Showing 69001 words to 72000 words out of 321711 words
Chapter 24 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt
mata, da harara ya bi ta yace "Xaki ga
ko xaki sake leka kofar gate din gidan nan balle har in kai ki gidan Umma ki samu daman hawayen iskanci"
Kamar jiran jin hakan take ta fashe da kuka sosai tana kallonsa tace "Don girman Allah kayi hakuri, wllh
kewarta nake bana son in rabu da ita shi sa nake kuka, don Allah kayi hakuri" ko tanka ta bai yi ba ya nufi
kofar shiga gidan ta bi bayansa da sauri tana kuka, ko tsayawa bai yi a parlor ba ya wuce bangarensa, ta
shiga dakinta ta ci kukanta me isarta bayan ta sannan ta kwanta. Karfe sha daya da kusan rabi yayi
knocking kofar dakin ya shiga, ganin tayi bacci ya bude warmer din abincin da ta ajiye kasan dakin, yaga
bata ta6a ba duk da yasan ta ci abinci a can gidan, ko kayan jikinta bata cire ba, wannan dalilin ne yasa ya
tasheta, mikewa xaune tayi da sleepy eyes dinta tana murxawa, yace "Me ya hanaki wanka kafin ki
kwanta?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Dama bakya wankan daren da nace maki kenan?" Da sauri ta
bude ido sosai tace "Wllh ina yi bansan sanda nayi bacci ba" Yace "Toh tashi kije kiyi wankan" Kallon agogo
tayi da sauri, ya hade rai yace "Tashi nace" A sanyaye ta mike xata shiga bandakin yace "Da kayan xaki yi
wanka?" bata ce komai ba, amma ta ki cire kayan a gabansa, ya daure fuska yace "Ba magana nake maki
ba" Ta d'an kallesa tayi narai narai da ido tace "Tawul din yana bandaki ne" tana fadin haka ta shige
bandakin, gefen gadon ya xauna yana naxarin maganganun da Umma tayi masa a waya bayan sun dawo
gida, he is finding it hard to forget her words and move own, yasan no matter what Ahmad baxai ta6a gaya
mata xaman da yake da Jiddah a gidan nan ba, yasan baxai ta6a ce mata ma bbu aurensu da Jiddah kamar
yanda ya sanar masa ba, but her words carried weight this night, he have a very good intention toward
jiddah, ba shi da nufin ya cuceta ko ya walakantata ko ya saka rayuwarta a garari, his intentions are nothing
but pure, dafe kansa yyi, lkci daya ya dago jin wayar dake hannunsa yayi vibrate ya duba ya ga Aneesah ce
ke kiransa, bai sake kallon wayar ba coz sun yi magana not too long, bayan kusan minti sha biyar jiddah ta
fito daga bandakin sanye da kayan da ta cire, kasa kallonsa tayi ta ja gefe ta tsaya, wani kallo ya dinga mata
kafin yace "Meye hakan kika yi?" Ta ki yarda su hada ido tace "Ni baxan iya fitowa babu kaya ba bayan kana
xaune dakin" Daga sama har kasa ya dinga kallonta yana mamakin abinda ta fada, can dai yace "Ke kina da
wani abinda xaki boye min a jikin ki dama, kwaila da ke?" Ta d'an turo baki ta juya masa baya, Tsaki yyi ya
mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo, murya can kasa tace "Eh amma ai ni ba muharramarka bace da xan cire
kaya...." Ganin ya juyo tayi tsit, ganin impression din fuskarsa gabanta ya fara faduwa, yace "Kika ce me?"
