Showing 291001 words to 294000 words out of 321711 words
ashe, bari in Shiga" Shi dai yayi shiru yana sauraronta xuciyarsa na throbbing, ya ji
tace "Captain bata ciki fa, na duba bathroom ma ban ganta ba, let me check downstairs" Ya dake yace
"Ohk" again bayan wani lkci tace "Bata nan wllh captain, and I can't even see her shoes da ta bari bakin
kofa daxu da ta shigo, probably taje siyo abu ne a waje" yace "Ohk, gobe da safe xan dawo in sha Allah"
Tace "Toh Allah ya kai mu my captain" Katse wayar yayi ya xauna gefen gado yana jin wani mugun bugawa
da xuciyarsa ke yi, is this for real? Wait ina ma ta tafi tukun? Bai san sanda ya bude baki ba mamaki kaff ya
gama cikasa, sai yake ganin abun kamar film, Aneesah?? Ya kara bin dakin nata da kallo ya kalli xanuwan
gadon da suke xube a kasa, mikewa yayi ganin sachet kusan hudu dake xube daga gefen xanin gadon ya
karasa ya durkusa ya dauka yana dubawa, sai dai xuciyarsa ya daina aiki na kusan second biyar, ya dinga
kallon sachet din babu ko kiftawa da wani expression da ya fi kama da na shock, juyasu ya dinga yi yana
kallonsu kamar idanuwansa xa su fito, lkci daya ya runtse ido ya nufi kofa ya fice daga dakin ya tafi
bangarensa, bai ga Jiddah a nan ba ya shige bedroom ya kwanta jin kamar sanyi yake ji, ya fi minti ashirin a
haka duk jikinsa yayi wani irin sanyi, he is really shocked, ruwa ya sauka sosai, can yayi karfin halin tashi ya
tafi bandaki ya hada ruwan dumi yayi wanka ya fito, yana ta xaune gefen gadonsa yayi wannan tunanin
yayi wancan tunanin, can ya mike da kyar wearing just his short nd singlet ya fita dakin, dakin Jiddah ya tafi
ya kunna wutan dakin ya ganta kwance ta rufa da duvet, idonta biyu kuma ba bacci take ba, ita duk
tunaninta wajen Aneesah ya tafi ya bar ta xaune parlonsa kawai, ya kashe wutan a hankali ya tafi kusa da
ita ya cire duvet din gently ya kwanta drawing her closer to him ya juyo da ita, underneath his breathe
yace My Precious Gift... Ta ki bude idonta tana sauke numfashi a hankali....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_
Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*
If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp
Da asuba Abuturrab na dawowa masallaci ya xauna downstairs ya jinginar da kansa a hankali jikin kujera ya
rufe ido, gaba daya ya rasa me ke masa dadi, upon how sweet the night was to him bai yi wani baccin kirki
ba, he was disturb all through, and he is still finding it hard to believe Aneesah bata kwana cikin gidan nan
ba, yana ta xaune parlor har bakwai saura sannan ya mike da kyar ya haura sama yana jin kansa na sara
masa, bude kofar dakin Jiddah yayi ya sameta ta koma bacci bayan ta idar da sallah, ya nufeta ya lulluba
mata duvet a hankali yana kallon innocent face dinta, ya daura lips dinsa a nata ya lumshe ido, sai kuma ya
mike ya fita, gently ya kullo kofar don ya san she really need the sleep, ya tafi parlonsa ya xauna ya rike
kansa yana jin damuwa a ransa, sai kuma ya jawo wayarsa ya shiga dialing number Aneesah, har ya katse
bata daga ba, ya kuma kiranta sai ta daga cikin muryan bacci tace "Hello my Captain" Yace "How was ur
night?" Tace "Alhmdlh, are u still coming back today?" Yace "Yeah at 10" tace "Alright dear Allah ya kai mu,
