Showing 267001 words to 270000 words out of 321711 words

Chapter 90 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt

tace "Ta shi mu je, idan kowa ya hallara sai a dawo ayi magana sinka sinka" Ya kalli
Abbansa, Abba yayi masa alaman da su tafi, mikewa yayi ya bi bayanta suka fita, shi fa duk gaba daya
tunaninsa na kan Jiddah amma shakkan xuwa gidan Umma yake, bai ta6a tunanin xai yini yau ba tare da
ita a gefensa ba, is she even feeling much better now? Ta iya ta ci abinci kuwa, duk wa ennan tunanin suka
taru suka damesa a dakin Hajja, wanda kawai Hajja surutunta take bai san me take cewa ba, Da karfi Hajja
tace "Ko ba haka ba Aliyu?" Ya daga kai ya kalleta duk da bai san me take cewa ba a hankali yace "Haka ne"
Tace "Atoh, kowa xai san ni er banxa ce wllh, shiru shiru na nacutata tun ba yau ba na sani" Yana kallonta
yayi kasa da murya yace "Hajja don Allah idan an xauna kice masu su bar ni in tafi da matata, sai ta xauna
bangarena kafin a canxa mata kayan daki, ita kuma Aneesah dama xance taje gida ta huta ne na kwana
biyu don na gaji da halayyanta wllh" Hajja tace "Nima nan da ba gida daya muke ba na gaji da ita balle kai,
ita kuma Jiddah uban wa ya isa ya hanaka tafiya da ita mutum da matarsa, ai dama tare nace Ramlah su
taho, kafarta kafarka, babu shegen da xai shiga hakkin ka ina gidan nan" Sosai Abuturrab ya ji hankalinsa ya
kwanta, sallama aka yi bakin kofar dakin, Hajja ta daga kai da sauri tayi mici mici da ido kamar me son gano
muryar, Sai kuma ta amsa tace "Bismillah" Aka bude kofar Aunty ta shigo dakin kanta a kasa hannunta rike
da karamin cooler, Hajja sai satan kallonta take, Aunty na murmushi ta xauna saman carpet bayan ta ajiye
coolern hannunta tace "Sannu Hajja" Hajja tace "Yauwa sannu" Cike da ladabi kanta a kasa tace "Ina yini
Hajja?" Hajja ta hade hannunta yanda manya ke gaisuwa tace "Lafiya lau Hafsah, lafiya lau wllh" Aunty
tace "Fatan mun same ku lafiya, ya jiki jiki" Hajja tace "Aa wllh Alhmdlh, ashe kina dai kadunan" Aunty tayi
d'an murmushi tace "To ya xa ayi Hajja, muna nan wllh, sai yanda hali yayi" Hajja tace "Allah sarki, to sannu
da xuwa" Aunty tace "Yauwa Hajja, rayuwar ce sai hakuri wllh" Abuturrab da ya dauke kansa da farko don
bai yi niyyar gaisheta ba sai kuma ya juya ya d'an kalleta babu yabo babu fallasa da nufin gaisheta, amma
me?? buda ido yyi sosai ganin abu take kokarin cusawa karkashin gadon Hajja tana jan Hajja da xance, ya
kalli Hajja dake ta wani murmushi tana cewa "Hakuri kam ai ya xama wajibi a wannan xamanin" Aunty ta
gama tura abinda xata tura ta dauke hannunta da sauri, sai kuma ta mike tace "Toh Hajja bari in karasa
parlon Yallabai shi yayi kirana dama" Hajja tace "Aihoo ai ni nace ya kiraki, ni na sa shi wllh" Aunty tace
"Allah sarki Hajja, bari in je in dawo" Xata fita suka kusa cin karo da Umma, Aunty ta koma gefe, Umma ta
shigo Aunty na wani murmushi tace "Ina yini Hajiya Ramlah" Umma bata tsaya ba tana tafiyarta tace
"Lafiya lau" Kujera ta nema ta xauna, Aunty ta amsa gaisuwar Jiddah da wani irin fara'a tace "Sannunku da
