Showing 132001 words to 135000 words out of 321711 words

Chapter 45 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt

ta ta6a aure, yarinya ce fa yar karama bata wuce Nafisah
kanwar mutumin nan dake xaune ba, kuma ai ni na samu labarin wannan auren da tayi ba aure bane don
babu abinda ya ta6a shiga tsakaninta da mijin, a gantale aka yi auren kuma a gantale aka yi sakin, yar
yarinya ce karama fa nake gaya maka wllh, sannan kakan Aliyu nima ai a bazawarar ya aureni tunda sai da
na auri kakanka aka haifi Kabiru da Aisha sannan kishiyoyi suka fiddani, Allah ya hadani da kakan Aliyu ya
aureni sannan na haifi su Usman da Nafisah" Shi dai El-Basheer murmushi kawai yake yace "Toh shkkn ai ni
nasan baxa ki min xabin da xai cutar da ni ba Hajjaju" Hajja tace "Haba haba ai na cuci kaina kenan idan na
cuceka, in sha Allahu xabi ne har xabi na maka, kar ka ji komai a ranka, bari dai mu gama da bikin wannan
mutumin tukun" Abuturrab dai bai daina kallon Hajja ba, El-Basheer yace "Toh baxa mu samu ko d'an
ruwan shayi ba, ni yunwa nake ji fa" Hajja tace "Kaji ka, ai magana xaka yi, har abincin ma akwai naga sun
dafa idan kuna so a xubo maku" El-Basheer yace "Aa shayin dai, bamu yi breakfast ba" Hajja ta mike tace
"Toh bari in sa a kawo maku" Fita tayi dakin xuwa parlor, har sannan su Jiddah na parlor, Hajja tace "Yar
nan ajiye masu sharan su ki xo in sa ki aiki kinji" Jiddah ta ajiye broom din hannunta ta karaso gun Hajja,
Hajja tace "Xuwa xaki yi kitchen ki wanke hannu da kyau, don baya son kazanta Bashir, bayan kin wanke
hannunki ki dau babban faranti da naga suke fafa da shi a gidan nan ki daura masa flask da cokali da kopi
daya sannan ki ajiye kayan shayi a gefe, to shi kuma dayan mutumin ban san ko xai sha ba don ko gaisheni
ma bai yi ba, amma dai baxa a biye ta halinsa ba, shi ma ki dora masa kofi da cokali daya mu mayar masa
da aniyarsa, ki tabbatar duk ki dauraye kofunan don kinsan sarakan tsafta ne su, kuma duk a wajena suka
gado, bayan nan idan akwai burodi ki daura kan tray din duk ki kawo masu" Jiddah tace "Toh" sannan ta
juya ta wuce kitchen, Hajja ta koma daki tace "Toh ba shikenan ba bakina alekum, da wannan gantalallun
'ya yan na saka sai in samu me xagina ma tunda ba isasshen tarbiya garesu ba" Jiddah tayi duk yanda Hajja
ta ce mata, tray biyu tayi ta daura kayan shayin da bread din a daya, dayan kuma ta daura cups da spoon
sai flask din a kai, na flask din da cup ta fara dauka ta fito kitchen din suka kusa cin karo da Aunty ta koma
gefe da sauri, Aunty ta hade rai ta ja gefe, Jiddah ta sunkuyar da kai ta bi gefe ta fita don tun sassafe ta
gaisheta bata amsa mata ba, Jiddah na shiga dakin Hajja, Hajja ta mike ta shimfida rug da sauri tana cewa
"Yauwa yar albarka, sannu kin ji, taho ki ajiye" Jiddah ta sunkuya ta ajiye tray din tace xanje in dauko
dayan, Hajja tace "Toh yi maxa" Shi dai El-Basheer kallonta kawai yake, ta juya ta fita, Hajja tace "Wllh ba
sawa ba hanawa, tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin nutsattsiya me tarbiya irin wannan yarinyar ba,
gashi bata fushi ko kadan yanda ka san ni ce ina karama" El-Basheer yyi murmushi yana shafa kansa yace
"Toh ko dai canje xaki min da sakin wawan da kika ce" Hajja tace "Aa kai dai kayi shiru kawai ka kyaleni
yanda ka gan ni, ban fiye son surutu ba gaira ba dalili ba...." Abuturrab kallon wayar hannunsa kawai yake
amma babu abinda yake da wayar, Jiddah ta dawo da tray din kayan shayin ta ajiye, Hajja tace "Yauwa er
