Showing 78001 words to 81000 words out of 321711 words
it from her" Mikewa El-Basheer yyi ya dau makullin motar Abuturrab yace "Ni kace min bata
sani bane, ga ta nan tana ta kira, pick and find what to say to her" daga haka ya nufi kofa ya fita, Abuturrab
ya bi sa da kallo xuciyarsa na tafarfasa. Daukar wayarsa yyi yaga calls din Aneesah har biyar yayi silencing
wayar ya bi bayan El-Basheer.... Bangaren Aunty suka fara shiga suka gaisheta bayan sun isa gidan, Aunty
na kallon El-Basheer tace "Har ka iya xuwa wai gidansa El-Basheer, ni fa na tattare lamarin Abuturrab na
watsar a gefe, i see no reason da xai dinga boye boyen cewar ya saki yarinyar nan, ko meye fa'idan xama
gida daya da ita bayan ya saketa, who is he deceiving?? To wllh I've made up my mind cewar Abbansa na
dawowa sati me xuwa xan sanar masa komai, wannan ae iskanci ne, to ko minti biyar ba ayi da muka gama
waya da mahaifiyar Aneesah ba, labari ya je masu, kana tunanin xaka iya ci gaba da boye masu ne dama??
Wllh yanxu haka duk hankalina a tashe yake, nayi kokarin fahimtar da su ba auren amma ya faskara...."
Kallonta kawai Abuturrab yake yi, shi na Aneesan ma bai damesa ba kamar na Abba da tace xata sanar ma
ya saki Jiddah kuma yana xaune tare da ita, gaba daya yaji hankalinsa yyi mugun tashi, Waje ya nema ya
xauna jin har kansa ya fara juya masa, El-Basheer yace "Ni banga abun boye boye a nan ba, let this be
known to everyone that she is no longer ur wife, kana xaune gida daya da macen da ba muharramarka ba,
who does that??" Abuturrab ya kalli Aunty da ta ci gaba da abinda take bbu fara'a fuskarta, yyi kasa da
murya yace "Amma Aunty kinsan Abba won't be happy idan yaji na saketa, he will be highly disappointed
at me, kuma ni sbda bana son bacin ranki ya sa na saketa wllh, idan kika gaya ma Abba cewar nayi hakan
yanxu he won't take it likely with me, i am just confuse Aunty" Aunty ta juyo a fusace tace "Ni kuma dole in
sanar masa duk abinda xae faru ya faru ba, are u this happy being with the girl da yasa ka daina dawowa
weekend gidan nan sae dai ka sauka gidanka ka karashi weekend dinka ka wuce, haka xaman naka da ita
yayi dadi duk da ba matarka bace ashe?? To kuwa xaka sha mamakina kuwa wllh" Ya girgixa kai yace
"Aunty ni weekend din ma gaba daya na daina dawowa fa, Jiya ne kawai na dawo sbda El-Basheer yace
min yana hanya" Aunty tace "Wato ita kadae ke yanda ta so a katon gidan? Ka sakar mata babban gida
haka ta ci karenta ba babbaka, to baxai yiwu ba ne wllh" Shiru yyi bai ce komai ba, Aunty tace "Don kuwa
da ta ci gaba da xaman gidan nan naka gwara ka dawo da ita nan, dama mai aiki xata tafi garinsu jibi, kaga
ba wani xai ce ta bar nan gidan ba wataran..." Kallonta kawai Abuturrab ke yi gabansa na bugawa, tayi
masa tsawa tace "Kallon ne amsan ka? Ko baxa kayi abinda nace bane??" Ya girgixa kai yace "Aunty can din
ma ina assuring dinki ba sae wani yace ta tafi ba xata tafi, wllh ita kadai ce bbu kowa" Aunty ta kara masa
wani tsawa tace "Nace ka dawo da ita gidan nan, ko ban isa ba??" Ya sunkuyar da kansa lkci daya jikinsa yyi
sanyi, can ya kalleta cikin sanyi yace "Toh" Sannan ya mike ya nufi kofa ta bi sa da harara tana huci, El-
Basheer ya d'an yi murmushi yace "But how can a normal human being do what Abuturrab did?" Cike da
