saboda yadda zuciya take
tafarfasa, yasan ko Yana hauka bai isa karawa da Junaid ba a fagen neman mace, Abu
daya zai nunawa Junaid shi ne yarinta Amma Bayan haka bai da komai ba kuma da
Abinda zai tunkara Sulaim dashi. Ya tuno lokutan da take yawan ce mishi *If you
love someone, make sure you hold that person tight but if you didn't, others will
surely do!* ga maganarta ta tabbata, ta samu Wanda ya fishi shi kuma ya tashi a
tutar babu, he has completely messed up! Se muce Ja'afar ayi hakuri!

Baba ya bude Baki da niyyar magana farin ciki fal zuciyarshi har ya gagara boyewa
seda ya bayyana kan Fuskarshi, Mami tayi saurin fadin

Aure kace Junaid?

Seda gabanshi ya fadi Don Mami hardly ta kirashi da Junaid, idan ta furta to tabbas
abu yayi tsamari. Kanshi a kasa yace

Eh Mami aurenta nake son Yi.

Saboda 'yar gaban goshi bata nan, saboda kana son amfani da ita ka hukunta matarka,
ai Junaid har yanzun Kai ba namiji bane, bakayi wayon rike mata biyu ba Tunda har
ka kasa controlling mace daya, se biyu.

Kanta ta girgixa ta cigaba da fadin

'Yata Sulaim ba wadda zaayi auren huce haushi da ita bane, don haka ka manta da
maganar auren ka jira matarka ta dawo.

Ita kanta Mami ta tsorata da yadda idanun Junaid suka koma amma ta dake, ta dauke
idanunta kar ma tausayinshi ya rinjaye ta, bawai tana kin abin bane tafi kowa farin
ciki amma dole ta nunawa Junaid laifinshi saboda ya sakar ma Subay'a da yawa, idan
Jabir ne bazai taba haka ba.

Idanunshi jajur tamkar jini haka cikin wani tashin hankali wanda ya baibaye
zuciyarshi Lokaci daya saboda jin furucin Mami, amma ya sani shi yake nema dole ya
Dukar da Kai, cikin nitsuwa da kwantar da murya yace

Mami Wallahi bazaki taba kamani da wofantar da 'yarki ba, kinsani mutumin da Daddy
Aminu da Anty Zahra suka nuna suna so ma bazan bari a cutar dasu ba Balle gudan
jininsu Sulaim kiyi hakuri.

Kanta ta kawar gefe tana jin yadda zuciyarta Ke tausayawa Junaid,

Ka bar maganar kawai.

Juyawa yayi ya dubi Baba with pleading eyes akan ya saka baki amma ya Kaudar da
kanshi don suna yara idan Mami ta hana abu gurin Baba suke zuwa haka shima idan ya
hana amma yau abin Yana neman juyewa. Ko cikin tunaninshi bai taba tunanin cewar
zai kawo proposal din auren Sulaim ayi declining amma gashi yayi. Mikewa yayi
saboda Baba yace mishi yaje ya huta. Babu musu ya Mike ya nufi masaukinshi dake
cikin gidan, Tun zuwanshi aka gyara hakan yasa ya wuce bayi Don yin wanka. Gaba
daya zuciyarshi tamkar ana gobara haka yakeji , kenan rayuwarshi ta koma idan yana
neman abu bazai samu ba a wannan lokacin.

Ana gama lectures suka fito kamar Koda Yaushe dukda yanzun sun zama su uku don tuni
Khulthum ta cire kanta daga garesu, to ba kullum take Zuwa ba ma yanzun a sha ruwan
tsuntsaye take wa Zuwa makarantar.

Aimana tace da Sulaim Bayan sun Yi sallama da Khairi ta wuce hostel.

Kwana biu duk kin zama wata iri, Meye ne Ke damunki dan Allah?
Kallonta Sulaim tayi tace

Babu komai Aimana, kawai Kwana biyu Bana jin dadi ne.

Dama tasan bawai zata fada mata bane amma dole Tunda tare suke.

Kodai Salim dinne har yanzun?

Wata muguwar harara ta maka mata tace

Lallai ke dinnan, Salim kuma ni Sulaim ce ba Khulthum ba.

Dariya tayi tace

Haka ne kam, kinga muyi sauri saboda Yaya Nu'uman bazai zo ba.

Hakane kinga Yaya Yaje kaduna gashi bai ma kira yace min yaje ba.

