Showing 207001 words to 210000 words out of 321711 words
ya maida
mutane kananun mutane kenan yake nufi ko me?" Abba dai da alama ransa idan yayi dubu ya baci, daukar
wayarsa yayi ya tura ma Abuturrab text kamar haka, "call me immediately after switching on ur phone, i
said immediately!!!" Alhaji Lawal yace "Lallai kuwa tunda har ya turo message din nan Komawa yaron nan
yayi aka daura masa aure da yarinyar ba tare da sanin kowa ba, tunda ya san waliyanta sannan tun farko
shi dama babu wanda yayi masa waliyyanci a cikinmu, don haka abu ne me sauki garesa" Abba dai baya
cewa komai a parlon...
Har bayan sati da text din nan wayar Abuturrab a kashe yake, Jiddah na xaune daki tare da Maimoon da
daddare tana son mata magana amma ta kasa, don bata ma san ta ina xata fara maganar ba, tun 3 days
ago maganar ke cin ta amma ta kasa yi mata shi, can dai ta dake a hankali tace "Maimoon ya jikin Ya
Aliyu?" Maimoon ta kalleta tace "Wllh I don't know, I can't reach him for a week now" Jiddah tace "Both
Whatsapp?" Maimoon tace "Baya hawa...." Jiddah bata kuma cewa komai, Maimoon dai sai kallonta take,
mikewa tayi ta koma side din da take kwanciya tayi kwanciyarta.... Ranan Friday bayan an sauko sallan
Juma'ah, Jiddah na xaune xaune bakin tap din compound din gidan tana wanke hijabs dinta biyu don
Safiyya na wanki a washing machine aka bude gate din gidan, daga kai tayi a tunaninta Ahmad ne don in
dai ya shigo kd ya kan fara xuwa ya gaida Umma kafin ya tafi gidansa, tun da ya shigo take kallonsa kamar
yanda shi ma yake kallonta, saukarsa kasar kenan kuma babu inda ya fara nufowa sai gidan Umma......
My strength ends here wllh... Thank you!!
*Wa enda nake bi dari biyar su ji tsoron Allah su xo su biya bashi su sauke nauyi ko ince hakki!! alfarman
wannan ranaku da muke ciki, domin fatan yin ibada amsasshe... Allah ya amshi ibadunmu ya sa muyi sallah
lafiya Ameen*
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada
wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;
Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan
kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun
fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan
wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan
link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697
Jiddah ce ta fara dauke idonta ta ci gaba da wankin da take a hankali, har ya wuceta sannan ta bi sa da
kallo ta durkusa tana ci gaba da daurayan hijabs dinta, bayan minti goma ta gama ta shanya su sannan ta
dauraye hannunta ta wuce cikin gidan, Xaune ta gansa a parlon yana danna wayarsa, su Maimoon na daki
Umma ma na bedroom dinta, Huraira kuma na kitchen tana girkin lunch, ta karasa cikin parlon tana
kallonsa a hankali tace "Sannu da xuwa..." Kallonta shi ma yake yace "Kema sannu" Xata tafi dakin Umma
taji yace "I will be back later" Ta juya tana kallonsa, mikewa yayi ya nufi kofa ita dai tana tsaye har ya fita
parlon. A hankali ta nufi dakin Umma ta yi sallama sannan ta bude, Umma na xaune tana waya, Jiddah ta
xauna saman carpet ta jira har ta gama ta ajiye wayar, Umma na kallonta tace "Ya aka yi Jiddah?" Tace "Aa
dama xan tambayeki sanda xa ayi awaran da kika ce ne" Umma tace "Au kinga ma na mance ni, duk sanda
