Showing 60001 words to 63000 words out of 121650 words

Chapter 21 - MACE A YAU by Shatuuu

Shatuuu   

12 May 2026

449

su Ahmad
gidansu.

Unbelievable! So take ta yadda da Abinda Junaid ke fada mata what if I love her
zaki hanani aurenta?

Kenan kana sonta?

Ta Kara tambayarshi idanunta jawur, Baice da ita kanzil ba ya cigaba da Abinda yake
a ranshi Yana Allah Allah Sati ya cika su koma Nigeria ya bawa kanshi 'yanci.

Yana fita sallar maghrib ta wuce balcony tayi dialing number Hajiya seda ta katse
ta Kara bugawa kafin ta dauka tana korafin me ye yasa Tun dazu bata kira ba.

Hajiya ki bar maganar kawai.

Se kuma ta Fara kuka sosae tana jin zuciyarta tamkar zata fito Daga kirjinta. Tsaki
Hajiya tayi Subay'a tace

Hajiya kinsan Junaid......

Ya isheni Malama, bakida aikin da ya wuce complain Karki tashi ki kwatarwa kanki
'yanci kiyi ta zama Tunda ke shashasha ce. Kuma maganar tafiyarku Keda su Samiha
tana nan, visas dinku gaba daya are ready se kisan yadda zakiyi.

Hajiya ni bazanje ba gaskia....

Ke Subay'a ki shiga hankalinki ranki zai baci, ubanwa nake yiwa gata idan baku ba?

Hajiya dan.....

Se Anjima ta kashe wayar, shiru Subay'a tayi tana ta tunani yadda zata bullowa
Junaid, tasan future impossible shi ne yardar Junaid Amma ya zatayi hajiya fa? Her
only happiness!



Shatuuu ♥️
[7/29, 4:30 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU*
29

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad



Two weeks Later!

Hannunta ta dauraye a sink din toilet sannan ta goge da towel tareda kallon kanta
jikin mirror tayi murmushi sannan ta fito ta dauki handbag dinta da key din mota ta
fito, Ahmad da Muhammad na Zaune suna kallon cartoon se Atika dake gyaran parlon
saboda gama lunch dinsu kenan.

Anty zanje

Muhammad ya fada Yana daga mata hannu, kanta ta dafe tace

Yanxun zan dawo kunji, me zan siyo muku?

Kuka Muhammad ya fara hakan yasa dole ta koma dakinta ta dakko musu kaya ta Fara
canja musu. Tana gamawa suka fito tare Tace da Atika

Duk abinda ya kamata dan Allah ayi bazan dade ba.

Kanta ta gyada tace

Allah ya kiyaye hanya uwar dakina.

Murmushi Sulaim tayi ta fita zuwa mota. Yau Baki daya bata fita ba ta dan kwana
biyu Bata fitan ba kasancewar Ahmad bashida lapiya yayi reacting ma man shanu, Seda
sukaje asibiti anan aka fada mata yana da allergy da man shanun. Don Haka har
daukin fitar take uwa uba gobe gwarzonta Junaid zai dawo Tana jin kamar yau din
Bata sauri Shiyasa Tun safe suke aikin gyara da share sharen gida, yanzun ma
shopping zataje don so take ta fara aiki yau dinnan.

Shoprite suka Fara zuwa tayi siyayya yadda ya dace sannan suka fito ta dubi Ahmad
tace
Waye zaisha ice-cream?

Ni!

Duka suka fada, dariya tayi tace

Bari muje See Sweet muci burger.

Daga haka ta cigaba da driving ta saka wakar Celine Dion ta That's the way it's!
Tana son wakar saboda tana kara mata courage akan son Junaid da take.

To bansan yadda zan kira zuwan Sulaim See Sweet ba, Zamu iya kiran abun tsautsayi
ko karar kwana. A parking space dinsu tayi parking ta fito suma su Ahmad suka dafo
mata baya Sede kafin ta shiga hankalinta ya kai kan wata karamar kyakyawar farar
mota anyi parking nesa da tata, ta kusan minti uku tana son tuna me motar, cap ta
tuna ita ce motar da Salim yaje gurinta dashi a Jega. Kenan he might be in.
Murmushi ta saki at least sun Kwana biu basu hadu ba dukda ya rage kiranta a waya
da Kuma yawan zaryar da yake mata a school, if she can remember rabon da su hadu
Tun ranar da ya bawa Khulthum Lift bai kara Zuwa gurinta ba.