xuwa" Jiddah ta sunkuyar da kanta ta karasa parlon ta xauna saman carpet daga kusa da Hajja, Abuturrab
sai kallonta yake babu ko kiftawa, Aunty dai ta fita parlon ta nufi bangaren Abba tana murmushi. Hajja ta yi
wani murmushi tace "Shegiya matsiyaciya wai ni xata yi ma siyasa kamar warce bata yi xaman Masar ba, to
xata ci kaza kazanta yau wllh" Tana fadin haka ta bude warmer din da Aunty ta ajiye taga farfesun kayan
ciki sai turiri da xuba kamshi yake, Hajja ta kalli Jiddah da ta sa hijab har kasa tace "Maxa Dauki d'an iskan
naman nan ki boye a hijabinki ki tafi can kwararo ki juye ki dauraye mata kulanta ki kawo, maxa maxa"
Jiddah ta mike ta amshi warmer din ta nufi kofa a hankali Abuturrab ya bi ta da kallo, yana son tashi ya bi
bayanta but he have to bring out abinda Aunty ta tura karkashin gado kuma yana son yin hakan ne ba tare
da kowa ya lura ba, a hankali ya gaida Umma ta amsa tana danna wayarta, Hajja tace "Bari Jiddar ta dawo
duk mu baxama parlon Usman" Umma dai bata ce komai ba, ba a wani dau lkci ba Jiddah ta shigo ta ajiye
warmer din sannan ta xauna Hajja tace "Allah ya maki albarka, tashi parlon Usman xa mu tafi" mikewa
Jiddah ta kara yi, Hajja ta mike Umma ma ta tashi suka nufi kofa gaba daya Abuturrab ya bi su da kallo,
bayan fitansu ya tashi ya tafi karkashin gadon dai dai ta inda Aunty ta xauna ya tura hannunsa a hankali
yana laluban kasan, bai ga komai ba alamar ta wuntsular da shi can ciki, hakan yasa shi dage katifar dakin,
can ya hango wani katon abu kamar laya an garkame da wani irin kwado ya dinga kallon abun snn ya ciro
handkerchief dinsa ya durkusa ya dauka yana kallo da wani irin mamaki, nannadesa yayi da handkerchief
dinsa ya saka a aljihu snn ya mayar da gadon yanda yake ya fita dakin xuwa parlon Abbansa. Abba ne
xaune parlon sai Aunty, Ummi da Aneesah dake xaune kasa daga gefen Ummi, Jiddah kuma ta xauna kasa
kusa da Umma, Hajja ta shimfida darduma tayi xamanta a kai ta mimmike kafa tana kallon Aunty da
Aneesah kasa kasa, xaunawa Abuturrab yayi shi ma a kasa, Abba ya bude taron da addu'a sannan yana
kallon Hajja yace "Kin yi kirana kwanaki kadan da suka wuce ban samu tahowa ba sai yau, ina fatan lafiya
Hajja" Hajja ta gyara xama tace "Toh ni dai kafin ince komai a nan so nake in ji ko kauron Mama nayi maka
ya sa kaji gwara ka mayar she ni gantallaliya kawai Usman" Abba dai yayi shiru yana kallonta, Hajja ta kalli
Aunty da kyau tace "Maimaita abubuwan da kika gaya min a parlon Aliyu ranan" Sosai gaban Aunty ya fadi
ta dinga kallon Hajja.


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp



A fusace Hajja tace "Ba kallona xaki tsaya yi da idanuwa kamar bakwainin kwarkwata ba Hafsah, cewa nayi
ki maimaita abubuwan da kika gaya min gidan Aliyu yanxun nan" Aunty ta gyara xama ta d'an daure fuska
babu ya6o babu fallasa tace "Kamar me kenan? Dama mun hadu a gidan Aliyu ne Hajja?" Hajja ta saki
salati tana tafe hannu tace "Huhuhu duniya ta tara sheggu, wato bamu hada gidan Aliyu ba?" Aunty ta ki
cewa komai, Hajja ta kalli Abuturrab da karfi tace "kai Aliyu wani rana ne muka hadu da Hafsah a gidanka?"
