Showing 45001 words to 48000 words out of 321711 words

Chapter 16 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt

"Naji sauki" Ya d'an yi jim kafin yace "Iyayenki sun daura
maki aure..." Da sauri Jiddah ta daga kai ta kallesa, yaki yarda su hada ido ya ci gaba yace "Amma ba da
mutumin nan ba" Kallonsa kawai Jiddah take ko kiftawa babu, ya shafa kansa yace "Amma shi wanda aka
daura maki auren da shi xai sake ki, sai ki ci gaba da xama a nan wajen Umma ko gidanmu wajen Ummina,
amma fa sai kin amince babu ke babu Baabar nan taku don ba sonki take ba, kuma baxata ta6a sonki ba,
neman kudi take da ke" Cikin sanyin murya Jiddah tace "Toh da wa aka daura min auren??" Yace "Fada
maki ba amfani xai yi gareki ba, kawai dai abinda na sani xai sake ki, sai kiyi xaman ki a nan ko kuma ki
xauna gidanmu, ki fara karatu islamiyya da boko, kinsan wacece ke, kinsan daga inda kike, kawai na shiga
rayuwarki ne ba don komai ba sai don in taimakeki in samar maki yan cin ki, idan ba don haka ba, ni bana
shiga abinda bai shafeni ba...." Kallonsa kawai Jiddah dai take a sanyaye, lkci daya hawaye ya kawo idonta,
a hankali tace "Jiya Umma da daddare ta shigo ta tambayeni in gaya mata gaskiyan wacece ni, kuma ya aka
yi na xo gidan nan" Cikin rawar murya ta ci gaba tace "Ni kuma baxan iya mata karya ba" Abuturrab na
kallonta yace "Kin dai gaya mata ko?" Ta gyada masa kai yace "Good, xuwa gobe duk inda kika ce xa ki
xauna nan xa a kai ki, ko gidanmu ko nan" A hankali tace "Toh idan na xauna nan xaka dinga xuwa?"
Kallonta yake da kyau, ya hade girar sama da ta kasa yace "In xo in yi maki me??" Kasa cewa komai tayi
tana wasa da fingers dinta, yace "Ae ba lallai ki gan ni ba, ki ma daina min kallon sani daga yanxu, ki kama
Umma da su Siyama ki rike sosai, they will like you, ni ba lallai a shekara ma kike ganina ba" Kai kawai ta
gyada masa hawaye cike idonta, yace "Sai ki tsaya kiyi karatu da kyau domin al'umma da wa enda suke
tare dake suyi alfahari dake..." Nan ma ta gyada masa kai kawai, yace "Allah ya kara lafiya" Daga haka ya
nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita dakin, hawayen da bata san dalilinsa ba ya dinga sauka idonta,
Abuturrab ya amshi medical report dinsa wajen Ahmad kawai ya bar gidan coz baya tunanin har ya koma
aiki da akwai abinda xai sake dawo da shi gidan, he now felt relieved, yaji baya tare da duk wani damuwa.