Kanta ta girgixa ta rasa me soyayya take nufi da ita, shikenan da an faro ringidi
ringidi se gayyar ta watse, ranta a jagule tuna son Wanda bai ma San tanayi ba da
take ya kara bata ranta. Da suka shiga da kanta tayi order suka zauna suna ci. Suna
gamawa ta Mike Don ficewa wayarta ta Fara ringing hakan yasa ta koma ta zauna
tareda karawa a kunne tace

Yaya Hanan

Daga Dayan bangaren Hanan tace

Sulaim yakike

Lapiya lau Alhmdllh, Yasu Alhaji Tsoho?

Duk suna lapiya

Ta bata amsa sannan tace

Baki bawa Ya J sakona ba?

Waye Ya J?

Sulaim ta tambaya with confusion don da gaske bata gane ba

Come-on Ja'afar nake nufi

Gaban Sulaim ya fadi jin ta ambaci Ja'afar Lokaci daya taji ranta ya baci tuno
artabunsu shima bai kara nemanta ba Abinda bai taba yi ba a tsawon soyayyarsu no
matter who's at fault Ja'afar zai sakko ya Bata hakuri Amma wannan Karon bai kuma
duba inda take ba. Tun tana saka idon ko zai kira har ta hakura Sede she's lonely,
her heart is lonely she needs someone.

Ki tambayeshi mana, ni zan rike miki abu ne.

Tana fada ta kashe wayar tare da kokarin mikewa amma hakan ya gagara sakamaakon
mugun ganin da idanunta sukai. Idanu ta zaro Don tabbatar da Abinda Ke gabanta Amma
the image seems Kai is real kawai, Khulthum ce cikin fitted gown kanta babu
dankwali se fixed hair da ta zubo har bayanta, fuskarta completely dolled up Tana
ta dariya hannunta rike da na Salim wanda yake cikin Denim jeans da top yayi kyau
sosae kunsan yadda mutumin yake se Sulaim take ganin tamkar an dada mishi kyau ne.
Shima dariyar yake yasa Dayan hannunshi ya rungumo Khulthum zuwa jikinshi suna
sakkowa daga upstairs Din, haka suka wuce ta don da duka zaa Tambayesu bana tunanin
sunsan da wanzuwar halitta a gurin.

Kanta a take ya fara sarawa idanunta sukai ja, zuciyarta tana bugawa da sauri da
sauri kamar zata fito Daga thoracic cage dinta. Tafi 15 minutes kanta a kasa kafin
abinda take ji ya sassauta saboda kiran sunan Allah da takeyi. Hannun yaran ta Kama
suka fito se surutu suke mata amma ina bata hayyacinta. Daga haka ta saka kurani
tana saurare har sukaje gida. Booth ta bude me gadi ya fito da kayan sannan ta
kulle motar ta nufi ciki hankalinta har lokancin bai gama dawowa jikinta ba.

Atika shigo da kayan ciki, zan dan kwanta Zuwa anjima mu fara aiki.

Kanta ta gyada ta fita ita kuma ta kunna musu cartoon channel sannan ta shige
dakinta ta fada gado tayi rub da ciki!

Tana kan sallaya tana addu'a Allah yasa dukkan abubuwan da suke faruwa cikin
rayuwarta ya zama mabudin bude kofofin alkhairi. Knocking akai hakan yasa ta
karkare adduar ta fito, Atika ce rike da Muhammad wanda yayi bacci, sulaim tace

Ya akai yayi bacci ai kuwa my baby you're going to wake up yanzunnan.

Hannu tasa ta karbeshi ta nufi parlour dashi dake ta gefen dining area dinsu akwai
sink nan taje ta wanke mishi fuska, Yana bude ido ya bare baki don yin kuka tace

Yi hakuri babyn Anty muje na baka sweet kaji but don't sleep.

A kafadarta ta dora shi Ahmad na rike da hannunta har lokancin ita daya tasan
Abinda takeji a zuciyarta amma haka dole ta yakice abin ta nufi kitchen dan fara
aiki. Kan working space ta daurasu duka ta ciro candy ta basu suka Fara aiki itada
Atika ita kuma Laraba tana gyara abubuwa da yanke yanke. Seda komai ya zama ready
Washegari akan ta harhada abubuwa. Da wurwuri ta kwanta Don yaran ma tuni sunyi
bacci itama tana son kadaici tana son yin tunani Bata taba tunanin Khulthum zata
iya abinda tayi mata ba amma wata zuciyar tuna mata take matsayin Khulthum din a
gareta. Ta dade kafin bacci me nauyi ya dauketa.

