Showing 30001 words to 33000 words out of 121650 words

Chapter 11 - MACE A YAU by Shatuuu

Shatuuu   

12 May 2026

137

kanta.

Motoci na wucewa da hanzari kowa Yana son reaching destination dinsa, Khulthum na
tsaye gefen titi Tana ta bin motocin da suke wucewa da kallo a ranta tana tunanin
inama ta wawaso zuciyar wani, tunanin hakan yasa ta gyara tsayuwarta tana dan
karkada jiki yadda zata jawo hankali, aikuwa babu jimawa wani azababben guy cikin
azabbabiyar bakar mota ya parka gefenta tareda wining glass kasa yace

Kyakyawa kamarki Bata cancanci dukan rana ba.

Murmushi me kyau tayi Wanda duk wanda akayiwa se zuciyar shi ta kwaidaitu da burin
kasancewa tareda me shi. Lumshe idonsa yayi yace

Idan da kinji yadda tsayuwarki gurinnan take taba ni ina tunanin da ko second Baki
kara a waje ba.

Kalamanshi sunyi mata dadi, motarshi me kyau kamar yadda yake me kyau bata wani ja
ba tayi wa kanta masauki gefenshi, Tana rufewa yaja suka tafi, shima suit ce
jikinsa. Suna tafe Yana bata labari yayinda take amsa mishi da Mhm, a'a ko Eh
saboda dole taja class dinta. Seda ta sanar dashi inda zai kaita kuma baiyi kasa a
gwiwa ba ya kaita har kofar Faculty ya amshi numbers dinta yayi storing cikin
wayarsa sannan ya wuce, Baki daya ta kasa rufe bakinta tana ganin tafi kowacce mace
sa'a a Wannan ranar, irin mazan da take so kenan sune taste dinta Amma me zaayi da
Ashir wanda kyauta baya iya yin ta dubu Daga 500 shikenan.

Tana nan tsaye Sega Khairi da Aimana sun fito Daga class, inda suke ta nufa tana
binsu da kallo, kowacce cikinsu tana cikin abaya yar gaske me Tsada ,khairi tata
fara ce tayi rolling Baki itakam Aimana baka tasaka all through se jikin veil dinne
akwai Polk dots na fari, fuskarsu babu kwaliyya Daga powder se lip balm akai amma
sunyi kyau, a ranta tace kudi kenan da Hutu Shiyasa Baku kwaliyya don kunsan no
matter how you look zaku samu miji mu kuwa seda ita.......... Wannan shi ne
perceptions din wasu mata not all but many na ganin se kayi kwalliya zaka samu
miji, ba haka bane hasalima wani bayason kwaliyya, is not that ki fito kamar jaka
a'a but powder, khol da balm a lips is OK, amma too much foundation, powder,
concealer da sauransu Yana altering skin integrity saboda dukkansu chemicals ne.

Baza'ayi class bane

Ta Tambayesu lokacinda suka iso inda take, Aimana ta kalleta babu Abinda ta tsana
kamar kwaliyyar da Khulthum take, har yau ta kasa banbance meye matsalar Khulthum
ne idan ka ganta kamar ta waye amma ko oho. Khairi mutuniyarta tana washe Baki tace

Kinyi kyau matar handsome in a flashy car.

Dariya Khulthum tayi tace

Allah ya karba bakinki yanzu na hadu da wani azababben guy har nan ya kawoni.

Dariya khairi tayi cikin jin dadi tace

Haba! Shiyasa Naga Bakin ya kasa rufuwa. Kinga lecturer wai se karfe biyu zaiyi
holding class din shima ba Zuwa zaiyi ba idanshi zaizo wani Dr waye? Oho!

Ta fada Tana son taunawa, itadai Aimana na tsaye batace uffan ba seda suka gama
tace

Muje Nan cikin quarters akwai gidan yayata mu zauna kafin time din.
Seda sukai nisa sannan Khulthum tace

Banga Sulaim ba ko bata zo ba?

Aimana ta girgixa Kai tace

Tazo Tana class

Class? Kuka baro ta? Ita kadai?

Tsaki Aimana tayi tace

Meye zai kamata, kamar tana da damuwa ne munyi munyi taki biyo mu Shiyasa muka
barta.

Kai Khulthum ta kada amma se taji babu dadi cikin ranta har zuciyarta take son
Sulaim, there's something unique about her. Aimana dake tsakiyarsu ta kalla
Khulthum in a polite manner yadda tasan words dinta bazasu Bata ran Khulthum ba
tace

Nikam Khulthum me yasa kike wearing makeup zuwa school ne? Kwatakwata bai dace ba
se kace ba professional course kike taking ba.