albarka, sannu" Sai kuma ta kalli El-Basheer tace "Ko ta soya maka kwai, naga ta iya, jiya da uwar rikonta ta
sa ta soya mata naga tayi sa da kyau snn bbu karni ga albasa ta yankasa rimi rimi a kai abun zar sha'awa, ni
dai har Ramlah ta gama cin kwan nan banji karni ba" El-Basheer yace "Aa ba sai na bata wahala ba ta bari
kawai" Hajja tace "O'o Allah ina ruwanka da wannan batun, kai dai ba a soya maka kwai ba ka hada da
burodi ka ci, da tana da son jikinta ai baxan ma fara sa ta ba, kaga na bi ta kan yaran gidan nan" Jiddah ta
kalli El-Basheer tace "Xan iya" Yace "Toh je ki soya" kofa ta nufa ta fita, Hajja ta kalli El-Basheer murya can
kasa tace "Ga tsafta kamar tsatsonmu wllh, ko kai baka gani ba?" Shafa kansa kawai yake yana murmushi,
tace "To ni dai ba ruwana, kawai a barni yanda aka gan ni ba banxa nake ba" Bayan kusan minti goma
jiddah ta dawo da kwai rufe a plate da fork biyu a kai ta dora, ta sunkuya ta ajiye plate din kan carpet, Hajja
tace "Allah yayi maki albarka kinji" Jiddah tayi murmushi ta mike suka hada ido da Abuturrab da ya dago
kansa, sunkuyar da kai tayi ta nufi kofa ta fita, El-Basheer ya sauko ya fara hada shayin yana kallon
Abuturrab yace "Hey dude come let breakfast" Abuturrab ya mike yace "Alhmdlh" Daga haka ya nufi kofa
ya fice. Da yamma Jiddah na dakin Hajja ita da Nafeesah, El-Basheer ya shigo da sallama yace "Hajja xa mu
je dauko su Maman Farida" Hajja ta washe baki tace "Ehh wllh yanxu mijin ya kirani wai sun sauka ashe"
yace "Toh dama xance maki sai gobe ne, don ni daga can baxan dawo ba" Hajja ta xare ido tace "Saboda
mene?" Yace "Aliyu xai karaso da su ni xan sauka gida in huta ne" Hajja tace "Aa ba ruwana ba haka Kabiru
yace min ba, bai ce min xaka sauka a wani waje ba nan ba, nan din ba gidanku bane, sannan ba ga dakin
Aliyu ba idan ma bak'in hali Aliyun ke maka ba ga dakin wancan yaron da ya gantale ba Salem yake kowa,
ni tunda na xo har yau ban dora ido a kansa ba idan anyi magana sai uwar tace yana benue, tsafin suke
koya masa a can din oho mu dai ga mu ga Allah, bikin d'an uwansa guda ma gashi babu alamar xai xo, ni
dama a tsorace nake da yaron tun asali" El-Basheer yace "Toh xan dawo" Nafisah tace "Yaya don Allah in bi
ka?" Yace "Airport din?" Hajja tace "Ehh mana ku tafi da ita ai yar makaranta ce" El-Basheer yace "Toh idan
da mijin Nafisan xamu dauko fa" Hajja tace "Toh ai mijin tun da muka dawo da shi bai koma ba, Nafisar ce
kadai ta taho ko yaro daya bata xo da shi ba ta bar ma wata makociyarta balarabiya me kirki, mijinta kuma
na Habuja" El-Basheer yace "Ohk" Nafisah na jin dadi ta dau mayafinta, Hajja tace "Toh gaskiya ni bana son
kai, idan har xa aje dake sai dai a tafi da wannan yarinya Jiddah itama tunda tare kuke, ita ma kuma ba
6are bace" El-Basheer yace "Toh ta dau mayafinta mu je" Nafisah tace "Amma Hajja kar ya Abuturrab ya
koro mu fa" Hajja tace "Xai ko aika, ku mu je gun motar gaba daya" A tare suka fita, suka tadda Aliyu xaune
cikin mota yana jiran El-Basheer, ganinsu gaba daya ya daure fuska, Hajja ta bude ma su Nafisah bayan
mota, Ita dai Jiddah gabanta sai faduwa yake don mayafi ne ita ma jikinta, kallon mamaki Abuturrab ke
masu gaba daya, can yace "Ina xa a kai wa ennnan?" Hajja tace "Usman ne yace a tafi da Nafisah su hadu
da takwararta a Iyapot, ni kuma nace a tafi da Jiddah tunda a kan kunnenta aka yi xancen kuma mu bama
