Showing 156001 words to 159000 words out of 321711 words
dinga kai ta, idan xata dawo kuma ta samu abun hawa tunda kinga hanya ce" Umma tace "In dai
am samu nan kusa kusa a samar mata admission kawai, don unguwar da kake yyi nisa" Ahmad bai kuma
cewa komai ba, can ya mike yace "Toh shkkn Umma, xa mu yi waya kar muyi missing train" Umma tace
"Toh Allah ya tsare hanya, ya kiyaye, kuma ku yi addu'a" Yace "In sha Allah" Daga haka ya fita dakin ya kulle
mata kofa.....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
*Assalamu Alaikum Everyone ba dogon labari bane ba🤗*
*Sunana Ummu Nuwairah (Known as Mîkyããj Sããdy)*
*Shin kina fama da kuraje ne ko tabo🤔,shin kina son ki haske? Shin kina fama da matsalar fata ne? Ko ko so
kike ki haske me aji ba wai kamfala ba, ki koma santsin madara yaukin zuma🥰*
*To matso kusa kiji 'yar mîkyããj Sããdy tazo miki da hadaddun kayan gyaran jiki, masu kamshi kaca kaca😍😍
kuma a cikin kudi kalilan😃kayan mu ingantattu ne babu sight effects a ciki, kuma ina mai tabbatar miki in
kika saya da izinin Allah sai kin dawo, kin kawo wasu, kema kuma ki fara sara💃🏻💃🏻*
_Domin ganin kayayyainmu ku bibiye mu ta Instagram @mik_yaaj_saady
WhatsApp no: 08061570778
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Em3E7rFyyhoGd7Upakosyk
Bayan kwanaki kadan da Umma tayi magana da Ahmad sai gashi ranan wata Asabar ya shigo gida rike da
admission form na Jiddah da receipt na kudin makarantar, Umma ta gama duba takardan da ya mika mata
tsaf sannan ta kallesa tace "Ba nace maka makarantar yayi nisa ba Ahmad?" Yace "Umma kece fa kike
ganin da Nisa amma ba wani nisa, sannan kan hanya ne ai..." Umma tace "Toh yanxu biya mana kudin
makarantar kayi?" Yayi dariya yace "Ehh tawa gudunmawar kenan" Umma tace "Toh Allah yayi albarka,
mun gode" Yace "Ameeen" Tace "Ina Ramlah?" Yace "Na ajiyeta gidan Captain" Umma tace "Ohk, yana
nan kenan" Ahmad yace "Ehh yana gari, jiya ya shigo" Tace "Toh madallah" Ahmad yace "Xuwa monday sai
a kaita schl din for documentation, in sha Allah hopefully xa su saka ta ss1, kinga in dai ya kara maida
hankali a ss2 kawai sai tayi waec dinta" Umma tace "Toh Allah ya kai mu, da kana gari ne sai ku je tare ai"
Yace "Ina nan har Tuesday" Umma tace "Toh shkkn sai ku je tare din xai fi" Yace "Allah ya kai mu" Daga
haka ya nufi kofa ya fita. Karfe biyu Maimoon da Jiddah suka shigo gidan daga saloon sun je kitso, Umma
ce xaune parlor tare da Hajja da ta yafa uban mayafi ga jakarta a gefe, daga ganinta kasan bata jima da
shigowa ba, A tare Jiddah da Maimoon suka gaisheta, Hajja tace "Har anyi kitson?" Maimoon tace "Ehh"
Hajja ta kalli Umma tace "Toh kince sai yamma xa su dawo kuma gasu ko minti ashirin ba ayi da shigowata
ba sun dawo" Maimoon da Jiddah dai suka wuce dakinsu, Umma ta ajiye wayarta da take dannawa tace
"Dama ba ce maki nayi in dai da layi saloon din xa su iya kai wa har yamma ba? Idan kuma babu layi xa su
dawo da wuri? Haka fa muka yi dake Hajja" Hajja tace "Atoh A masar dai magana daya ake, ko don baki son
ta rakani ne kika fadi hakan wa ya sani, ni fa nan da kike gani na Allah ne ke daura min son mutum ba wani
mahaluki ba, ga can gantalalliyar can Nafeesah me yasa bance ta rakani ba? kice saboda bata gaisheni,