Kafin Khulthum ta bada ansa, khairi tayi caraf tace

Ke Aimana ina ruwanki? Bakya gani kiyi shiru ne?

Hararar ta sakar mata Tace

Nasa bakinki, I taught ba da ke nake ba, Khulthum as I was saying ki rage kwalliyar
nan batada amfani a matsayinki na student. Kinada kyau basai kin hada da artificial
fixations dinnan ba shi ne banbancin ki da gidan biki.

Khulthum batace komai ba don ta rasa abin fada se can tace

Kwaliyya ai Itace mace, in the first place Meye ruwanki da kwaliyyata so bakyayi
shikenan ni bazan yi ba? Rayuwarki daban tawa daban.

Very calm ta fadi hakan kamar ba Khulthum ba, Aimana taja bakinta ta tsuke tana
nadamar dalilin da yasa tayi magana.

Kwanaki hudu kenan da faruwar incidents din Sulaim, Ja'afar da Junaid... Love
triangle kenan.... Ta rame tayi xuruxuru saboda yadda ta kwarzabi Rayuwarta she's
going through a hard phase, ita kanta idan kace Meye damuwar ba lalle ta sani ba
Sede mu hadashi da Marin Junaid don har lokancin ba sui communicating da Ja'afar ba
ita tayi parking dinsa a side. Junaid kam ba'a magana ta hukunta shi ko kuma nace
tana hukunta shi kamar yadda take hukunta kanta ba tareda sanin ta ba. Shiyasa
gabaki daya ta zama moody ta rasa me yake mata dadi gaba daya kanon ma ta fita a
kanta sede babu damar tafiya Don kuwa 2 weeks ya rage a fara exams. Tana nan Zaune
a class itada daidaikun mutane yawanci karatu haka itama ta daure ta samu tayi
karatun hakan yasa ta danji dadi a ranta. Mikewa tayi saboda yadda cikinta yake
gugi, jin hakan yasa ta tuna yau Batayi breakfast ba kuma jiya ba taci dinner ba
kuma ga mamakinta Junaid ko takanta bai bi ba hakan shi yake sakawa take kara zama
very mad at him, yaya zaiyi laifi kuma ya fita fushi wannan ai son kai ne, da
hanzari ta Mike ta dauka handbag dinta ta fita a class din don taci abinci wayarta
dake rike a hannunta ta Fara ringing alamun kira na shigowa, a mamakance ta sake
duba wayar Dan tabbatar da cewar Junaid ne me kiran, shi dinne kuwa haka kurum se
taji tamkar ana cire mata damuwar dake dankare a cikin ranta da ziciyarta.
Ni dai nace magulmata...... Halo wattpaddians double, triple, quad appreciation
goes to you for the comments and votes. Thank you very much..... I'm proud of you
and as such d page is completely yours.


Shatuuu♥️
[7/5, 11:46 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
13

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad


*Hello pipu of whatsapp...... Here's your page habibties I'm very grateful.....
Have the page*



Se kawai ta samu kanta da kin picking call din a ranta tana fadin ko iya haka aka
tsaya babu damuwa tasan Rabin damuwarta ta tafi, ita kanta tana mamakin halin da ta
jefa kanta a ciki, yadda ta dauki Junaid ta bashi wani mugun mukami a
zuciyarta..... Wayarta ta sake ringing a Karo na biyu hakan yasa batada wani zabi
face tayi picking, kafin tayi magana cikin muryarshi me Amon dadi yace

Ina jiranki a office yanzu.

Ta bude Baki dan protesting taji ya kashe wayar babu yadda zatayi haka ta juya ta
nufi offices din dake cikin faculty. Kafin ta isa kiran Yaya Jb ya shigo, soja
kenan marmari Daga nesa. Dan tsayawa tayi ta amsa call din suka gaisa yana
tambayarsa ko akwai matsala ta nuna mishi babu komai sannan yace mata

Ayi mana addu'a zamuje Riyadh ganin wani gynae ni da yayarki.

Kanta ta gyada kamar yana kallonta, Tana jin tausayin Yaya Imratu da Ya Jb komai is
abundant cikin rayuwarsu haihuwa ce kawai Allah bai kawo ba, to dama mutum Tara
yake ba goma ba amma tasan ba kowanne so bane yake zama samu.