bacin rai Aunty tace "Atoh... Isn't this irritating Bash?? Wllh da lamarin nan nake kwana nake tashi a raina,
ya ce ya saketa quite alright he did that, na sani, to kuma xaman me suke tare idan anyi magana yace
Abbansa, ance masa da Abban nasa ya san ya saketa xae barsa ya ci gaba da xama gida daya da ita, ga
yarinyar ido a bude, to xaman iskanci yake son fara yi da ita ko me, don dai shi ma ba saiti garesa ba kuma
ba jin magana yake ba, ka sani, na sani, shi yasa bai dauki xaman da yake under same roof with her wani
abu ba" El-Basheer ya mike yace "Allah ya kyauta" daga haka ya fita. Ko bangaren Ummi Abuturrab bai
shiga ba ya fice daga gidan ya shiga motarsa ya jinginar da kansa da kujera yana jiran El-Basheer, dalilin da
yasa bai son xuwa gidan kenan idan ya dawo weekend, ganin har bayan minti sha biyar El-Basheer bai fito
ba Abuturrab yyi dialing numbersa, El-Basheer na dagawa, a fusace yace "Inyi tafiyata ne?" El-Basheer yyi
murmushi ya katse wayar, kallon wayar Abuturrab ya dinga yi, sai ga text ya shigo masa, bude content din
yyi, "C'mon wani irin gaisuwa kake son inyi ma Ummi, gaisuwan minti goma? Tunda kai kaki shigowa
gaisheta ni baxan iya ba" Abuturrab ya mayar masa reply yace "Ka sameni a gida then" daga haka ya ajiye
wayar ya tada motarsa ya bar anguwar. Yana parking ya shiga parlor ya xauna kujera ya jinginar da kansa ya
lumshe ido yana jin ransa ba dadi, text ne ya shigo wayarsa ya bude ido a hankali ganin Aneesah ce tayi
text din ya bude content din, "Abinda ka min was the least i expected from you Aliyu, ban yi xaton haka ko
a mafarki ba, amma ka sani ka cuceni, ka ci amanata, ka yaudareni, ka ruguza min rayuwa, i gave u all my
trust but u ended up betraying me, why Aliyu, did i deserve this harsh treatment from you?" Ko gama
karanta text din bai yi ba yayi mata reply kamar haka "Since you never expect this from me... Then u
consider me... Aure kuma sai idan kece kika ce baxa kiyi da ni ba, as for me you will be my first and last
wife in sha Allah.... i will call u in 5 hours time in sha Allah" daga haka ya tura mata text din ya ajiye wayar
ya mike ya wuce sama. Har bayan Magrib El-Basheer bai shigo gidan ba, hakan ya sa Abuturrab yyi dialing
number sa, yana fara ring El-Basheer ya daga yace "Gobe xan shigo before leaving, Ummi tace i should
spend the night here" Abuturrab yace "Ohk" daga haka ya katse wayar. Mikewa yyi ya wuce sama ya bude
kofar dakin Jiddah, tun da ya dawo ko motsinta bai ji ba, tana xaune gaban mirror tana ma gashinta kitson
kalaba, ganinsa ta dau hulanta ta saka, yana tsaye bakin kofa yace "Meye hakan kike yi?" Tace "Aa ina
kitson gashin ne, yana karyewa idan ban yi kitso ba" Yace "Sai anyi kitson ne baxai karye ba?" Ta gyada
masa kai, yace "Toh kwance wannan abinda kika yi, tunda a garinku ne aka ce maki xai karye idan ba ayi
kitso ba, a tsefe xaki bar gashin, haka nake so" Ta kallesa da sauri, that was when he realized what he just
said, lkci daya ya hade rai yace "Ko kina ganin kitso a gashin su Ramlah, mu a nan ba a kitso" Cikin sanyin
murya tace "Toh" ta fara tsife dogon gashin nata da ta kitsa, har ta gama tsefe daya bata ji ya tafi ba, hakan
yasa ta leko sa ta cikin gashinta da ya rufe mata fuskarta gaba daya, suna hada ido ya juya ya fita dakin.
