Showing 174001 words to 177000 words out of 321711 words

Chapter 59 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt

Umma dai bata ce komai ba, Jiddah ta mike a hankali ta nufi kofa,
Abuturrab na kallon Umminsa yace "Aunty na nan?" Ummi tace "Sai kaje ka duba" Bai ce komai ba, sai
kuma ya mike yace "Bari in gaisheta in dawo yanxu" Daga haka ya nufi kofa daga Ummi har Umma suka bi
sa da kallo, Umma tace "Mu je ciki akwai magana yaya" Ummi ta mike tace "Toh" a tare suka shiga
bedroom din Ummi... Abuturrab na fitowa bangaren Ummi kitchen ya nufa direct, Jiddah ta juya da sauri
jin an shigo kitchen din, suna hada ido ta juya masa baya, kana ganinta kasan duk a tsorace take ta ma rasa
me take yi, sai kuma ta tuna miyan ganyen xata xuba a bowl, tana cikin xubawa taji muryarsa yace "Saboda
nace ki daina gaisheni shi yasa idan kika gan ni sai ki min kallon banxa ki wuce right?" Kasa ce masa komai
tayi amma banda bugawa babu abinda xuciyarta yake gashi taki juyowa, bude kitchen din aka yi ta juya da
sauri, Mai aikin gidan ce ta shigo ganin Abuturrab ta koma xata fita, da sauri Jiddah ta ajiye bowl din miyar
hannunta ta fice ta kofar da tagani a kitchen din wanda ke a bude, da mamaki ya bi ta da kallo, har ta
xagayo gaban compound din gidan waige waige take ko ya biyota amma bata ga haka ba, mai gadi ya bude
gate sai ga mota ya shigo, ko parking din motar ba a yi ba, motar na tsaye tsakar compound din aka bude
back seat sae ga Hajja ta sauko da katon jakarta, Jiddah ta karasa gunta don amsan jakarta, Hajja sae
kallonta take can tace "Wannan kafafuwa naki haka kamar a Masar, kinsan su ma haka kafafuwansu yake
farare tass da yake larabawa ne, to ke kuma ba balarabiya ba sae dai ko sadaka yalla" Jiddah dai tayi
murmushi ta amshi jakar Hajja tace "Sannu da dawowa Hajja" Hajja tace "Yauwa wajen d'ana sarkin Bauchi
naje, ai da ke nayi niyyar xuwa Usman ya hanani wai inyi ta kaina, banda haka da na kai ki kinga ikon Allah,
to ina takalman naki kike yawo haka ke kuwa? Ita mace ae ba a santa da yawo babu takalmi ba, barin ke da
taki kafar kamar ta 'yan Masar" El-Basheer ya sauko daga mota yana kallon Jiddah, Jiddah ta d'an kallesa
tace "Ina yini?" Yayi murmushi yace "Lafiya lau Jiddah, how are you doing?" Tace "Alhmdlh" Hajja tace "To
ki tsaya ku gaisa a tsanake idan kun gama sai ki taho min da jakata kin ji" Daga haka tayi wucewarta, Jiddah
ta d'an kallesa, Murmushi yayi yace "Ya karatu?" Tace "Lafiya lau" yana kallon kafafuwanta yace "Ina
takalmanki" Tace "Aa ta kofar kitchen na fito ne" Yace "To muje ciki" Tana gaba yana biye da ita suka wuce
parlor din gidan, Abuturrab na xaune parlor Hajja na tsaye sai basa labari take, shi kam ko kallonta baya yi
banda danna wayarsa da yake, Jiddah ta shigo parlon tare da El-Basheer, Hajja ta kallesu tace "Har kun
gama gaisawa?" Jiddah dai bata ce komai ba tayi hanyar dakin Hajja da jakarta bayan ta saci kallon
Abuturrab, Hajja ta bi bayanta murya can kasa tana cewa "Ki daina abu kamar er kauye 'yar nan, kamata
yyi ki buda baki kuyi tadi da shi sosai, ba wai ki ta sunkuyar da kai kina murmushi ba, ubansa fa shine
sarkin Bauchi gaba daya, kuma ni na haifi uban, na ya6a da hankalinki ne shi sa nake ta cusa masa ke,
amma naga ke kuma kina abu kamar wawa, haba kar kyanki ya tashi a banxa mana er nan" El-Basheer na