Asubar fari ta tashi da dama dama saboda murnar dawowar Junaid, wayarta ta dauka ta
Kara duba arrival time dinsu daya turo mata 9am. DA sauri ta karasa kitchen ta Fara
aikinta har takwas da Mintina kafin ta kammalla ta wuce daki dama tuntuni an shirya
mata su Ahmad hakan yasa tana fitowa ta dakko Wannan sabon farin lace da cone
pattern baki a jiki, dinkin skirt da Riga ne, har ta ware se ta jingina da jikin
bango tana tuhumar kanta dalilin da yasa zatayi kwalliya har haka? Mijinta ne? Ko
saurayinta ne? None of the above so meye abin zakewa kawai se ta mayar ta dakko
gown na atamfa milk da red. Tana gama shiryawa wayar Aimana ta shigo, da sauri ta
dauka gabanta na faduwa don batasan Abinda zai fitar da ita

Aimana how far?

Test din Family Law Nanda 30mins kiyi sauri.

Oh no! Ta furta ranta a bace amma ya zatayi haka ta dauki key da veil da Jakarta ta
fito gaskiya an karya mata budget da yawa.

Atika test gareni na fita, nasan su Yaya sun kusa Dan Allah komai ya zama in place.

Kanta ta gyada tace

Se kin dawo.
Waving tayiwa yaran ta fice cikin hanzari, ranta duka a jagule kamar zatayi kuka.
Tana yin parking ta fito sega wasu yan mata su biyu suna tsaye ko abu suke jira
oho. Tana fitowa dayar tace mata

Dan Allah ke sister Dr Junaid ce?

Kallonta Sulaim tayi, irin Ajebos dinnan ne yar gayu kana kallonta kasan naira ta
Jikata yadda take magana kadai abin kallo ne.

Me ya faru?

Ta tambaya Tana kare musu kallo har yar rakiyar.

Dama ina crushing dinsa ne so please ko zakiyi hooking dinmu up?

Batace komai ba saboda abinda zai fita a bakinta ba Mai dadi bane hakan yasa ta
gewaye su zata wuce, dayar tace

Please mana help a soul, Munga Kuna Kama sannan ga motarshi Kina zuwa da ita.

Ta fada Tana nuna motar da hannunta, juyawa tayi tace

Mijina ne ba yaya na ba!

Gaba daya suka zaro ido tare da kokarin kare kansu ta wuce ta Barsu a gurin gwiwa a
sake, ranta a matukar bace ta shiga cikin class din, ina irin yanayin da Kake jin
tamkar kowa da komai is against you, irin you're helpless haka ta dinga ji idanunta
sukai ja tamkar me shirin kuka. Idanunta akan Khulthum dake gefen Khairi ya fara
sauka, Tana zaune Tana duba wayarta, yi tayi kamar zata wucesu se ta fasa ta dawo
ta zauna kusa da Aimana, kafin suyi magana Dr. Halliru me family law din ya iso,
babu bata Lokaci aka Fara test, test din tayi wuya duk yadda kayi karatu hakan ya
karawa Sulaim tension. A haka aka kammalla ya karba sannan ya fice, mikewa tayi Don
tafiya taji Aimana na fadin

Ki zauna akwai mood trial Anjima.

Kanta ta dafe tace

Tafiya zanyi kice banida lapiya.

Hannunta Aimana ta rike tace

Zauna Sulaim me yene yake damunki?

Shi ne furucin da bata so idan tana cikinhi damuwa aikuwa se hawaye da sauri ta
tsugunna don Bata son wani yaga halin da take ciki, Aimana ta damke hannunta
batareda tace komai ba su kuwa su Khulthum suna ta faman instagramming so basu lura
da halinda ake ciki ba. Seda ta sha kukanta kafin ta Mike fuskarta a rufe ta fita
don wanke fuskar at least taji dan sanyi cikin Zuciyata she have let out some
emotions. Ruwan hannunta tasa ta wanke fuskarta sannan ta dawo ciki kafin ta karasa
ta hangosu sun nufota itama bayansu tabi anan Khulthum ta kalleta ta tabe Baki tace

Ke kuma yau me ya sameki kike bata rai.

Aimana tayi saurin fadin

Batada lapiya ne.
Allah ya sawwaqe.

Ta fada itakuma khairi ta juyo tace

Ayya kanwar Yaya sannu.

