Showing 315001 words to 318000 words out of 321711 words

Chapter 106 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt

dankali tana bi layi layi da shi a kai tana siyarwa, shine fa jikana matukin jirgin
sama ya ganta cikin mugun yanayi yaji tausayinta ya rabota da wnn anguwa ana kiransa da hayi, in dai
kunsan kaduna xa ku san hayi, kuma duk wanda ya ji hayi ya san sauran, to a can dai jikina Aliyu ya aurota
ya kawota cikinmu, babu abinda muka ragata da shi yau shekaranta biyu kenan tare da mu, kanwar uwarsa
ce uwarta da ubanta matar ta rike ta da amana ko er ta sai haka, don isa da gadara kawai take xubawa a
kanta tayi ta nuna ta fi kowa sonta" Duk aka dinga kallon Hajja a parlon, Hajiya Dada ta girgixa kai tace
"Allah ubangiji yayi maku abinda ku ka mana Hajiya, Ina matar uban nata?" Hajja tace "Wa?? Tana can
duniya ta juya mata baya aka ce, idan xa ku ji shawarata ku fita harkarta kawai, don wllh ina da yakinin har
da bala'inta ya kashe isuhun naki, duk ita ce ta fitinesa, to me xa ayi da ita kuma?" Hajiya Dada tana
hawaye tace "A dai a kawo min ita ko a kai ni inda take Hajiya, duk wani abu da ya shafi Yusif ba abinda
xanyi banxa da shi bane" Hajja tace "Atoh, amma dai Jiddah kam yau shekaranta biyu rabonta da matar
uban gaskiya" Hajiya Dada tace "Allah ya saka maku da alkhairi Hajiya, Allah ya saka, Allah ya saka, yau na
daya daga ranakun farin cikina a rayuwa, Allah ya rubuta baxan bar duniya ba tare da na ga jinin yusif ba,
har in koma ga mahaliccina ni da yarana baxa mu mance da wannan halaccin naku ba, Allah ya saka maku
da alkhairi Hajiya" Hajja ta dinga wani murmushi tace "Ameen Ameen" Hajiya Zuwaira fourth born din
Hajiya Dada ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "Toh dangin mahaifiyarta fa?" Hajja ta gwalo ido tace "Ke
kin ta6a ganin wanda ba a san asalinsa ba a dau yarinya me asali a basa? To wllh abinda ya faru kenan, ita
kanta uwar Jiddan a yanda shi isuhun yake ita ma a haka take, wato dai ba a san asalinta ba, mu ai aiki biyu
ne a gabanmu, yanxu munyi daya saura daya, duk inda dangin uwarta suke su ma sai mun nemo su, ko
kuma mu bar ku da wahalan ku mu, ai munyi kokari haka" Alhaji Sulaiman yace "Haka ne Mama, wnn kam
aikin mu ne in sha Allah duk inda yan uwan mahaifiyarta suke xa mu yi bakin kokarinmu na ganin mun
nemo su, da izinin Allah kuwa" Hajja tace "Ina sha Allahu, shine kadai gatan da xa ku yi mata don duk
wanda xaku mata ba birgeta xakuyi ba tunda ta samu a wajenmu da wajen jikana Aliyu" cikin sanyi Hajiya
Dada tace "Toh shi jikan nawa baxai xo in sa mashi albarka wannan namijin kokari da yayi haka ba" Hajja
tace "Huhuhu.... Namijin kokari kuwa, kaff Najeriya babu matukin jirgi bahaushe sai shi, hatta turawa ji
suke da shi wllh don ya iya sarfa jirgi, a lkcn da ya auro Jiddah fa wllh ko da kudi aka hadaka da ita baxaka
amsheta ba, talaka ma wllh da kyar xai amince ya aureta, wahala tayi wahala, ba arabi ba boko sai talla,
fatar nan nata yayi wani dukun dukun malam, kai!!! wllh Aliyu yayi kokarin da ba kowa xai yi ba, amma
sbda xuciyarsa irin tawa ce wllh haka ana masa dariya ana xolayarsa ya rufe ido ya aurota ya kawo mana
gida, ranan da ya kawota kuwa duk sai da muka girgixa muka fita hayyacinmu, biyar baxaka siyi Jiddah ba
wllh wllh, ko da yake dai duk ina Masar aka yi hakan" Hajiya Fatima dai sai murmushi take tana kallon
Hajja, Hajiya Dada kuwa ta makalkale Jiddah kamar xa a rabata da ita.