kika shirya ba matsala ki xo ki amshi kudin ingredients din, ke da Huraira ko Maimoon ku tafi kasuwa"
Jiddah tace "Toh Umma" Daga haka ta mike ta fita daga dakin. Abuturrab na isa gidansa ya sauka daga d'an
sahun da ya kawo sa, sai a sannan ya tuna ba shi da currency din kasar a tare da shi, ya nufi gun Mai
gadinsa da ya taso yana welcoming dinsa da fara'a, yace "Ka basa dari biyar idan kana da shi" Mai gadin ya
taho gun Mai adaidaitan da sauri xai basa kudin Abuturrab ya shiga cikin gidan, the compound looks so
neat saboda yayi employing masu shara da gyaran flowers da ba su ruwa, yana isa entrance din shiga
parlon ya murda kofar gently ya shiga ciki, kida ne ke tashi an kure sa har kusan karshe a parlon, ya dinga
bin parlon that looks very untidy and unkept da kallo, ga plates sun fi kala biyar a kan carpet da duk ya baci
da shinkafa da kwallin lemo, kayan kallon da suka yi uban k'ura ya dinga kallo, ya kalli dining area can ma
duk plates da cups ne da breads ko kulle ledan ba ayi ba, calmly yake tafiya ya nufi stairs, shi ma duk yana
jin yana taka k'ura kasan tiles din, bangarensa ya tafi ya bude kofa, sun fi su bakwai xaune parlonsa nan din
ma dai plates ne da kwalaye na ciye ciyen da aka yi, suna ta labari ga kida na tashi a parlon ma amma bai
kai na parlor ba, Duk suka juya jin an bude kofa, Aneesah dake xaune kan carpet sanye da zani da ves a
jikinta ta mike da mugun mamaki tana kallonsa tace "My Captain saukan yaushe babu notice? Mun fa yi
waya jiya baka ce min kana tasowa ba" Bai sake kallonta ba balle ta sa ran amsa ya bude kofar bedroom
dinsa, Safara'u dake parlon ita ma da daurin kirjin ta mike da sauri tana cewa "In ji dai bai gan ni ba??"
Bata jira an bata amsa ba ta fice da sauri daga parlon, Kawayen Aneesah duk biyar din su ma suka mike
suka bi bayanta suka bar Aneesah tana xaxxare ido tana bin parlon da yayi kaca kaca da kallo, gashi takasa
bin sa cikin bedroom din, Abuturrab ya fi minti biyu tsaye yana bin bedroom din nasa da kallo, kaya ne ta
ko ina a xube tun daga kan gado har kasan tiles da carpet, bayan kaya har da takalma, ga farin bedsheet
din saman gadon har ya fara fita hayyacinsa duk ya yamutse, sababbin jakunkuna na kayan sa wa har uku
ya gani jere a dakin su ma duk a wangale, tun da yake bai ta6a sanin bedroom na iya xama haka ba sai
ranan, wannan ya wuce untidy ko unkept, har wani tsami tsami mara dadi yaji bedroom din ke yi, ga kofar
bandaki a hangame, ya lumshe ido ya juya ya bude kofar
ya fita, har sannan Aneesah na tsaye sai wuwwurga idanuwa take, bai kalli direction dinta ba ya fice, wani
dakin daban ya tafi ya bude ya ga Safara'u xaune saman gado wanda shi ma din duk a yamutse yake, har
lkcn daurin kirji tayi, ganin sun hada ido ya gaisheta, bai jira amsa dogon gaisuwan da take jere masa ba
bayan ta jawo zanin gado ta yafa, yace "Alhmdlh mun gode Allah" Daga haka ya fice ya kulle mata kofa,
wani dakin ya bude ya ga kawayen Aneesah sun yi dai dai a dakin ya kullo kofar ba tare da ya amsa
gaisuwansu ba, bai sake bude wani dakin ba ya sauka downstairs ya fice daga gidan gaba daya, Abuturrab
ya fi minti goma tsaye a kofar gida gashi babu cash a jikinsa babu Atm card, luggages dinsa kuma bai dauko
daga airport ba, wayarsa ya ciro daga karshe ya shiga kiran layin Maimoon, tana dagawa bayan sun gaisa
