Showing 21001 words to 24000 words out of 321711 words

Chapter 8 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt

idonsa ba balle a
bata ta ci, sai da Jiddah ta bar gidan da bokitai sannan Zulai ta rike kunnenta daya tace "Anya ba son jiddah
mutumin nan yake ba kuwa Hansai, banda haka hidimar uban me xai maku, ku da ku ke gida, ga almajirai
can a titi, ga gidajen marayu a gari" Hansai tayi kasake, sae kuma tace "Sonta kuma? Ta ina xai so ta Zulai,
babban mutum ne fa, kudi yake bata ta kawo min mu kula da kanmu tun bayan mutuwar Isuhu fa...." Zulai
tayi wani murmushi irin na boss tace "Lallai Hansai, ashe har ynxu da sauran ki, to wllh da kyar idan ba
sonta yake ba me yasa bai mika ma Bibalo ta kawo kudin ba sai Jiddar" Hansai tayi tsaki tace "To Bibalo
sana'a take min a bakin titi da xai ganta ya bata? Ai sai dai Jiddar dake bakin titi kullum" Zulai tace "To wllh
ki farka daga wnn baccin da kike, kada ki kuskura ki bada kofar da xai shigo da wani batu bayan ihsanin da
yake maku, idan kuwa kika yrda to kina ruwa, ga dai Bibalo ai ita ya kamata a so tunda da gatan ta, amma
har kika yarda ya shigo maki da wani batu kan Jiddah to kashin ki ya bushe kina ji kina gani Jiddah xata
xama matar babban mutum...." Shiru Hansai tayi tana kallonta ko kiftawa babu da alamar xancen Zulai ya
gigitata, Zulai tace "Atoh, kada ki kuskura wllh, ihsanin ma idan son samu ne kada ki sake amsa don a bisa
dukkan alamu ya ga Jiddah ne ya kyasa, to jiddah kuma a wa Allah na tuba, yarinyar da ko dangin kirki bata
da, kai ina ma ta gansu, ke fa kadai ce gatan ta a duniya, ba dangin uwa balle na uba, yau da xaki koreta sai
dai ta bi duniya bata da wajen xuwa...." Hansai tace "Toh wai hauka nake yi ne Zulai, bayan an amshi
gaisuwa gun Iliya so kike d'an iskan ya 6a66aka ma gidan nan wuta mu shiga uku? ai jiddah yanxu bata da
maraba da matar aure, Iliya ya kawo komai sadaki kawai ya rage da daurin aure, shi ma ni ce na ja lkcn ai
an sa ranan kusa kusa na daga" Zulai tace "Atoh, tun wuri sanar masa ya dawo ayi ayi auren kawai, kinga
wannan mutumi kam dole ya komo ma Bibalo...." Hansai ta sharce wani xufa tace "Ni dadina da ke akwai
hangen nesa wllh Zulai, kinga bbu wanda ya xo ya wayar min da kai banda ke ina nan ina ta haukana, bari
in sa a kira min Iliyan dama sbda kudin katifar da xan siya mata ya sa nake ta jan auren naki yrda a sa sati
biyu kamar yanda ya bukata, amma tunda haka ne kuma ga wnn bawan Allah ya bamu kudade masu tsoka
kema har na cire maki dubu biyu a ciki, sai ki rakani kawai gobe ko tsohuwar katifa ce in siya mata da 'yar
robobin aikin gida" Zulai tace "Shkkn kuwa" kasa karasawa cikin compound din Jiddah tayi da bokitin ruwa
a kanta jin abinda su Hansai ke cewa, ta fi minti uku tsaye duk tana sauraronsu Zulai tace "Idan kin kirasa
kice yace a sa bikin sati biyu kawai kin shirya a wuce wajen" Hansai tace "In sha Allahu haka xan yi" A
hankali Jiddah ta karaso ciki ta juye ruwan kanta duk suka yi tsit, ta juya ta fita tsakar gidan lkci daya
hawaye ya kawo idonta, ita dai bata ji xancensu na farko ba amma daga inda suke cewa xa su ce Iliya ya
dawo ayi auren ta tsinci maganar su. Bayan ta fito ta so shiga gidan Iyah amma sbda irin warning din da
Hansai tayi mata yasa bata shiga ba, inda xata shiga tayi kukanta me isarta take nema, a haka ta dinga jan
kafa har ta isa inda pampon yake ta jingina da bangon wani gida tana share hawayen dake makale idonta,