sannan wannan bakar yarinyar Aisha sace sace take min a daki, komai aka kawo ta wawura ta boye, shi
yasa bata da fasali wllh, to ni ba ruwana ta kaina nake bana biye su, yau dai ina tashi da sassafe nace ma
Usman tunda wannan yaro Aliyu yayi aure muka kai masa amarya ban sake komawa gidan ba, kuma ko
yanka ni xa ayi idan na hadu da amaryar a hanya yanxu dai ba ganeta xanyi ba wllh, Usman ya fahimceni
yace in shirya in je to, barin ma yau Asabar yana gari yana hutu, to ni a gaskiya bana son tafiya ni daya
kamar mayya, shine nace kawai direba ya kawoni nan in samu wannan yarinya Jiddah ta rakani muje, ita
dama yar ki Maimuna tun wani fada da nayi mata ta daina gaisheni sai yau da taga idonki, banda jiddar
babu me mun biyayya yanxu wllh tllh" Umma dai ci gaba da danna wayarta tayi kawai, Jin Hajja tayi shiru
tace "Banda abunki Hajja ai jiya juma'ah da babu Islamiyya ya kamata ki xo ba yau da xa su tafi Islamiyya
ba" Hajja tace "Toh yau Allah ya bani ikon bude baki ince xan je gidan amarya, ke fa Ramlah wani lokacin
Sai in rasa gane inda kika dosa, sannan ni Usman bai wani ce in xo in nemi izininki in tafi da yarinya ba,
kawai cewa yayi direba ya kaini in dauketa mu tafi, ni fa ba tsohuwar banxa bace Ramlah, banda tsautsayi
babu abinda xai dawo dani daga Masar wllh, a can banda ganin girmana da mutuntani babu abinda
larabawa ke yi, don dai Nafisah ta tafi gun mijinta a Habuja ne da ta baki labari da kanta, amma ku banda
raini babu abinda ke tsakaninku da babba a kasar nan" Umma tace "Yanxu dai Hajja ga ki ga Jiddah, ni
bance kar ki tafi da ita ba, maganan Islamiyya nake, malaman basu yarda da fashi ba" Hajja ta kundumo
wani xagi tace "Su malaman Allah ne su da sai ace lallai sai abinda suka gindaya xa a bi? Ni me iya xuwa
makarantar ce yanxu ince masu Jiddah baxata je ba sbda wani uzuri da ya taso" Umma tace "Toh rana dai
na yi, sai ku tashi ku tafi" Hajja tace "Xuwa xa kiyi ki sanar mata ni ba ruwana duk an ma bata min rai,
kamar warce xanje in siyar da Jiddar, ni da na sani ma ban yadda na dawo kasar nan ba wllh, yaushe xa a
ga haka a Masar" Umma tace "Wannan Masar din dai Allah ya kai mu muga yanda ake yi a can din Hajja"
Da sauri Hajja tace "Aa, ba ko wani gantallale ake bari ya shiga kasar ba ma, nima da yaya suka yarje min
na shiga, ke dai kawai a bar kaza cikin gashinta" Dariya Umma tayi ta mike ta wuce dakinsu Maimoon, har
sun fara shirin Islamiyya, Umma na kallon Jiddah da har ta saka uniform tace "Jiddah xaki raka Hajja gidan
amarya wai" Jiddah tayi shiru tana kallon Umma tana son sanin wace amaryar tukun, Maimoon tace
"Wace Amaryar Umma?" Umma ta ta6e baki tace "Gidan Aliyu wai" Sosai gaban Jiddah ya fadi, lkci daya
mood dinta ya canxa har hakan bai boyu a fuskarta ba, Umma duk ta lura da hakan kuma, Umma tace
"Kina kai ta dama xan baki kudin mota ki lallaba ki dawo, ko minti ashirin kar kiyi a gidan" A sanyaye Jiddah
tace "Umma Islamiyyar fa?" Umma tace "To na gaya mata ta hau ni da fada, kawai kiyi hakuri ki rakata din,
kuna isa gidan ki juyo abun ki" Jiddah tace "Toh Umma mu je da Maimoon idan ya so kawai sai mu wuce
makarantar daga can" Umma tace "Ehh kuma haka ne, ku shirya ku fito, hakan ma shine dai dai, bari in