Allah ya kiyaye Yaya yasa a dace mu samu baby.

Da sauri yace

Amin Lil, wannan adduar taki ina fata ubangiji ya amsa ta. Yayarki na toilet me
zance mata?

Kace ina gaisheta, safest trip and Allah's khair.

Murmushi yayi sannan sukai sallama kafin ta ja kafarta Zuwa office din Junaid, haka
kurum se zuciyarta ta Fara increasing bugun da takeyi wanda kullum idan hakan ta
kasance se ta rasa gane ko dai she's psychologically sick ne ko kuma me? Itakanta
tayi iyakar tunani akan me yasa take jin ireiren stuffs dinnan idan ta doshi inda
Junaid yake, Sede ta rasa amsar ta kuma rasa me Bata.

Seda tayi knocking yayi mata izinin shiga kafin ta murda kofar ta shiga, yana zaune
kan kujerar shi, table din yana cike da takaddu daban daban, ya cire coat din saman
se white long sleeve shirt a jikinshi, tie dinma yayi loosing dinshi kadan,
idanunsa cikin farin medical glasses wanda yasa yayi kyau sosae dukda Fuskarshi na
nuna gajiya amma hakan bai hana kyanshi, cikar haiba da kuma zati fita ba. Tunda ta
rufe kofar ta tsaya a gurin ba tareda tace dashi komai ba, se lumshe idonta da tayi
saboda yadda Acn office din ke aiki babu hutawa, se taji inama tayi bacci. An kusa
Mintina biyar kafin ya aje pen din hannunshi tareda mikewa yayi baya da kujerar ya
iso tsakiyar office din tareda zura hannayenshi cikin aljuhun wandonshi yace

Zo ki zauna.

Babu musu ta taho kamar wata chameleon ta zauna kan soft sofas din da suke aje daga
extreme din office din. Seda ta zauna kafin ya iso shima ya zauna Yana dubanta Irin
kallon da bai taba yi mata Irinshi ba, kallo ne Wanda ta ko ina ta kasa fassara shi
se ya zamana idanun nashi sun takura mata ainun, taji tamkar ta Mike ta fice, ga
zuciyarta is adding more issues to her yadda take bugawa tamkar zata balla chest
wall dinta ta fito. Bakinta ta turo mishi hakan yasa yayi murmushi sannan yace

Sulaim

Tamkar magnet haka muryar ta fito wadda ta tilasta mata dole seda ta dago ta zube
idanunta cikin nashi. Yadda taga idanun nashi yana wani maiko tamkar an disa mai
ciki ga wasu molecules dake fita daga nashi idanun suna piercing Sclera and cornea
dinta yasa babu Abinda ta iya yi face ta maida kanta kasa. Murmushi me taushi ya
kuma saki yace

Me yasa kika daina min magana? Me yasa kika daina cin abinci?

Bata dago kanta ba bare ya saka ran zata bashi amsa se ma yatsunta ta dinga wasa
dasu. Ganin haka yasa ya sauke ajiyar zuciya me nauyin gaske tareda sake tattara
hankalinsa kanta yace

Saboda na mareki ko? I'm sorry.... I'm very sorry I shouldn't have been mad na
yanke hukunci cikin fushi I'm sorry kinji.

Maimakon magana kawai se ta Fara kuka kamar wadda aka tuna mata wani abu, tayi
cupping fuskarta a tafukan hannayenta tana kuka Wanda ita kanta bata san dalilinshi
ba,

Oh God! Sulaim please ki daina kukan nan bakisan yadda kukanki ke damuna ba.... I
said I'm sorry ko na juya fuskata ki rama.

Dago idonta tayi ta kalleshi tareda tunzura bakinta tana share hawayen fuskarta, to
meye abin kukan ta tambayi kanta, dadi kuma ta dinga ji tareda jin komai ya wuce
tunda har yasan yayi laifi kuma ya bada hakuri


Zaki rama din na juyo?

Ya fada cikin wani Irin sauti Wanda seda yasa taji ilahirin Tsikar jikinta ta zuba
tareda lumshe idonta se kuma ta turo Baki tace

Ni bance ba

Nima ban ce ba Sede idan baki hakura ba feel free ki rama indai zaki daina fushi
Dani kinga we're even.

