Showing 75001 words to 78000 words out of 121650 words
wani call Daga Cyprus don bai shirya jin
rubbish Daga bakinta ba.
Washegari Bayan sunyi breakfast Mami ta wuce daki ta bar Junaid da Ja'afar da
Sulaim, parlon yayi shiru se Lokaci zuwa Lokaci biyun Kan dago su dubu junansu
saboda chatting suke ta whatsapp.
Junaid: Mami tace bata yadda na aureki ba saboda wai bana sonki.
Juanid: kije ki fahimtar da ita ina sonki Kema haka.
Kanta ta girgixa ta dago ta kalleshi se taji jikinta yayi sanyi tayi replying
Sulaim: I can't, kunyarta nake ji.
Dagowa yayi ya dubeta da pleading look sannan yayi typing
Jumaid: Kema haka kike gani Bana sonki ko?
Sulaim: no I'm sure of the love, amma bazan iya tunkarar ta da maganar ba.
Kanshi ya dafe tareda mikewa ya nufi dakin Mamin, Tana ganin hakan ta bar parlon
Zuwa dakinta. Yana shiga ya sameta Zaune Kan cushion idanunta cikin fararen medical
glasses hannunta rike da wani littafi na judges tana dubawa. Tunda yayi sallama ta
amsa, ta aje littafin ta bishi da kallo har ya zauna gefen gadon ta yace
Mami sannu da hutawa.
Hutu yana gurinku Baban Ahmad.
Dan murmushi yayi sannan yace
Mami dan Allah badan na isa ba Mami ki taimaka min ki yadda da proposal dina.
Junaid! Ka bar Wannan maganar kawai dan Allah.
Kanshi ya dafe saboda yadda yake kokarin tsagewa gida buyu saboda azabar Sara mishi
da yakeyi yace
Kiyi hakuri Mami amma idan kika fada min dalilinki ni kuma na miki alkawarin zan
hakura.
Kanta ta girgixa don tasan bazai taba hakura ba tace
Kasan Ja'afar na sonta? Jiya bayan Kaje ka kwanta yazo yana min kuka akan na aura
mishi Sulaim, bana son tarwatsa gidana da hannuna, idan na aura maka ita zaice na
soka, idan na aura ma Ja'afar banyi maka adalci ba!
Hatta itama Sulaim din Mami, maganar akan wa ake ba Sulaim bace? Ki kirata ki
tambayeta wa take so cikinmu inhar ta Ja'afar shikenan magana ta wuce Mami. Amma
inason kisan cewar Ja'afar bashi bane right choice ga sulaim ba.
Inda ace Jabir ko Jawad ke sonta, bazaki taba jin nace ina sonta ba amma Ja'afar no
Mami! Kuma ki tuna ranar da Daddy ya cika Kwana bakwai da rasuwa kika cemin idan
lokacin auren Sulaim yayi ni zan zaba mata miji.....
Wannan ya Junaid, kayi hakuri ka manta da sulaim nafi son ta kawo bare na aura
mishi ita.
Mikewa yayi a hankali idanunshi sunyi ja, veins en kansa sun tashi, ya kalli Mami
sannan ya tsugunna gwaiwowinshi a kasa ya kama hannunta yace
Nagode Mami amma NA HAKURA DA SULAIM
Abinda Mami bata taba kawowa ba kenan, maganar tayi mugun bugunta amma ta kasa
tabuka komai. Hakan baikai yadda maganar ta sauka kunnuwan Sulaim ba wadda ta zo
niyyar kawowa Mami wayarta da Baba ke kira taji NA HAKURA DA SULAIM. Bata Gama
shiga tashin hankali ba seda Junaid ya fito ko kallonta baiyi ba, uwa uba yanayin
da yake ciki. Wani kuka ne ya taho mata hakan yasa ta koma daki Tana jin kamar
zatayi hauka, Tana jin bakin ciki, radadi da zafi Marar misaltuwa cikin zuciyar ta!
Window taje ta tsaya daidai lokacin ya bude motarshi ya shiga!
*When you feel alone I'll be your shoulders, with the tender touch you know so
well. Somebody once said is the soul that matters, Baby who can really tell when
two hearts belong so well, may be the walls will tumble and sun may refuse to
shine.... When I say I love you...*
Shatuuu ♥️ *MACE A YAU*
37
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
Tun tana zuba idon ganin kiran Kabir a wayarta har ta hakura amma ranta tana
tunanin Irin rashin mutuncin da zatayi mishi shi da Salim. Ta tsani rashin cika
alkawari no matter what indai tayi alkawari ko alkhairi ko sharri se tayi kokarin
ganin ta cika shi.