Ta girgixa kai da sauri tace "Ban ce komai ba" Dawowa dakin yyi, ta marairaice tana kallonsa tace "Don
Allah kayi hakuri ni bance komai ba" Yace "Kika ce ni ba muharraminki bane?" Ta girgixa masa kai da sauri
bakinta na rawa tace "Aa bance haka ba" Sai da ya iso gabanta ya tsaya, sbda tsoro taji ta ma kasa tsayawa,
calmly yace "A ina kika san wanda muharraminki ne da wanda ba muharraminki ba?" Jin taki cewa komai
ya mata wani tsawa da yasa ta duka hawaye ya kawo idonta, yace "Idan baki bani amsata ba na fara ball
dake sai kin ganki downstairs yanxu" Cikin rawan murya tace "Ai da ina xuwa islamiyya" Ya gyada kai yace
"A islamiyyan kuma basu sanar maki hukuncin wanda yace xai kashe kansa ba?" Kasa cewa komai tayi, ya
wani hade rai yace "Mike ki cire kayanki" Ta sake marairaice masa amma ganin kallon da yake mata ta mike
da kyar, ta gefen ido ta kalli bandakinta, lkci daya kamar kiftawan ido ta shige ta sa makulli hannunta na
rawa, ya dinga kallon kofar, can yyi murmushi yana shafa kansa, lkci daya kuma ya hade rai ya fice daga
dakin, bai karasa bangarensa ba wayarsa yyi vibrate ganin me kiransa sai da gabanaa ya fadi, har ya katse
bai dauka ba, sai da aka sake kira sannan ya daga, murya can kasa yyi sallama yace "Ina yini Aunty" ba tare
da ta amsa ba tace "Aliyu kana ina??" ya d'an bude ido yace "Aunty ai ina kano, ban dawo ba..." Bude
kofarsa yyi ya shiga ya kulle hade da lumshe ido jin abinda take cewa. Washegari da safe wanda Abuturrab
ya sa ya samar masa mai gadi ya iso gidan da mai gadin, Abuturrab na kallon matashin mai gadin yace
"Yaranku nawa da matar taka?" Mai gadin yace "Daya ne kawai Alhaji, sabon aure ne" Abuturrab yace "Ba
damuwa, yau nake son xaka fara aikin sai ka koma ka taho da iyalan naka" Mai gadin ya risina da ladabi
yace "Toh nagode Alhaji, xan je kauyen namu yanxu sai in taho da su in sha Allah, Allah ya saka da alkhairi"
Abuturrab yace "Ameen, amma kada ka wuce karfe biyar na yamma don xan koma gun aiki a yau" Mai
gadin yace "In sha Allah Alhaji" dubu biyar Abuturrab ya basa kudin motar xuwa taho da iyalan nasa, shi
ma wanda ya kawo sa ya basa dubu biyar, bayan sun tafi ya koma cikin parlor.... jiddah na kitchen tana
dumaman tuwon da umma ta bata jiya, yatsine fuska yyi yana kallon kitchen din don ko by mistake baya
son warin miyar kuka, barin ma yanxu da take dumamawa, hakan ya sa ya dau makullin motarsa ya bar
gidan xuwa inda xai je yyi breakfast, jiddah na jin fitan motarsa ta jigina jikin bango tunda taji yana waya ko
minti sha biyar ba ayi ba yace yau xai koma gun aiki ta ji duk mood dinta ya canxa, gaba daya bata son
xama ita kadai a gidan, a sanyaye ta kashe gas din ta xuba tuwon amma ta kasa ci, Duk da xamansa a gidan
da rashin xamansa kusan daya don ba wai wani magana me tsayi yake mata ba, kuma ba waje daya ma
suke xama ba amma idan yana gidan bata jin kadaici da kewa na damunta, duk sonta da tuwon saboda
yanayin da ta shiga sai ta kasa ci da yawa, haka nan ta mike ta kai kitchen ta wanke plate din, sama ta wuce
ta wanke bakinta, komai da take yi a gidan tayi, turaren wuta ne kawai bata sa ba, ta dau turaren ta sauka
parlor ta sa sannan ta xauna tana kallon yanda yake fita a hankali, kana ganinta kasan jikinta a sanyaye
yake, bude kofar parlon aka yi Abuturrab ya shigo ta daga kai ta kallesa sannan ta sauke idonta, sai da ya
karaso cikin parlon tace "Sannu da dawowa" Bai amsa ba yyi wucewarsa sama ta gefen ido ta bi sa da kallo
har ta daina ganinsa, a sanyaye ta mike ta wuce sama ta shiga dakinta ta kwanta tana kallon fuskarta ta
madubin press din dakin. Da yammacin ranan tana tsaye jikin window aka bude kofar dakin, tunda ta
kallesa sau daya ta dauke idonta, yana bakin kofar a tsaye yace "Shuka kika yi wajen nan da kike tsayawa