Tissue box din dake aje Kan glass center table din ta dauka ta goge fuskarta kafin
kuma ta kalleshi ta sakar murmushi, shima murmushin yayi mata yana jin wata nutsuwa
ta baibaiye shi sede wata zuciyar na ganin me yasa zai zauna Yana apologizing ma
karamar Yarinya wannan ai ya siyarwa kanshi raini ne, Baibi takanta ba don idan ya
biyewa thoughts dinnan haka zasuyi ta zama da Sulaim bai gyara barakar da ta wanzu
tsakanin su ba har Ja'afar yayi nasarar dauketa. I mikewa yayi ya koma mazauninsa
tareda daukar wayarshi yayi kira dake hankalinta kwatakwata baya kanshi tana nan
tana lissafi farin cikin da Lokaci daya ya zama ta bata ji abinda yace ba se gani
tayi an shigo an hada lunch a inda take Zaune Kan table. Dagowa tayi ta dubi
abincin sannan ta dubi Junaid wanda ke sallamar dan aiken kafin ya dawo da
hankalinshi kanta, suna hada ido ta dauke kanta tareda yin wani side murmushi
shikam kanshi ya girgixa yace

Fara ci gani nan sakkowa .

Babu musu saboda bata kasance me yin musun ba ta bubbbude wrapped plates din dake
gabanta, jollof rice ce da hadadden salad se pepper soup na kayan ciki. Nata ta
zuba cikin separate plate ta Fara ci, saboda yunwar da take ji gani take Bata taba
cin abinci Irin wannan ba, Seda ta kusa gamawa kafin ya sakko yayi joining dinta.
Massalaci ya fita ya barta tayi a office din, yana Dawowa daya da Rabi tayi gashi
ta dan kintsa mishi kan table din nashi da shelf dinsa. Yaji dadi har yace

Tukwicin abinci na aka min gyara.

Dariya tayi siririya kafin ta Mike tace

Yaya na tafi class, munada class by 2pm.

Kanshi ya gyada yace

Better go, we meet after.

Ficewa tayi shikuma ya tsaya Yana kallon ficewar tata seda ta rufe mishi kofar
kafin ya saki murmushi tareda shafa kanshi a ranshi yace

Junaid what's all this?

Shima baisan amsan ba haka ya Fara shirin abinda zai aiwatar. Sulaim na fita taji
tamkar irin born again dinnan zuciyarta tayi wasai kamar anyi mata albishir. Tana
zama a sit dinta mutanen ta suka shigo baki daya inda take suka zo.

Kinci abinci?

Aimana ta tambayeta, murmushi tayi tace

Naci, kun dawo?

Khulthum ta gyada Kai kafin suka Fara hira ko nace yawanci suna brainstorming ideas
ne akan karatun da sukai babu laifi Baki dayansu kwari ne kansu na ja. 2pm daidai
ajin yayi tsit saboda shigowar lecturers guda uku na gaba kana kallonshi kasan ya
manyanta na bayanshi is a well known personnel amma a gurin Sulaim kadai hannunsu
na rike da Apple System dinshi wannan gajiyar dake tattare dashi lokacinda ta
sameshi a office yanzun babu se kamar farin ciki da yake tattare dashi though babu
wani fara'a a tattaredashi amma kuma Sulaim ta fahimci hakan. A bayanshi level
coordinator dinsu ne . Gaba daya ajin yayi tsit level coordinator yazo ya gabatar
da Prof shu'aibu as Deen din faculty, cikin nitsuwa ya basu welcoming address
wanda bai samu yayi ba Don lokacin matriculation Dinsu baya gari so bai samu yaje
ba. Ya basu fatherly advice sannan ya dan tabo musu Irin gwagwarmayar da yasha
wajen karatu, don haka yake basu shawarar they should never give up no matter what.
Yana gamawa ya fice saboda meeting da zasui da VC a haka ya fice sannan level
coordinator ya bawa Dr Junaid damar yin magana.

Yana tsaye gaban podium din, ya gyara zaman glasses dinsa, ya kunna system dinshi
kafin ya dago idanunshi masu haske ya dubi students din dake Zazzaune.

Khulthum Tunda ya dago ta bude Baki tare da fadin

Khairi kinga wata halitta?

Da sauri Sulaim ta kalleta, se taji Khairi tace

Oooooo dama akwai Irin wannan charming guys din a Faculty nan, gaskiya ya hadu.

