Showing 108001 words to 111000 words out of 321711 words

Chapter 37 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt

in
bar ta ba, ita Ummi bak'i sun mata yawa, babu abinda xata yi noticing, and Aunty sai aikenta take tana fita
titi, what for?? I hate it when someone is being maltreated kai ma ka sani" Ahmad yace "Hmm, ka gano
wani abu kuwa Abuturrab?" Abuturrab na kallonsa yace "Me kenan?" Ahmad yace "You are starting to
develop feelings for Jiddah, na lura da hakan tun ba yanxu ba, wannan ya wuce tausayi da kwatar mata
'yan ci, gashi kayi gaggawar rabuwa da ita, don babu aure tsakaninka da ita believe it or not, ko da kuwa
baka saketa ba shelan da ka dinga yi kana sanar ma kowa cewar ka saketa, ta saku babu wani
kwaskwarima... Babu wani aure tsakaninku ynxu Captain, sannan kar ka manta babu idda a kanta..." Katse
sa Abuturrab yyi yace "Nigerians have a very very poor thinking mentality, me yasa baxa ku yi koyi da wasu
kasashen da suka fi ku wayewa ba, Shikenan ba dama mutum ya nuna rashin jin dadin abun da ake yi ma
mace sai ace yana sonta? Ohk fine... Yanxu in xuba ido ayi ta cutarta kenan tunda ba sonta nake ba, ina ce
ita ma mutum ce kamar kai, kamar ni, kamar kowa ma? To don me baxan kwatar mata right dinta ba, ko ka
mance akan kwato mata right din nata yasa har naje na aureta? Sannan still a kan kwatar mata right din
nata ne yasa na datse auren dake tsakaninmu, and duk wannan wa'axin da kake min ni na ta6a bude baki
nace maka da aure tsakaninmu ne?? Ko kuma idan ma da auren gaya maka aka ce xanyi" Ahmad yyi
murmushi yace "You are just confusing and disorganizing ur self, shi lamarin da ya shafi addini babu wayo a
ciki dai, anyway Ummi is jet angry at you, gwara ko koma yanxu ka dau jiddah ka kai ta can gidan tunda
dinner xa ayi yau, daga wajen dinner din sai ka wuce da ita gida, gobe Saturday ka kawota yini tunda baxa
ka iya barinta a gidan ba, amma kasan me? Kawai ina ji a jikina xamanku tare da ita ya kusa xuwa karshe"
Da ido Abuturrab ya bi Ahmad har ya fita. Motoci biyu ne lafiyayyu suka yi parking kofar gida, El-Basheer
ya juya yana kallon warce ke xaune bayan mota ta sha glass yace "Toh ai sai ki sauka mun iso" Da mamaki
tace "In sauka fa kace, a kan titin xan sauka d'an nan, motoci sun daina shiga get din gidan ne xan sauka a
bakin titi" Yace "Toh ai babu wajen parking a ciki, ke baki ga mutane bane...." Tace "Toh ina ruwana da
mutane, har yanxu dama Najeriyan bata canxa ba, mu ba haka ake yi a Masar ba wllh, idan ana biki ko
wani shagali wllh dai daikun mutane ake gayyata da daddare, sai a tarfa ma kowa yar gurasar alkama a
gefen faranti, a daura kofin madara a gefe, idan da yar cinyar kaza a saka a gefe shi ma, Allah ba a taro irin
haka kamar ana yunwa, shi Kabirun yasan haka mutane xa su cika gidan xai bada mota a kawoni nan salon
in gantale? wllh mu bamu saba haka a Masar ba, a gaskiya idan baxai yiwu ba a juyar dani kawai a mayar
dani Bauchi, daga baya kada Usman ya kullaceni sai in dawo inyi Allah ya sanya alkhairi, amma wllh baxan
sauka bakin titi ba duk k'ura ta kare min abinda babu a Masar, ko shi Usman din bai san ina hanya ba ai
Aliyu ya sani tunda na sanar masa ta waya.... Aa gaskiya ba dole Allah ya sanya alkhairi juya mu koma
kawai... Mu ba haka ake a Masar ba, komai bisa tsari ake yin sa" Kashe motar El-Basheer yyi yace "Kinga
Hajja idan xaki sauka ki sauka ni xan tafi gun daurin aure ne, ga ki ga gate kice baxa ki sauka ba" Bude baki
tayi tana kallonsa, can tace "Aa toh gaskiya Najeriya ba wajen xuwa bane, tunda nake a masar ba a ta6a
min rashin da'a irin wannan ba, sun san girma da mutuncin tsoho..." Tana kai wa nan ta ciro wayarta fuska