Abuturrab ya daga kai a hankali ya kalli Aunty, wani shegen kallo take masa fuskarta a daure, Ya kalli Hajja
yace "Ranan Juma'ahn da ya wuce" Hajja ta gyara xama tace "Aa kai kuma ba haka xaka ce ba, labari xaka
dauko tiryan tiryan na dalilin xuwa na gidan naka sannan da naje me ya faru a can din, kana yin abu kamar
dai kana tsoronta" Abuturrab ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Ranan Juma'ah na dawo daga wajen aiki na
biyo nan na daukeki xuwa can gidan nawa..." A fusace Hajja tace "Toh ai sai ka fadi dalilin kai ni gidan
naka" Abuturrab ya sunkuyar da kai, Hajja ta bude baki tace "Kun ga algungumi ko? Da gasken dai tsoron
Hafsah kake... Wasu narka narkan zawarawa yan uwan Nanisa su biyar da wannan mata Hafsah ne fa suka
tafi suka ta re masa a gida na kusan wata daya suna xuba tsiyarsu kamar ya yan tasha, to uwarsa Hauwa ba
tsayayya ba balle ta kwatar masa gida ta fatattakesu, kanwar uwarsa kuma abu kadan ta kwaso hukuma
tana gaba suna biye da ita, to yabawa da yayi da hankalina da natsuwa da iya magana ya sa shi xuwa ya
daukeni domin in je in masu nasiha akan cewar bai dace su tare a gidan yaro ba, su kama gabansu su tafi,
don wllh sun mayar masa gida gidan xawarawa shi kuma bashi da bakin magana, ai ko na shirya naje gidan,
in gaya maku suna xaune sun yi washarere dasu a parlon babu kunya babu tsoron Allah, nayi masu sallama
na gaishesu nace A'a Hafsah dama kina kaduna ashe? Ai a tunanina kina Benue?" Hajja na demonstrating
tana jujjuya ido da hannu tace "Ba sai mata ta dinga jujjuya min ido cike da axababben rashin kunya da
fitsara take ce min ehh kwarai ina nan ban je ko ina ba, babu kuma wanda ya isa ya sani in je wani gurin, ko
baki da labari ni da Usman mutu ka raba, sannan ko ke da kika durkusa kika yi nakudarsa kika haifesa kinyi
kadan ki raba ni da shi wllh ki ji in gaya maki kinyi kadan, wato ke a xaton ki ya sakeni ko?? To kin yaudari
kanki tsohuwa, don kuwa babu abinda ya canxa a kan matsayina a wajen Usman, ina nan a matsayin
matarsa lokaci kawai ake jira ki ga ikon Allah, ai ba sabon abu bane rabo ya kashe mutum...." Hajja ta rike
kai tace "Huhuhu.... in gaya maku ta wani ja min tsoki da na ji sa har tsakiyar kai na, ni dai nayi shiru duk
jikina yayi sanyi" sai kuma ta fashe da kuka ta kwance ha6ar xaninta tana shessheka, Abba dai kansa na
kasa duk yana sauraronta, Aunty tayi karfin halin cewa "Ni? Ni muka yi haka dake Hajja?? A ina muka hadu
muka yi haka? ki ji tsoron Allah...." Tsawa Abba yayi mata yace "In my present??" Aunty ta wani ta6e baki
tana jijjiga kafa tana hararan Hajja kasa kasa, Hajja ta share hawayenta cikin rawar murya tace "Usman ai
ko da ace gallaza maka nayi kafin ka kai matsayin da kake yau ya kamata in ci darajar haihuwar ka da nayi,
ballantana ba daya kanwar biyu, gata dai wannan ka samu kamar xan kashe kaina a kanka, ko Kabiru bai
samu kulawa da son da na nuna maka ba tunda shi ubansa ya ha'ince ni na dai bar komai sai gobe kiyama
kawai, kai kuwa ubanka mutuwa ce ta rabani da shi bawan Allah, to Usman duk sadaukarwan da nayi a
kanka yau sai ka rufe ido ka xabi mace a kaina? Dubi fa wahalan da nayi tayi a kanka amma sakayyar da
xaka min kenan? Har xagina matar nan ta ta6a yi a gabanka shekaru ashirin da suka wuce ta ci min
mutunci ta walakanta ni, kafin xuwana Masar na farko, amma wai sai kayi mata saki daya a wancan lkcn