*Wannan littafi dai ya ki karewa bayan nagaji da shi shima ya gaji dani☹️
ko da yake nasan me xanyi* 😁


_4 years later_..... 🫣



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp



Parking Aunty Rahama tayi a kofar gidan Abba, Hajja dake bayan motar tana washe baki tace "Allah ya
maki albarka, in sha Allahu nan da kwana biyu xan dawo anguwan naku gaba daya kin ji?" Aunty Rahama
na murmushi tace "Toh Allah ya kawo ki lafiya kaka" Jiddah dake gaban mota tace "Mun gode Aunty"
Aunty Rahama na mata murmushi tace "In kun shiga ki gaida su mama kin ji" Hajja tace "Au ni da nake
xaton xaki shigo ku gaisa" Aunty Rahama tace "Aiki xan tafi kaka, na makara wllh" Hajja tace "Aa kin
makara gaskiya gashi har tara saura, to ke mijin naki ba a kasan yake bane?" Tayi murmushi tace "Allah ya
mashi rasuwa kaka" Hajja ta saki wani salati tayi tagumi cike da damuwa tace "Allah sarki, Allah ubangiji ya
gafarta masa, to baki da 'ya ya da shi ne?" Tace "Ina da, su biyu ne, suna gun yayansa a Abuja, sai hutu ake
kawo min su" da sauri Hajja tace "Aa ki amshe yaranki, ce masu kika yi baxa ki iya kula da su ba ko salon
kar yaran su ji kanki su san ciwonki" Ita dai murmushi kawai take, Hajja tace "Wllh amshe abin ki, ni ban
yarda da rikon d'a ba..." Daga haka ta bude motar ta sauka, Jiddah ma ta sauka tana kara yi ma Aunty
Rahama sallama suka shiga gidan da Hajja, tun daga parlor Hajja ke kwala ma Ummi kira, Ummi na fitowa
tace "Toh dai Jiddah ba yar matsiyata bace, kuma kakarta na nan da ranta sai kin ga abun arzikin da aka
mana a wannan gari na gombe, mutanen kirki mutanen arxiki suka cika garin, sun karrama mu sun daraja
mu sun mutunta ba, wllh basu so mu taho ba amma wannan yayan baban nata Alhaji Sani naji ana ce
masa ko wa? Wannan dai da ya mana jagora xuwa garin shi ya axalxala mu taho, in don ta nine da bamu
dawo ba wllh, jiya da daddare muka dawo to yau naga wnn yarinya Jiddah sai wani nukurci take taki kulani
nace to ko kewan mijinta take shine dai nace su maido mu gida da safe, amma wllh dangin ubanta en arxiki
ne babu talaka ko kwaya daya a cikinsu, ke kin ga gidan ma kuwa, wllh yayi biyar din wannan, kuma kinsan
gidan waye, gidan uwarsu ne, su suka gina mata gwanin ban sha'awa, ai ita kam ta more rayuwa wllh...."