hope u slept fine?" Yace "Yeah, can u pls take ur phone to Jiddah?" Ta wani shagwabe tace "Captain naga
kamar fa ba don ni kake yawan kiran nan ba, kawai kai dai kira kake saboda matarka, banda haka ni a rana
daya ma a ina nake ganin call dinka, i assume this call isn't for me" Yace "Aa ba haka bane...." Ta katse sa
tace "Alright, i will go give her d phone now, I was only joking my captain" Yace "Ohk" yana ta sauraronta
har bayan minti biyu ta fara knocking tana kiran sunan Jiddah, sai kuma tace "Captain bata ciki fa? It seems
bata dawo jiya ba" Yace "Bata dawo jiya ba?" Tace "Wllh, her door is open and the room is still d way it
was yesterday da kace in kai mata waya, bari in sauka kasa" Ya kasa ce mata komai wani axababben
mamaki ya cikasa, bayan few seconds tace "Bata dawo ba kam Captain" A hankali yace "Alright, sai anjima"
Tace "Ohk my Captain, i love you" a hankali yace "Same" sannan yyi maza ya katse wayar ya rike kansa da
yayi masa wani nauyin bala'i yana jin xuciyarsa na wani tafarfasa, lkci daya ya mike ya tafi gaban mirror
dinsa ya bude yana kallon abubuwan da ya kwaso a dakinta jiya bbu ko kiftawa, xaunawa yayi gefen gado
ya kara dafe kansa maganganun Ahmad na dawo masa tiryan tiryan. Karfe takwas Jiddah ta farka ta bi
dakin da kallo, da sauri ta mike xaune har xata shiga bandaki ta tuna tayi wanka tayi komai da asuba, ta
tashi ta dau hularta ta saka sannan ta fita dakin ta sauka downstairs tana tafiya a hankali ta wuce kitchen,
tunanin abinda xata yi for breakfast ta shiga yi, can dai ta fara wanke few plates din dake kitchen din da
Aneesah ta bari, sannan ta gyara kitchen din tsaf ta daura ruwan shayi, ta fara fereye doya... Karfe tara da
few minutes ta fito da breakfast din parlor ta durkusa ta ajiye saman carpet, dai dai nan aka bude kofar
parlon ta daga kai da sauri. Aneesah ce ta shigo parlon ta kulle kofa tana kallon Jiddah daga sama har kasa
kallon rigima, Jiddah ta dauke kanta ta mike tsaye, Aneesah ta cire takalmanta ta jefar da jakanta saman
kujera tace "Kin gama guje gujen naki kin dawo??" Jiddah ta ki tanka ta, Tana tafe hannu cikin daga murya
tace "Toh gobe ko kallon banxa aka ce ki min wllh sae kin zagi wanda ya baki wannan shawaran, don yau
sai naga d'an kuturin uban da ya tsaya maki a garin kaduna, ba dai ni kika kwala ma vase kika fita a guje
ba...." Jiddah ta bar wajen da sauri ganin ta nufota fiercely, ganin da gaske take sae xaga parlon suke ta
kwala wani kara da karfi gabanta na faduwa, Aneesah tayi wani kukan kura ta cafkota ta sa ta a hammata
ta shake wuyarta, Jiddah dae sae ihu take da karfi tana kokarin kwace kanta, ko gama buttoning shirt dinsa
bai yi ba yake saukowa stairs da saurin sa, still Aneesah tayi tana kallonsa baki bude, kamar ranan ta fara
ganinsa, Jiddah ta fashe da wani kuka ta xube nan kasa, ya shigo parlon walking faster, Aneesah bakinta na
rawa tace "Ca.. Captain yaushe ka shigo..." Bata rufe baki ba ya kifa mata wani mari, without letting her to
recover ya kuma sauke mata wani ya shako wuyarta, ta gwalo idanuwa cike da axaba ihun ma ta kasa, ya
turata da karfi har sae da ta xube kasa, da hannu bibbiyu ta dafe kuncinta bayan ta fadi kasa, ya daga
Jiddah ya wuce sama da ita, Aneesah ta kasa kwakkwaran motsi a inda take tsaye ta bi su da kallo, ita ba
ma ta marin da shakan da yyi mata take ba, kawai so take ta ji sanda ya dawo gidan, da sauri ta nufi kofa