Da yammacin ranan Abuturrab dake bedroom dinsa ya dau wayarsa dake ring, ganin number Abbansa yaji
gabansa ya fadi sosai, dagawa yayi ya kai kunne hade da sallama, Daga daya bangaren Abba yace "Ka
sameni parlona ynxu" Kafin yace komai Abba ya katse kiran, lumshe ido yayi ya bude, bayan few minutes
ya mike a hankali still holding to his phone ya nufi kofa ya fita, a main parlor suka ci karo da Aunty, yayi
kasa da kai yace "Ina yini Aunty" Ko kallonsa bata yi ba balle ta amsa shi tayi wucewarta, ya bi ta da kallon
gefen ido sannan ya ci gaba da tafiya xuwa parlon Abbansa cikin sanyin jiki, a hankali yayi sallama sannan
ya shiga, sosai gabansa ya fadi ganin Abbansa da brothers dinsa biyu, a sanyaye ya karasa shiga cikin parlon
ya xauna kasa sannan ya gaishesu, uncles din nasa suka amsa, ya kalli Abba amma bai ce komai ba, Alhaji
Lawal yayan Abbansa ne yace "Mun ji abinda ke faruwa Aliyu, ko kuma ince mun ji abinda ya faru" kasa
cewa komai Abuturrab yayi, Alhaji Ibrahim kanin Abbansa yace "What u did is something very good but ba
ta yanda ya kamata kayi ba kayi, kada ka manta ba kai ka haifi kanka ba, kana da iyaye, no matter what ya
kamata ka nemi consent dinsu, ya kamata ka basu girmansu su san abinda kake ciki, ba sae da abu ya
kwabe ba....." Daga kafada yayi yace "Anyway, wannan duk maida hannun agogo baya ne, tunda abinda ya
faru ya riga da ya faru, sae dai a tari na gaba" Abuturrab bai iya yace masu komai ba, Alhaji Lawal yace "So
what next now? Yarinyar tana ina?" A hankali yace "Tana gidan Umma" Alhaji Lawal yace "Wacece
Umma?" Abba yace "Kanwar Hajiya Hauwa" Alhaji Lawal yace "Ohkk, am asking what ur next action is
now" Abuturrab ya sunkuyar da kai yace "Abba sakinta xanyi sai ta yi xamanta tayi karatu that was my
intention dama" Alhaji Lawal yace "Ka saketa a saboda me?" Abuturrab ya kallesa ya marairaice yace
"Abba dama wllh niyyata kenan, ai baxai yiwu inyi aure iyayena basu sani ba, ni kawai na amince na aureta
ne sbda kubutar da ita daga hannun matar babanta, amma ai ni baxan iya aurenta ba" Alhaji Lawal yace
"Wannan ba magana bane Aliyu, ka aureta, ka aureta kenan, babu wani kwaskwarima, Allah ubangiji ya
baku xaman lafiya, kada ka sake tunanin sakinta, kaddararku da ita ne a haka" Bude baki Abuturrab yayi
yana kallonsa without knowing cewar yayi hakan, Alhaji Ibrahim ya gyada kai yace "Hakuri xaka yi son, ka
xauna tare da ita, ka cike ladanka, ai Allah ya ga xuciyarka, idan ka saketa baka kyauta mata ba, akwai
hikima cikin auren nan...." Abuturrab ji yayi kamar ya fara masu kuka gaba daya, Abba ya sauke ajiyar
xuciya yace "Dama ni nace baxai saketa ba, cikin weekend din nan ya dauketa su tare, ai ba wani ya jawosa
ya aura masa ita ba, sai yayi hakuri ya rungumi kaddara" Abuturrab was lost of words amma ganin musa
masu baxai yi masa amfani ba yayi shiru duk yana sauraronsu, sai dai xufa kawai yake yi, to lkcn da ma xai
saketa din sani xa su yi? Tunanin hakan ya saukar masa da relieve, Muryar Alhaji Lawal yaji yana cewa