kallon Abuturrab da ya ki dago kai yace "Na kira ka daxu wayarka a kashe" Abuturrab ya kallesa yace "Ohk
kilan na kashe then, ya hanya" El-Basheer yace "Wannan mata ta fiye fitina wllh, i have to drive her all the
way from kano, and in sha Allah gobe xan koma Bauchi" Abuturrab ya mike yace "Toh muje can gidana,
tafiya xan yi nima" El-Basheer ya d'an buda ido yace "Ae ban gaisa da su Ummi da Aunty ba" Abuturrab
yace "Duk basa nan, if u are going mu tafi yanxu don ni tafiya xanyi, gobe idan xaka koma Bauchin sai kaxo
kayi masu sallama da safe" El-Basheer ya d'an shafa kansa yace "Ohk, i can even still come back at night in
gaisa da su" Abuturrab yace "Eh xai ma fi" Daga haka suka fita parlon, a hanya Abuturrab yayi masu take
away din abinci, El-Basheer na kallonsa da mamaki yace "Aneesah bata yi girki bane?" Abuturrab yace
"Ehh bata jin dadi" El-Basheer yace "Toh Allah ya sauwake" Abuturrab yace "Ameen" sai da suka kusa
gidan Abuturrab ya fara xullumin condition din da xai je ya tarar da gidan nasa with El-Basheer. Amma ga
mamakinsa yana bude kofar parlor yaji wani kamshin turaren wuta me dadi ya doki hancinsa, ga sanyin Ac
da ya cika parlon, suka shiga ciki tare da El-Basheer, the parlor was more than clean, banda kyalli babu
abinda kayan kallon parlon suke, bin ko ina Abuturrab ya dinga yi da kallo yana mamakin anya gidan nasa
ne kuwa wannan, El-Basheer ya xauna yana sauke wani numfashi yace "Gidan Amare daban yake, so cool"
Daga sama Aneesah ta sauko da atamfa riga da skirt da ya kamata ta kashe dauri, fuskarta kuma tayi light
make up, tayi kyau sosai kamar a sace a gudu, da murmushi ta karaso cikin parlon tace "Sannunku da
xuwa, bako muka yi captain" El-Basheer yace "Fatan mun same ku lafiya amarya?" Tana ci gaba da
murmushi tace "Alhmdlh, u are welcome" karasawa tayi kusa da captain ta xauna gefensa tace "Welcome
my captain" Yana gyara xama yace "Yauwa thank you" Murmushi bai gushe a fuskarta ba ta mike ta wuce
kitchen, sai gata ta dawo da ruwan gora biyu da drink sai cups, ajiye masu tayi tace "Ga ruwan sanyi" El-
Basheer yace "Thank you Aneesah" Ta xauna one sitter tana kallon captain dake ta danna wayarsa, El-
Basheer ya dau ruwa ya fara sha, tace "A kawo abinci yanxu?" Sai da captain ya daga kai ya kalleta jin
abinda tace, tayi fari da ido tace "Eh, ko sai anjima" El-Basheer yace "Aa kawo min ni dai, Captain sai ya ci
take away din da yayi" Ta mike ta dau ledan take away din ta wuce kitchen tana cewa "Shi ma baxai ci ba,
ga dai abinci nayi" Captain ya bi ta da kallo, manyan warmers kusan biyar ta kawo parlon ta dire kan
carpet, ta koma ta dauko plates, da serving spoon ta ajiye masu tana murmushi tace "Bismillah" daga haka
ta wuce sama, El-Basheer ya sauka kasan carpet yana bude warmers din, Abuturrab ma sae kallon
warmers din yake, wani lafiyayyen fried rice ne a warmer daya, dayan kuma wainar shinkafa sai tiriri yake,
ga hadadden miyar taushe dake ta kamshi, wani warmer kuma peppered chicken ne that looks so enticing,
last warmer din pepper soup din kayan ciki shi ma sai kamshi yake, kallon foods din kawai Abuturrab yake,
tuni El-Basheer ya fara diban abubuwan da xai diba, Abuturrab ya ci gaba da danna wayarsa, sai kuma ya
mike ya wuce kitchen, ko ina fess a kitchen din babu kayan wanke wanke, ya fara dube duben inda xai ga
take away din da ta dauke a parlor bai gani ba, hakan ya sa ya bude kofar kitchen yaga a bola ta jefar, ya fi