kamar mahaukaciya xuciyarta na wani irin bugawa ta nufi mai gadi, tasowa yayi... tana kokarin calming
kanta tace "Salisu yaushe mai gidan ya shigo? Yaushe ya dawo???" Yace "Tun jiya bayan magariba Hajiya"
Bata san sanda ta furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un da karfi ba, taji cikinta ya hautsine, da sauri ta juya
xata koma ciki sae a sannan ta lura da motar Jiddah a parking space don da ta shigo bata lura ba, shi dai ya
bi ta da kallo ya girgixa kai kawai ya koma ya xauna, gaba daya hankalin Aneesah yyi mugu mugun tashi,
bata ta6a shiga tashin hankali irin na wannan moment din ba, ta ma rasa wani kalan tunanin xata yi, jikinta
na rawa ta dau handbag dinta ta haura sama da gudu ta bude zip ta ciro makulli xata saka taga makulli jikin
kofar already, all her body was shaking, ta murda kofar ta ji a bude, ta jefar da jakanta kan gado ta shige
bandaki a guje, sae da tayi minti goma sannan ta fito har sannan jikinta rawa yake, ta kalli xannuwan gadon
dake xube a kasa, ko ta kansu bata bi ba ta ciro wayarta ta shiga kiran Rabi'ah, tana dagawa ta sakar mata
kuka tace "Rabi'ah wllh na dawo na tadda captain a gida, kuma a gidan ya kwana Rabi'ah, Rabi'ah am i not
done today???" Rabi'ah tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ya dawo??" Aneesha ta kara fashewa da
matsanancin kuka tace "Na shiga uku na Rabi'ah, na shiga uku na lalace, yanxu me xance masa, ta ina xan
fara? What will i tell him, ki gaya min don Allah Rabi, ina xance masa na kwana??" Kuka take kamar xata
haukace, Rabi'ah tace "Tabdi, kawai kice masa daga gidana kike, to me xaki ce da ya wuce haka?" Aneesah
jikinta sai rawa yake tace "No Rabi'ah baki san waye captain ba, jiya fa mun ta waya da shi da daddare a
sunan Ina gida, ashe yana gidan muke ta wayar" Xubewa kasa tayi tana kuka da karfi tana cewa ta shiga
uku, Rabi'ah tace "Atoh tunda uwarsa shegen saukin kai gareta kawai kiranta xakiyi ku hada baki kice ta
rufa maki asiri tace daga can kike, a can kika kwana, ko kuma ki fito kawai yanxu mu je mu sameta a gida
sai ince mata wllh gidana kika kwana baki da lafiya sosai, nasan dai baxai wuce tayi ta fada ba kamar
rubabbiya daga nan sai kuma a wuce wajen ta samar maki mafita" Aneesah dai hawaye take tana naxarin
shawaran Rabi'ah gaba daya she is just confuse and afraid, bata son wani abu da xai yi sanadin captain ya
rabu da ita, baxata ta6a rayuwa babu shi ba, sai kuma ta share idonta jikinta na rawa tace "Gani nan
tahowa" daga haka ta figi jakarta da waya ta fice daga gidan. Lallashin Jiddah dake hawaye Abuturrab ya
dinga yi a bedroom dinsa, yana stroking bayanta a hankali yace "Komai ya xo karshe in sha Allah Babynah,
it's all over now...." Ita dai bata ce masa komai ba tayi lamo jikinsa idonta a lumshe, in dai tana jikinsa jin ta
take kamar a sky, the feeling is just heavenly, ta goga fuskarta a bare chest dinsa a hankali, and that
immediately turned him on... Ummi ta dinga kallon Aneesah da mamaki ta ma rasa me xata ce mata,
Aneesah ta durkusa da gwiwowinta biyu cikin matsanancin kuka tace "Don girman Allah Ummi ki
taimakeni ki rufa min asiri, wllh kawai don bani da lafiya ne ta xo ta daukeni xuwa gidansu, shima kuma
yasan bani da lafiya don har asibiti ya kai ni, Na rantse babu abinda nake iya yi da kai na Ummi, shi kuma