Kanta ta gyada musu har suka isa joint din da suka saba cin abinci. Khairi ce tayi
placing order yayinda Sulaim ke mamakin sauyawar Khulthum akanta, tabbas tayi
mamaki ba kadan ba ta yadda Khulthum tayi watsi da ita Abinda bata taba ba kenan,
kowa yasan yadda Khulthum da Sulaim suke different Womb sisters.

Seda sukaci abincin sannan Khairi ta Fara magana tace

Tohm, kowa ya bani hankalinshi nan saboda muhimmiyar magana zanyi.

Babu Wanda baiyi complying ba saboda Khairi is always not serious amma duk
lokacinda tayi magana a nutse to tabbas she's serious.

Seriously, banji dadin Abinda ya faru ba, cikin class kowa se ya nuna mu saboda
friendship dinmu Tun level 1 amma se kawai abu ya shigo ciki na cin amana da
yaudara.

Tayi shiru Tana binsu da ido, Khulthum tace

Malama ki fadi Abinda zaki fada mana.

Kallonta tayi tace

Komai a kanki ne Khulthum, ta yaya kina kawar Sulaim ki kwace mata saurayi?

Da sauri Sulaim tace

No please Khairi.....

Da sauri Aimana tace

What the hell? Khairi da gaske?

Khulthum dake binsu da kallo tace

Eh da gaske ne! Se meye a ciki?

Khairi tayi mata kallon wulakanci tace

Se jin kunya, Wallahi kinji kunya ki rasa ......

Ke rufewa mutane Baki kija gefe, ina ruwanki Naga zan iya ne.

Sulaim ganin attention din mutane zai dawo kansu ga Khulthum ta Fara daga murya
yasa tace

Dan Allah magana ya wuce indan Salim ne let her have him Sede abu daya na sani,
Salim is a bad person Tunda zai iya ketare dangantakar mu yayi soyayya dake. Have
him sannan ki sani Salim bashi ya hada mu ba Allah ya hadamu.

Khulthum cikin ranta taji babu dadi sosae saboda bata taba tunanin haka Sulaim
zatayi reacting ba, amma bata nuna ba se ta Mike tace

Ai na fada muku Duk wadda tayi sake da nata sede wani bashi ba, Sulaim Allah ya
bada karfin zuciya

Tana fada ta fice, khairi ta Mike zata bita Aimana ta hanata, Duk sukai shiru ranar
haka aka tashi babu dadi kuma taki basu fuskar yin magana ma. Ana gama mood trial
kowacce ta fito sukai sallama ta shiga mota ta nufi gida, farin cikin da take ciki
ilahirin shi ta nemeshi ta rasa kuka kawai take son tayi ko taji sanyi Amma ya
kamata ta isa gida kilan idan taga farin cikin rayuwarta ta ji sanyi.

Honk tayi Baba ya bude mata ta daga mishi hannun ta shigo inda ta samu motoci kusan
hudu tasan 'yan sannu da zuwa ne. Parking tayi ta fito Tana sauke ajiyar zuciya,
nan aka bude kofa Subay'a ta fito tayi kyau se kyalli take ga haske da ta kara tayi
kubul jikinta, take wani kishi ya dirar musu lokaci daya, bayanta yan uwanta ne su
hudu Baki daya suka saki Baki suna kallonta lokacinda take rufe motar Junaid din.
Dauke kanta tayi ta nufo inda suka ja tunga tamkar masu jiranta. Dama ranta a bace
yake hakan yasa ko inda suke bata kalla ba ta gebare su tayi ciki. Salima wadda
karo na farko da ta Fara ganin Sulaim tace

Wacece Wannan yarinyar Subay'a?

Cikin Bacin rai tace

Sulaimi ce kanwar Junaid

Bata ganmu bane? Idan idona daidai ya nuna min kamar motar Junaid na gani a
hannunta.

Surayya tayi dariya tace

Subay'a da gaske ne? Ko kuwa hallucination nake motar mijinki a hannun wata?

Samina tace

Ku muje Dan Allah, ko bakuga kallon da take mana ba .....

Na yan iska ko?

Suhaila ta fada muryarta Cikeda tsanar.

Mu fara kashe kurar dake gabanmu kafin mu dawo kanta. Ku muje.

Haka suka wuce suka bar Subay'a tsaye tamkar mutum mutumi, Tunda suke da Junaid bai
taba ko da wasa bata motarshi ba amma gata hannun Sulaim Wallahi yau ko ita ko
sulaim.

A ciki kuwa.........