Ana kiran isha ta gama parking din dogon gashin nata ta kitse jelan sannan ta sa hularta. Karfe tara saura
wayar da Abuturrab ya bata ya fara ring a gaban madubi, karasawa tayi ta dauka tana kallon number jikin
screen din sannan tayi picking ta kai kunne, muryarsa taji yace "Ina jiranki a parlor" Daga haka ya katse
wayar, ajiye wayar tayi ta sa Hijab dinta ta fita, shi kadae ne xaune parlon ta durkusa jikin kujera a hankali
tace "Gani" Yace "Me kika ci?" Ta sunkuyar da kanta tace "Taliya na dafa" ya nuna mata ledan dake gefensa
yace "dauka" mikewa tayi ta isa kusa da shi ta duka ta dau ledan, ya rike numfashinsa sbda wani kamshi na
daban da ya doki hancinsa, ganin kwalin lemo a cikin ledan ta cire xata ajiye, ya saki breath dinsa ya hade
rai yace "Har da shi xa ki tafi" Innocently tace "Ban iya sha ba" Yace "Haka xa ki je ki koyi sha yau, tunda ke
yar kauye ce" Bata ce komai ba ta mayar da kwalin cikin ledan sannan ta mike ta nufi stairs, bin ta yyi da
kallo tana isa stairs ta juyo suka hada ido, da sauri ya dauke idonsa, tace "Nagode" sannan ta wuce sama,
jinginar da kansa yayi a hankali da kujera yana jin damuwa iri iri a ransa, gasasshiyar kaza ce da yaji Jiddah
ta bude a dakinta, sai kamshi kazan yake, ta kalli kwalin hollandia din sannan ta bude ta d'an sha kadan, ji
tayi yayi mata dadi a baki sbda gardinsa, ta lumshe ido ta kara sha sannan ta ajiye ta fara cin naman a
hankali, lkci daya rayuwar da tayi a gidansu ya fado mata, tura kazan tayi tuna Babarsu da tayi.
Abuturrab na kwance wajajen sha daya a parlor, waya na kare kunnensa, he felt relieved bayan yayi
convincing Aneesah a kan kaddara ce ya sa shi auren jiddah sannan kuma bashi da aurenta a kansa yanxu,
daga daya bangaren cikin sanyin murya tace "Amma why is she still at ur resident My captain??" Yace "Ina
kike son in kai ta yanxu?" Tace "Ni ko gidanmu ma ka kawota su Mummy baxa su ce Aa ba wllh, ni nasan
karyar da xan masu, ka barta ta dawo gidanmu plss" Bai san lkcn da yyi wani murmushi ba, a hankali yace
"Koh?" Ta marairaice tace "Sure dear" yace "I will think about that, xuwa nan da short period of time" tace
"Do so fast plss Captain" daga kai yyi jin footstep a stairs, lkci daya yace "I call you in some minutes time"
bai jira cewarta ba ya katse wayar, yayi kasa da idonsa kamar me bacci, A hankali Jiddah ke tafiya duk
xatonta bacci yake hannunta rike da ledan kazan da ko yanka uku bata ci ba, to bata saba da shi ba shi yasa
bata iya ci sosai ba, drink din ne ma ta d'an sha ba laifi, kitchen ta tafi ta ajiye ledan kazan a fridge ta ajiye
lemon ma sannan ta fito, a hankali take tafiyar ta nufi stairs ya bi ta da kallo, nighty ne jikinta wanda ya
wuce kneels dinta da hularta a kanta, sai da ta isa stairs ta juyo ta kallesa suka hada ido, sosai ta tsorata,
yyi saurin mikewa xaune pretending to be awake at that moment yace "Me kike yi a nan" ta nuna masa
kitchen tace "Na kai abu na ajiye" yace "Je ki dauko abinda kika ajiye" Tayi narai narai da ido ta ki motsawa
daga inda take, ya hade rai yace "Baki ji abinda nace ba?" Da gudu ta wuce sama, ya mike tsaye da mamaki
yana bin ta da kallo, har ta shige dakinta.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last
bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd
getting rid of any skin problems
Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta
samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar
rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata
masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda
zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada
Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240
Washegari da safe Abuturrab ya sauko downstairs wajajen karfe takwas, jin motsi a kitchen ya fasa shiga
kitchen din ya xauna parlor, bayan kusan minti ashirin Jiddah ta fito, tana ganinsa ta yi kasa da kanta kamar
munafuka, ta nufi jikin kujera ta durkusa, a hankali tace "Ina kwana?" hararanta yake, taki yarda ta hada
ido da shi ta mike tayi wucewarta sama, sae a sannan ya tashi ya wuce kitchen din, wanke wanke ya ga tayi
ta goge ko ina na kitchen din, fridge ya bude ya dau apple uku ya dau karamin plate ya daura a kai sannan
ya fita ya koma ya xauna yana cin apple din yana danna wayar sa, danna bell aka yi, ya kalli kofar da
mamaki, can ya mike ya nufi kofar ya bude, ido hudu yayi da Aunty a tsaye ta hade girar sama da ta kasa,
gabansa ya fadi sosai, ya kalli El-Basheer da ya xauna saman kujeran dake balcony din ya daura kafa daya
kan daya, bangajesa Aunty tayi ta shiga parlon, ya bi ta da ido sannan ya kalli El-Basheer fuska daure,
mikewa El-Basheer yyi yace "She only said in rakata anguwa, and i never knew nan xata xo" Wani kallo
Abuturrab yyi masa ya juya ya koma cikin parlon, tsaye ya tadda Aunty fuskar nan nata babu alamar wasa,
yyi kasa da kai da ladabi yace "Ina kwana Aunty?" tace "Ban kwana ba Aliyu, ina yarinyar take?" Yyi kasa da
murya yace "Aunty dama ai anjima kika ce in kai ta can gidan ko" Cikin tsawa tace "Ta fito yanxu mu wuce,
na hutassheka ba sai ka kai ta ba" a hankali yace "Toh" Daga haka ya fara wucewa sama, ta bi sa da harara
tana girgixa kafa, sai da ya haura sama ya d'an juyo ya kalleta ganin bata ganinsa, ya nufi dakin Jiddah da
sauri, Tana gyaran gado ya shigo, ta mike tana kallonsa, ya hade rai yace "Mu je" Tana kallonsa tace "Ina?"
Fixgo hannunta yyi ta xaro ido tana kallonsa har suka fita dakin, ganin bangarensa ya nufa taki ci gaba da
tafiyar tace "Me xanyi..." wani kallo ya jefa mata, hakan yasa ta ci gaba da tafiyar, parlonsa ya kai ta, ya
bude kofar balcony yana kallonta yace "Shiga" da mamaki tace "Saboda me" shigar da ita balcony din yyi
yana kallonta da kyau yace "Idan kuma so kike Auntyna ta tafi dake sai ki 6ara baki kiyi kuka har ta ji ki"
Daga haka ya kulle kofar, ya sa makullin a aljihunsa, ya fita parlon a stairs ya hadu da Aunty, tace "Ta kasa
sakkowa ne har yanxu xaka shanya ni a parlor" With confusion yace "Aunty I don't know, na duba dakin da
take ban ganta ba, amma jiya Maimoon ta xo, ban san ko...." Wani tsawa tayi masa tace "Ni xaka raina ma
wayo Aliyu?? Xuwa kayi ka boyeta?" Ya marairaice yace "Boyeta kuma Aunty, a ina xan boyeta ki shiga duk
inda xaki shiga ki duba, ni fa jiya sai kusan sha biyu na dawo gidan nan, i don't know ko sun tafi tare da