sanar mata" Daga haka Umma ta juya ta fita ta koma parlor, tana kallon Hajja tace "Hajja ita da Maimoon
xa su rakaki, idan ya so kuna isa gidan bayan sun gaisa da amarya sai driver ya karasar da su makarantar, da
uniform a jikinsu ma xa su tafi, ina ga hakan xai fi ko" Hajja tayi tagumi tace "O'o Allah ina ganin jarabawa
ni Dije, yanxu Ramlah ko ke kika haifi er nan Jiddah kya dinga min wannan axababben walakancin da kike
min, ina ruwana da wata Maimu? Maimu da bata daraja kowa xaki hadani da? Dama ba Jiddah kawai nace
ta rakani ba, a gaskiya a xo a kira min Usman, ya xaki dinga min kamar wata bare Ramlah?? Sannan da
Aliyu bai je ya jajubo mana Jiddar ba a ina xaki santa ki nuna iko? A fa ta dalilin jikana ma aka san da wata
jiddah a duniyar nan, ni dai wllh ki ajiye son kai kiji tsoron Allah Ramlah, ace a Masar ne ai sai anji dalilin
wannan abinda kike min yanxu" Juyawa Umma tayi tace "Ni da ma kira kawai kika yi a tura maki Jiddar da
wannan dogon xancen ba sai kin xo ba Hajja" Hajja tace "Oho dai ba ruwana da tashin hankali dake, ni
yarinya ce da xan biye maki, banda dai kina kanwar Hauwa a ina xan sanki" Umma na shiga dakinsu
Maimoon ta bude kofa tana kallon Jiddah tace "Ki canxa kaya ki xo ku tafi Jiddah" Daga haka ta bar dakin ta
wuce nata dakin, Babu yanda Jiddah ta iya haka ta shirya cikin atamfa ta dau hijab dinta ta saka, Abinda
Maimoon bata ta6a ganin tayi ba take yi a lokacin wato kumbure kumbure, fuskar nan nata kamar bata
ta6a dariya ba kana gani kasan ko kadan ranta bai so ba, jakarta ta dauka ta fice daga dakin, ta wuce dakin
Umma, Umma na kallonta tace "To ya xa ayi kiyi hakuri, amma kuna isa ki ce xaki Islamiyya ki fito, ga kudi a
gaban mirror ki dauka kiyi kudin mota da shi" Jiddah ta karasa a hankali ta dau kudin sannan tace "Nagode
Umma" Fita tayi daga dakin, bata san Umma ta ma fita jin takaicin rakiyar ba, Hajja na ganin Jiddah ta mike
tace "Mu je, ai ba ita taje ta nemo ki a duniya ba da xata dinga nuna isa da iko a kanki, mata ta wani narka
kiba uwa fanken Masar tana ma mutane rashin kunya kawai" Ita dai Jiddah bata ce komai ba ta bi bayanta
tana tafiya a hankali, Driver na ta xaune mota yana jiran ranan fitowar Hajja, Hajja ta bude bayan motar
tana kallon Jiddah tace "Toh shiga, halan ta kitsa maki karya da gaskiya ne, naga ranki kamar ba dadi" Ita
dai Jiddah tayi murmushin karfin hali ta shiga motar, Hajja ma ta shiga ta kulle tace "Ae laifin wa enda suka
bar ki a wajenta ne, kowa fa yasan matar bata da mutunci, nan da nan take maka mutum kotu ko ta kaisa
gidan yan sanda ayi ta bala'i shi yasa kowa ke shakkarta a pamily, da akwai wani lkci da ta kira ma Hafsah
yan sanda a kan ta xagi yar uwarta Hauwa, aka yi ta dauki ba dadi ana bala'i daga karshe dai Allah ya
yayyafa ma abun ruwan sanyi, to idan tana ji da bala'i nima ai A ce, kawai nayi sanyi ne tunda naga su
Masar basa haka, ni kuma sai inje in kai masu wani halin daban? Aa shi sa na daina wllh" Jiddah dai bata ce
mata komai ba har driver ya kama hanyar gidan Aliyu. Suna isa gidan xai yi parking a kofar gida Hajja tace
"Kai ya haka, baka san waye mai gidan ba, jikana ne fa, ni na haifi ubansa, ka danna masu han kawai a
bude maka ka shiga" Yana danna horn mai gadi ya leko, Hajja sai kallon Mai gadin take ganin yaki bude