Who wants to know wani Irin kallo zaayi tsakanin Junaid da Sulaim? Don't miss it
out! Ga Junaid ya dawo will he let the word out? Meye Subay'a zatayi kuke ganin?


Shatuuu ♥️
[7/30, 10:36 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU*
30

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad


Hey pipu.....I'm sorry for the late update, wallah yau kam I was so busy ne....
Amma gashi na baku sleeping mate, I hope everybody will enjoy it!



Na taba fada muku yadda Sulaim take? OK let's go Sulaim is an Epitome of beauty
kyakyawa ce ta gasken gaske. Fara ce fari me sanyi me kuma haske bamai dau ba,
saffa saffa. Fuskarta oval shape ce wadda ta samu brows me cikakken gashi baki
wuluk tamkar anyi shaping haka girar take wadda saboda yadda gashinta na kai yake
har goshi yasa yake neman haduwa da girar fuskarta. Idanunta suna da haske me
rikitarwa, idonta nada girma amma saboda yadda suka Saba da kuka yasa ba a ganin
girman saboda bata ware su da kyau se on special basis. Hancinta Mashaaaa Allah
very pointed me kyau Wanda yayi fitting fuskarta, bakinta ba me girma bane daidai
yake, lebenta sirara masu taushi, Tana da wushirya me Dan girma sannan da both side
dimples. Sulaim ba gajeriya bace doguwa ce saboda ta gaji tsayi daga gurin Daddy da
Mummy Baki daya, jikinta me kyau ne well shaped Sede tsayinta ke boye kirar ta ta.
Sulaim mutum ce very gentle, Tana da nutsuwa sosae, Tana da addini sauran kunfi
kowa sanin su!

A hankali ta cigaba da takawa zuwa parlon, fuskarta babu walwala ga gajiya da tarin
kunci da suka mata kakanakayi, sede gabanta babu Abinda yake banda faduwa sosae,
zuciyarta ta tsananta bugawa ga dauki. Tana yin sallama sassanyan kamshin Fierce
cologne by Abercrombie and Fitch yayi mata sallama wanda ya tabbatar mata
mamallakin turaren na gurin, cikin nitsuwa ta dago idonta ta dubi kujerun parlour,
Yana zaune idanunshi a kanta Wanda ko kyafta idon ya kasa samu yayi, tamkar an
canza ta haka yake kallonta ko kuma bai taba ganinta ba se ranar. Tayi mishi haske
dukda rama da tayi amma idanunta kadai shows farin cikin da Bata taba tunanin zata
tsinci kanta a ciki ba Wanda ganinshi ya Kore tarin kuncin da take ciki na abubuwan
da suka mata yawa. Idanunta ta kyafta se hawaye Sharrrrrrr! Ya fara mata zarya kuma
ta kasa daina kallonshi, hawayen yaki daina zuba mata. A hankali ya mike ya nufi
inda take tsaye hannunshi cikin pocket dinshi, sede murmushin dake fuskar shi ya
dauke se tarin damuwar ganin hawayen da take yi.

Menene kuma? Are you not happy?

Ya fada a hankali wanda I'm sure ba kowa bane zaiji se itan da dukkan hankalinta ke
kanshi taji, da sauri ta girgixa kanta tace

A'a.

Then why kike kuka?

Hannunta tasa ta goge fuskarta tace

Banida lapiya.

Da sauri ya kalleta yace

Je canza kaya kizo muje asibiti, me yasa baki fada min ba? Why will you stay with
sickness haka.

Kanta ta girgixa ganin yadda ya rikice tace

Kaina ne kawai yake ciwo kuma ina tunanin stress ne.

Wata ajiyar zuciya me nauyi ya saki wanda Sulaim ta Lura sakamaakon kirjinshi da ya
bude sannan yayi relaxing.

Duk da haka jekiyi changing I'm waiting for you.

Ya fada Yana kallon wrist watch dinsa, babu musu ta wuce dakinta kamar tana taka
iska haka take ji saboda wani abu me sanyi da yabi ya mamaye jini, tsoka da jiki.
Tana shiga ta wuce bayi ta cire kayanta ta saki ruwa, ta kasa tantance me takeji
farin ciki takeji wanda babu kamar shi, Yaya ya dawo me take nema kuma? Baki daya
ta manta da Khulthum, Hanan, Ja'afar da Salim. Junaid ne kawai a duniyarta a Wannan
lokacin.

Tana fitowa fuskarta tayi fayau ga wani lallausan murmushi akai wanda yaki tafiya
se ajiyar zuciya datake saukewa akai akai, sau uku tana dakko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login