second biyar yana kallon ledan abincin kafin ya gyada kai ya kulle kofar ya fice daga kitchen din, ya dawo
parlor ya xauna, El-Basheer yace "Kai baxa ka diba abincin ba?" Ya girgixa kai yace "Na ci abinci a can gida
ai" Yace "Ohkk" Abuturrab da El-Basheer suna tare parlon har kusan magrib, ita dai Aneesah na sama, duk
da yunwan da Abuturrab ke ji amma ya ki cin abincin, ana kiran magrib suka yi alwala a toilet din
downstairs, Abuturrab yyi mamakin ganin toilet din ma fess, ana idar da sallah bayan sun fito masallaci El-
Basheer yace ma Abuturrab xai koma can gida don su gaisa da su Ummi tunda gobe da safe xai koma,
Abuturrab yace "Toh bari in dauko makullin motar" yana shiga ciki ya dauko makullin motarsa ya fito suka
wuce can gidan, El-Basheer ya nufi bangaren Ummi don gaisheta, shi kuma ya tafi dakin Hajja, Hajja na
gyara labulayenta Jiddah kuma na durkushe tana sa turaren wuta a garwashin da Mai aiki ta kawo ma Hajja
a kasko, Hajja na ganinsa tace "Aliyu wllh bauchi da naje baka ga wata yar yarinya da na maka sha'awa ba,
duka duka yarinyar bata wuce Jiddan nan ba, amma abinda yasa ban ce masu komai ba saboda ban san
irin tsaftar yarinyar ba, kaga yanxu shi Bashir warce nake sa ran hadashi da ita nasan tsaftarta, to ita
wancan gaskiya ban sani ba" Abuturrab dai bai ce mata komai ba, Hajja tace "Duk kwanan nan da kai nake
kwana a raina nake tashi, saboda nasan kana cikin jarabawar auren mata kazama, amma in sha Allahu ka
sha kurumin ka ina nan ina maka fafatuka, yanda na samar ma Bashir yar kirki me tsafta kai ma haka xan
samo maka, Shi kansa Kabiru yyi farin cikin wannan xabin da nayi ma Bashir, uwarsa kuma babu abinda
xance da ita sae dai ta ci kanta ni ba ta ita nake ba... Yanxu Usman nake jira ya dawo inji ynda xa a yi, ko shi
ne xai xama waliyyin yarinyar to... Bashir kuma yace min shi dai a shirye yake ko gobe ne a daura, amma ae
ba gaggawa ake ba ina laifin ma nan da sati uku" Abuturrab yace "A ina kika samar masa matar?" Hajja ta
wani kallesa tace "Aa wannan kuma ba ruwan ka ae, wllh Kabiru yace min ya amince indai Bashir din na so,
ae karfin xuwa na Bauchin kenan..." Abuturrab ya shafa kansa ya ki cewa komai, can ya kalleta yace "Toh
ban ci abinci ba, yunwa nake ji" Hajja tace "Aa ba ma ga yunwa ba a gidan nan, ga dai abinci kaca kaca ka
wani ce yunwa, bari wannan yarinyar Nafisah ta shigo ta xubo maka, naga lafiyayyen girki aka yi a gidan, ae
Hauwa dama Allah ya hore mata iya sarrafa hatsi" Yace "Sae Nafisa ce xata ban abinci?" Hajja tace "Aa
nima sae in je in xubo maka, meye a ciki" yace "To ita warcan baxata iya xuba min ba" Hajja ta kalli Jiddah
dake duke da turaren wuta kusa da ita har sannan tace "To ke tashi ki xuba masa" Jiddah ta wani 6ata
fuska, Hajja dae sae kallonta take, can ta mike ta nufi kofa ya bi ta da kallon gefen ido, Hajja ta rike ha6a a
hankali tace "Sae naga kamar ta fara kiwiya ita ma, to ni dae fa kar ta sa inji kunya a kan abinda nake shirin
yi, ko dai tana boye wasu halayyanta ne ban sani ba" Mikewa Abuturrab yyi ya fita daga dakin... Yana shiga
kitchen din ya kulle ta juya tana Kallonsa kamar dama tasan xae biyota, ya rungume hannunsa yace "Yanxu
ma ki fita ta inda kika fita daxu" Ita dai bata ce komai ba ta ci gaba da dibar masa abincin a hankali, yace
"Bude kofar ki fita nace" still taki kallonsa, tsawa yayi mata yace "Baki ji na ne" Ta kallesa kamar xata yi
