Showing 3001 words to 6000 words out of 121650 words

Chapter 2 - MACE A YAU by Shatuuu

Shatuuu   

12 May 2026

445

ko?

Idan ta tuna wannan jinta take burinta yana daf da cika, idan ta tuna makaranta
kuma university itadinma BUK tana jin kamar da saa aka haifeta

Abu daya zan rokeki, ki maida hankali Kiyi karatu, kada kina comparing kanki da
wasu kowa rayuwarshi daban Allah ya tsara mishi abu na karshe ki kula min da kanki
ki rike min alkawari.

Bata ce dashi komai ba Don alkawarin yayi tsauri Bata tunanin zata iya wannan amma
karatu confirm zatayi to dole ne ma ai duk kudin da ta kashe wajen registration da
komai tayi wasa ai kanta tayiwa.

Ranar ta kasance Monday...... Monday tushen aiki Formula uwar lissafi. Tun asuba
Sulaim ta farka, gaba daya kewar Mami take dukda Kwana biu da tayi amma ji take
tamkar sunyi shekara basu tare, sallah ta Fara yi sannan tayo wanka ta Fara
shiryawa tana yi tana azhkar har ta Kamalla ta Fara kiran Mami sede kafin ta kai ga
shiga Mamin ta kirata through her other phone, sun kusa 10 minutes suna waya Tana
sake mata nasiha da jin ko akwai wani abu amma tace komai lafiya, a haka sukai
sallama kafin ta fito parlour, lokacin shida daidai ta buga, parlon babu kowa amma
tana jiyo motsi Daga kitchen hakan yasa ta nufi can, yanmata ne guda biyu suna ta
aikin hada breakfast, da sallama ta shiga suma duka suka amsa suka gaisheta fuska a
sake, ta ja kujera ta zauna Tana bin movement dinsu da yadda suke aiki Cikeda
kwarewa da alamu dai sun samu training a wannan harkar, hira suke Yi suna sako ta a
ciki Jefijefi tana basu amsa a haka suka kammalla komai daidai shigowar matar
gidan, Tana Sanye da bakin skirt irin boutique dinnan daya Kama Nata jiki se top
Fara da matching waist coat a jikinta, kanta bakar hula ce, Tana shigowa gaba daya
sukai shiru tamkar ruwa ya cinyesu se gaisheta da suke, kamar kullum babu digon
wasa ta amsa se sannan Sulaim tace

Ina Kwana

Juyowa tayi ta dube inda Sulaim ke Zaune, ita bata Lura da ita ba ma kwatakwata,
Memakon amsa gaisuwar Tace

Me kike Yi anan? Aren't you going for lecture?

Kanta ta gyada tace

Na shirya kawai shigowa nayi.

Kafada ta daga Irin damuwarki ce ta dauki abinda zata dauka ta fice itama Sulaim
sallama tayiwa su Atika ta nufi dakinta ta shirya cikin simple gown ta lace, ta
hada komai cikin karamar backpack dinta ta fito parlour, wannan karan kusan tare
suka fito gaba dayansu har yaran.

Yaya ina Kwana?

Ta gaida Junaid wanda ya fito Yana nannade hannun rigarshi, with concern yace

Auta kin tashi Lapiya

Brightest smile ta saki tace

Lapiya lau Alhmdllh.

Basu Kara fadin komai ba suka nufi dining table inda Atika take tsaye Tana jiransu,
suna zama Muhammad ya tashi ya dawo cinyar Sulaim, kallonshi Subay'a tayi tace

Koma seat dinka.

Baki ya turo tareda kankame Sulaim, murmushin nan tayi ta shafa kanshi tareda rada
masa abu a kunne, take ya fara dariya hakan yasa Ahmad shima tasowa ya dawo
gefenta, cikin iyayen basu Kara fadin komai ba haka aka ci abinci wanda kusan Rabi
wasa ne tsakanin Sulaim dasu Ahmad. Subay'a ce ta Fara tashi tare da wiping bakinta
da saviette ta matso inda Junaid yake ta bashi peck a kumatu tace

Ni na wuce

Murmushi kawai yayi yace

All the best!

Thanks! Ahmad bye.... Muhammad be a good boy.

Daga haka ta zari key din motarta da handbag tayi waje abinta. Junaid ya kalli
Sulaim wadda tayi shiru deep in her own thoughts yace

Sakawa Muhammad uniform kuzo mu tafi.

Tohm Yaya .

Basufi 10 minutes ba suka fito shirinsu tsaf waya a kunnenta tana waya, tunda ta
fito Junaid Ke binta da ido har Seda ta gama wayar ta kalli gefenshi kafin yayi
saurin dauke idonshi, bata damu ba tace

Yaya we're set, ina Ahmad zai zauna.