tsuke ta mika masa tace "Kira min Kabirun, ai shi na haifa ba kai ba" Bude motar El-Basheer yyi ya sauka
yayi wucewarsa cikin gidan, ta bi sa da kallo baki bude, sai kuma ta sauko ita ma ta bi bayansa. Jiddah ce
xaune bedroom din Umma kanta a kasa tana wasa da gefen hijab dinta, Umma tace "Jiddahh" dago kai tayi
a hankali tana kallon Umma, Umma tace "Ina sauraronki, idan kika min karya kuma kar ki manta Allah na
kallonki, kuma nasan kinsan makomar makaryaci" Lkci daya hawaye ya kawo idonta, Umma tace "Ina jin ki"


Those nulls reading my book for free and still commenting nonsense should know that i owe dem 500....
subhanallah!!! It's their gut for me wllh. In ma ku biya in ma kar ku biya babu pardon tsakanin mu. My
diehard fans kuma we move.... 💖



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last
bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd
getting rid of any skin problems

Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta
samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar
rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata
masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda
zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada

Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240




Jiddah ta goge idonta still ta ki cewa komai, Umma tace "Baxa ki min magana ba Jiddah?" A hankali Jiddah
tace "Umma yace min babu aure tsakanina da shi" Umma tace "Kamar ya babu aure a tsakanin ku?" Jiddah
ta gyada kai tace "Eh haka yace, wai shi ba mijina bane" Umma tace "A ina yace hakan?" Jiddah tace "A
can gidansa, ya rubuta ne a takarda ya bani" Umma ta dinga kallonta kafin tace "Ina takardan?" Cikin
sanyin murya tace "Ya ki bani" Umma tace "Amma ya nuna maki?" Jiddah tace "Ehh" Umma tace "Cewa
yayi ya sakeki a takardan?" Nan ma tace "Ehh haka yace, shi ba mijina bane" Umma ta gyada kai bata kuma
ce mata komai ba, bayan kusan minti goma ta mike ta fita dakin rike da wayarta, wani dakin daban ta shiga
tayi dialing number wata aminiyarta tana dagawa tace "Hajiya karfe nawa xa ki taho?" Hajiya Rukayya tace
"Ina hanya yanxu haka" Umma tace "Babu kowa gidanki?" Hajiya Rukayya tace "Toh na bar su dai suna ta
shirin tafiya dinner da wani abu ne?" Umma tace "Toh shhkn tunda ba kowa, dama wata yar uwarmu ce
aka kawo biki to bata son hayaniya, kinga nan din ma akwai taro shine da nake son ta xauna gidanki har
bayan biki" Hajiya Rukayya tace "Ohh Allah sarki, to amma Badiya mai aikina na nan ai, ba sai su xauna
tare ba" Umma tace "Yauwa toh, xan sa driver ya kai ta can din kawai, sai ki kira ki sanar mata bakuwa na
xuwa" Hajiya Rukayya tace "Toh ba damuwa" Umma ta koma dakin da Jiddah ke ciki tace "Kaya kala nawa
kika taho da?" jiddah tace "Na yau ne da gobe kawai" Umma tace "Ohk, xaku fita da driver xai kai ki gidan
kawata yanxu, tunda naga ke ba son taro kike ba ai" Jiddah ta d'an yi shiru, sai kuma a hankali tace "Umma
ai yace xai dawo anjima ya daukeni" Umma tace "Ehh kafin ya dawo din, sai yaje can gidan ka ya daukeki,
ki tafi da jakar kayanki kawai" Jiddah tace "Toh" Bayan mota Umma ta sa ta shiga ta ajiye mata jakarta a
gefenta, sannan driver ya bar gidan bayan ta sanar masa inda xai kai ta, tafiyar kusan minti ashirin da wani
abu suka yi suka isa gidan Hajiya Rukayya, Drivern yayi ma mai gadi maganan cewar yayi leading dinta har
entrance din gidan, tana shiga cikin compound din mai gadin ya nuna mata direction da xata bi, ta makale
jikin kofar ta kwankwasa a hankali, ta fi minti biyar tsaye sannan aka bude kofa, wata mata ce ta bude kofar
ganinta tace "Ke ce bakuwar da Hajiya ta sanar kina xuwa?" Jiddah ta gyada mata kai kawai, Badiya ta