Sulaim Baki daya se taji haushi baki daya ya rufeta, ga tana ta kallon yadda Mata
ke kallonshi da admiration fal idanunsu wani Irin nauyi taji kirjinta yayi mata
kawai se ta janyo wayarta ta kunna data ta shiga instagram, lokaci Zua Lokaci tana
jiyo muryar da take ratsa mata ilahirin jikinta sede ta kasa dago idonta ta
kalleshi saboda batasan kallon da mutane Ke yi mishi Amma baki daya hankalinta yana
kanshi. Duk yawancin Maganganunshi suna kan exams din da zasui da rules da suke
guiding exams. Yana gamawa ya bada room for question kawai wata budurwa very
courageous tace

Sir we need to know your name

Dama kanshi Yana kan wayarshi hakan yasa seda ta maimaita kafin ya tuna cewar bai
yi introducing kanshi ba, a nutse yace

I'm Dr. Junaid Lukman Birnin kudu, I'm a lecturer here amma Bana daukar class dinku
se kunzo level 3, I'm the exam officer of the Faculty.

Daga haka aka ta mashi tambayoyi yana bada amsa amma ko sau daya Sulaim bata bari
sun hada idanu ba Duk yadda yake son hakan saboda tun zuwanshi class din ya marking
inda take. Seda ya gama komai kafin ya basu best wishes sannan ya fice. Daga haka
class coordinator ya sallamesu, suna fitowa taga message din Junaid akan ta jirashi
yanzu zasu wuce gida. Tare suka fito duka su hudun kuma Monday Za'a Fara exams don
haka sukaiyi akan zasui karatu su hadu Washegari.
Sulaim tace

Gaskiya I'm not sure idan zanzo amma dai zan fada ma yaya idan ya yadda.

Aimana tayi dariya tace

Kanwar Yaya, kullum yaya zanso naga wannan Yayan.

Dayake Sulaim Abinda tafi ambata kenan Yaya, tayi dariya a ranta tace ai yau kowa
yaga Yaya. Sunanan tsaye Sega Motar Hu ta iso kafin ta Daga kafarta kamar Da hadin
baki Sega Ashir akan Lifan dinshi sannan da azababben guy cikin azabbabiyar mota
shima ya iso, idanu a waje ta dubi Sulaim wadda ita tasan Ashir saboda sun taba
fita tare suka hadu dashi anan yasan Sulaim itama ta sanshi, Hu kuwa Duk sun sanshi
se Yusuf Wanda dazu ta hadu dashi. Kallon Aimana tayi tace

Ya zanyi dan Allah?

Aimana ta dauke kanta don batasan me zatace da ita ba Balle Sulaim wadda Baki daya
mamakin abin take amma ga mamakinsu se kawai ta nufi inda Hu yake da murmushi da
komai tace

Yau duka bamu hadu ba Inata missing dinka.

Murmushi yayi yace

I missed you more, Munje ko?
Kanta ta girgixa tace

Ga uncle dina can yazo daukata muje ku gaisa.

Tana fadar haka ta nufi inda Yusuf ke tsaye ko kallon inda Ashir yake Batayi ba se
kallon ta yake mamaki kamar ya kasheshi, Tana zuwa suka gaisa kafin Hu ya iso tace

Ga brother na ku gaisa yazo daukata.

Yana zuwa suka gaisa tabi Yusuf suka tafi Hu yaja motarshi yayinda Ashir ya iso
inda su sulaim suke seda suka gaisa, Sulaim tayi introducing dinsa ma su Aimana
shima haka,

Su waye wanda Khulthum taje gurinsu suka fita a mota?

Yayi directing tambayar ga Sulaim, kallon Aimana tayi tace

Answer him please.

Hakan yasa ya kalla Aimana yace

Aimana Ku Fada min Kada Ku damu ba zance mata ku kuka fada ba, sannan na dade da
sanin tunda Khulthum ta samu admission halayenta sun canza, gaba daya ta dauki wata
rayuwa da bata taba kuma bata dace da ita ba.

Kafin Sulaim tayi magana kiran Junaid ya shigo ta musu sallama akan ko meye Ashir
yayiwa Aimana bayani.


Shatuuu ♥️
[7/6, 7:09 PM] Shatuuu😍:
*MACE A YAU*

14

✍️Shatuuu♥️

🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

#⃣Shatuuu095@wattpad

Disposable cup din dake Cikeda da sassanyan ruwa ta kafa bakinta akai Seda ta
shanye tas kafin ta wulla cikin bin dake gefen table dinta. already ta kamalla
tattara kayanta lokaci kawai take jira yayi ta samu ta koma gida don Baki daya yau
a gajiye take tubus kamar wadda Tasha wani aikin. wayarta da tuntuni take cikin
hand

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login