muna ta waya da shi ban san ashe yana gidan ba, kuma bai nuna min ya dawo ba, don Allah Ummi ki ce
masa s gidan nan na kwana" Kuka take kamar ranta xai fita ta kife kanta da kujera tana kukan da karfi,
Ummi tace "Wannan wani irin shashanci ne ki bar gidan mijinki ki tafi gidan kawa ki xauna wai baki da
lafiya Aneesah, Jiddah bata gidan ne da baxa ta taimaka maki ba idan baki da lafiya?" Aneesah ta dago
cikin kuka tace "Ummi har amai na sha yi a gabanta ko sannu bata ce min ba, ko ruwa xan sha dole haka
xan lallaba in sauka kasa da kaina, har gida Rabi'ah ta xo ta daukeni ba wai da kaina na tafi can din ba
Ummi" Ummi dai ta rasa abinda ma xata ce, can ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Allah ya kyauta, xan kirasa
amma gaskiya baxan ce a nan kika kwana ba, menene amfanin karya a rayuwa? Maimakon ya gyara maka
lamarinka ma sae dai ya cakudesa, don haka xance gidan kawarki kika kwana kuma xan basa hakuri..." cikin
rawan murya Aneesah tace "Nagode Ummi" Rabi'ah bata dade a gidan ba ta wuce.... throughout ranan
Aneesah a kwance ta yini kamar mara lafiyar ta lulluba da uban bargo a dakin Ummi, she wish xa a gama
issue din nan a wuce wajen ta samu rest of mind, da taji an Shigo parlorn Ummi sae ta kasa kunne ta ji ko
captain ne. Abuturrab na kallon Hajiya Fatima bayan ta gama jawabin da take, a hankali yace "Allah ya kara
girma Mama, mun gode kwarai da wannan effort din naki, in sha Allah xa mu je can din gaba daya xuwa
goben da kika ce in sha Allah" Tace "Madallah da fahimtata da kayi Aliyu, su kuma iyalanka ina ga idan da
hali da ka raba masu gida, amma ka fara shawartar iyayenka yanda ku ka yi da su, in my thought hakan
kadai ne xai sa kai ma hankalinka ya kwanta kayi concentrating a aikin ka...." Yayi Murmushin karfin hali
yace "Haka ne Mama, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi" Ta mayar masa da murmushin tace "Ameen
my son" Mikewa yayi jin an tada sallan azahar ya mata sallama yace "Xan shiga masallaci" Tace "To shkkn
Aliyu, a gaida Jiddar" Yace "Xata ji in sha Allah Mama, bacci take ne shi yasa bamu shigo tare ba" Tace "Toh
maa sha Allah" Fita yayi daga gidan ya shiga masallacin dake layin, bayan an idar ya koma gidansa, makullin
main entrance din gidan ya ciro a aljihunsa ya bude kofar ya shiga, sama ya haura ya shiga bangarensa
xuwa bedroom, bacci Jiddah ke yi har sannan, ya xauna gefen gadon yana shafa fuskarta a hankali ta bude
idanuwanta, ya hade goshinsa da nata yayi kasa da murya yace "Sallah... My lazy wife" ta lumshe idonta
bata ce komai ba, yayi kissing lips dinta yace "Wa ya koya maki shagwaba haka?" Ita dai bata bude idonta
ba, ya juya yana kallon wayarsa dake ring ya mike ya tafi gun wayar ita kuma ta tashi xaune ta sauka daga
saman gadon ta shiga bandaki, Abuturrab ya daga wayar ya kai kunne ganin Ummi ke kiransa ya xauna
gefen gado yayi mata sallama sannan ya gaisheta, ta amsa tace "Kana gari ne?" Ya d'an yi jim, sai kuma
yace "Eh na shigo jiya da daddare" Tace "To ina nemanka yanxu" yace "Toh Ummi, hope all is well?" Tace
"Alhmdlh" yace "In sha Allah xan shigo nan da some minutes" Tace "Maa sha Allah" daga haka ta katse
wayar, yana xaune dakin har Jiddah ta idar da sallah sannan ya kalleta yace "Ki shirya xa mu je can gida"