ko da yaushe?" Tana wasa da fingers dinta ta girgixa masa kai, juyawa yyi ta bi sa da kallo ganin jakar
hannunsa, da sauri ta bi sa tace "Tafiya xaka yi?" Ya juyo yace "Kina bukatar wani abu ne?" Lkci daya jikinta
yyi wani sanyi, shi dai kallonta yake yana lura da ita duk a lkci daya, sauke idonta tayi saboda hawayen da
ya kawo idonta, yace "Nace kina bukatar wani abu ne" ta girgixa masa kai hawayen dake makale idonta ya
gangaro ta juya da sauri ta koma ciki, da ido ya bi ta, kafin ya bi bayanta xuwa dakin, durkushe ya ganta ta
daura kanta saman gado, da mamaki yake kallonta, can yace "Ke kina da lafiya kuwa" kin dagowa tayi tana
shessheka, ajiye jakar yyi yana kallonta, can ya karasa kusa da ita ya tsaya yace "Tambayar ki nake, kina da
lafiya kuwa?" Still taki dagowa, ya daka mata tsawa yace "Baki ji na ne" mikewa tayi hawaye na kai koma a
idonta, ya dinga kallonta kafin yace "Me aka maki?" Ta girgixa masa kai, ya mata wani kallo yace "Me aka
maki nace?" Cikin rawar murya tace "Ba komai" rungume hannu yyi yana kallonta, can yace "Kina bukatar
wani abu ne" Wasu sabbin hawayen na xubo mata cikin rawar murya tace "Tafiya zaka yi ka barni ni kadai
babu kowa, alhalin tsoron gidan nake ji" kallonta kawai yake ya ma rasa me xai ce mata, can dai yace
"Shine yasa kike kuka?" Ta gyada masa kai tana kallonsa with tears in her eyes, yace "Ohk, ynxu in tafi da
ke kenan?" Tayi shiru still crying tana kallonsa, yace "Bude baki ki bani amsa, in tafi da ke kenan yanxu?" A
hankali ta gyada masa kai, daga sama har kasa yake kallonta, tausayinta yake ji har kasan ransa amma bai
nuna hakan ba, to ina ma xai kai wannan yanxu wani yayi xaton matarsa ce?? Ta ina xai fara tafiya da ita?
Ita dai kanta na kasa, bayan few seconds yace "Ina wayar da na baki" juyawa tayi a sanyaye ta nufi gaban
madubi ya bi ta da kallo, har ta dauko wayar ta dawo, ta mika masa, amsa yyi ya shiga call log, yace
"Matso" ba musu ta matso kusa da shi tana kallonsa, ya hade rai yace "Wayan xaki kalla ba ni ba" Kallon
wayar tayi, ta madubin press din dakin ya kallesu, duk tsayinta iyakarta kirjinsa, jin bai ce komai ba sai
kallon wayar take ta daga kai a hankali ta d'an kallesa, ganin inda yake kallo ta kalli madubin ita ma, a
hankali ta d'an koma baya ganin dab take da shi ta sunkuyar da kanta, dauke idonsa yyi daga madubin, as if
bai son maganan yace "Ga number na nan, duk idan kina son wani abu ko kina da wani magana sai ki
danna nan sannan ki sake dannawa ki kirani" Kai kawai ta gyada masa ya jefar da wayar kan gado ya nufi
kofa ta bi sa da kallo sabon hawaye na taruwa idonta har ya fita, yau din ma ta waje ya kulle kofar parlon
duk da kasancewar mai gadi da matarsa da yaronsu dake gidan yanxu. Kuka sosai Jiddah tayi bayan
tafiyarsa, taji komai bai mata dadi a duniyar ynxu, kullum ita kadai kamar mayya a gida babu kowa, tun
tana tsoro sosai har tsoron ya ragu, tana sallan isha ko abinci bata ci ba ta kwanta ta takure cikin duvet,
nan da nan bacci ya dauketa.... Abuturrab na xaune saman gadon hotel wajen karfe goma da rabi, ya gama
abinda yake a laptop ya ajiye yana duba agogon wayarsa, call log dinsa ya shiga har yyi dialing number sai
kuma ya katse, mikewa yyi ya kashe wutan dakin ya kwanta yana karanto addu'ar kwanciya, jawo wayar yyi
ya d'an yi dube dubensa, sai kawai ya shiga call log din yyi dialing number, he just can't because he have a
problem with conscience, abu kadan ke sawa conscience dinsa yyi judging dinsa... Karan wayar ya farkar da
Jiddah, bacci ne sosai idonta haka dai ta dau wayar dake saman gadon tayi picking sannan ta kai kunne ta
rufe ido bata ce komai ba, jin shirun yyi yaww Abuturrab yace "Ni xan gaisheki" ta bude ido cikin muryar
bacci tace "Aa" nan da nan ya gane ta fara bacci, ya dai ce "Me kika ci?" Shiru bata amsa ba, yace "Kee?"