"Gobe asabar ka tare kawai da matarka, Allah ya sanya alkhairi, not too long sai ku shirya da ita ku tafi
gaida mai martaba a bauchi" Abuturrab bai samu courage din ce masu komai ba, but he is boiling inside,
dama taimako na iya xama fitina da tashin hankali haka bai sani ba??? Alhaji Ibrahim yace "Sai a kira Hajiya
Hauwa ita ma aji ta bakinta tunda tana da right a kansa ko?" Abba ya dau waya ya kira Ummi, har da
Aunty, Abuturrab ya ji dadi da Abba ya kira har Aunty don yasan she will stand for him, ba a dau lkci ba
suka shigo parlon, duk suka yi ma 'yan uwan mijin nasu sannu da xama don tun xuwansu gidan suka gaisa,
Alhaji Lawal ne yayi masu bayanin shawaran da suka yanke, Ummi dai ta kasa cewa komai, ita babban
tashin hankalinta asalin yarinyar nan ba wai tana kin auren bane, ba a san wacece ita ba gashi yace uwarta
da ubanta sun rasu sai kishiyar uwar, Aunty ta mike tana girgixa kai cikin tashin hankali tace "Haba
fisabilillah, an ta6a aure dole ne? Tunda yace bai so, yayi auren nan ne kawai don taimako to a barsa ya
datse wannan kaddararren auren mana, ai ya gama taimakon da yayi niyya, to meye kuma xa ayi ta cusa
masa yarinya kamar ku ka aura masa ita, wannan ai kamar neman suna ne ku ke yi, banda haka wllh ko
mahaukaci baxai amince da irin wannan auren ba, yarinyar da bata da asali ku ke burin d'an ku ya xauna
da?" Alhaji Ibrahim yace "Ke kinje kinyi bincike kinga bata da asali Hafsah?" A fusace tace "Banda yanxu da
na kawo maganan asalin ai babu wanda ya damu da hakan, haka kawai xaku yi ma yaro dole kuce sai ya
xauna da yarinya yana ce maku baya so?" Alhaji Lawal na kallonta da kyau yace "Tunda ni ko d'an uwana ko
Ibrahim babu wanda ya ja Abuturrab ya kai sa aka daura masa aure he just have to dance to his music, ko
yaki ko ya so haka xai hakura ya xauna da yarinyar, mu ba kananun mutane bane, yanda bai yi shawara da
mu ba yaje yayi abu gaban kansa bai isa yace yanxu ma xai juya mu ba, Allah ya basu xaman lafiya" Abba ya
gyada kai cikin gamsuwa, Aunty na masu wani kallo gaba daya tace "Ai ko baxan ta6a xuba ido Abuturrab
ya cutu ba in dai ina numfashi..." Daga haka ta fice daga parlon fuuu, Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh
Allah yayi abinda ya fi alkhairi, ya sa mu dace" Alhaji Lawal yace "Ameen Hauwa" ta mike ta fita parlon ita
ma, Abuturrab dai kansa na kasa, Abba na kallonsa da kyau yace "Kafin gobe kayi duk abinda xaka yi a
gidan nan ka tare da matarka, kamar yanda Alhaji Lawal ya fada maka, idan an kwana biyu kuma ka kai ta
ku gaisa da mai martaba" Still Abuturrab ya kasa cewa komai, sai da suka yi masa ixinin fita sannan ya mike
ya fita xuciyarsa na tafarfasa, Alhaji Lawal yace "This should serve as a lesson for him, next time baxai sake
yin abu gaban kansa ba" A bedroom dinsa ya tadda Aunty tana ta jiransa tana girgixa kafa, a sanyaye yake
kallonta, Tace "What next now?" A hankali yace "I don't really know Aunty, but ni nasan baxan yi rayuwa
da ita matsayin matata ba wllh" Aunty tace "Toh dama ina hakan xai yiwu, a ina xaka xauna da ita bayan ga