Misalin karfe Sha biyu na dare har bacci ya fara awan gaba da ita taji ringing din
wayarta, hakan yasa ta bude idonta a hankali ta janyo wayar, new number ce hakan
yasa tayi tunanin Kabir ne. Tashi tayi ta zauna sannan tayi picking call din,
muryar kabir din taji Yana fadin
Ran gimbiya ya dade !
Gyara zamanta tayi tace
Tare da naka.
Muryarshi ya gyara yace
Naso tun dazun na kiraki amma hakan bai samu ba saboda wata yar hidima da ta tsayar
dani. Ina fata baki damu ba.
Ko daya Don na manta mun hadu da Kai!
Dariya kabir yayi yana mamakin halin Khulthum, shi bai mata bayanin kanshi ba amma
gashi har ta gane shi kuma tana gaya mishi hakan.
Ayya! Lemme get straight to the point, wato Khulthum tun da na ganki naga kin dace
da wani friend dina Musbahu, saboda yadda yake fadar features din matarshi da yake
so, se naga kina dashi.
Abokin ka kuma?
Ta fada da mamaki, Bama kanshi yake yiwa kamu ba abokinshi yake yiwa to fa? Kuma ma
aure ta! Jin tayi shiru yasa Kabir yace
Ko dai wani ya Riga mu ne? Mu nemi wata.
Kanta ta girgixa kamar yana kallonta tace
Ni yanzun babu aure cikin tsarina kwatakwata, ban shirya committing suicide ba.
Suicide!?
Ya tambaya idanu a warwaje
Of course haka nake daukar aure suicide, tunanin yin aure kawai is suicidal
attempt, saboda tamkar ka dinga cin jollof rice ne kullum na shekaru babu adadi,
babu free life komai an take ka anyi caging dinka.
Kanshi ya girgixa yana Kara tabbatar da Khulthum tayi fitting position din matar me
titαΦ.
Kada ki damu gobe da karfe Tara na safe zanzo na kaiki inda yake, idan har mukaje
kika ji Baki son aurenshi kada ki damu bazan Kara takura miki ba. Seda safe.
Daga haka ta kashe wayar ta kwanta ta rufe idonta zuciyar ta fal tunanin wanene
Musbahu? Meye aikinshi? Dan wanene?
Washegari da wuri ta tashi ta gyara dakin tayi wanka, ta Nemo kayan da take son
sakawa, yau shadda ta dakko wadda Tasha embroidery design me kyau, shaddar coffee
ce akai aikin milk a jiki don haka tayi amfani da milk accessories, dinkin skirt da
Riga da yayi fitting dinta. Karfe Tara daidai ta kammalla komai da takeyi ta fito
Tana fitar da kanshi me kashe jiki. Mama dake zaune tsakar gida Tana zuzzuba abinci
taga fitowar Khulthum, itafa yarinyar nan ta Fara tsorata ta, ta Fara bata tsoro
ina yarinyar take zuwa da Wannan uwar kwalliyar kamar me zuwa dakin miji?
Ina zakije da Safiyar nan? Wai ina tukunna kike Zuwa kike kaiwa dare Baki dawo ba.
Anya Khulthum hanyar da kika dauka zata bulle miki?
Murmushi tayi tace
Mama gidansu Sulaim zanje wadda nake Baki ku gaisa a waya.
Take bakin Mama ya washe Tace
Yarinyar arziki Sulaim ki gaida min ita sosae, bari na baki kuka da Daddawa ki
kaiwa babarta.
Bata fuska tayi tace
Haba Mama Duk Wannan kwalliyar na kare da daukar kuka? Zan dai ce Kina gaisheta .
Daga haka ta fice Don tuni taji kiran kabir tasan yazo, Tunda ta nufoshi yake Raya
Irin kyau da Allah ya bawa Khulthum inda ace Musbahu is Musbahu da yayi Saar mace,
komai daya dace mace tana dashi Bata rasa ba.