Tace "Uhn" yace "Kin yi bacci ne?" Kai kawai ta gyada masa ba tare da tace komai ba kamar yana ganinta,
shiru yyi, bayan wani d'an lkci yace "Amma sae da kika yi wanka??" Tuni Jiddah tayi nisa baccinta, bayan
few seconds yace "Jeeddarh" jin shiru ya katse wayar kawai ya ajiye sannan yayi rub da ciki nan da nan shi
ma baccin ya daukesa. Washegari Jiddah na kitchen yau dai shinkafa da miya take yi tunda ya koya mata
yanda ake amfani da blender, ji tayi kamar ana bude kofar parlor, ta tsaya kitchen din tana saurare har taji
an shigo parlon, da sauri ta fito, ido hudu tayi da Ahmad tare da Maimoon, kallonsu kawai take da mamaki,
ya sakar mata murmushi yace "Toh ko dai mu koma ne?" ta girgixa kai da sauri tace "Aa sannunku da
zuwa" Duk suka karasa parlon yana kallonta yana murmushi, Maimuna na kallon Jiddah ita ma tana
murmushi tace "Sannu da gida Aunty Amarya" Murmushi jiddah ta kirkira ta karaso ita ma cikin parlon, har
ranta taji dadin ganinsu, Ahmad ya xauna yace "Ya gidan Jiddah?" A hankali tace "Lfya lau, ina yini?" Yace
"Fine Alhmdlh, dama an kawo mai gadi gidan ne?" Kallonsa kawai Jiddah ke yi kafin tace "Nima ban sani ba
ai" Tausayinta Ahmad ya ji, can yace "Toh baxa a kawo mana ruwa ba?" Tashi Jiddah tayi tana murmushi a
kunyace ta wuce kitchen ta kawo masu har da lemo, tun jiddah na kin sakin jiki, har daga karshe ta sake
gaba daya, Ahmad ya dinga mamaki ganin ashe tana da baki, ga zakin murya kamar zaabiya, sosai
Maimoom taji tana son Jiddah, har abinci sai da ta kawo masu, ana kiran azahar Ahmad yace mata xasu
wuce don yau ma xai koma Abuja, lkci daya mood dinta ya canxa, Maimoon sai taji tausayinta, makullin
gidan Ahmad ya mika mata yace "Su Maimoon xasu dinga xuwa taya ki hira a kai kai idan captain din baya
gari so kar ki damu kinji" kasa basa amsa tayi don har hawaye ya kawo idonta, dariya ta basa, yyi kasa da
murya yace "Amma fa kar ki sanar masa xuwan mu kinji? Wataran idan naxo tafiya xanyi dake daga gidan
gaba daya" Ta gyada masa kai, a haka suka tafi duk yanda ta so daurewa ta kasa sai da tayi kuka. Bayan
la'asar wajajen karfe biyar ta gaji da xaman dakin da tsayuwar window ta fito, kallon hanyar da xai kai ta
part din Abuturrab tayi, tun ranan da suka fito daga wajen bayan ya nuna mata takarda bata sake bin
hanyan ba, tsaye tayi tana ta kallon direction din, can dai ta karasa tana tafiya a hankali har ta isa kofar
parlonsa ta bude tana lekan ciki, komai na parlon fess ko alamar datti bata gani ba sai wani kamshi ma da
take ji, shiga parlon tayi tana bin ko ina da kallo gabanta ya dinga faduwa, can ta karasa wani kofa da ta
gani, bude kofar tayi a hankali tana lekan ciki, daki ne da wani babban katifa da bedsheet a kai, babu
abinda bbu a babban dakin, karasawa tayi ciki tana kallon wani table da jirgi a kai, xaro ido tayi tana kallon
karamin jirgin, dauka tayi da hannu biyu tana jujjuyawa ta kai idonta tana leka d'an windows din jirgin,
hotonsa ta gani jikin bangon dakin da fararen kaya ya rike hula tsaye kusa da wani katon jirgi, a ranta