yace "Give the phone to ur frnd" Maimoon ta mika ma Jiddah dake gefenta waya, Jiddah ta amsa tana
duba me kiran kafin ta kai kunne, Maimoon ta fita daga dakin, Jiddah tace "Ina ji" Yace "Did u tell them i
am back?" Ta girgixa kai tace "Aa" Yace "Ohk, kina da cash wajen ki?" Ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Aa sai
a account, wanda Ya Ahmad ke sa min saboda makaranta" Calmly yace "Ohk ki bar wayar a wajenki..." Bai
jira tace komai ba ya katse wayar ya karasa bakin titi, ya samu adaidaita ya koma gidan Umma, bai bari ya
shiga can cikin layin ba ya sake kiran Number Maimoon, Jiddah ta daga, yace "Ki kawo min Atm card dinki
waje yanxu" A hankali tace "Toh" ya katse wayar, ta mike ta dau jakarta ta cire atm card din ta mayar ta
ajiye sannan ta dau gogaggen Hijab dinta ta saka ta bude kofa a hankali ta leka parlor bata ga kowa a
parlon ba hakan ya sa ta fito da sauri ta nufi kofar fita, har ta isa gate tana waigen entrance din gidan, tana
fitowa kofar gida ta dinga kalle kallen inda xata gansa, daga nesan ya hangota ya sauka daga kan
adaidaitan, hakan ya sa ta gansa, ta karasa inda yake tana tafiya a hankali, idonsa na kanta har ta iso, ya
sauke idonsa ya amshi Atm card din yace "Pin?" Ta gaya masa, yace "Thank you" daga haka ya shiga
adaidaitan yace su tafi, ita kuma ta juya ta koma cikin gida. Abuturrab na cire kudin ya tafi yyi lodge a
hotel, yana shiga dakin da aka bass ya kashe wayarsa, bayan ya huta yayi ordering abinci, Ana la'asar kuma
ya fita xuwa airport don daukan luggages dinsa ya dawo hotel din a taxi, ya shiga da kayan ciki, bai sake
fitowa hotel din ba sai da aka kira magrib ya fito yin sallah, bayan sun idar ya siya fruits ya koma cikin hotel
din.... Washegari Asabar karfe tara ya kunna wayarsa ya shiga kiran Ramlah, tana dagawa da fara'arta tace
"Yaya ka dawo ne?" Yace "Ahmad na gari?" Tace "Aa bai shigo ba satin nan, yace sai next week" yace "Ohk
xan xo in amshi makullin motarsa yanxu" tace "Toh yaya sae ka xo" katse wayar yayi da yake ya shirya ya
dau cash din da ya ciro jiya ya sa a aljihunsa sannan ya fita ya kulle dakin, a adaidaita ya isa gidan Ramlah,
bayan ya sallamesa ya shiga ciki yana amsa gaisuwan mai gadi, ya wuce parking space, yana tsaye a nan ya
shiga kiran Ramlah, bayan ta daga yace "Ki fito min da makullin parking space" tace "Yaya baxa ka shigo
ba?" Yace "Ehh" tace "To bari in fito" ba a dau lkci ba ta fito rike da makullin motar, tana murmushi ta nufi
parking space din ta risina ta basa tace "Ya hanya yaya?" Yace "Alhmdlh, ba sae kin ce masa na dawo ba"
tace "Toh Yaya" bude motar yyi ya shiga yyi warming dinsa ita dai tana tsaye tana kallon sa, har daga
karshe ta daga masa hannu ya fita da motar ita kuma ta koma cikin gida... Abuturrab ne xaune kansa a
kasa yana sauraron uncle dinsa, Alhaji Lawal dake ta kallonsa da kyau yace "To ko dai kana shan wani abu
ne wanda mu bamu sani ba Aliyu?" Shi dai bai ce komai ba, Alhaji Lawal yace "Dago ka kalleni ina maka
magana" Ba musu Abuturrab ya dago kansa yana kallon Uncle din nasa, Alhaji Lawal yace "Tell me what
exactly is wrong with u? Do we deserve being taking for granted Aliyu?" Abuturrab ya girgixa kai yace "Aa
Abba ku yi hakuri, kuskure ne..." Alhaji Lawal ya dakatar da shi yace "You called this mistake also Aliyu??