ko yaushe xai kawo mata piya piyan da yace xai kawo mata, ji tayi baxata iya jiransa ba kuma, gwara kawai
ta siya da kanta duk da kudin da ya rage mata yanxu bai wuce dari biyu ba tunda Hansai ta rabata da
Usman dinta ta karfi da yaji, don kuwa wanke kafa tayi ta tafi har gidansu can cikin gari ta sanar ma
iyayensa su ja ma d'an su kunne ya fita harkar 'yar ta jiddah don an sa mata rana, tun daga sannan kuma
rabonta da Usman. Washegari da sassafe Hansai ta fita xuwa gidan Zulai don daga can xasu wuce kasuwan
dillalai yi ma Jiddah siyayyar aure, wata tsohuwar katifa ce da ko riga babu suka siya a farashi me sauki da
pillow kwaya daya, sai robobin kitchen su ma duk tsofaffi, hatta wuka basu siya sabo ba sai tsoho, suka dai
kwaso tarkacen da xa a iya kai ta gidan miji da shi, suna shirin barin kasuwan Zulai tace "To baki siya xanin
gado ba" Hansai tace "Ina da wani a karkashin akwati xai yi shekara goma da ajiyesa sai in bata kawai, buta
kuma ta tafi da na ubanta yana can ba amfani muke da shi ba" A barrow suka kima kayan suka dau hanyar
gida. Tunda Jiddah taga siyayyar da suka yi wanda ke nuna cewar an kusa aurenta da Iliya hankalinta yyi
mugun tashi, Hansai kuwa tuni tayi kiran Iliya da ya sanar mata sun ma kusa shigowa kaduna, bayan ta
katse kiran tana kallon Zulai da wata kawarsu Dije da ta rakasu siyayya tace "Atoh ai shkkn, yace sun wuce
Abuja, kun ga wannan karan kenan da matarsa xai koma legas din" Zulai tace "Ahh shkkn, Allah dai yasa ayi
bikin da mu" Dije tace "Ameen, ai Hansai 'yar halaq ce, babu wanda yayi tunanin xata yi ma jiddah wannan
abun arxikin, kowa gani yake tunda Malam Isuhu ya kwanta dama shkkn watsi xata yi da jiddah, sai gashi ta
ba mara da kunya, kuma in sha Allahu baxa ki ta6e ba, kin cika yar halaq wllh" Hansai tayi murmushi tace
"Toh Allah na tuba ko uban na da rai wllh ba samun hakan xata yi daga garesa ba, sai in idanuwansa xai
kwakule ya siyar yyi mata kayan daki, uban me garesa banda wannan rubabben gidan, bashi da komai sai
wahala wllh" Zulai ta kwashe da dariya tace "Allah dai ya ji kansa, gashi nan kin rufa masa asiri kin rufa ma
'yar sa asiri, kin mata abun arxiki" Washegari Hansai ta azalzali Iliya da kira nan ya sanar mata nan da
kwana biyu xa su je can gidan kawun nata da ake xancen auren a wajensa tare da magabatansa sai a saka
sati biyun da tace, amma fa ba shi da kudin sadaki a yanxu sai dai a biyosa bashi, Hansai tayi shiru tana
sauraronsa, can tayi kasa da murya tace "Iliya da kudin sadakin fa nake son yi mata dinki tunda ba lefe xaka
yi mata ba kace baka da halin yi...." Ya katse ta cikin fada yace "Gashi nan da duk kudin hannuna na siyo
maki masara kwano 8 da gawayi, ko in siyar in kai kudin sadakin?" Da sauri tace "Aa to ai tunda kace idan
ka samu xaka bada babu wani damuwa xan ma kawun nawa bayani, Allah yayi maka albarka, ai kowa yasan
kai me xuciyar yi ne Iliya, to a ina xaka ajiye Jiddar?" Yace "Ehh akwai shago daya gaban gidan kakana sai ta
xauna nan kafin in sama mata haya" Tace "Atoh shkkn, ni na xata legas din xaku wuce tare ince shkkn xaka
rabani da Jiddah gaba daya" Yace "Aa nan xan bar ta, mu ma gareji muke kwana a legas din" Hansai ta xaro
ido tace "Atoh Allah ya rufa asiri, tunda ga gida ka samar mata a nan din shkkn, Allah ya kai mu wannan
rana dai" Yace "Ameen" daga haka ta katse wayar tace "Toh ba shkkn ba"

Abuturrab na kwance cikin resting cabin din jirgin da yayi piloting tare da Co-pilots dinsa daga lagos xuwa