A kofar tangamemen company TitαΦ Flours anan yayi parking tare da kallon Khulthum
wadda take bin ko ina da kallo, idanunta kawai zaka kalla kasan abubuwa ne fal
ciki, mamaki, tsoro. Tare suka jera anata gaishe dashi har suka isa inda lift yake
suka shiga ya danna 3rd floor inda anan office din Musbahu yake. Duk yadda taso
daurewa kar kauyancinta ya fito seda ya fito tun ba a wajen lift ba, ji take kamar
ta kankame Kabir, shi kuwa hankalinshi Yana kan wayar da yake bai lura da
yanayinta. Tana tsayawa suka fito Yana gaba tana bayanshi cikin nitsuwa tana satar
kallon gurin se taga first floor ba kawai bane compared to Wannan don hadasu ma bai
taso ba. Seda secretary dinsa ya sanar dashi shigowar su Kabir ya bada izini kafin
suka shiga ciki.
Lokacinda ta hango cikin office din seda numfashinta ya kusa daukewa, wata
nannauyar ajiyar zuciya ta aje har Seda kabir ya juyo tareda kallonta yace
Bismillah.
Cikin takun jan hankali ta shigo ta zauna kan kujerar da Kabir ya nuna mata, Seda
ta zauna sannan yace
Se kin fito.
Kafin ta bude Baki tayi magana har ya fice, yayinda Musbahu ya juyo da Fuskarshi
Baki daya yana facing Khulthum wadda tayi mutuwar zaune, wannan kyakyawan me kudin
shi ke sonta? Gira ya daga mata yana binta da kallo sosae sannan ya tako a hankali
yazo ya zauna cushion din dake opposite din inda take. Ya jima yana kallonta haka
kurum taji ba zata iya kallonshi cikin idanu ba, idanun sun mata kwarjini da yawa,
taji tsoro Yana shigarta sannan tana ayyana Anya kuwa kamar wannan yace yana sonta,
Anya line dinnan intact yake ko wani abu yayi breaking?
Khulthum right?
Ya fada Yana kawar da kanshi cikin siriryar murya wadda zaka rantse mace ce. Kanta
ta gyada a hankali ta kasa dago idonta balle ta kalleshi, murmushi ya danyi yace
Nasan Kabir ya miki bayani a kaina, Abinda bai fada ba zaki fahimta with time, zan
aureki Inshaaa Allah nan da sati biyu zan turo gidanku sede akwai wasu dokoki da
nake dasu kuma duk Wacce ta aureni se tasan da Wannan. Na farko in kika aureni na
miki murna Keda kishiya har abada, bazan Kara kallon wata mace ba da sunan ta
birgeni ba, na biyu namiji ya haifeni, cikin maza na tashi, Maza ne Abokaina idan
kin ganni dasu bana son tambaya. Na karshe ni kaina bansan iya dukiyar da na
makalla ba, babu Abinda zaki nema ki rasa don haka inason ki tsaya a matsayinki.
Idan kikayi haka we're good.
Dago idonta tayi wanda ta lumshe saboda yadda words dinsa ke sinking cikin
kwakwalwar ta sede bawai auna su take ba, a'a greed ya dibe ta saboda furucin
karshe, me take so kudi, me kudin gaske, me kyau gashi yazo! Ina Aimana da Tace
masu kudin Nigeria duniyarsu daban take? Gashi ta cin musu cikin kano batareda ta
wahala ba. Kanta ta dago tace
Na amince!
Kanshi ya gyada yace
Jibi juma'a zanzo na gaida babanki.
Daga haka ya koma inda ya tashi, Sega Kabir ya shigo suka danyi maganganu wanda ba
jinsu take ba hankalinta yana wata duniyar. Suna gamawa ya Mika mata sabuwar iPhone
X! da envelope sannan ya maida kanshi kan Abinda yake yana jin hankalinshi Yana
kwanciya saboda zai cikawa gwoggo daddan barinta shima ya samu hankalinshi ya
kwanta.
Gado ta zauna ta saki kuka me ciwo, me radadi, shi kenan ya daina sonta, ya hakura
bazai aure ta ba kenan? Mikewa tayi ta dakko wayarta ta Fara kiran Imratu wadda
take kitchen, Tana ganin kiran ta dauka amma jin kukan Sulaim yasa jikinta yayi
sanyi, hankalinta ya tashi tace
Sulaimi Menene
Yaya yace ma Mami ya fasa aurena, ya zanyi?
Shi ne kike wannan kukan Sulaim?
Yaya fa Anty! Yaya!!
Idanunta ta runtse hakan ya kara bawa hawaye damar gangarowa, sunanshi kawai da
take fada ji take dukkan jikinta na amsawa, zuciyarta na harbawa da sauri da sauri!
Oh Allah what will life be without Junaid?! Shi ne kawai Abinda ayyanawa.