Aneesah, uban me xaka ci da ita?? kuma idan ka saketa sani xa su yi?" Ya girgixa kai yace "That's what i
have in mind Aunty, xan saketa babu wanda xai san hakan sai ke a gidan nan, quite alright xan tare da ita
gobe din amma ba matsayin matata ba wllh" Aunty tace "Ai xaman naku ne bana so kwata kwataaa
Abuturrab" Yace "Aunty a hankali ake bin komai" Tace "Toh da dai ya fi, don wllh abun dariya xaka xama
gun colleagues dinka da yan uwanka, wa ka ta6a jin yayi irin wannan auren? Auren ma na yar talaka" A
sanyaye yace "Na sani Aunty" Ta nufi kofa tace "Ba dai tarewa suke so ba, xaka tare din da ita sannan ni
xan san abun yi" Daga haka ta fice a fusace, ko ba komai Abuturrab na samun relieve tunda akwai warce ke
supporting dinsa dai. Daren ranan Umma ta kirasa yana kwance sai tunane tunane yake yana imagine
yanda lkci daya Jiddah ta shigo rayuwarsa tana neman tarwatse masa farin cikinsa da kwanciyar hankali, a
hankali ya dau wayar ya kai kunne bayan ya daga, cikin sanyin murya Umma tace "Kana ji na Aliyu?" Yace
"Ina ji Umma" Tace "Kayi hakuri ka bi abinda iyayenka suke so sai kaga haske sosai a lamarinka, Yaya ta
kirani ta min bayanin komai, ka janye batun saki, kaga dai yau jiddah kwananta uku ko sama da haka a
gidan nan, amma har yanxu ban ga aibun yarinyar nan ba wllh Aliyu, gata da hankali da nutsuwa da sanin
ya kamata ga uwa uba kawaici da hakuri, baxa kuma a dau lkci ba xata waye don na lura tana da
kwakwalwa, taka kaddarar ce a haka ka amsheta hannu biyu Aliyu, kada ka mance Allah ne ya tsaro maku
hakan kayi hakuri ka yarda da kaddara my son, duk sanda xaka koma wajen aiki sai ka dinga kawo min ita
nan ina gwada mata abubuwa, daga nan din ta dinga xuwa boko da islamiyya, wllh lkci daya xata dawo dai
dai taste dinka, nasan damuwarka kenan, in sha Allah xaka yi mamakin wayewar da Jiddah xata yi"
Abuturrab yaji baci ransa kawai yake da wannan shawaran da ake basa, ya ma rasa abinda xai ce mata,
how on earth suke tunanin xai iya rayuwa da yarinyar nan matsayin mata idan ba cutarsa suke son yi ba,
ina duk burinsa na auren wayayyiyar mace me tsafta 100%, ji yayi kamar ya fara mata kuka wannan wacce
irin kaddara ce haka ake forcing dinsa ya amsa, a ransa yace no way sai dai duk suyi hakuri, he just have to
disappoint them because no amount of their sugar quinted mouth will convince him to live with that girl
as wife, he will only live with her as a guardian.... Jin shirun yayi yawa Umma tace "Are u there son?" Ya
runtse ido yana jin ransa na dada baci, cikin dakewa yace "Ina ji Umma, nagode Allah ya kara girma" Tayi
murmushi tace "Ameen my son, Yaya tace min Abbanka yace ku tare gobe ko?" Cijen lips dinsa yayi yana
jin wani mugun takaici, amma ya daure yace "Ehh haka ne" Tace "Toh Allah ya kai mu goben lafiya son,
may Allah reward u abundantly for this deed" Ya bude idonsa da ya kada sosai.... forcing his self yace
"Ameen" Sallama suka yi ya jefar da wayar kan gado xuciyarsa na tafarfasa ya mike xaune ya rike kansa.