tunani ta shiga yi kilan shi ya ta6a ganin jirgi tunda gashi yayi hoto kusa da jirgin, ita dai a sama kawai suke
hangosa dan mitsili, kallon fuskarsa ta dinga yi, lkci daya gabanta ya fadi tana ganin kamar xai iya magana a
hoton, a hankali ta juya, taga wani kofa ta karasa ta bude ta ga wani makeken bandaki da abu kamar katon
glass a ciki har tana iya hango ciki, kwata kwata bandakin ba irin nata bane, ga shi da girma sosai, ko ina a
bushe yake sai kamshi bandakin yake, a hankali ta rufo kofar sannan ta bude wani kofar da ta gani daga can
end, xaro ido tayi ganin view din, karamin balcony ne, ta dinga bin gidan da kallo daga kasa wanda ke
shimfide da carpet grass ga wasu flowers a gefe, sosai wajen ya mata kyau ba kadan ba, ta kalli wani
babban gidan dake opposite dinta suka yi ido hudu da wani dake xaune shi ma a balcony, laptop ne
gabansa da drink, shi dai kallonta kawai yake, ta Sunkuyar da kanta da sauri ta juya ta koma ciki ta kulle
kofar, da sauri da sauri ta koma dakinta. Daren ranan bayan isha Abuturrab na Abuja a gidansa sbda
weather bai bari sun koma kano ba, Aneesah ce xaune kusa da shi a dakinsa, yace "Kince kina da lectures
da safe, why not sleep now?" Ta hade rai tace "Toh ae it's not a crime idan nayi bouncing lectures din ko?"
Ya gyada mata kai yace "Haka ne...." Lamo tayi ta lumshe ido kusa da shi, ya ci gaba da abinda yake, bayan
few minutes ta bude ido tana kallonsa tace "In tambayeka mana captain" Yace "Ina jin ki" tace "This days
kamar u are not longer eager being with me, why?" ya buda ido sosai yace "Why do u say so?" Ta
marairaice tace "Haka naga alama, or do u have anything in mind?" Murmushi yyi yace "Yaushe rabon mu
hadu? It's almost 10 days now" ya ja hancinta yace "And ke kin fiye ma mutum jan aji ne" Rungumesa tayi
cike da shagwaba tace "Wallahi ba haka bane, ae kai din ne sai ka xo Abuja kake neman mutum" ya cire
hulan kanta yace "Ohh really??" Dariya tayi tace "Aa wasa nake my captain ni kadai...." yyi murmushi yace
"In few days time su Abbanmu xa su je gidanku in sha Allah" ta wara ido tace "Da gaske my captain?" Yace
"In sha Allah" Rungumesa tayi tace "I can't wait Babynah" ya d'an hade rai yace "Baby kuma?" Dariya tayi
sosai tace "Au.. to yi hakuri na manta baka son sunan, amma fa kada wataran ka xo kayi ta rokana in kiraka
da Baby" yace "Sai kace wani jariri" Dariya kawai take tana kallonsa don tun ba yau ba tasan bai son irin
wannan soyayyan da yawanci yake kiransa da na yarinta, ta daura kanta saman shoulder dinsa tana jin
wani sabon sonsa na fixagarta... Karfe daya saura few minutes Abuturrab ya fito bedroom dinsa bayan yayi
wanka ya shirya cikin jallabiya, xaunawa yyi parlor yyi dialing number ya kai kunne, sae da ya katse ba a
dauka ba sannan ya kalli agogo, ajiye wayar yyi ya kwanta saman doguwar kujera ya lumshe ido...
Throughout week din nan Jiddah bata ji kadaici sosai ba don ranan laraba ma sai da Maimoon ta xo gidan,
A ranan kuma Abuturrab yyi niyyar dawowa amma cikin ikon Allah sai bai samu dawowan ba, ranan
alhamis Maimoon ta kara xuwa tare da