Ummi tace "Toh Alhmdlh, nayi murna sosai, Allah ya bayyana dangin mahaifiyarta haka" Hajja tace "Allah
gidan yayi ukun wannan kuma tsohuwar kadai ke rayuwa a ciki, duka duka fa bai fi ta girmeni da shekara
uku ko hudu ba, amma sai kin ga abinda yaranta suka kera mata, tana xaxxaune ta mike kafa sai dai ayi
mata komai" Ummi ta amsa gaisuwar Jiddah da ta duka kasa ta gaisheta, Ummi tace "Ya hanya, fatan kun
dawo lfya, ya kuma ku ka bar mutanen can din" Hajja ta amshe tace "Alhmdlh, babu abinda basu mana ba,
yanxun ma fitowa muka yi ba shiri ita kuma warce ta kawo mu tana ta sauri xata aiki, banda haka in gaya
maki ai tsarabanmu da yanxu haka ba a gama shigowa da su ba, to sunce anjima da yamma xa a taho
mana da shi, ke dai ki bari kawai Hauwa, karramawa da mutunci na inda yake, ni kam bani da abinda xance
ma mutanen nan" Daga haka ta wuce dakinta, Ummi da ta bi ta da kallo tace "A kawo maki kumallo Hajja"
Hajja tace "Meye kuma kumallo? Aa mu mun yi lafiyayyen kari, kawai a bani makullin d'an kuturun dakina"
Ummi ta tafi dauko mata makullinta ta kai mata, ta bude ta shige ciki tana kyabe baki, Ummi ta dawo
parlor ta xauna tana kallon Jiddah tana murmushi tace "Kin je kin ga kaka da kawunnanki ko?" Murmushi
Jiddah tayi ta gyada mata kai, Ummi tace "Toh Alhmdlh, Alhmdlh, i am so happy for you daughter" Jiddah
dai ta sunkuyar da kanta kawai, Tashi Ummi tayi ta tafi parlon Abba, Jiddah ta dinga kallon hanyar dakin
Abuturrab amma ta kasa tashi, ta fi minti biyar sai ta kalli dakin sai ta dauke kai, can dai ta mike a hankali
ta nufi dakin kamar munafuka muryan Ummi taji tace "Ai bai nan ya koma aiki Jiddah" kunya ta ji kamar ta
nutse, ta kasa juyowa ta kalli Ummi, jin shiru sai kuma ta juyo a hankali, gani tayi Ummi bata ma wajen, da
sauri ta wuce dakin Hajja. Washegari da safe Jiddah na dakin Hajja, Hajja na cewa "Kin ga ai ni bana kai
kaina inda Allah bai kaini ba kuma bana takura ma yarana ince sai sun min abu dole, da wata ce yanxu duk
sai ta kwarzabi yaranta tace sai fa an mata gini irin na wannan kakar taki, amma ni kam Allah ya kiyaye inyi
haka sai kace wata er banxa, ni ko burgeni gidan bai yi ba balle inji sha'awa ince a min irinsa" Jiddah dai
kallonta kawai take amma bata ma san me take cewa ba, kewan Abuturrab kawai take, ji take kamar ta fi
wata daya rabon da ta gansa, she's a kind of sad, gaba daya ta ji gidan ya isheta, gashi bata san sanda xai
dawo ba, ga surutun Hajja dake sa mata ciwon kai, tayi mata xancen gidan Dada ya fi sau ashirin daga jiya
xuwa yau, har Umma da ta xo jiya ta bata labari, Hajja ta ta6e baki tace "Ba ruwana da sa ma wani ido
wllh, nagode Allah da inda ya ajiyeni, shege ne kawai xai dinga hangen abun wasu" Bude kofar dakin aka yi
Ummi ta shigo tayi ma Hajja sannu, tana kallon, Jiddah tace "Ur husband said he will be back in the
evening of today, so get ready after Zuhur, i will instruct the driver to drop u home" Tace "Toh Ummi"
Juyawa Ummi tayi ta fita, Hajja ta ta6e baki tace "To ko matansa ma basa hanasa ya min kantamemen gini
ba don bakin ciki, ai kai dai kawai ka haifar ma mace yaro kawai, bayan haka baka da sauran martaba a
wajensa" Tun da Ummi ta fita Jiddah ke counting agogo sai taga baya sauri, wai karfe goma da rabi, har
bacci tayi ta tashi wai karfe sha daya, kawai daga karshe ta mike ta fita daga dakin Hajja ta tafi part din
Ummi... Ummi ta ajiye littafin hannunta tana kallonta tace "Ya aka yi Jiddah?" Kunya taji ya rufeta, Ummi
tace "Ko har kin shirya?" Tayi karfin halin cewa "Ehh Ummi ina son xanje inyi girki ne" Ummi tace "Eh
gaskiya kam, bari in kira driver din, shiga ki dauko jakarki to" Kanta a kasa ta shiga dakin Ummi ta dau