Se yaji dadi ganin she's concern akan yaranshi yace

Nanny dinsa tana hanya ki barshi gurin cooks din can.

Cikeda gamsuwa ta wuce ta kaishi se kuka yake akan shi binta zaiyi, haka ta taho
tana jin wani iri cikin ranta.

Seda yayo baya ya sauke Muhammad a Al'azhar kafin ita dashi suka nufi new site,
kasancewar sune most reserve a yaran Mami yasa tafiyar haka akai yita shiru kamar
babu mutane. Cikin sa'a wayarta ta Fara ringing, hannunta ta zura ta ciro ta Daga
purse tana dubawa taga LUFF, se taji bazata iya picking ba haka wayar ta katse
Ja'afar ya sake kira anan ne Junaid ba tareda ya kalleta ba yace

Pick up your call.

Swiping tayi ta Kara kunnenta take Wannan muryar tashi me dadin sauraro ta Fara
zagaye mata ko ina na jikinta wanda take ya saka mata wani Irin shauki, ta tabbatar
Ja'afar is beyond words ya iya tafiyar da Wannan harkar.

Uhmmm ina Kwana?

Murmushi tayi ta kalla gefen Junaid wanda Baki daya hankalinshi a zahiri yana kan
titi ne amma a badini yana gurin Sulaim.

Eh muna hanya........ To zan kiraka Anjima a gaida Mami da Yaya Jawad.

Wannan furucin Nata ya tabbatar masa Ja'afar ne, maida wayar tayi handbag dinta a
haka suka isa Faculty of Law, wani Irin dadi taji a zuciyarta this is the beginning
of the journey......

Tare suka fito ita dashi, a nutse suke tafiya a haka ya rakata har class Seda ta
zauna kafin ya fita dama tun a mota yace Duk Abinda take so ta kirashi saboda shima
a Faculty yake.

Ranar Bata wani Saba da kowa ba, taji dadin classes din musamman na English for
legal writing, amma logic dinnan ne se a hankali. A haka ranar ta Kare Junaid ya
dawo daukarta batareda ta Saba da kowa ba don Tana ganin is too early ta samu kawa.

*I've seen every of your prayers, your comments and wishes. I'll forever remain
grateful...... But dont be xpecting post everyday because I've so many things to
attend to but will try my every best to see that I didn't keep you
waiting......Thanks for understanding*

Shatuuu ♥️
[6/20, 11:56 AM] +234 701 517 3116: *MACE A YAU!*

3

✍️Shatuuu ♥️

Shatuuu095@wattpad

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
Tunda me napep ya direta a layin da zata shiga gidansu kasancewar machine ne kadai
yake iya shiga shida keke cikin kwanciyar hankali amma sauran kam sede addu'a
saboda yadda kwata take cike ga kuma tsuku da gurin yayi kowa yasan idan akace
Rimin kebe a kano Irin merciless ghetto area dinnan to nan gidansu Khulthum yake,
tunda ta sakko mazan dake zaune yan kashe wando suke buga ihun

Talaka me girman kai.......

Se wasu suce

.......Allah zai kona shi.

Sarai tasan da ita suke da Wannan sabon su ne har ta Saba, haka ta ratse ta wuce,
gaba daya yau bata wani fahimci karatu ba saboda yadda take kalle kalle tun kafin
ta shiga class taga yadda yara kanana suke zuwa cikin manyan dankara dankaran
motoci, shiga iri iri ta Kece raini se taji tamkar kowa ita yake kallo a gurin, ga
hottest phones da ta dinga gani a hannun mutane ita kuwa tata Nokia torch light ce.
A haka ta isa gida amma Tun Daga nesa ta hangi Ashir a tsaye da dukkan alamu ita
yake jira , se taji for the first time ta rainashi taji bata tunanin tana ganin
Irin wannan mazan a waje zata iya Auran Ashir ta cigaba da zama ghetto gaskiya ina,
yadda ta tashi cikin talauci gaskiya ba zata dawamma a cikinshi ba no! And never!
Tana zuwa inda yake ta tsaya tana dubanshi shima kallonta yake yana mata murmushi,

Duk gajiyar ce haka ko gaisuwa ban samu ba, bare Ayimin murmushi

Murmushin ta danyi tace

Na gaji Wallahi, ruwa kawai nake son naji a jikina.

Kanshi ya gyada yace

Bari na barki ki shiga gida dama zuwa nayi na ji yadda ramar ki ta kasance, amma
anyways gobe ki shirya da wuri zanzo na kaiki....