kano, ko minti talatin basu yi da alighting ba, idonsa a lumshe suke duk da ya rufe fuskarsa da hulan
uniform dinsu na pilot dake jikinsa, tapping dinsa aka yi a kafa, ya xame hulan a hankali, Co-pilot dinsa ne
tsaye kansa, pilot din yyi wani sigh yace "Done with the Secure Cockpit checklist.... Can we??" Abuturrab
ya mike xaune yace "Alright..." Pilot din yace "Ain't you changing??" Abuturrab ya kalli uniform din jikinsa
yace "Not at all" Jakunkunansu suka dauka suka sauka jirgin, sai da suka gaisa da incoming crew da suka
hadu da sannan suka shiga cikin airport din. Driving Abuturrab ke yi cikin motarsa da yake bari a airport,
hotel din da yake sauka yawanci idan yana kano ya nufa, duk da Abbansa na da gida nan kano wanda ke a
kulle babu kowa ciki baya sauka gidan don baya son xama shi kadai shi yasa ma idan kwana ya kamasa a
Abuja, it's either su kwana gidansa tare da Ahmad ko Aneesah ta xo tayasa xama, ya so tafiya kaduna yau
amma bai samu flight me xuwa kaduna ba or even private jet, yana shiga hotel din ya karbi daki kamar
yanda ya saba, wanka yyi ya sauya xuwa kananun kaya, yayi sllh sannan ya bude pepper soup din hanta da
ya sa a kawo masa with cup of coffee, ya fara ci a hankali, ajiye spoon din hannunsa yyi tunawa da yayi bai
samu Mu'axxam yayi masa magana ba a kan yarinyar nan ta Hayin rigasa, ya dafe kansa don shaff ya
mance, tun a jirgi da ya tuna yake Allah Allah suyi alighting ya samesa da maganan, he can even go to d
extent of taking all the marriage responsibilities in har Mu'axxam din yace bashi da hali, tsaki ya d'an yi
don gobe da sassafe yake son driving xuwa kaduna baxai shiga airport din ba, a hankali ya ci gaba da shan
pepper soup dinsa har ya ji ya ishesa sannan ya tashi ya shiga bandaki ya wanke bakinsa ya fito yayi
kwanciyarsa. Washegari Saturday karfe goma saura Abuturrab ya shigo compound dinsu... Parking yyi kusa
da motarsa da yake amfani da a kaduna, ya sauka sannan ya shiga ciki, part din Aunty ya fara nufa ya
sameta parlonta tana breakfast, ganinsa tace "Daga ina haka kamar an jefoka captain?" ya xauna kasan
lallausan carpet din parlon yana murmushi yace "Daga kano nake" tace "Ikon Allah welcome son..." Yace
"Ina kwana Aunty?" Tace "Lafiya lau ya hanya?" Yace "Alhmdlh" mikewa tayi tace "Let me get u breakfast"
Bata jira cewarsa ba ta fita, sae gata ta dawo tare da mai aiki rike da tray din breakfast din, Mai aikin ta
gaishesa sannan ta ajiye, ganin kallon da yake ma tray din Aunty tayi dariya tace "Taimaka min kawai tayi ta
dauko flask din ba wai ita ta hada maka ba..." Bai ce komai ba ya dau cup dake a kife ya juya yana kallon
ciki keenly kamar yana neman abu, Aunty tace "To yanxu da ba Aneesah bace budurwar ka ya xaka yi da
wannan kyankyanin captain, yan matan yanxu da son jiki duk ya sa sun xama kazamai" Ba tare da ya kalli
Aunty ba yace "Allah ya ga xuciyana shi sa bai hadani da mara tsaftar ba" Dariya kawai Aunty tayi tace "Jiya
ma Aneesar ta kirani mun gaisa ashe ta koma Abuja" Yace "Ehh ta koma..." Tace "Idan ka gama sai ka
ajiyeni U-rimi don Allah, driver baya nan kuma bana son driving" Yace "Alright" Yana gama breakfast din
kuwa ya mike, tuni ta dauko mayafinta da yar jaka, yace "Salem fa?" Tace "Tun yaushe Salem ya koma
makaranta" Abuturrab yace "Ohh yea mun yi chatting ya gaya min, but na manta" Sai da suka fita parlon ya
tuna bai je gaida Umminsa ba, ya d'an buda ido yace "Aunty bari in shiga in gaida Ummi yanxu in fito" Ta
d'an 6ata rai tace "Yanxun nan fa xaka ajiyeni ka juyo Captain, cikin mintuna kadan xaka dawo ai" Bai ce