jakarta ta fito dama da Hijab dinta a jikinta, bayan Ummi ta kira driver ta mike ta tafi daki ta dauko mata
makullin gidan nasu, tana mika mata tace "ki je ki ma Hajja sallama kice mata xaki gidan Umma ne" Jiddah
tace "Toh" Ummi tace "Idan kin mata sallaman ki samu driver din yana waje" Jiddah tace "Ummi ina son in
siya wasu abu a kasuwa ne..." Ummi tace "Kina da kudi wajen ki ne?" Girgixa mata kai tayi, Ummi tace
"Toh bari in baki Atm card, idan ya dawo sai ya maido min da card din nawa" Atm card din ta dauko ta mika
ma Jiddah ta gaya mata pin din tana kara nanata mata kar ta manta, Jiddah ta risina ta amsa tayi mata
godiya ta fita, kallonta Hajja ta dinga yi sai kuma tace "Me ake yi a gidan Umman?" Jiddah tace "Kawai xan
je ne" Hajja tace "Toh sai mijin naki ya dawo xamu koma can gidan kin dai ji abinda nace ma dangin ubanki
kar su daukeni makaryaciya idan basu gan ni ba" Jiddah tace "Ehh sai ya dawo" Hajja tace "Toh ki gaida
Ramlan" Jiddah ta juya ta fita, sai da driver ya fara ajiyeta kasuwa ta siya ingredients din fried rice da zobo
drink, tunda suna da nama a deep freezer bata siyi komai ba banda liver, daga nan driver ya ajiyeta gida
tayi masa godiya ta shiga ciki bayan ta gaida mai gadi. Tana shiga cikin gidan ta kai kayan girkin kitchen ta
tafi sama ta canxa kaya xuwa kanana sannan ta fara gyaran gidan, ta tsaftace ko ina tayi mopping da goge
goge ta kunna turare a burner, sai da tayi azahar sannan ta shiga kitchen.... Kafin la'asar ta gama hada
lafiyayyen fried rice dinta with zobo drink, ta soya kajin tayi pepper chicken da shi, sai farfesun offals da
tayi kadan, duk ta jera abincin a dinning, ta koma ta tsaftace kitchen din kamar bata yi komai a ciki ba ya
dawo fes fes, sama ta wuce dakinta ta shiga wanka, da alwalanta ta fito sai da tayi salla snn ta fiddo da
kayan da xata sa, ta dau kusan minti talatin tana shirya, ta saka wasu ubansun English wears masu daukan
hankali, ko ina na jikinta wani sanyayyan kamshi ne ke tashi, tayi packing gashinta da ribbon leaving it that
way, she look just like a princess, tayi kyau sosai, bude gate taji anyi ta karasa window tana kallon waje
yaga Abuturrab ne ya shigo da motarsa... Sauka tayi downstairs ta tafi bakin kofa ta tsaya, she is just so
happy, ta labe a gefe daya har ya bude kofar, wani kara tayi da nufin basa tsoro, ya jawota jikinsa yana
kallonta daga sama har kasa yana murmushi, 6ata fuska tayi yayi kasa da murya yace "Jirgi bai bani tsoro
ba sai matata?" Dariya tayi ta boye fuskarta jikinsa a hankali tace "Welcome my Man" Ya lumshe ido ya
bude yana shafa bayanta yana kare ma dressing dinta kallo yace "U look sexy in this wife..." Sai kuma ya
kankameta yace "Wllh i have missed u so much wife, Hajja bata kyauta min" amsar jakan hannunsa tayi
tana murmushi tace "I missed u more dear... Abinci ko wanka?" Ya girgixa kai yace "Sallah" Tace "Toh mu
je" Sai da yayi sallah sannan yayi wanka bayan ta hada masa ruwan wankan a bedroom dinsa, kafin ya fito
ta ciro masa kayan da xai sa, sannan ta sauka downstairs ta dauko girkin da tayi xuwa parlonsa, xata shiga
bedroom bayan ta gama hayowa da abincin suka kusa cin karo, sai taga ko kayan da ta ciro masa ma bai sa
ba sai short, daukanta yayi kamar baby xuwa bed din dakin, ta marairaice masa tace "Dear ga fa abinci
can..." Bai bata daman ta karasa ba, ya dinga ce mata yayi missing dinta so much, kamar yanda ya tara
mata gajiya ita ma dai hakan tayi masa, bai ta6a tunanin da akwai sanda jiddah xata sake haka da shi ba
balle har ta maida masa martani.... Sai bayan ya dawo magrib ta xuba masa abincin da ta girka masa, yana
kallonta ta gefen ido yace "Ke dai fadi gaskiya Baby wannan abincin daga gidan Ummi kika taho da shi ko?"