ma, ko awa biyu kuma ba ayi ba ka maidata ba da sanina ba sbda lalacewa ta sameka Usman..." Sai kuma
ta fashe da kuka, Aunty dai ta kasa xaune waje daya jin abubuwan dake fitowa daga bakin Hajja, Cikin kuka
sosai Hajja tace "Na xata ko bare yace xai walakanta ni sai inda karfinka ya kare balle a cikin gidanka, shkkn
na xama er banxa kenan bani da gata, matarka sai dai ta takani ka saketa a gabana ka koma bayana ka
mayar da ita? Duk xamana da Hauwa ko kallon banxa bata ta6a min ba balle ta mayar min da magana duk
fitinata da bala'i na, to na ta6a ce maka ta min??" Hajja ta dinga matse hawaye tana kuka, Abba ya daga kai
a hankali ya kalli Aunty yace "Ki je na sake ki Hafsah" Mikewa Aunty tayi xumbur don furucin nasa ya xo
mata unexpected, tana kikkifta ido tace "Kayi me?" Abba na kallonta yace "Na sake ki" Girgixa kai ta shiga
yi cikin tashin hankali tana nuna sa take cewa "Plss stop this joke Usman, I don't get ka sakeni? Kamar yaya
kenan? A saboda me ka sakeni? I don't understand, Kasan kuwa me kake cewa? Shikenan fa igiyar, are u on
ur right senses?" Abba dai bai ce mata komai ba, ta fashe da wani mahaukacin kuka tace "Usman ka sakeni
fa kace? Ka mance igiyar saura daya ne? Are u for real? Ka datse aurenmu kenan kake nufi?" Jin Abba bai
tanka ta ba ta dau jakarta da sauri tana goge hawayen idonta tace "Wait for it Usman" xata nufi kofa
Abuturrab ya mike yace "kinyi mantuwa dakin Hajja daxu!!" Juyowa tayi tana kallonsa, ya nufeta sannan ya
ciro handkerchief din ya ajiye kasa gabanta bayan ya bude abun ciki a sarari ya mike yana kallonta, kallon
layan ta dinga yi with so much shock, kowa na parlon ma kallon layan yake a firgice, Hajja ta mike da sauri
tace "Huhuhu meye wannan kamar laya, ina ka samo sa Aliyu?" Abuturrab yace "Daxu ta bar maki shi a
daki kafin ta fito" Hajja ta bude baki a tsorace ta dafe kirji tace "Ta bar min shi??" Da sauri Aunty ta juya ta
fice daga parlon har tana bugewa da kofa, Hajja ta saki salati ta dau hankicin ta kai har gaban Abba ta ajiye
masa ta fashe da kuka tace "Wato bakina ya rufu in kasa ta6uka komai a rayuwata ta duniya, to sai dai
bakin uwarta dake kabari ya rufu ba dai nawa ba, in ji kaga matar da kake aure shekara da shekaru Usman,
inji yau ka gane ma idonka" Abba dai sai kallon layan yake da mamaki ko kiftawa babu, Ummi dai duk
jikinta yayi sanyi, Umma kuma sai murmushi take me sauti tana girgixa kafa, Sai da Hajja ta bari Abba ya
gama kare ma layar kallo snn ta nannade tace "Toh Alhamdulillah, Allah nagode maka da ka kawo mana
karshen wannan annoba dake cikinmu shekara da shekaru, Allah nagode maka, in ji dai ka gani Usman, to
haka ta kulle bakinka kana ta tafka tsiya kana walakanta matarka ta arxiki, kana walakanta uwarka" Umma
ta daga hannu sama da karfi tace "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, dama Hausawa sun ce shi
ramin karya kurarre ne, kuma na sake tabbatar da cewa mahakurci mawadaci" Ummi ta goge hawayen da
ya kawo idonta ita dai bata ce komai ba, Hajja ta fashe da kuka sosai tace "Ina ma Nafisa da su Kabiru na
nan su ga wannan rana ni 'ya su, yanxu ya Hafsah xata yi da hakki jama'a? Ya xata yi da hakkin Hauwa da
'ya yanta? Har ma da hakkina da na d'a na" Abba dai ya kasa cewa komai kansa a kasa, kana ganinsa kasan
he is really shocked, Amma fa babu wanda ya kai Aneesah shock a parlon to aka saki Aunty balle ita karan