Ina?

Tayi saurin tambaya, dariya yayi yace

School mana Tunda munada machine inaga zai rage kudin xirga xirgar

Da sauri ta girgixa kanta tace

A'a dan Allah nagode, Dan Allah Kada ka gwada hakan, I'll be OK hakan nan.

Bata jira abinda zai kara fada ba ta shige zaure a ranta tana fadin lallai Ashir
Bakada hankali wasu na Zuwa a mota kawai se a ganni kwam kan Lifan Haba dai! Allah
ya kiyaye. Shikam baki bude ya tsaya Yana mamakin sanyin Khulthum, hakan nan dai
jiki babu kwari ya burga Lifan dinsa ya wuce.

Zaune ta samu Mama da Aisha se Amir suna hira, gidan kalkal yasha Shara gwanin
shaawa saboda daga Mama har yaran babu Wanda zakaga element na kazanta a tattare
dasu, shikanshi simintin dake malale tsakar gidan an wanke shi tas se kyalli yake,
dama bawai tana sallama bane Tunda ba koya maka akai ba kuma baji take a Nayi ba
balle tayi picking, haka ta shigo kadaran kadahan kana kallonta kasan rana ta
daketa ga gajiya da tayi mata rubdugu, gefen dakin da suke Kwana ta zauna wanda
kusan nata ne ma kawai Kwana kawai yaran keyi amma baki daya kayansu da komai yana
dakin Mama saboda Khulthum ta kafa ta tsare.
Da kulawa Mama tace

Khulthum an dawo Daga makarantar.

Fuska ta yatsina tace

Mama akwai wahala.

Murmushi Mama tayi tace

Se hakuri, Aisha tashi zubowa Yayarki abinci.

Turo Baki A'ishan tayi tace

Mama ita taje ta zuba da kanta mana, Kinsan ko an zuba mata zatace ba zata ci bane.

Mama tanada wani abu matsawar ta saka Abu ka Kiyi to tabbas zata tashi tayi da
kanta, Sede abinda ka koyawa yaro shi zai tashi dashi don kuwa ance Tun ranar gini
Tun ranar zane, idan baka aje ba Kada Kace zaka dauka. A wannan zamanin kayiwa
yaranka tarbiyya ma ya aka Kare balle Bakai ba, tashi tayi da kanta taje kitchen ta
zubo mata abinci ita kuwa tana zaune ta harde kafarta se cika take tana batsewa,
saboda yadda Khulthum bata fara'a ko tayi kwatakwata Bata mata kyau, mutum ce da
bata fara'a a cewarta gwara ka tsare gida saboda gudun raini, gata da girman kai
kuma haduwar ku ta farko kallon kaskanci Xata fara Yi maka not knowing dukkan
kaskanci a kanta ya kare, haka babu wata muamala me kyau tsakaninta da yan uwanta,
idan tayi musu magana to tabbas aike ne ko rashin mutunci.

Mama na kawo abincin Khulthum ta yamutsa fuska tace

Mama wannan ne abincin?.....Innalillahi!

Ta dafe kanta, kallonta duka sukeyi babu wani mamaki a ciki don wannan shi ne least
abinda Khulthum zata iya yi Balle yau Baba bai bada kudin cefane ba haka ya fice
Don yace shi ko sisi bai Kwana da ita a jikinshi dama gurinta yake karba idan Irin
haka ta faru to Tun safe ta tafi makaranta hakan yasa ya fice abinshi itakuwa Mama
ta sirfa gero ta hada da wake ta dafa matsayin kundin kaza. Kafin Mama ta fadi wani
abu tuni Khulthum ta shige daki, se gata da kwano ta fito hakan ya tabbatar musu
abinci zata siyo,

Wallahi Mama duk laifin kine abinda Khulthum takeyi, kawai saboda Bakuda kudi mu
talakawa ne shi ne take Wannan rashin mutuncin, kina kallo ta fita Siyan abinci
amma kin kasa magana, Haba Mama!

Amir ya fada bayan fitar Khulthum, Aisha ce tace

Wallahi kua talauci ba hauka bane kawai don Bakuda kudi se ya zamana shi kenan se
ta dinga juya Ku? Kun kasa yin komai kun zuba mata ido.

Nanma har Aisha da Amir suka gama 'yan mitocinsu Mama batace uffan ba. Babu dadewa
Khulthum ta dawo da abincinta me rai da lafiya.