Sulaim ta fada fuskarta dauke da damuwa. Kallonta Aimana tayi amma batace komai ba
har suka samu napep suka shiga zuwa gida. Koda Sulaim taje gida duk tunaninta zata
tarar Subay'a ta dawo amma ga mamakinta kofar parlonta a kulle, yaran suna zaune
suna kallo suna jiyo sallamar ta suka taho tarar ta. Rungumarsu tayi tana shafa
kansu tareda tambayar kowa school kafin suka raka ta daki Don yin wanka. Tana
fitowa taga kiran Imratu ita Duk tunaninta Junaid ne Tunda call dinsa take ta
expecting amma shiru, dauka tayi ta placing wayar a speaker saboda tana shiryawa.
Da wasa da dariya kamar yadda suka Saba suka gaisa sannan Imratu tace

Ke ashe Hajiyar gidanku Cyprus ta tafi karatu?

Cikin rashin fahimta Sulaim tace

Wace hajiyar gidanmu kuma?

Dallah, Subay'a nake nufi.

Idanu a waje Sulaim Cikeda mamaki tace Cy what? Dan Allah da gaske.

Wallahi, yanzun ya kira Soja yake fada mishi wai ya hanata Bayan ya tafi office ta
tafi.

Innalillahi wa Inna ilahil rajiun! Yaya Imratu Nikam a rayuwata I've never seen a
bad mother and wife kamar Subay'a ba. Ayya Shiyasa Yaya jiya Tunda na dawo gidan
daga school naga akwai damuwa tattare dashi.

Ba dole ba Sulaim, bari kiji abinda yasa na kiraki, kinga a yanzun babu Abinda
Papan Ahmad ke bukata Irin support, inason as much as u can kiyi supporting dinshi
ki bashi kulawar da ya rasa, ina son ki zame mishi sanyin idanuya Kina jina?

Baki Sulaim ta turo tace

Kai! Ni kuma a wa? Se kace matarshi.

Tsaki Imratu tayi tace

Matsala ta dake kenan taurin Kai, ai ya fadawa soja cewar yayi miki proposing kuma
bana son ki yaudare kanki kina son Papan Ahmad....

Ni kuma? Shi ya fada miki? Lallai ma Wallahi ba wani.
Seda Imratu tayi dariya yadda take so sannan tace

Hakan da kikayi ya tabbatar min zargin mu, Papan Ahmad bai san Kina son shi ba amma
shi Yana miki so me suna so, me tsanani wanda ya gaza boyuwa. Inason Kiyi amfani da
damar da Allah ya baki, ki bashi Abinda ya rasa cikin rayuwarsa.....

Kenan zan aureshi ba don so ba sedan Maye gurbin wata? Dama shi yasa yace Yana sona
jiya saboda matarshi ba Tanan?

Kai Imratu ta dafe saboda batai tsamannin abin zaizo haka ba.

Shekarunki Nawa sulaim?

Last month nake nineteen.

Ke Yarinya ce har yanzun, kiyi tunani sosae akan maganar mu, kuma inason Kisa a
ranki ko da Subay'a ko babu ita Junaid na sonki, he proposed jiya without knowing
ta tafi, ki sani ke kadai ce hope dinshi a wannan lokacin idan kika barshi then
Bana tunanin Kinyi mishi da kanki adalci.

Kafin Sulaim ta bata amsa ta katse call din, kasa tashi tayi daga gurin ta xurfafa
tunanin maganganun Imratu, tabbas ko haka bata faru ba Tana jin tausayin Junaid
tausayi me tsanani na gasken gaske wanda hakan shi ne Abinda ya fara saka sonshi
cikin zuciyar ta, to yanzun bazata iya ba kenan? Abubuwa nawa Junaid yayi mata,
wani Irin sacrifice ne bai mata ba, wannan kadai ya isa ya tabbatar mata Son gaske
yake mata. Tun rasuwar Daddy dinta komai nata shi ke daukar nauyinsa, cin ta, sha,
sutura da karatun ta. Ita kuma se ta kasa bashi farin ciki, ta kasa amsar
soyayyarshi. Da sauri ta girgixa kanta, ta Mike jiki a matukar sanyaye ta nemi
shirt da dogon wando ta saka sannan ta rufe kanta da hula.

Wayarta ta dauka ta kira Imratu tana picking murya a sanyaye tace

Yaya Ya zanyi to ?

Murmushi Imratu tayi tace

Kada kice mishi kin amince a baki, ki kyaleshi amma ki bashi kulawa yadda ya
kamata. Kin gane?

Kanta ta gyada tace

Inshaaa Allah.