Baka tsoron Allah ne da xaka kara kiran wannan ma da mistake??" Sake baki Alhaji Lawal yayi yana
kallonsa, Abuturrab bai iya yace komai ba, Alhaji Lawal na jinjina kai yace "Lallai baka da hankali baka da
manners, ka kuma mugun raina mutane ka daukemu for granted, ashe dama kai ka haifa kanka bamu sani
ba?" Abuturrab yyi kasa da murya with remorse yace "Don Allah ku yi hakuri Abba, i know i wronged u all,
but this the only way out for me, Abba baxai saurareni ba, so is Ummi... No one will give me a listening
ear" Alhaji Lawal yace "Ohk ni kuma sbda ka yi shegen raina ni yanxu kake tunanin xan baka listening ear??
No... I am not giving u dat, and i am sorry babu wani abu da xan iya yi" Abuturrab ya kasa ce masa komai,
Alhaji Lawal yace "I can't do anything about this... ina ce ita wannan yarinya idan ban mance ba babu irin
hakuri da ban bakin da bamu baka ba a kan ka xauna da ita, ashe ka maida mu shashashai ne a lkcn ka je
ka saketa kuna ta xama tare duk don sbda kana ganin ita ba class dinka bace or whatever, bugu da kari
kuma u bluntly admitted baka sonta, to yanxun da ka koma ka aikata shirmen da ka aikata son nata ka fara
yi kenan???" Nan ma dai Abuturrab bai ce komai ba, Alhaji Lawal ya daka masa tsawa yace "Bude baki ka
bani amsa my frnd.. i am talking to u" A hankali yace "Ina son xama da ita yanxu Abba" Alhaji Lawal yace
"U are very stupid, ae ba tambayar da nayi maka ba kenan.." Kasa basa amsa Abuturrab yayi nan ma,
Ganin yanda Uncle din nasa ke kallonsa ya sunkuyar da kai, Alhaji Lawal yace "Toh ka saka a ranka cewar
kamar yanda muka xaunar da kai kwanaki muka baka takarda da biro ka datse auren naku wannan karon
ma hakan ne xai faru, mu ba 'yan banxa bane da xaka dinga controlling dinmu yanda ka so, kana aikata duk
abinda ya xo kanka without our consent, we birth u..." Abuturrab ya marairaice masa yace "Abba don
girman Allah ku yi hakuri, wllh ban koma na aureta da nufin in cuceta bane wannan karan, wancan lokacin
ma kuskure aka samu, don Allah Abba kayi hakuri, i mean no harm to her..." Alhaji Lawal yace "Da nufin
me ka koma ka aureta yanxu? Bani amsar tambayar nan" Abuturrab yace "Ina son xama da ita ne na har
abada" Alhaji Lawal ya girgixa kai yace "Kamar dai yanda na fada you are very stupid, kawai ka koma ka
aurota saboda kana son ku xauna tare har abada, wait!! are u mad??" Abuturrab yace "Abba ni dama fa
ban ta6a buda baki nace bana sonta ba, kawai sharrin shaidan ne da kuma yanda kowa baya son auren shi
yasa na aikata abinda na aikata, amma wllh ban ta6a cewa bana sonta ba" on a serious note Alhaji Lawal
yace "Daga Hajja a rashin alkibla sai kai, anyway... I am so dedicated today, don haka idan Allah ya amince
mana gobe xan shiga kadunan, xaka iya tafiyar ka sae na xo goben..." A hankali Abuturrab yace "Xan jira
mu tafi tare goben in sha Allah" Alhaji Lawal yace "Allah ya kai mu" Godiya Abuturrab yayi ma uncle din
nasa sanan ya mike ya nufi kofa hoping this will be the only challenge he is to face till end, Alhaji Lawal ya