Safiya ce ta asabar, gabaki daya gidan yayi shiru kasancewar kowa hutawa yake, a
hankali aka turo kofar dakin na Sulaim inda take kwance saman gado tayi daidai, a
hankali Atika ta Dan taba ta, dake baccin bayan asuba ne ba wani Nisa yayi ba hakan
yasa ta bude idonta, se kuma ta rufe idon saboda yadda hasken yayi mata yawa, a
hankali ta sake budewa lokacinku ta gama adjusting to rays din.

Ina Kwana Anty Sulaim.
Bata fuska tayi tace

Atika lapiya dai ko?

Kanta ta gyada tana kuma murmushi tace

Lapiya lau, an gama breakfast.

Hannunta ta daura a kai tace

Amma Atika se a barki, ina bacci......

Se kuma tayi shiru kawai kafin tace

Ina fitowa.

Daga haka Atika ta fice Sulaim ta sauka tayi brush sannan ta wanke fuskarta ta zura
hijabi ta fito, Ahmad da Muhammad na parlour sunyi wanka an saka musu kaya me kyau
Wanda zai baka clue din fita zasui, suna jin sallamar ta suka nufe ta inda ta tsaya
tana jin maganganun su Tana dariya, a haka Junaid da Subay'a suka fito, hannunsu ta
rike baki bude tace

Yaya good morning, Ina Kwana Anty.

Seda ya kare mata kallo wanda idan bawai kana kallonsa bane ba zaka fahimta ba
kafin yace

Morning Sulaim

Subay'a ya kalla wadda Baki daya hankalinta yana kan Ahmad yace

Suby answer her.

Dago kanta tayi ta kalli Sulaim wadda itama kallanta take, ciki ciki tace

Lapiya.

Tana rufe bakinta Atika ta iso ta fada musu an gama komai, tare suka jera zuwa
dining, Atika ta bubbbude warmers da plates din, babu inda Subay'a ta sauke idonta
se akan danwaken dake gefe,

What nonsense is this Atika?

Ta fada Tana daga murya hakan yasa gaba daya kowa hankalinshi ya koma kansu,

Dan wake? Wayace kiyi.

Sulaim ce ta dubi Subay'a tace

Ni na saka Ayimin Inaso zanci.

Wani kallo ta watsa mata yayinda Atika jikinta ke rawa don halin Subay'a bbu wasa,
Dama seda ta fadawa Sulaim strictly ake bin timetable din ba'a canjawa se da
izinina Subay'a amma tace itadai ayi mata

Wayace miki ana canja mana tsarin timetable dinmu? Wa ya Baki izinin ki bawa cook
dita order? This is.......

Meye haka Subay'a? Bana son irin haka, Bana so kowa Yana da right ya zabi abinda
zaici, ba dole Se wanda kika gindaya ba.

Junaid ya katse ta, iya kulewa takai , take ta aje spoon din hannunta ta koma daki,
bai kara fadin komai ba, itama Sulaim din se taji komai ya fita mata a kanta hakan
yasa ta Mike da nufin komawa dakinta Amma tana aje wannnn spoon din taji wannan
sharp eyes din da duk duniya bata tunanin akwai Wanda kallonsa yake affecting dinta
kamar Junaid ba, kallonshi is skin piercing se ya tsaga dukkan fatar mutum ya shiga
jiyoyinsa, kallon yasa ta duburburce ta Fara fadin

Yaya bari nayi wanka......

Kici abinci tukun

Ya fada a nitse amma muryar kawai zatace maka order aka bayar, haka nan babu yadda
zatayi ta zauna taci abinci, dake wasu abubuwan Sulaim exactly Irin na Junaid take
hakan yasa seda Subay'a ta fito basu gama breakfast ba, gefenshi ta tsaya tace

Zamu wuce.

Ba tareda ya kalleta ba yace

Allah ya kiyaye.

Itama been the Subay'a yasa Bata bi takanshi ba taja yaranta wanda tuni suka gama
shiryawa don al'ada ce duk wata Saturday din duniya zata tafi gidansu wanda ke
Magajin Rumfa a cikin kano. Amma daga aurenta zata iya irga sau nawa taje Kaduna
gidansu Junaid, bai taba mata maganar hakan ba Sede ya kwashi yaran Yaje dasu. Shi
ya fara gamawa yace

By 2pm zan fita idan zaki bini to?

Agogon dake jikin bango ta kalla, karfe Tara da yan Mintina hakan yasa tace

Allah ya kaimu.