Murmushi tayi tace "Ae wannan ma da na ta6a xuba ma Colleagues dinka da dadewa ka kusa cinyewa baka
sani ba... Shi ma ai daga gidan Ummi...." jawota yayi jikinsa ya matseta ya buda idonsa yace "Ni xa ki ma
sharri?" Dariya tayi tace "Kai ka fara min sharri ai" ya lumshe ido yana murmushi yana shafa dogon
gashinta yace "U are really a good cook wife, i know i am blessed... tun daga wannan ranan da kika xuba
ma Colleagues dina abinci na dandana na san haka, i was stunned after tasting ur food that day, how
possible i thought to my self many times" Tana murmushi tace "Saboda i am too local then ko?" Ya dago
kanta yace "Daga sanda na raba ki da hayi kika bar locality dinki a can, u left that locality behind... Ban ta6a
tunanin xaki fahimci abubuwa ki koyi abubuwa lkci daya ba jiddah, u were a fast learner... A iya xamanmu
na farko I can't say ko na ta6a maki wani correction kan abubuwan da na koya maki" Ita dai murmushi
kawai take, yayi kasa da murya yace "Tun daga sannan kika fara burgeni, when i notice u were always
clean" Ta d'an saci kallonsa tace "Ashe ina burgeka" He couldn't help it but laugh, sai kuma ya rike kansa
yace "Sosai Jiddah, in dai na barki a gida na tafi aiki bani da sukuni up in the sky sai na dawo gidan nan, i
hate seeing u sad or worried hakan na karyar min da xuciya..." Ta kwantar da kanta kan shoulder dinsa
tace "Kawai dai so na ne baka yi a lkcn ko??" Jin yayi shiru ta daga kai ta kallesa, kallonta taga yana yi babu
ko kiftawa, sai kuma ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace "Na kan yi sha'awanki a lkcn" Ta d'an
buda ido tana kallonsa tace "Wani iri" Ya lumshe ido yana shafa laps dinta yace "Irin wannan but i always
try hard to fight it away, i always put in the back of my mind that i am just ur guardian" ita dai Murmushi
kawai take, ganin ya ki daina abinda ya ke mata a kafa ta turo baki tana kallonsa, tuni taga idanuwansa
suka canxa, ta marairaice tace "Ni wllh na gaji ko abincin fa ban ci ba..." Wannan fried rice din dai sai wajen
karfe sha daya na dare aka ci sa, Abuturrab ne ya fara tafiya sama bayan ya wanke baki ya kwanta cause he
is so very exhausted, ta gama wanke duk abubuwan da suka 6ata, ta sa turaren wuta ta jira yayi a parlon
sannan ta kashe komai ta wuce sama, bedroom dinta ta tafi ta sake wanka ta wanke baki sannan ta saka
kayan baccinta ta kashe wutan dakin ta kwanta, nan da nan bacci ya dauketa, can wajen karfe biyu
Abuturrab ya koma dakinta ya kwanta because he can't resist sleeping without her close to him... Haka
rayuwarsu ya ci gaba da gudana cike da so da kaunan kamar su maida junansu ciki, in dai yana gari bata da
sauran sukuni har ma ta sa6a da kwarzabanta da yake, ya kuma yi programming dinta a yanda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login