Sulaim ki nutsu kina jina, Mami tana da dalilin Hana papan Ahmad aurenki, duk inda
akaje aka dawo Kece a Wahale. Mami bata san Junaid na sonki ba seda matarshi ta
tafi sannan ya gabatar da bukatar shi, Ta yaya kike tunanin baza tayi tunanin
amfani yake son yi dake wajen hukunta subay'a ba? Wannan abinda take threat ne tafi
kowa farin ciki kuma shima Yayan bazai taba hakura dake ba, fada kawai yake don
haka kiyi shiru ki nutsu Kada kiyi abinda zaki koma jin kunyar Mami har abada. Kin
gane?
A hankali taji zuciyrta tana sanyi, taji ta gamsu da maganganun Imratu hakan yasa
ta share hawayenta Tace
Nagode Anty.
Kanta ta gyada tace
Allah ya zaba muku mafi alkhairi.
Amin ta furta da dusashiyar muryarta. Suna sallama ta kwanta gefen gadon hawaye na
Mata zarya, ita dai soyayya bata karbeta ba, da zarar ta saki jikinta da mutum se
wani abu yazo ya datsa tsakiyarsu, yanzun dukkan hope dinta yana kan Junaid gashi
yanzun abubuwan da suke kunno kai. Ta dade a gurin bata daina kukan ba seda bacci
yayi gaba da ita bayan Azahar ta Mike kanta nayi mata azababben ciwo kamar zai fado
amma a haka tayo wanka da Alwala tazo tayi sallah sannan ta Fara neman layin Junaid
sede har ta gama ringing ba'ayi picking ba, hawayenta ta share ta aje wayar akan
gado ta fito parlour Don neman su Ahmad ko taji saukin abin dake damunta.
Tana fitowa taji mummunan labarin da har duniya ta nade bazata taba mantawa dashi
ba, ba zata taba daina kuka akan wannan abin ba haka........ Muryar Mami ce cikin
kuka take fadin
Junaid ya rasu......?!
Shi ne kadai abinda Sulaim ta jiyo taji tamkar an saka Rodi an caka a kahon
zuciyarta, hakan yasa ta rike kirjinta wanda yayi mata nauyi, se baki da ya gifta
daga idanunta ta zube sumammiya a gurin.
_Innalillahi wa Inna ilahil rajiun! Kui hakuri haka labarin yake, dole haka
xa'ayi!!!_
*If only you could see the tears in the world you left behind, if only you could
heal my heart just one more time, even when I close my eyes there's an image of
your face and once again I come to realize you are a loss I can't replace......*
Shatuuu ♥️ *MACE A YAU*
38
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
*I've seen your comments all Wanda nake in touch dasu, kuyi hakuri Amma akwai abu
da nake son ku fahimta ko a rayuwa ta dan Adam akan samu irin wannan abubuwan suna
faruwa, ina son kusan cewar ba kowanne so ne yake zama samu ba... Haka rayuwar take
ko kuma Kaga dole Se ka bi rough hanya kafin ka wuce ta smooth one. To haka rayuwar
take is not everything that's at our disposal, akwai abubuwan da dole Se Kasha
wahala kafin ka samu.... Nagode sosae Allah ya bar zumunci naga comments dinku nima
ina baku hakuri, nasan Wanda suka fadi wasu abubuwan is out of anger banyi fushi ba
ina fatan wanda sukai fushi su sakko.*
Wata razanannen ihu Ja'afar yayi wanda ta janyo hankalin Mami da Baba dake parlon,
da gudu ya isa Kan sulaim din ya fara jijjiga ta Yana kiran sunanta amma ko motsi
ba tayi balle asaka ran zata farfado, Ahmad da Muhammad da suke wasa suka taho
kanta suna kukan AMMIEY don Junaid yace musu sunanta kenan baya son anything like
Anty. Sosae Mami take kuka kamar ranta zai fita hakan ya janyo hankulan ma'aikata
dake gidan suka hayo saman. Mama talatu me aikin Mami ta dakko ruwa ta zubawa
Sulaim wanda Daga Baban har su Ja'afar saboda tashin hankali Babu Wanda yayi
tunanin hakan, wata ajiyar zuciya me nauyin gaske ta saki kafin ta Fara bude idonta
a hankali har tayi adjusting da hasken gurin, murmushi ta saki don ta tabbatar
mafarki tayi, mummunan mafarki ma kuwa, wai yayanta mahadin rayuwarta ya rasu, yabi
Daddy da Mummy Kai ai kuwa da ta cika marainiya Don tana ganin farin ciki sede a
lahira kuma!