Washegari Saturday Umma na xaune dakinta tana kallon Jiddah dake juya kayan hannunta ta kasa sawa,
jira take ta sa kayan ta gyara mata gashinta da ta sa ta wanke, murmushi Umma tayi da ta lura kunya ce
yasa take hakan, sabon kaya ne da ta dinka ma Ramlah, sae ya kasance Ramla bata xo gidan ba har sannan
shine ta ba Jiddan ta sa, mikewa tayi ta fita dakin, Jiddah ta bi ta da kallon gefen ido, sae a sannan ta fara
sa kayan da sauri, wani kunya na musamman Allah yayi mata ita kam, komai da Umma ta bata ta saka sabo
ne, sosai riga da skirt din ya amsheta kamar don ita aka dinka, kallon kanta ta dinga yi a madubin dakin
tunda take iyakar atamfar da ta ta6a sa wa na dubu biyu ce, lkcn ko Ahmad ya kawo mata atamfa me tsada
sae Hansae ta amshe ta siya mata roba roba ko half cotton, yau kam ga tsadadden atamfa ta saka duk da
bata san me tsadan bane ba ma, bayan wani lkci Umma ta dawo dakin, sosai hankalinta ya kwanta ganin
powder kawai jiddah ta shafa a fuska sai kwalli, ta bar mata har kayan kwalliya kawai don taga irin
kwalliyan da xata yi sae gashi alama ya nuna iyakar kwalliyarta kenan ba irin na yan kauye take yi ba a lafta
ja gira da jan baki, ta madubi take ta kallon jiddah da ta kasa kallonta, Jikin Umma yayi sanyi ganin irin kyan
Jiddah, wai ma tun bata waye ba kenan, kuma jikinta bai fara samun hutu yanda ya kamata ba, ae
balarabiyan Africa xa ayi a nan, a hankali Jiddah ta juyo tana kallon Umma, Umma ta sakar mata lallausan
murmushi tace "Kinyi kyau my daughter" Jiddah tayi murmushin karfin hali, Umma ta xauna tace "Taho ki
xauna in gyara maki gashin" Jiddah ta karasa ta xauna ta janye hulan Siyama dake kanta, Umma tace "Idan
kin wanke gashi bari ake ya bushe kafin a sa hula kin ji?" Kai kawai Jiddah ta gyada mata, Unma ta fara taje
mata dogon gashin nata, murmushi Umma tayi ganin tsayin gashin Jiddah a ranta kuwa tunani take ko
ruwa biyu ce dai ita, sosai gashinta ke da kyau da tsayi sai dai babu gyara, Umma ta xuba mata man kai me
yawa a gashin da ya dinga sheki da kamshi sannan ta yi mata parking da ribbon, mikewa Jiddah tayi tace
"Nagode" Umma tace "Ki daura dankwalin yanxu" Jiddah ta dau dankwalin amma ta kasa daurawa, Siyama
Umma ta kira tayi mata daurin, Siyama sae murmushi take tace "Kinyi kyau" xuwa yanxu har Maman
Abdallah tasan matsayin jiddah a gidan, sae kusan karfe sha daya Umma ta bar gidan xuwa gidan yayarta
da Jiddah, well ironed Hijab ne nude colour har kasa jikin Jiddah, kasancewar akwai kalan a jikin atamfar
jikinta, sanyayyen kyau tayi, Hijab din yayi matukar amsarta, Driver ne ya kai su gidan don Ahmad kin
amincewa yyi he knows definitely Abuturrab will be mad at him wato da shi xa a kai masa mata......



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
*mg's skincare*

Shin Ina matan sukemaza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir
dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan
shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin
kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na
bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk
wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai
kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho
wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan
fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin
Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali
jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set
dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride
Glow

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee


Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166




Umma ta sauka motar bayan drivernta yayi parking, Jiddah ma ta sauka tana kallon babban gidan, Umma
ta kalli driver tace "Ka je kawai idan xan dawo anjima xan kiraka..." Cike da ladabi yace "Toh Hajiya" ta kalli
Jiddah tace "Mu je" Bin bayanta Jiddah tayi tana tafiya a hankali har suka isa main parlor din gidan,
kasancewar ranan asabar ne su Ramlah duk sun tafi islamiyya, Mai aiki ce kadai parlon tana aikace aikace,
ban da kamshi babu abinda ke tashi parlon, mai aikin ta gaida Umma da ladabi, Umma ta amsa da fara'a
tana mata sannu da aiki sannan ta kalli Jiddah tace "Toh xauna Jiddah" Xata xauna kasa Umma tace "Aa
tashi ki hau kujera" Mikewa tayi ta xauna saman kujeran Umma ta nufi bangaren yayarta, sai a sannan
Jiddah ta gaida mai aikin, matar ta amsa mata da murmushi tana ci gaba da abinda take, Muryar Abuturrab
Jiddah ta ji ta d'an saci kallon gefenta amma bata gansa ba, slowly yake tahowa waya kare kunnensa yana
waya tare da wani colleague dinsa da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login