amshi jakar hannunta tace "Toh sannu da xuwa, Bismillah" Bin bayanta Jiddah tayi, ta xauna parlor, Badiya
ta shiga dakin yan matan Hajiya Rukayya ta ajiye mata jakarta. Karfe biyar saura Abuturrab ya isa gidan
Umma, ya fi minti biyar cikin mota sanin da mutane gidan shi kuma ba iya shiga xai yi ba, daga karshe
kawai Maman Abdallah da ya gani a compound ya aika ta kira masa Jiddah, ba a dau lkci ba sai ga ta, tace
"Wllh yallabai Umma tace suna can gidansu amarya" Da mamaki ya dinga kallonta, can yace "Toh nagode"
Tada motar yayi ya bar layin ya dau hanyar gidansu, bayan yayi parking a waje ya dau waya ya kira Siyama
tana dagawa yace "Ki ce Jiddah ta fito" Tace "Yaya mu muna wajen make up fa, kuma har muka bar gidan
bamu ga ta xo ba" ya d'an yi shiru, kafin ya katse wayar. Tunanin wanda xai kira ya dinga yi a ciki amma ya
ga ba kowa kuma don ko hauka yake ya san baxai kira Ummi ba, d'an tsaki yyi ya tada motarsa ya bar
wajen. Tun da Abuturrab suka isa wajen da ake dinner tare da Ahmad da sauran abokansu yake xuba ido
yaga inda xai hango Jiddah a wajen amma bai ga alama ba, hakan bai wani damesa ba don dama xuwa
dinner din ne baya son ta xo ya kaita can gidan Umma, tun sanda Aneesah ta kyallara ido ta gansa take
masa zarya a wajen, barin yanda taga yayi wani kyau cikin fararen shaddan da duk abokan Ahmad suka
saka, ita a dole sai ta ankarar da jama'a cewar saurayinta ne, Ko mayafi bata daura kan damammen
doguwar rigar jikinta ba shi dai sai bin ta yake da kallo, wani abokin Ahmad dake side din Ahmad din
Abuturrab ke ta kallo yana son tuna inda ya ta6a ganinsa, he looks familiar amma dai bai ce masa komai
ba, karfe goma saura Aneesah ta xo ta samesa tana yauki tace "My captain wai xaka xo ka maida su
Mummy gida yanxu" Ya d'an kalleta yace "Toh ai bani na taho da motata ba, ban ma san inda yake yanxu
ba, nima abun hawa na samu ya kawo ni nan" Tace "Haba Captain, ko wajen daya daga abokanku baxa ka
amshi mota ka maida su gida ba...." Ko rufe baki bata yi ba sai ga aunty ita ma ta sha wani ubansun lace
tana goge xufan goshinta da handkicin hannunta tace "Aliyu ka tashi ka maida su Hajiya Safiyya gida" Bai
ce mata komai ba, tace "Ko baka ji na ne?" Yace "Toh bari in nemi wanda makullin motata ke wajensa"
Juyawa tayi ta bar wajen, ya kalli Aneesah da ta hade rai tana kallonsa, d'an murmushi yyi yace "Kema dai
kinsan wasa nake, dole in nemo mota ko na waye in maida su" Yana fadin haka yayi patting shoulder din
Umar dake side dinsa yace "Bani makullin motarka pls" Umar ya mika masa sannan ya mike yace "Kice su
fito" Daga haka ya nufi hanyar fita daga hall din.... Karfe daya Abuturrab ya koma gidansa bayan sun maida
duk bak'in da suka je dinner masaukinsu, ya fi minti goma xaune a parlornsa thinking of where Jiddah
might be, daxu da ya maida Mum din Aneesah har gida ya shiga bai ga alamar tana nan ba, shi kuma ya
kasa tambayar Ummi, akwai wasu bakin da still ya mayar can gidan Umma, can ma ya shiga bai ganta ba,
bayan kuma ya tambayi Maimoon tace ai tana gidan Umma, mikewa yayi daga karshe ya wuce sama xuwa
dakinsa don ya gaji sosai. Da asuba kiran sallah ya farkar da jiddah, ta mike xaune daga kan gadon da take
tana kallon yarinyar dake kwance saman gado gefenta, tun xuwanta gidan jiya banda ita da Badiya bbu
kowa a gidan har tayi bacci wajajen karfe goma saura, bandaki ta tafi ta dauro alwala ta fito sannan ta tada
yarinyar da baxata wuceta ba, yarinyar ta mike xaune, ita kuma ta shimfida darduma ta fara sllh.... Karfe
tara saura yarinyar da tayi wanka ta shirya cikin atamfa ta kalli Jiddah tana murmushi tace "Ya sunanki?"