gate din ya karaso gun motar tace "Ji wani yakunanne don Allah, kace masa kakar mai gidan ce kai Bala"
Drivern ya sauke glass ya sanar ma mai gadin, yana hada ido da Hajja da ta wani sha kunu ya koma ya bude
gate din, Hajja tace "Fitsara suke ma mutane idan sun samu waje wllh, banda haka shi xai ce bai ga
kamanni ba, kawai neman magana malam" Driver ya ja motar xuwa cikin gidan, Kai kana ganin Jiddah xaka
xata wani mugun waje aka taho da ita, gaba daya taki sakewa, driver na parking Hajja ta sauka, kafin tace
komai Jiddah ta sauka ita ma, Hajja tace "o,o Na shiga uku, yanda kike yi da fuskar nan taki wani ba sai yayi
xaton sato ki nayi ba er nan, a gaskiya Ramlah da kyar taga annabi, ni yanxu ta ya xan sa abinda ta kitsa
maki kike ta daure fuska haka fisabilillahi, matar nan fa ta fita hanyata a kasar nan wllh" Jiddah ta kirkiri
murmushi tace "Bata ce min komai ba Hajja" Hajja tace "To ni ba ruwana, ta ji da munafurcinta" Daga haka
ta fara tafiya xuwa main entrance din gidan Jiddah ta bi bayanta, da sauri Hajja ta juyo tana kallon driver
tace "Ka tafi kawai kai, Aliyun sai ya maida mu gida idan muka shirya" Amsa gaisuwar da mai gadin gidan
ke yi mata tayi tace "Mai gidan na ciki?" Mai gadin yace "Ehh Baaba yana ciki" Hajja tace "To madallah"
Daga haka ta yi gaba Jiddah na biye da ita, murda kofar Hajja tayi bayan ta murda ta ji sa a kulle, ta kalli
Jiddah tace "Toh ko meye na garkame kofa da rana tsaka haka" Bata rufe baki ba aka bude kofar, daga
sama har kasa yake kallonsu, sai kuma ya koma gefe still looking at Jiddah, Hajja ta shige parlon abunta,
Jiddah dai sunkuyar da kanta tayi taki yarda ta kallesa, ya gama kare mata kallo sannan ya juya ya koma
parlon yana kallon Hajja yace "Sannu da xuwa Hajjaj, daga ina haka?" Hajja ta rike ha6a tace "Ohh ikon
Allah, aure me seta mutum, yaushe rabon xancen kirki ya hadani da kai Aliyu, yau wai kai ne ke min sannu
da xuwa fuska a sake haka" Ya shafa kansa yana murmushi yace "Daga ina ku ke?" Tace "Daga gida wllh, na
dai ce bari in xo gidan amarya yau" Ta gefen ido ya kalli Jiddah da taki xaunawa ta tsaya daga bayan kujera,
muryar Hajja yaji tace "To ina amaryar?" Ya dauke kai yace "Tana sama" xata sakko yanxu, yana fadin haka
ya xauna yana tambayarta mutanen gida, Hajja ta kalli Jiddah, girgixa kai tayi tace "Ban san haka er nan
take ba sai yau da nace ta rakani, ashe ita ma duk kanwar ja ce, Duk Ramlah ta xugeta tunda muka kamo
hanya take min wasu abubuwa me nuni da cewa bata son biyoni, ni ai na xata kirkin gaske gareta wllh, to
banda haka meye xa ki makale jikin kujera kamar na kawo ki gidan yankan kai? Ni da na sani da Nafisah na
taho duk da halinta ko Aisha" Jiddah ta karaso parlon ta xauna kasan carpet a sanyaye, mikewa Abuturrab
yyi ya wuce sama, Hajja ta kalli Jiddah tace "Ba fa baren waje muka xo ba ki saki jikin ki, jikana ne ni na
haifi ubansa, ke ma kuma ai kin san sa, kar ki bari matar tayi mana dariya tace mun xo muna ta dari dari a
gidan, ki sake jikinki duk abinda kike so kiyi babu wani shakka, wllh bbu me hanaki kin ji" Jiddah tayi
murmushin karfin hali, tana son cewa Hajja xata wuce Islamiyya amma ta kasa, don bata san me xai biyo
baya ba, Hajja tace "Yanxu tashi ki tafi kitchen ki kwaso mana ruwa da lemo, ki duba robobin garanta ki