A hankali ta gyara kwanciyarta amma se taji muryar Ja'afar yana fadin
Mami ta farka!
A hankali Baba ya durkusa ya riko hannunta, idanunshi sunyi ja yace
Ummu_Sulaim me ya faru dake.
Wani numfashi taja me karfi, ta kalli Mami wadda take kuka cikin karyewar zuciya,
Ahmad da Muhammad, ga Ja'afar sannan Baba, ga ma'aikatan gidan kowa hankalinshi a
matsanancin tashe, kuka ta saki ta damke hannun Baba tace
Baba Yaya ya rasu da gaske? Ya tafi ya Barni? Bayan ya min alkawarin bazan Kara
kuka ba shine ya tafi....... Me yasa? Me yasa?
Ko ya ka kai da danne zuciyarka se kayi kuka, saboda yadda take kuka from the
bottom of her heart, how's that feeling Irin abu kike jira all your life se kuma
yazo lokacin kike gaf da samu abin ya barki..... That's shattered dreams!!!
Juyawa Baba yayi ya dubi Ja'afar yace
Nayi booking tickets Tun kafin na shigo gidan, ka wuce airport yanzun Zamu karaso.
Wani kuka Sulaim ta Kara saki cikin matsanacin tashin hankali tace
Shi kenan I'm shattered, na zama marainiya Baba, banida gata kuma a duniya.
A takaice Seda Sulaim tasa Baba ya zubarda hawaye Balle Mami wadda da kyar ta debo
kayanta da na Baba, haka suka fito with a heavy heart Zuwa Airport. Sulaim Tunda
suka shiga jirgi ta rungume Ahmad da Muhammad a jikinta tana zubar da hawaye wanda
ta rasa a yananyin da take ciki, yaran sunyi shiru se kallon kowa suke.
Tunda Sulaim take bata taba ganin most dreadful journey Irin wannan ba, tamkar da
kafa take tafiya haka take ji, a haka ya kare bazai kare ba suka sauka a cikin
Aminu Kano international airport. Ana Fara fitowa, Ja'afar ya dakko Muhammad a
kafada, yana jan hannun Ahmad, Baba hannun Sulaim ya kama wadda take ta kallonshi
yasan bayani take bukata amma yasan bazata taba fahimta ba Yafi son taga komi da
idanunta.
Basu jira wani yazo daukarsu suka samu cab ta daukesu zuwa National orthopedic
hospital dake Dala a birnin Kano. Tun a gate suka so hanasu shiga amma kallon
Sulaim kadai bazai barka kayi Abinda kayi niyyar ba. Ta lalace Lokaci guda ta rame,
idanu sunyi jawur tamkar garwashi ko jikinta ka kalla kasan akwai damuwa. Jeans ne
jikinta se top Fara iya gwiwa da karamin veil wanda babu inda ya rufe mata, haka
kuma babu Wanda ya lura da shigar dake jikinta Don babu me wannan nutsuwar.
Dr. Halliru suka Fara hangowa me Family law da Ridwan suna tsaye suna jiran isowar
su, Tunda ta hada idanu da Ridwan ta saki hannun Baba ta nufeshi kamar zata kifa
tareda ruko hannun shi tace
Ka fadamin Yayana ya tafi ya barni? Na zama marainiya ko? Bai cika alkawari ba, he
said he'll be my home, my shelter, the shoulders I'll cry on.......
Ja'afar ne ya ruko ta dan baki daya Ridwan da Halliru sun kame a gurin tamkar
gunki, me Zasu ce mata? Ya mutu? Ko kuma he's battling with his breathing.
Kuka sosae take har suka isa building din SOPD inda Tanan suka hau sama zuwa new
Aminity. Hannunta ta fixge Daga hannun Ja'afar tana kokawa da numfashinta, so yake
ya fita amma hanashi take ta fison ko zai fita ya fita bayan ta ga Rabin rayuwarta,
taga better half dinta. Tayi nasara cigaba da tafiya sede kawai kafar take wullawa
batasan inda take zuwa ba.
Suna isa kofar room din, doctors wajen ashirin suka fito Daga ciki, Blue Team, Pink
Team, White team da Green Team kowanne yana son ganin Team din da zaa aje Junaid
din ciki.
Dukansu Suka tsaya suna kallon Sulaim wadda ta taryi babban consultant din Pink
Team dake gaba, ta rike hannunshi me rikeda waya da stethoscope da bai samu ya
makala a wuyanshi ba tace
Doctor tell me