Tace "Toh" tashi tayi ta nufi kofa xata tafi dakinta, ya bi ta da kallo har ta fita, ya lumshe ido ya kwanta
saman gadon yana jin wani sonta na musamman na ratsa can kasan xuciyarsa, she is just the perfect wife a
man can pray for, both on bed and vice versa.... Karfe biyu da minti sha biyar Abuturrab ya bar gidan tare
da Jiddah xuwa gidansu, lkci lkci yake murxa hannunta a cikin motar har suka isa gidan,, parking yyi a waje
suka shiga compound din, tana biye da shi suka shiga parlon Umminsa bayan Jiddah ta gaisa da Ummi ta
mike ta fita xuwa dakin Hajja, Ummi tace "Me ya hadaku da Aneesah Aliyu?" Da mamaki yace "Aneesah
kuma? Tace wani abu ya hada mu ne?" Ummi tace "Ehh ce min tayi ta maka laifi koh" Yace "Ohh ohk,
kawai tasan abinda tayi bata kyauta bane shi yasa ta damu kanta, ae ni ban ce mata komai ba, ta kira ki
ne?" Infact tun da ya shiga dakinta yaga bata nan bai sake bin ta kanta ba, Kuma da ya ganta shi kansa
yasan hukuncin da xai dauka a kanta ba karami bane, Ummi tace "Tana gidan nan" shiru yyi ya ki cewa
komai, Ummi tace "Tace taje gidan kawarta har ta kwana without ur knowledge kuma tayi maka karya tana
gida without knowing kana gidan kai ma, is that so?" A hankali yace "Ummi ban dau issue din personal ba
ni, it's okay..." Ummi tace "Kayi hakuri Aliyu, i know it's painful ko don karyan da ta maka, shine ma worst
part din, bata kyauta ba wllh, amma just over look it, tunda har ta gane kuskurenta and she is
remorseful..." Yayi murmushin karfin hali kawai yace "Babu komai Ummi" Ummi tace "Good, but she is still
sick tun safe take kwance abincin ma bata iya ci wai, asibitin xaka mayar da ita?" Yace "Toh Ummi" mikewa
tayi ta fita, ya jinginar da kansa ransa na wani irin baci, she even have the guts to come to his mother, rike
bakinsa yyi cike da mamaki da takaici, can ya ciro wayarsa yyi dialing number Ahmad yana fara ringing
Abuturrab yace "Plss tell me u are in kaduna" Daga daya bangaren Ahmad yace "What happened?"
Abuturrab yace "Tell me so pls" Ahmad yace "Yeahh i am in..... Abuja" Abuturrab ya hade rai, Ahmad yyi
dariya sosai jin Abuturrab yyi shiru don ko ba a gaya masa ba yasan hade rai yyi, Ahmad yace "Toh me ke
faruwa kake hoping am in Kaduna?" Abuturrab yyi kasa da murya cike da damuwa yace "It's something
very very urgent Ahmad, i have nobody to talk to da ya wuce kai wllh" Ahmad yace "Ba a maganan ta waya
ne?" Abuturrab yace "Ya fi karfin ta waya Ahmad" Ahmad yace "So what are you insinuating? In taho kd
yau?" Abuturrab yyi kasa da murya yace "Plss" Ahmad yace "Ka ci kai, to matata labor take a tsattsaye, and
she just start today, don haka kaga baxan bar ta in taho kd ba" Abuturrab yace "Allah ya raba lafiya, but
baxa ka taho tare da ita ba" Ahmad yace "Saboda issue din Captain sae matata ta haihu a titi?" Abuturrab
yace "I was thinking sati uku ake dauka ana labor din ae" Dariya Ahmad yayi yace "Aa sae dai wata uku"
Shiru Abuturrab yyi, and Ahmad gets that he is so disturbed nd tensed, Ahmad yace "Xa mu yi magana,
sae anjima" a hankali Abuturrab yace "Alright" daga haka ya katse wayar ya dafe kansa. Sae kuma ya mike
ya fice daga parlon, Ummi da ke can main parlor tace "Xa ku tafi asibitin ne yanxu?" Yace "Ahmad xae xo
dubata yanxu, ae munje asibitin few days ago" Ummi tace "Eh