dau faranti ki debo mana duk abinda kika gani ki kawo" Jiddah ta kasa mata musu amma bata tashi ba,
Hajja tace "To tashi mana" Mikewa tayi rai ba dadi ta nufi kitchen din, ta fi minti daya tana kare ma kitchen
din kallo, kitchen din na nan yanda yake banda kayan kitchen da aka cika masu tsada, ta dinga kallon wajen
wanke wanke dake cike da dirty plates, ta kalli wajen gas taga duk yayi baki alamar ba a gogewa, bin kasan
kitchen din tayi da kallon mamaki ganin how untidy it is, daukan plate tayi ta tana kare ma plate din kallo,
kawai taje ta dauraye snn ta karasa store ta bude robobin da ta gani ta diba duk abubuwan ciki, wani tray
ta dauka ta daura ruwan gora biyu da cups snn ta fito kitchen din, xaune taga Aneesah a parlor tana kallon
Hajja dake ta xuba, Aneesah ta dinga kallon Jiddah da wani irin mamaki, don bata ma san da ita aka xo ba,
Hajja tace "Yauwa, kinga kinyi dubara, sannu" Jiddah ta ajiye tray din hannunta ta d'an kalli Aneesah da
mood dinta ya sauya lkci daya tace "Ina yini" Aneesah ta hau danna wayarta, Hajja tace "Gaisheki fa take
Nanisa kike ko?" Aneesah ta daga kai tace "Ohk, sannu, lfya lau" Jiddah ta mike ta xauna saman kujera tana
kallon Tv dake aiki, mikewa Aneesah tayi tace "Na gaisheki Hajja, ina d'an yin abu ne a sama" Daga haka ta
wuce Hajja ta bi ta da kallo, ta rike ha6a murya can kasa tace "Tabdi" Jiddah dai kallon tv kawai take, Hajja
tayi kasa da murya tace "Kaji min shegiya, ta sanki ne ta maki wannan walakancin ni ya su?" Saukowar
Aliyu yasa Hajja tayi shiru, ta kallesa tace "Amma ba a nan parlon xa a yashe mu ba kamar marasu
makabuli ko Aliyu" Yace "Mu je sama" Mikewa Hajja tayi ta kalli Jiddah tace "kwaso mana kayan flawan da
lemon" Jiddah ta dau tray din ta mike suka hada ido da Abuturrab da sauri ta dauke idonta, Tuni Hajja tayi
hanyar stairs Abuturrab ya bi bayanta, sai sannan Jiddah ta fara tafiya ta wani hade rai. Dakin da Jiddah ta
xauna a lkcn da take gidan ya shigar da su, Hajja tace "Ba shakka, ko mutum xai yi sati a nan babu wanda
xai san abinda yake ciki abunsa" Jiddah ta ajiye tray din ta xauna kasan carpet, Hajja ta cire mayafinta ta
linke ta bude press ta ajiye, katon jakarta kuma ta rataye sa a bag rack, sai kallonta Jiddaj take da mamaki,
ta juyo tace "Ki cire wannan Hijabin ki sha iska abun ki, ai nan ba bakon waje bane, gidan Aliyu ne fa"
Jiddah tayi gathering courage tace "Hajja ni fa makaranta xan wuce yanxu dama, tunda akwai sauran lkci"
Hajja ta kalli Abuturrab tace "Kaga jaraba ko, Ramlah ce ta koya mata haka fa kafin mu fito, to ko dai
Ramlan nan kanwar uwar Jiddan ce bamu da labari??" Abuturrab dake kallon Jiddah, calmly yace "Baxa ki
je ba" Hajja tace "Atoh dai, su makarantar basu san uxuri bane" Wani kallo Jiddah ta masa ta gefen ido lkci
daya ta dauke kanta ta daure fuska, Da mamaki ya dinga kallonta babu ko kiftawa, can ya shafa kansa yace
"Wani abincin xa ku ci Hajja?" Hajja tace "Ni ko tuwo aka samu a ban Aliyu" Yace "Ohk" sannan ya juya ya
fita, Hajja tace "Ikon Allah, yanxu Aliyu ne ke nan nan da ni kamar wanda nayi ma wani abun arxiki, wllh ni
tunda muke bai ta6a girmama ni ya mutunta ni irin yau ba, ohh Allah mai iko" Jiddah dai bata ce mata
komai ba.