nuna banbanci a xuri'armu" Abuturrab yace "Aa ni baxanje da kowa ba sai dai El-Basheer yaje ya dauko
Aunty Nafisar a Airport" Hajja tace "Amma kasan ina lura da yanda ka raina ubanka, shi fa ya fada bani ba,
albarkacin daga bakinsa hakan ya fito ai sai kayi masa biyayya ko ba ta dadin rai ba kayi abinda yace, ba fa
goyasu xaka yi ba balle kace aiki aka hadaka da, ko wacce xaunawa xata yi a bayan mota har kuje ku dawo,
gaskiya ka sake hali Aliyu, wllh Bashir ba haka yake ba kai dai bar shi da tsokana da mugunta, amma kai
wllh kana da bakin hali" Abuturrab yace "Duk naji su sauka kawai" Hajja tace "Allah ya tsine min idan sun
sauka, a kira min Usman" El-Basheer dake dariya kasa kasa bayan ya shiga front seat ya kalli Abuturrab
yace "Plss let them, it's Abba's instruction" Dama Hajja ko sake kallon Abuturrab bata yi ba tana kallonsu
Nafisah tace "Ku shiga kawai" Nafisah ta turo baki ta shiga motar tana kallon yayanta, Jiddah tace "Hajja ni
ai kince xan wanke maki bandaki ko?" Hajja tace "Aa wancan me fuskar uwar tata xata wanke min, wato
Aisha" Jiddah ta girgixa kai tace "Hajja ni xan wanke kawai su tafi" A fusace Hajja tace "Oo Allah ya ana
yabonki sallah sai ki kasa alwala, bayan nabi duk na barbada ma duniya cewar baki da musu kuma yanxu ki
nemi karyatani gaban yaran nan??" Jiddah ta sunkuyar da kanta tace "Toh kiyi hakuri" Daga haka ta shiga
motar, Hajja tace "Yauwa, ku je Allah ya tsare, idan kinga yalo a hanya ki tuna masu idan sun ga dama sun
siya min to" Daga nan ta kulle motar tayi wucewarta ciki tana cewa "Da ban masa haka ba koran min 'ya
yan xai yi, gwara ma yayi aure kowa ya huta wllh yaje can su ci kansu da matar ni dai xan dinga kai masu
ziyara kawai da d'an rakiya" Tada motar Abuturrab yyi fuska daure ya danna horn mai gadi na bude motar
ya fita compound din ya dau hanyar titi, ta madubi El-Basheer ke kallon Jiddah da ya lura she is
uncomfortable yace "How is ur studies going Jiddah?" Nafisah ta kalli Jiddah dake gefenta, Tana wasa da
gyalenta tace "Alhmdlh" Ya dinga kallonta kafin yace "Hope u are assimilating what u are being taught?" Ta
d'an yi murmushi tace "Ehh" ya langwabar da kai yace "Ni ai ba da Hausa na maki ba ko" sake kallonsa tayi
suka hada ido, sai kuma tayi murmushi, yace "Do you have any idea of where we are heading to now?" Ta
kalli Nafisah dake ta kallonta tana murmushi, Nafisah ta gyada mata kai alamar tayi magana, Shi dai El-
Basheer na ta jiran respond dinta, ta d'an kallesa tace "Ka sake fadan abinda kace" Yace "Ohk.. Did u have
any idea of where we are heading to now?" Ta d'an kalli Abuturrab da fuskarsa babu yabo bbu fallasa yana
kallon titi yana driving, cikin sanyin murya tace "Yes i have" El-Basheer yace "So where are we going to
now?" Tace "Hajja said we are going to take Aunty at the...." Sai kuma tayi shiru, ya gyada kai yace "Yess
good, ci gaba" Tace "Airport?" Murmushi El-Basheer yayi sosai yace "Ohh yes, Hajja said we are going to
pick Aunty Nafisa from the Airport" Ta sunkuyar da kai ita ma tana murmushi, Nafisah dai sai kallonta take,
El-Basheer yace "So can you brief me about ur self?" Ta d'an yi shiru sai kuma ta kallesa yace "I am all ears"
Tace "My name is Hauwa Jiddah yusuf, i was born and brought up in kaduna hayin rigasa, i lived with my
step mum not until..." Da sauri Abuturrab ya kauce ma mai mashin da ya kusa bugewa, Nafisah da taga
yanda abun ya faru tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da mamaki El-Basheer yace "How manage?"