kada miya?? Gaba daya hankalinta idan yayi dubu ya tashi, tana son Aliyu so me tsanani kuma bata fatan
abinda xai rabata da shi, tana tsoron ace ta rabu da Aliyu tasan kilan mutuwa xata yi gaba daya, duk
wannan abun da ake Jiddah ta ki dago kanta a parlon, Hajja na shessheka tace "Toh ai xuwan Jiddah
pamilyn nan namu alkhairi ne, gashi dai a ta dalilin xuwanta abubuwa iri iri na boye da na fili suka dinga
billowa har ya kai ga tonon asirin Hafsah, duk mugayen abubuwan da Hafsah ke yi shekara da shekaru bai
bayyana ba sai xuwan Jiddah, mata ki raba d'a da uwarsa, ni gaya maku ne kawai banyi amma wllh akwai
sanda Aliyu ya sameni wai shi fa bai yadda Hauwa bace mahaifiyarsa, na yi matukar girgixa da furucin nan
nasa nace kai ko me yasa kace haka, sai ce min yayi shi baya jin ta kamar uwarsa a ransa, kuma sai ya ji bai
son ganinta ma wani lkcn, wllh idan ba yanxu ba ban sanar ma kowa ba ni dai na dage masa da addu'a,
komai sai yace Aunty, da xa ku ji uban dukiyar da yake narka ma Aunty a baya sai kun girgixa, har fili ya
ta6a siya mata ya gaya min amma wai kar in gaya ma Hauwa, alhalin bai ta6a tsinana Hauwan da komai ba,
kaiii Hafsah dole sai ta dawo ta nemi gafarar Hauwa da D'an ta idan ba haka ba garari kawai xata yi tayi a
duniya ta rasa tudun dafawa" Ummi dai ta kasa controlling hawayen dake xuba idonta tana tuna abubuwa
da yawa, Umma dai ta rungume hannunta kawai daga inda take xaune ita ma tana tuna irin takaici da
bakin cikin da yayarta ta dinga kunsa a gidan nan for almost 20 years amma take ta hakuri, kullum sai dai
tace watarana sai labari, gashi ko sau daya bata ta6a yarda wai asiri Aunty ke yi ba, gaskiyan Hajja shigowar
Jiddah rayuwar Abuturrab ne mafarin samun bond da Umminsa, ta dalilinta suka fara creating bond da
mahaifiyarsa, a da ko shawara bai yarda yayi da ita ba, komai Aunty, ita kadai tasan nawa yake samu wajen
aiki, ko wani lamarinsa ita ce, Umma ta girgixa kai ta ji ta kara jin tsoron duniya, yanxu ya Hafsah xata yi da
wa ennan hakkin? kin raba mata da mijinta hakan bai isheki ba kin rabata da d'anta kiri kiri komai yace sai
ke, Hajja ma don kin sameta tsayayya ce banda haka da tuni kin rabata da d'an ta ita ma, Umma ta share
hawayen da taji ya kawo idonta tana kara gode ma Allah da ya kawo karshen komai cikin sauki sannan a
lokacin da ba ayi xato ba, kuma a gaban kowa, Abba ya dago a hankali bayan few minutes ya kalli Hajja
yace "Hakuri xa ayi Hajja, Allah ya sa mu gama da duniya lafiya, ina ce shikenan ba wani abu kuma?" Kana
jin yanda yayi maganan kasan watse taron yake son yi, he just want to be left alone, Hajja ta share idonta a
hankali tace "Aa ba shikenan ba, Usman daxu ni da wannan mata Hauwa mun je gidan Aliyu, nice ma na
tilastata muka tafi ka santa ba wani wayewa gareta irin na matan xamani ba kamar dai yanda kaga yar
uwarta Ramlah take, to banda rashin wayewa ai babu wani me kunyan d'an fari a xamanin nan dai, ni kaina
banyi wannan kauyancin ba a xamaninmu, ni dai na ja ta muka je ashe bala'i xa mu je mu tarar Usman, in
gaya maka wannan yarinya me kama da Zabiya matar Aliyu tayi kwatsa kwatsa da kayan dakin Jiddah da
aka kai mata ko sati bai yi ba, kuma na samu labarin kayan miliyan uku aka kai mata" Abba ya kalli
Abuturrab yace "Where were u then?" Ya sunkuyar da kansa, Hajja na nuna Ummi tace "Wllh a kan idon
Hauwa aka yi komai, ni kuma na baxama


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login