Jiddah tace "Jiddah" Yarinyar tace "Ni sunana Amina, mu je parlor mu gaida su Mama sun fito" Jiddah ta
saka Hijab dinta ta bi bayan yarinyar suka fita parlor, yan mata biyu ne xaune parlon sai Hajiya Rukayya,
wanda Jiddah na ganinta ta gane mahaifiyarsu ce don sun yi kama, Jiddah bata yarda ta xauna kan kujera
ba ta gaida matar, ta amsa da fara'a tana tambayarta ta tashi lafiya, Jiddah ta sunkuyar da kanta, sauran
yan matan ma sai kallon Jiddah suke, Wani ne ya shigo parlon daga waje waya kare kunnensa, ganin
mahaifiyarsa a parlon ya katse wayar ya zauna yace "Ina kwana" Tace "Lafiya lau... Jiya kuma sai kayi
wucewarka ka bar mu a event center" Yace "Mama ciwon kai wajen ke sa min, it's been long da na tsaya
waje that's so noisy haka" Hajiya Rukayya tace "Toh Allah ya kyauta" Tun da ya shigo Jiddah ke kallonsa
kamar taga wani mugun abu, Ganin xai kalli direction din da take ta dauke kanta da sauri gabanta na
faduwa, Yace "Mama bakuwa ku ka yi?" Hajiya Rukayya tace "Ehh, ga breakfast dinka can a dining" Yace
"Ohk" sannan ya mike ya tafi dining din, Mikewa Amina tayi ta tafi dauko ma ita da Jiddah breakfast don
taga alamar yayyinta duk sun yi, kuma da ba don Jiddar ba tare xata je ta xauna su yi breakfast din da
yayanta, gaba daya Jiddah ta kasa sakin jiki a parlon, lkci lkci take satan kallon hanyar dinning din, daga
karshe dai ta mike xata wuce daki, Hajiya Rukayya tace "A daki xaki yi kumallon?" Ta d'an yi murmushi ta
gyada kai ta wuce daki da sauri, dole dakin Amina ta kai masu Breakfast din. A ranan bayan an sauko
juma'ah aka daura auren Ramlah da Ahmad... Abuturrab na tsaye daga bakin kofa a bedroom din Umma
bayan sun gaisa yace "Tana gidan nan ne Umma?" Umma ta kallesa tace "Wa?" Jin bai ce komai ba tace
"Wai Jiddah?" Yace "Eh" Tace "Ba a jima ba suka tafi can gidanku da Maman Abdallah" Bai kuma cewa
komai ba, tace "Hajja kuka tace tun da ta xo baka je ka gaisheta ba" Yace "Ai ban je can gidan ba Umma,
anjima da daddare xan shiga in gaisheta" Tace "Yauwa gwara kaje din da daddare dama ya fi, an kai maku
abincin kuwa?" Yace "Ehh an kai" daga haka ya juya ya fita. Da yamma su Amina duk suka tafi gidan yinin
Biki, Hajiya Rukayya kuma tun karfe goma dama ta bar gidan, gidan ya rage daga Jiddah sai Badiya, tana
kitchen tare da Badiya tana tayata girkin dinner, wayar Badiya dake parlor ya fara ring, Badiya tace "Dauko
min wayar Jiddah..." juyawa tayi ta fita xuwa parlor, dai dai nan kuma aka bude kofar parlon suka hada ido,
sanye yake da farar shadda idonsa sanye da glasses, sosai gabanta ya fadi, ta sunkuyar da kanta tana kalle
kallen inda xata ga wayar Badiya, kasa karasowa cikin parlon yyi, sbda rudewa ta ma rasa inda wayar yake