Abuturrab ya sauke glass ya ba ma mai mashin din hakuri ya ja motarsa ya kara gaba ba tare da ya tanka
kowa ba, El-Basheer yace "Are u sure hankalinka na kan tukin nan Aliyu?" Abuturrab bai tanka sa ba still
yana driving din, El-Basheer yace "Toh Allah ya tsare" Maida dubansa yayi kan Jiddah ta madubin gaba
yace "Go on Jiddah" tace "I am currently living with Umma at Unguwar Dosa..." Sai kuma tayi shiru,
kallonta kawai El-Basheer yake, tayi murmushi tace "Shikenan" Yace "Yea, kinyi kokari sosai Jiddatul Khair,
maa sha Allah" Ita ma murmushin tayi tana daga kai suka yi ido hudu da Abuturrab dake kallonta ta
madubi, ta sunkuyar da kanta, Nafisah ma duk tana lura da kallon da yake ma Jiddah ta dinga fatan Allah
ya sa kada yaje ya sake buge wani kuma. Aunty Nafisah ta rungume takwararta cike da murnan ganinta
tace "Haka kika girma Nafisah" Nafisah dake ta washe baki tace "Aunty me yasa baki taho da su Farida
ba?" Aunty Nafisah tace "Suna makaranta ne amma in sha Allah xa su xo wani lokacin" Sai a sannan ta kalli
Jiddah, Jiddah ta gaisheta da ladabi, Aunty Nafisa ta amsa da fara'a tana kallonsu El-Basheer tace
"Wacece?" El-Basheer yace "Yarinyar Umma ce" Aunty Nafisa tace "To madallah" Tuni Abuturrab ya wuce
da trolley dinta, duk suka bi bayansa xuwa mota, bayan ya saka jakan a booth ya shiga driver seat, Su ma
suka shiga motar sannan ya bar airport din, hira kawai El-Basheer ke yi tare da Aunty Nafisah da ta fita
harkan Abuturrab ganin yanda ya tarbeta a airport, shi dai driving dinsa kawai yake, suna fara shigowa gari,
Jiddah na kallonsa tunda ita ce setin kujeransa ta d'an matsa, El-Basheer ya kalleta ta gefen ido, a hankali
tace "Yaya... Hajja tace a taho mata da Yalo wai" Abuturrab da ya ji ta sarai don setin ears dinsa tayi
maganan yyi shiru yana driving dinsa, El-Basheer yace "Kina son wani abu ne Jiddah?" Ta kallesa tace "Aa
Hajja ce tace a siyo mata yalo" El-Basheer yace "Ohk idan an gani sai a siya mata" Luckily suka samu yalon
El-Basheer yace "Oga ka samu waje kayi parking a siya ma Hajja yalo" Abuturrab yace "Wa ennan
rubabbun abubuwan" Daga haka ya ja motarsa ya ki tsayawa, Aunty Nafisah dai bata ce masu komai ba, El-
Basheer yayi wani murmushi shi ma bai ce komai ba, sai da suka kusa gida Abuturrab yace "Aunty ya baki
taho da zee ba?" Tace "Ban sani ba" Murmushi kawai yayi ya shiga layinsu, a kofar gida yayi parking, El-
Basheer ne ya fara sauka, Aunty Nafisah ta sauka, snn Nafisah, Jiddah xata sauka Abuturrab yace "Tsaya"
kallonsa tayi, ya hade rai yace "Ke har wani nishadi kike kiyi ta hira da kattin maza kina washe baki don baki
da kamun kai koh? To daga yau na sake jin kin wani bude baki kina ma wani turanci xan baki mamaki,
sannan ki ci gaba da yawo da kananun gyale" Ita dai kallonsa kawai take, yace "Saukar min a mota" bude
motar tayi ta sauka ta wuce cikin gida ya bi ta da kallo.....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last
bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd
getting rid of any skin problems

Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta
samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar
rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata
masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda
zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada

Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240



Washegari har karfe goma na safe Abuturrab na dakinsa kwance, babu wanda ya san yana cikin gidan
banda Aunty da ta shigo tun karfe takwas wai ya tura ma Aneesah kudin make up, wanda ya tura da farko
yayi kadan, babu yanda ya iya haka ya tura kudin, bayan nan kuma bata sake shigowa ba. Goma saura yan
mintuna El-Basheer ya shigo gidan tare da Ahmad, don ba gidan ya kwana ba, El-Basheer ya dinga kallon
Abuturrab yana 'yar dariya yace "Wannan ai ko kaine amaryar sai haka, ka wani makale a daki tun jiya
kamar wanda xa ayi ma auren dole, kamar dai ba Aneesah bace matar" Ahmad yyi murmushi shima yana
kallon Abuturrab yace "Captain duk xullumin auren ne ya ramar da kai haka..." Abuturrab yace "Saboda ita
ce xata aureni ba nine xan aureta ba ko?" Ahmad yace "Toh wa ya sani, ita dai tana can tana ta sabgar
gabanta da kawayenta, kai kuma kana nan ka makale a daki" El-Basheer ya nufi kofa ya fita xuwa dakin
Hajja, Hajja na ganinsa tace "Ina Aliyun?" El-Basheer yace "Yana dakinsa" Hajja tace "Dama yana gidan
nan?" El-Basheer yace "Yana nan" Ta mike tace "Ni ba ruwana, gida duk jama'a sun cika kilan babu wanda
ya bi ta kan ko ya ci abinci ko bai ci ba, ita Ramlah naga sai masu kudi kawai take ma marhaba tayi ta nan
nan da su duk ina lura da ita, kaga ai ko shigowa ta tambayeni ko an kawo min kumallo bata yi ba wllh,
gwara ma Hauwan ta kawo ma Nafisah da kanta...." El-Basheer ya bi ta da kallo yana murmushi har ta fita
sannan ya xauna yana kallon Aunty Nafisah yace "Ina kwana Aunty?" Tace "Lafiya lau Bashir, ashe baka
kwana gidan ba" Yace "Ehh yanxu na shigo, ya gajiyan ku" Tace "Gajiya ta bi lafiya, karfe nawa ne daurin
auren?" Yace "Sai an sauko Juma'ah in sha Allah" tace "To maa sha Allah" Ahmad ne ya shigo dakin da
sallama, Aunty Nafisah tace "Bokan turai ina ta xuba idon ganinka tun jiya ban ganka ba" Yana murmushi
yace "Sannu da isowa Aunty, ya hanya" tace "Alhmdlh Ahmad" Hajja na shiga dakin Abuturrab ta tsaya
daga bakin kofa tace "Kunga abinda nake gudu ko? Yanxu tun safe babu wanda ya kawo maka kumallo
kenan?" Ya d'an kalleta amma bai ce komai ba, tace "Toh ni ba ruwana wllh, wannan ai ba yi bane" Tana
fadin haka ta fita, dakin da yan matan gidan suke ta tafi ta bude, bak'i ne kawai a dakin ta gama kare masu
kallo tace "Tirrr" sannan ta fita tana girgixa kai tace "Abin dai ba tsari, wa xai yarda da wnn gayyar a Masar,
wasu ma rabonka da su ya fi shekara talatin amma suna jin biki xa su taho riiii, ko yar shinkafar suke ma
oho" Safiyya ta gani tace "Ke ina Jiddah?" Safiyya tace "Umma ta aikesu da Maimoon can gida" Hajja tace
"Toh kije duk yanda xaki yi a kitchen ban sani ba, amma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login