mata komai ba ta fara tafiya ya bi bayanta walking slowly. Abuturrab bai dawo gidan ba sai bayan la'asar
tare da ita, tana rike da ledojin atamfofi da ta sa ya siya mata a gidan da suka je, ta nufi part dinta, shi
kuma ya shiga bangaren Mahaifiyarsa, kanwarsa Ramlah kadai ce parlon tana shara yace "Ummi fa?" Tace
"Ta fita tare da driver yanxu" Ya shafa kansa yace "Ohk..." Juyawa yyi xai fita tace "Shine baka shigo ka
gaisheta ba kuma tun safe ka dawo yaya" Ya juya ya mata wani kallo yace "Yaushe na fara wasa da ke?"
Shiru tayi bata ce komai ba, yyi kwafa ya fice daga parlon. Bedroom dinsa ya shiga, sai bayan da yyi wanka
ya sauya kaya sannan ya fito main parlor rike da makullin motarsa, har xai fita ya nufi kitchen jin
movement a ciki, Safiyya ce a kitchen din da Ramlah sai mai aiki da alama dinner suke dafawa, yace "Is
there anything to eat here?" Safiyya ta kallesa tace "Aa ba a gama ba" Juyawa yayi ya fita daga kitchen din
ya bar parlon gaba daya, sai da yayi sllhn magrib sannan ya bar anguwar... Parking Abuturrab yyi yana
kallon cikin karamin layin da babu haske banda na wata, yara ne bakin wani tap suna ta diban ruwa suna
wasa da ruwan, tun da yamma ya so xuwa amma sbda comment din Umar a kansa ranan a hospital yasa
ya ki shigowa anguwar da yamman, ya sauke glass yana ta kallon yaran, da hannu yyi ma wani yaro cikin
yaran alamar ya xo, yaron ya taho da sauri, dari biyar ya dauka cikin motar ya mika ma yaron yace "Kaje
can gidan da ake siyar da awara ka kira min yarinyar dake siyar da awaran" Yaron ya ruga da gudu xuwa
gidan, yana isa ya kutsa kai ya shiga, Hansai na xaune tsakar gida Bibalo na haska mata fitila tana daure
busasshiyar kubewa a leda, Yaron yace "Ina wuni maman Bibalo" Hansai tace "Lafiya lau, me xaka siya?"
Yace "Aa wani me mota ne yace in kirawo me awara" Hansai ta kalli Jiddah dake duke bakin kwaroron
wanke wanke tana yi, Hansai tace "To ai kuwa xuwa xaki yi ki ji me ke tafe da shi, tunda yasan yanayin garin
kilan wani alherin ya xo mana, ko kuma Bibalo ta je, yan sa idon anguwar nan sae su iya juya mana xance
yanxu yanxun nan...." Jiddah dai bata dago ba ta ci gaba da abinda take yi, Mikewa Bibalo tayi da sauri ta
ajiye fitilan hannunta tace "Bari in je ni" Mayafi ta figa ta fice daga gidan tana ce ma yaron taho ka nuna
min inda yake, can bakin titi yaron ya nuna mata, Abuturrab ya dinga kallonta daga cikin motar, tun daga
tafiyar ya gane ba jiddah bace har kuwa ta iso bakin titi, tsaye tayi jikin motar, ya sauko yana kallonta, tayi
fari da ido tana wasa da mayafin kanta tace "Sannu da xuwa...." Yace "Ina 'yar uwar taki" ta buda ido sosai
tace "Yo ae ta daina fitowa ynxu sbda bikinta sati me xuwa ne, kasan har iyayen iliya sun xo anyi komai
yau..." Kallonta ya dinga yi ko kiftawa babu, tace "Idan wani abu ne gani ni ka bani in ji Baabarmu in kai
mata" Ya dauke kai daga kallonta yace "Mu je xan ba Baabar taku da kaina" Da sauri ta shiga gaba yana
biye da ita, sae wani rangwada take har suka iso kofar gidan, tace "Bari in je in mata magana" daga haka ta
shige ciki, Hansai na ganinta tace "Me ya baki?" Bibalo tace "Yace ki je yana kofar gida" Da sauri Hansae ta
figi gyale ta yafa ta fita kofar gida, dukawa tayi ta gaishesa ya sauke idonsa shi ma ya gaisheta, ta amsa cike
da nutsuwa tace "Sannu da xuwa Alhaji"

07087865788
✍🏻


💖💖 *Jiddatul Khair**💖💖




_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
8.....