kuka tace "In fita in je ina?" Yace "Inda kika je daxu" Ganin ya nufota ta tafi ta bude kofar ta fita tana
kallonsa xuciyarta na bugawa, banda hasken wata babu wani haske a wajen, fitowa taga shi ma yayi bayan
ya kashe fitilar kitchen din, bata san lkcn da ta tattare skirt dinta ba da xumar fallawa a guje yayi hanxarin
cafkota da sauri, sannan ya kulle kofar kitchen din, iyakar tsorata ta tsorata a lkcn, ta marairaice masa tayi
kasa da murya tace "Don girman Allah kayi hakuri ka sakeni... Wllh yanxu Umma xata fito mu wuce gida kar
ta fara nemana, tace min yanxu xa mu tafi" Yace "Toh ta nemeki din mana ina ruwana??" Kasa ce masa
komai tayi amma scene din ranan a kitchen din gidansa ne ke dawo mata wanda hakan yayi mugun daga
mata hankali, duk a tsorace take, ya daure fuska yace "Saboda nace ki daina gaisheni na lura har wani
nishadi kike duk sanda kika gani, kuma confidently kike wucewarki..." Tayi narai narai da ido tace "To
amma ai kai kace in daina gaisheka, kuma abinda kace min ai shi nake yi" yace "Amma kuma ai murna kike
don baki gaisheni?" Ta kasa ce masa komai gabanta na mugun faduwa, sai kuma ta fara kauda fuskarta
saboda saukan breathing dinsa da take jiyowa don dab da ita yake, yace "Ohk ni kike dauke ma fuska?" Ta
fashe da kuka tace "Ni don girman Allah ka sakeni ana jirana, don Allah fa nace maka...." Tana ganin xai
juyo da fuskarta saitin nasa ta rufe fuskar nata a jikinsa hankali tashe tace "Don Allah kayi hakuri bana so
wllh" wrapping dinta yyi jikinsa yace "Xan sake ki amma sai kin bani amsar tambayar da xan maki yanxu"
Banda bugawa babu abinda xuciyarta ke yi tana jiran jin tambayar tasa, ga kamshinsa me dadi da ya cika
hancinta, duk taji ta kasa ci gaba da tsayuwa, xata xame kasa yace "Kee" a hankali tace "Na gaji don Allah
ka bar ni in tsugunna" da bango ya hadata ta rufe idonta da sauri, sai kallon fuskarta yake a duhun, taji
yace "Duk xaman da muka yi dake a gida daya ki lissafo min abubuwan da na maki na rashin adalci..." A
hankali ta bude ido tana kallonsa, yace "Ina sauraronki" Ta girgixa kai tace "Aa babu" ya dafa shoulders
dinta yace "Karya kike" Tace "Ba karya nake ba, ban tuna abinda ka min na rashin adalci ba" Yace "To ina
son ki tuna sai ki gaya min" Tayi shiru, shi dai kallonta kawai yake, murya can kasa tace "Amma me yasa
kake ta6ani bayan kasan ni ba muharramarka bace, nasan kuma ka fini sanin hukuncin...." wani xaro ido
tayi jin cold lips dinsa a wuyanta, da duk karfinta ta turasa shi kuma ya rungumeta gaba daya, ai kam neck
dinta ya sha kisses iri iri ba a cewa komai tun tana iya turasa har ta hakura ta kasa komai, switch din fitila
da aka kunna a kitchen ya sa ya saketa da sauri, without looking at her ya bar wajen, xamewa tayi kasa ta
hade kanta da gwiwa amma hawayen ma ta nemesa ta rasa sae sauke numfashi take... Tunda makullin
motarsa na jikinsa gate kawai ya nufa ya fice ya shiga motarsa ya wuce gida, ko kallon Aneesah dake xaune
parlor duk ta cika turaren wuta bai yi ba ya haura sama yaki xuwa bangarensa ya bude wani daki ya shiga
ya kulle kofar da key ya wuce bandaki direct.... Maimoon ta mike xaune ta kunna switch din dakin dake
gefenta tana kallon Jiddah cikin muryan bacci tace "What happened Jiddah?" Ganin Jiddah taki bata amsa
kuma taki dagowa ta sauka kan gadon ta nufi kofa ta fita xuwa dakin Umma....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you