Maimoon, and tunda gari ya waye ban fito ba sai ynxu da ku ka xo" Bangajesa tayi ta nufi saman, dakin
Jiddah ta fara budewa, hankalinta yyi mugun tashi ganin dakin kamar na amarya ga gaban mirror taff da
kaya masu tsada, ta bude press, nan ma taga uban kaya, shi dai yana tsaye yana kallonta, ta juya tana
kallonsa... Da sauri yace "Ko biyar dina babu a nan Aunty, Umma ce da Abba da uncles dina duk suka yi
wannan siyayyan, ki tambayi Ummi ma" har bathroom sai da ta bude bata ga Jiddah ba, Juyawa tayi ta fita
ta shiga sauran dakunan nan ma bata ga alamarta ba, fita tayi ta tafi bangarensa, iya dubanta bata ga
Jiddah ba, kofar Balcony din ta murda, Abuturrab dake tsaye bakin kofa duk yana kallonta, yyi kasa da
murya yace "I can't find the key to that place, balcony ne ai kin sani" Da ido ya bi ta har ta fita parlonsa,
snn ya bi bayanta, Jiddah dai na tsaye balcony din, lkci lkci take satan kallon mutumin dake xaune a daya
building din, da ta saci kallonsa kuma sai su hada ido, daga karshe ta canxa position dinta, sai bayan minti
talatin Aunty ta bar gidan bayan ta ta66atar da gaske Jiddah bata nan, don ta duba ko ina, Ba tare ta koma
da El-Basheer ba bayan ta amshi makullin mota tayi wucewarta, Ko kallon El-Basheer Abuturrab bai yi ba
ya shige parlor, mikewa El-Basheer yyi ya bi bayansa, Abuturrab ya xauna saman kujera, El-Basheer ya
xauna yana facing dinsa yace "Now tell me d truth, Ina yarinyar take?" Abuturrab yace "You encouraged
Aunty to my house right?" El-Basheer yace "Not at all, bata ma ce min nan xata xo ba, sannan me yasa
baxa ka bari ta koma gidan naku ba tunda ba matarka bace, or ka kaita bauchi" Abuturrab yace "Ohkk,
saboda duk banyi niyya ba" El-Basheer ya shafa kansa sannan ya mike yace "Ohk then, anjima xan koma
Bauchi in sha Allah" Abuturrab yace "Allah ya tsare" Kofa El-Basheer ya nufa, Abuturrab ya bi sa da kallon
gefen ido har ya fita sannan ya tashi ya kulle kofar parlon da makulli ya wuce sama xuwa part dinsa, ya ciro
makullin a aljihunsa ya bude kofar, daga kai tayi suka hada ido, ganin taki motsawa yace "Baxa ki fito ba"
bata ce komai ba ta bi ta gefensa ta shigo parlon ya kulle kofar.....
Karfe biyu saura Jiddah ta sauko parlor sbda yunwan da taji take ji, tun bayan tafiyar su Aunty Abuturrab
ya sa ma gidan makulli ya koma parlon bangarensa, wayarsa dake saman center table ne ta ji yana vibrate,
kallon wayar ta dinga yi sannan ta karasa ta duka ta dauka tana kallon screen din, Cikin few seconds tayi
kokarin hade rubutun screen din wayar, "Blossom" katsewa kiran yyi aka sake kira, kamar ance ta juya suka
yi ido hudu da shi a tsaye ya rungume hannu yana kallonta, daburcewa tayi xata mayar da wayar ta ajiye
masa nan bakin center table din ya fado kasa, ta mike a tsorace tace "Dama kiran ka ake" karasowa yyi ya
dau wayar fuskarsa daure yana duba screen din, juyawa tayi da sauri xata bar wajen yace "Tsaya nan..."
Tsayawa tayi amma ta ki kallonsa, Sternly yace "Baki da hankali ne?? Ba na hanaki ma shigowa parlon nan
idan ina nan ba? Ko don kinga ina kyale ki??" Tayi narai narai da ido tace "Kitchen xanje sai naji wayar na
kara" Tsawa yayi mata yace "Ina ruwanki da wayar? Ko ke kika ajiye min a nan?"