Hansai ta shiga kame kame tace "Gashi babu ma wajen xama a nan Alhaji, ko xa ka shigo daga ciki a
shimfida maka tabarma" Yace "Aa nagode, hakan ya isa..." Tana murmushi tace "Allah sarki... Da yake
jiddar na daurayan kwanuka shine nace 'yar uwarta ta fito, jiki kam alhmdlh taji sauki sosai, duk ta shanye
magungunan nata..." Abuturrab ya sauke idonsa kasa yace "Allah ya kara mana lafiya gaba daya" Hansai
tace "Ameen, bari dai kawai in shiga in turo ta ku gaisa, ai yanxu nasan ta gama" daga haka ta shige gida
ganin dai babu alamar Abuturrab xai bata komai, jiddah ta nufa da sauri, murya can kasa kasa tace "Tashi ki
dau hijabinki ki saka ki fita yana nan kila ya fi gane ya baki, kada ki kuskura ku tsaya kofar gidan nan ki ja shi
can karshen layi sbda yan sa ido, gashi iliya na gari, daga nan ma sai ki sanar masa bikin ki sati me xuwa ne
idan Allah ya kai mu, kinga idan da akwai wani alkhairin da xai maki sai ya maki, kowa dai yasan ke
marainiya ce ba uwa ba uba" Bibalo da ke tsaye kansu tana sauraron abinda suke cewa tace "To Baabarmu
idan yaji xata yi aure fa kilan shkkn baxai sake dawowa ba, dama ba sbda awaran da take yi bakin titi bane
yake tausaya mana yake bamu kudi?" Hansai tayi shiru, can tace "To kuma aure ae dole tayi abu saura sati
daya dai har an gama komai, kawai ta gaya masa.. sannan ba ga ki ba, ai ke xaki ci gaba da yin awaran a
bakin titi" Bibalo tace "Cabdijam, wllh baxan yi awara bakin titi ba kawayena da samarina na ganina, haka
kawai?? sai dai ke ki dinga yin kayanki ni dai baxan yi ba, to ni ma ba sai a min auren ba kawai" Tana fadin
haka ta shige daki tana gunguni, Hansai ta rike ha6a tace "Ikon Allah, yau naga jarababbiya, a maki aure?
Duka nawa kike xa a maki aure, ita ma Jiddar ai don iliyan ya dade yana sonta ne kuma ya mana hidima ba
kadan ba, ko so kike ya mana tijara yace sai mun biyasa? A gidan uban wa ma xan samu abun biyansa? ke
kuma da nake da burin in samar maki makaranta cikin gari ki fara xuwa kya kawo xancen a maki aure, a can
din sai kiga Allah ya hadaki da miji dai dai ke, nan banda yan kato da gora, da yan adaidaita sahu, ga
leburori, ga yan gwangwan sai yan iskan anguwa, to waye sa'an auren ki duk cikinsu? Ai babu sa'an auren
ki wllh, ke da kike matar babban mutum" Hansai ta kalli Jiddah da kanta ke kasa har lkcn tana sauraronta,
ta hade rai tace "Baxa ki tashi kije ba kin bar bawan Allah tsaye a waje" Jiddah ta mike a hankali ta dauraye
hannunta ta shiga daki ta dau Hijabinta ta sa, ta saka takalminta sannan ta fita Hansai ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login