FZ BEAUTY SUPPLEMENTS
Dealer in all kind of dietary supplements such for skin whitening, skin glowing, weight gain, slimming, flat
tummy, infection killers, dark spots removers, fertility booster, Hips boosters, Breast firming and Enlarging,
Teeth whitening, eye, joint, stretch marks, and for marital pleasure. All supplement are available for
wholesale and retail. For more information contact FZ via wa.me/2348143821028



Umma na shigowa dakin ta karaso kusa da gadon tana kallon Jiddah tace "Lafiya Jiddah?" Jiddah ta dago
kanta da kyar hawaye na sauka idonta amma ta kasa cewa komai, Umma tace "Ciwon cikin ne?" Ta gyada
mata kai kawai, Umma ta kalli agogo dake nuna karfe hudu saura, fita tayi daga dakin ta dau wayarta ta
shiga kiran layin Ahmad, har ya katse ba a dauka ba, Umma ta tsaya tana ta tunanin yanda xata yi kuma,
gashi ita bata driving da duhu, har ta fara tunanin kiran driver dinta sai ga Ahmad ya kira, dagawa tayi tace
"Sorry i woke u up Ahmad, kana gari ne?" Ahmad yace "Aa ban shigo ba, me ya faru Umma?" Umma tace
"Wllh ciwon cikin Jiddah ne ya tasar mata, ni kuma ba driving nake a duhu ba..." Yace "Subhanallah, bata
taho da magungunanta bane?" Umma tace "Ka siya mata wasu maganin ne?" Yace "Ehh na siya mata a can
gida, But Umma Captain na gari ai, ki kirasa sai ya taho ya kai ku asibitin" Umma ta sake kallon agogo, sai
kuma tace "Toh shkkn" Daga haka ta katse wayar, Number Aliyu ta nemo a contact sannan tayi dialing
number, Abuturrab na kwance ya samu bacci kenan kiran Umma ya shigo wayarsa, da yake baccin nasa bai
wani nisa ba ya bude ido da kyar yana kallon wayar tasa, mikewa xaune yyi ya jawo wayar da mamakin me
kiransa at that time, number Umma ya gani a screen, ya daga ya kai kunne, Umma tace "Sorry na tashe ku
Aliyu, idan ba damuwa ka taho gida yanxu xa ka kai mu asibiti..." Yace "Subhanallah.. waye ne ba lafiya?"
Umma tace "Idan ka xo xaka gani" a hankali yace "Toh" daga haka ta katse wayarta, Mikewa Abuturrab yayi
duk da idanuwansa da suka masa nauyi don throughout first hours of the night idonsa biyu ya kasa bacci,
har sae kusan karfe uku da wani abu sannan ya samu sauki bacci ya daukesa, daukar wayarsa yayi ya fita
daga dakin... Ya tafi bangarensa ya bude kofar parlon a hankali sannan ya karasa bedroom dinsa nan ma he
was so careful opening d door, Aneesah na kwance tayi dai dai saman gado tana baccinta, ya karasa gun
kayansa ya dau kayan da xai dauka sannan ya nufi kofa xai fita kenan yaji cikin muryan bacci tace "Captain"
Juyawa yayi ya kalleta, ta mike xaune tace "Ina xaka by this time, naga ka dau kaya?" Bai tanka ta ba ya fice
daga dakin ta bi sa da kallo, ya koma dakin da yake yana cikin shiryawa ta shigo ta kulle kofar, bai ko kalleta
ba ya ci gaba da buttoning din shirt dinsa, ta karaso kusa da shi, sai kuma ta durkushe kasa ta hade
hannunta cikin rawan murya tace "Captain auren soyayya muka yi da kai fa ba auren kiyayya ba, wannan
altitude din da ka tsiro yana sa min ciwon xuciya, don Allah idan wani laifi nayi maka kayi hakuri ka yafe
min ba don halina ba" sai kuma ta fashe da kuka, ya girgixa kai yace "Ni nace kin min wani abu ne?" Cikin
kuka tace "Gashi nan you are ignoring me and giving me altitude for the pass 8 days now, don Allah ba don
ni ba kayi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login