bi sa da kallo har ya fita yana mamakin karfin hali da taurin xuciya irin na Abuturrab, kiri kiri yayi ta abu ba
tsoro. Abuturrab ya fi minti daya tsaye kofar parlon Abbansa ya kasa bude kofan, bai ta6a jin mugun
shakkan Abbansa irin na lkcn ba, bai san me ya sa wnn karan ko Aunty baya jin ta kamar yanda yake jin
Abbansa, ga bugun xuciyarsa da ya tsananta, it's been long da ya shiga yanayin nan da yake ciki yanxu,
muryan Umma yaji a bayansa ta rike ha6a tace "Kai kuma yaushe a gari??" Ya juya da sauri, yyi feigning
smile yace "Good evening Umma" tace "Saukan yaushe?" Ya d'an fara kame kame kafin yace "Jiya" tace
"Ikon Allah, to sannu da dawowa..." Bude kofar parlon tayi, lkci daya fara'ar da ke fuskarta ya bace, ta wani
sha kunu ta shiga parlon, tunda aka kirata aka ce ta xo gidan tayi tunanin xancen baxai wuce na auren da
suke shirin laka6a ma Jiddah ba, kuma ta sha alwashin yau kam sae inda strength dinta ya kare, dai dai take
da kowa, ganin Hajja xaune parlon ta wani kara daure fuska ta nemi waje ta xauna, Abuturrab ya shiga
parlon kansa a kasa gabansa na mugun faduwa, xaunawa yyi saman carpet ya kasa kallon kowa, a hankali
ya fara gaida Hajja kafin sauran occupant din parlon, Hajja dae fuskar nan nata babu ya6o bbu fallasa,
Umma ma babu yabo babu fallasan tace "Ina yini Hajja" Hajja ta rike kanta tace "huhuhu wllh tun da naje
Masar na samu saukin gaishe gaishen jaraban nan, yo kowa na ta kansa ina batun wani gaisuwa, su basa
haka a can wllh, duk wayayyu ne, a kasar nan kowa sae yace sae ya gaisheka alhalin wani gaisuwar ma bai
kai ciki ba, to ni dai na yafe, ko Usman ma ban amsa gaisuwarsa ba balle wani...." Ko kallonta Umma bata
sake yi ba tana jan counter dinta... Alhaji Umar ne ya bude wajen da addu'a, sannan bbu 6ata lkci kuma
babu boye boye in Brief Alhaji Lawal ya maimaita masu duk abinda Abuturrab ya sanar masa jiya a Zaria,
Babu wanda bai girgixa ba a parlon, Abba dai kallon ceiling kawai yake, gaba daya sauran mutanan parlon
kallon Abuturrab suke irin kallon tsoro, babu ko kiftawa, shi ko kansa na sunkuye xuciyarsa na bugawa,
Hajja dae sae wani murmushi take me sauti irin na bosawa tana girgixa kafa da kai, Bayan shirun kusan
minti biyu da ya ziyarci parlon, Aunty ta mike duk ta hada xufa daga sama har kasa tana girgixa kai tayi
wani murmushin takaici tana nuna Abuturrab tace "Wllh karya kake Aliyu, karya kake baka isa ka kunyata
ni ka toxarta ni, ka walakanta ni a idon duniya ba wllh... Karyanka ta sha karya wllh" kofa ta nufa ta fice
daga parlon da sauri, Umma da Ummi har sannan hangame baki suka yi suna kallon Abuturrab, Hajja na
kallon Abba a hankali tace "Yau da ace a Masar ne idan ba a garkame d'an ka a kurkuku ba shegiya nake
Usman, ae wannan shine ta'addanci mafi muni da mutum xai yi a hukuntasa a kasar Masar, kai ba a ma
ta6a haka a can ba wllh, Aliyu dai ya fita sahun mutanen kwarai, Aliyu mutumin banxa ne... Kiri kiri ya nuna
ma d'an uwansa na jini bakin ciki, da hassada, ba fa son yarinyar yake ba kawai