Daga haka suka koma dakunansu, wanka ta Fara yi ta Nemo kayanta ta aje, gado ta
fada ta janyo system ta Fara kallon Indian film na We're Family tana kalla tana cin
popcorn, a haka har tazo karshen film din, yadda Kajol take bankwana da yaran yadda
duk yadda take son yaran, take protecting yaran, take basu dukkan wata kulawa da
soyayya ya tsinka zuciyar Sulaim gashi ta mutu ta barsu, haka kowacce uwa Ke son
danta? ai kawai se ta tuna Mummy da Daddy dinta, kawai se ta kifa kanta ta Fara
kuka tamkar yau aka dakko ta Daga makaranta akace sun rasu haka abin ya dawo mata
sabo dal, ta dinga kuka Tana Shesheka I missed you Daddy and I missed you Mummy....
Allah ya haskaka kabarinku. Tafi Mintina talatin tana Abu daya kafin ta tashi ta
nufi bayi ta wanke fuskarta sannan tayi sallah ta daga hannunta sama cikin
kaskantar da Kai tace

Allah ni baiwar kace me tarin kurakurai, Allah ka gafarta min ka haskaka kabarin
Mummy da Daddy........

Se kuka ya kara kubce mata, ita kanta tasan ba karamin kokari tayi a rayuwarta ba
at this tender age ace ba tada Uwa bare Uba. A hankali ta kifa kanta kan gadon Tana
sauke ajiyar zuciya a hankali bacci ya dauketa, cikin baccin taji ringing din
wayarta hakan yasa a firgice ta tashi se taga sunan Junaid hakan yasa ta Mike zuwa
gaban dressing mirror tana kallon fuskarta ko yaro ya kalleta yasan Tasha kuka
Balle Junaid, khol ta murza a idon ta dauki shade ta saka ta fito. Tunda ta fito ya
maida dukkan hankalinshi kanta, Abun da yafi burgeshi da Sulaim shi ne tafiyar ta
yadda take tafiya a hankali Cikeda nutsuwa babu hargowa a ciki shi yake burgeshi.
_Your gaze Junaid it's Haram!_

Inner self dinshi ya fada mishi hakan yasa yayi kasa da kanshi, itama shade din da
ta saka shi ya bata damar kare mishi kallo, as usual kananan kaya ne jikinshi short
sleeve top se denim jeans da wrist watch me kyau da ya dace da fatar Hannunsa yayi
masa kyau, Tana zuwa gabanshi ya Mike ta biyo bayanshi har mota babu Wanda yace
uffan, seda ya hau titi sannan yace

Remove those shade zasu hanaki ganin hanya.

Babu musu ta ciresu cikin sa'a ya sauke idanunsa a kanta, take gabanshi ya fadi
ganin yadda idanunta sukai swollen, gangarawa yayi gefen titi yace

Meye samu fuskarki? Me ya sakaki kuka.

Ai kukan da ya ambata se ta kuma sakin wani she's missing them shekaru biyar kenan
amma kullum tana jin mutuwar sabuwa a ranta. Gaba daya hankalin Junaid ya tashi
yayi juyin duniya taki magana, yayi lallashin har ya gaji amma taki tayi shiru
hakan yasa yayi dialing number Mami, Tana dagawa ya fada mata Abinda yake faruwa
aikuwa tace ya hadata da Sulaim din, jin muryar Mami ya kara tada mata hankali
hakan yasa abinda ta Fara cewa

Mami I'm missing you!

Murmushi Mami tayi tace

Shiyasa kike kuka? Idan nayi miki aure kuma fa? Shima kuka zaki dinga yi idan kina
son ganina? Kiyi hakuri next week zanzo gaisuwa kanon nida Babanki, is that OK?

Kanta ta gyada taji dadi kuma hawayen suka dauke Allah ya mata replacing Mummy da
Mami , Daddy kuma da Baba. Seda ta tabbatar ta daina kukan kafin tayi magana da
Junaid, haka suka cigaba da tafiya jefi jefi yana mata tambayoyi dukda yawanci akan
makaranta ne. Acan kuwa Mami tana tunanin dalilin kukan Sulaim don tasan tana
missing dinsu amma bazaiyiwu ace shi ne yasa take Wannan kukan ba kuma daga
muryarta kasan ta jima tana yi. A haka dai ta hakura akan koma Menene idan tazo
zata gani. Ranar Junaid da Sulaim sun Sha yawo se maghariba ya maida ta gida Har
lokancin subay'a bata dawo ba.

Shatuuu ♥️
[6/21, 8:05 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU!*

✍️Shatuuu ♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad

Birnin kudu local government ce a jigawa state kuma tana karkashin Dutse emirate,
yawancin mazauna garin Fulani ne se kuma hausawa, garin suna da duwatsu da kuma
Nono. Malam Muhammadu shi ne sakataren local government a wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login