ta juya xata koma kitchen din taji yace "Jiddah" juyowa tayi suka sake hada ido, tayi murmushin karfin hali
tace "Ina yini?" Ya karaso cikin parlon yana ci gaba da kallonta da mamaki, bata jira me xai ce ba ta juya da
sauri ta koma kitchen din. Har Hajiya Rukayya ta dawo wajajen magrib Jiddah bata sake yarda sun hadu da
Yousuf ba, can daki ta shige taki fitowa through out, Hajiya Rukayya na shigowa gidan ta kira Yousuf a waya
don baya nan, yana shigowa tace "Don Allah bakuwar nan xaka ajiye min gidansu Ahmad yanxu, Hajiya
Ramlah tace ka kaita" Yousuf yace "Ohkk" Har mota su Amina suka raka Jiddah, shi da Yousuf na xaune
cikin motar tasa, Jikin Jiddah yyi sanyi ganin shi xai maidata, hannu kawai ta daga ma kanninsa har suka fita
compound, sai da suka d'an yi nisa taji yace "Dama ke yar uwar Ahmad ce?" Kai ta gyada masa kawai, ya
d'an kalleta yyi murmushi yace "Har yanxu sai kice min baki da waya ko?" Ta gyada masa kai, yace "What if
na baki tawa wayar?" Ta xaro ido tace "Sai in ce wa ya bani?" Yace "Ni" ta girgixa kai tace "Aa bana so" yace
"Jiddahh" ta d'an kallesa suka hada ido, yace "Kin san wani abu?" Ta girgixa masa kai, yace "Tun da muka
hadu dake a jirgi kullum nake addu'an Allah ya sa in sake arba da ke, sae gashi kin xo har cikin gidanmu,
kinsan me yasa hakan ya faru?" Nan ma ta girgixa masa kai, yace "It is because i have good intention
toward u..." Jiddah dai tayi shiru kamar ta gane me yace. And the rest of the ride was silent, yayi parking
dai dai kofar gidansu Ahmad ya juya yana kallonta, yace "Tunda baxa ki amshi wayata ba, xan kiraki ta
wayar Maimoon" Ita dai bata ce komai ba, ta bude motar ta sauka, ta bude baya ta dau jakan kayanta,
Yousuf na kallonta yace "Sai na kira" Tace "Toh" sannan ta nufi gate, shi kuma yayi reverse.... Dama Umma
Jiddah kawai take jira don har ta saka Hijab dinta tana parlor a xaune, Jiddah na shigowa kuwa ta saka
driver ya kai su can gidansu Abuturrab, har sannan da akwai sauran yan biki a gidan duk da tun wajen
shidda saura aka kai amarya, direct parlon Abban Abuturrab Umma ta nufa tare da Jiddah suka shiga da
sallama, Abban Abuturrab da brothers dinsa ne a parlon sai Hajja dake xaune kan carpet, bayan ta xauna
suka gaggaisa, ta gaida Hajja ma, Hajja tace "Ni dai tun jiya nake ta kallon ki Ramlah, ya aka yi kika amince
kika narka uban kiba haka, to ai ba kyau, mu a masar da tuni an kai ki asibiti duk hankali a tashe, mu ba ma
haka a can" Umma dai bata ce mata komai ba, Can ta kalli Jiddah da ta sunkuyar da kanta tun bayan gaida
su Abba tace "Ita kuma wannan sadaka yallar fa?" Nan ma babu wanda ya ce


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login