Daga haka sukai sallama ta koma ta zauna ta Fara neman layin Junaid, cikin sa'a ta
shiga Sede yana kallon "Dove" kamar yadda ya saka mata tana kira amma ya kasa
picking saboda har lokancin Samasama yake jin kanshi kuma muryarshi da yayi magana
zata nuna halin da yake ciki. Ganin baiyi picking ba yasa ta hakura kawai Amma
hankalinta yana gunshi. A haka har dare yayi baiyi returning call din ba. Seda su
Ahmad sukai bacci sannan ta tuna da safe Jawad yace mata yana kaduna Don haka ta
Fara kiranshi.

Friend Yaya Junaid Yana nan?

Ta tambaya yana picking,

Kya Bari mu gaisa ai, Yana dakinshi na kai mishi ne?

Da sauri tace
Yes please!

Kashewa yayi ya nufi dakin da Junaid yake, Yana zaune kan carpet ya kurawa screen
din system dinshi ido ga abinci Kan tray an jera Amma bashida appetite din ci. Dago
idonshi yayi Wanda ya fara washewa Daga jan da yayi ya dubi Jawad da ya zauna
gefenshi yace

Sulaim tace na kawo maka waya zatai maka magana.

Kanshi ya gyada cikin sanyin murya yace

I'll call her. Seda safe.

Sallama yayi mishi ya tafi shi kuma ya kashe system din ya koma gado don kiranta,
har ta gaji da jira ta Fara chatting kiranshi ya shigo, wani sanyi taji ya mamaye
dukkan jikinta babu shiri ta saki murmushi sannan tayi picking.

My Dove, I'm sorry

Dukda bata san dalilin da yasa yake kiranta da Dove ba, amma she have already
fallen for the name! Bakinta ta turo tace

Bakaga call dina ba tun dazu? Baka kira kace kaje lapiya ba, Muhammad suna ta
tambayarka.

Murmushi yayi me sauti Wanda seda Tajiyo hakan yasa ta sake fadin

Murmushi kakeyi ma ko?

Hannunsa ya rufe bakinsa dashi yace

Come-on Dove nace I'm sorry ko, nazo na samu abubuwan da suka cushe min Shiyasa.
Duk yaran sunyi bacci?

Kanta ta gyada tace

sunyi bacci, ina Mami

Mami tayi bacci, smile mana

A'a

Ta fada Tana bata fuska, hakan yasa yayi dariya a hankali wadda ta ratsa sulaim har
Seda ta sauke ajiyar zuciya. Haka sukai taba hira kafin yace

Kiyi bacci, nayi magana Za'a zo daukarku gobe Inshaaa Allah. Nima very early zan
dawo. Good night?

Kanta ta gyada kamar yana kallonta tace

OK, night.

Daga haka sukai hanging kowanne zuciyarshi fes, musamman Junaid da yaji hankalinshi
ya Dan kwanta Don Yana ganin bazai samu matsala da ita ba, Mami ce damuwarshi.

Washegari bakwai ya fito cikin shirin tafiya, a parlor Baba ya samesu suna kallon
news din safe a Aljazira, seda suka gaisa yace

Zan koma Kano.
Baba ne yace

Da wurwuri haka? Abinci fa?

Kanshi ya girgixa yace

Se naje zanci.

Kai Mami ta girgixa tace

Zauna yanzun Za'a kawo breakfast.

Bai musa mata ba haka ya tankwashe kafafunsa Yana kallon news dukda hankalinshi
Yana kan maganar da sukai jiya amma su kuwa hirarsu suke tamkar basu san dashi a
gurin ba. Ba a jima ba aka kawo breakfast babu musu yaci sannan ya Mike yace

Zan wuce se next week zan kawo su duka.

Baba yace

Allah ya tsare

Mami tace

Ayi tuki a hankali, ka kula da kanka.

Murmushin jin dadi yayi sannan ya aje musu envelope ya kara musu sallama a ranshi
Yana fadin

Mami is using son da nake yiwa Sulaim ta hukunta ni akan tafiyar Subay'a.


Unexpected right? Mami ta bamu mamaki har ni kaina? Na aza zata amince Amma taki ga
Baba yaki magana. So Wacce shawara zaku bawa Junaid? Yana jira.......see you later

Team #Junaid and Sulaim#

Shatuuu ♥️
[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU*
34

✍️Shatuuu♥️


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


#⃣Shatuuu095@wattpad



CYPRUS


Kwanaki bakwai kenan da saukarsu Subay'a birnin na Cyprus, tuntuni aka kama musu
Dan apartment me dakuna uku dake Sulma itada mijinta sukaje shima zaiyi wani course
a can. Se apartment din da take yana facing nasu, kuma bashida Nisa zuwa makarantar
da suke. Tunda suka sauka a garin gaba daya hankalin Subay'a ba'a kwance yake ba,
Dama da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login