Showing 318001 words to 321000 words out of 321711 words
Chapter 107 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt
yake, ya
maidata irinsa, shi yasa bata wani wahala ko gajiya da shi, kusan inda Abuturrab ya tafi wajen aiki ta kan
shiga gidansu Hajiya Fatima har ma ta yini, Hajiya Dada kuwa duk bayan 2 days ko ita bata kirata ba ita xata
kirata don Abuturrab ya siya mata exactly irin wayar da ya siya mata wanda Aneesah ta hade da kayan daki
ta dagargazar, hka sauran Uncles dinta da aunt duk suna gaisawa a family group da aka sakata a ciki, she
felt belong now, ko ba komai yanxu tana da wa enda xata nuna tace ai wa ennan dangina ne na jini, kowa a
familyn ji yake da ita, sau dayawa idan Alhaji Ishaq ya shigo kaduna komai ya kawo ma su khaleesat sai ya
raba dai dai da Jiddah ya bada a kai mata, hakan na yi ma Jiddah dadi sosai, jinsa take kamar mahaifinta na
gaskiya, Hansai kuwa ta kusa sati uku yanxu a gombe wajen Hajiya Dada.... Yau duk da tasan Abuturrab na
hanya sai duk ta kasa tashi tayi abinda ya kamata a gidan gaba daya wani kasala take ji tun da ya tafi ya bar
ta, da ta yunkura xata yi aiki sai taji ta kasa sai dai ta koma ta kwanta, gashi gaba daya appetite dinta na cin
abinci babu, ko a waya kuma bata sanar masa yanda take ji ba, ganin dai ya kusa shigowa ta mike da kyar
tayi karfin halin shiga bandaki ta hada ruwan wanka tayi wanka sannan ta fito ta saka turare sama sama ta
shirya, kwanciya ta koma tayi don taga alamar fa baxata iya ta6uka komai a gidan ba, tana jin shigowar
motarsa bayan la'asar, ta daure ta kara mikewa ta sauko downstairs, dai dai nan ya shigo parlon karasawa
tayi ta shige jikinsa kamar yanda ta saba in dai ya dawo, rike breathing dinta tayi sbda wani hautsine mata
ciki da kamshin turarensa yayi, ta sa hannu ta rufe bakinta da hancinta, da mamaki yake kallonta yace
"Baby me ya faru" Ta fara masa alamar amai na taho mata, da sauri ya ja ta xuwa bathroom dake parlorn,
ganin yanda take aman yace "Oh my God baby dama baki da lafiya ne?" Ta kasa basa amsa sai sauke
numfashi take, fitowa yayi da ita daga bandakin, ko minti biyar basu kara a gidan ba ya tafi da ita hospital,
tun da suka shigo Aneesah dake xaune reception ta dinga rurrufe fuskarta tana kallonsu kasa kasa, shi kam
ko lura da ita bai yi ba haka jiddah dake fama da kanta, bayan an duba Jiddah Abuturrab ya kasa boye farin
cikinsa bayan likitan ya sanar masa tana dauke da ciki na sati uku, he felt like kissing and caressing her in
public, he was so very happy, kasa daurewa yayi daga karshe ya rungumeta gam a office din likitan ya dinga
sa mata albarka, sai bayan kusan 30 mins suka fito haraban hospital din yana rike da hannunta da few
drugs da aka bata sbda amai da kasalan da take, gently yake tafiya da ita don bai son anything that will
stress her, don ma cikin mutane ne da daukar abarsa xai yi baxata taka kasa ba, tun shigowarsu asibitin da
minti goma aka sallami Aneesah amma ta kasa tafiya ta xauna karkashin bishiya a haraban asibitin tana
jiran taga fitowarsu, tana ganin sun nufi mota ta mike a hankali ta nufesu, da farko Abuturrab bai ma
ganeta ba sai da ya sake kallonta da kyau, ta dan yi murmushi tace "Good evening captain" Sosai gaban
Jiddah ya fadi ta juya tana kallonta, yana bude ma Jiddah back seat yace "Evening Aneesah how are you
doing, longest time" Tace "Alhmdlh" Jiddah ta shiga motar Aneesah na kallonta tace "Kwana da yawa
Hajiya Jiddah" Jiddah tace "Alhmdlh" Rufe motar Abuturrab tayi dai sai kallonsu take ta cikin glass, ya bude
driver seat yace "Toh ya aka yi Aneesah?" Tace "No dama gaisuwa ne" Yace "Toh nagode, baki da lafiya ne
kika xo ganin likita?" Tace "Ehh" Hannu ya sa a aljihu ya ciro kudi masu yawa yace "Ohk take this little
token" Ta dinga kallon kudin amma ta ki amsa, sai ta daga kai ta kallesa hawaye cike idonta tace "I just
want to ask u for forgiveness..." Yace "Nahh I've done that long ago Aneesah, na yafe maki
wholeheartedly, me yake damun ki kika xo gun likita?" Tace "Xaxxabi nake" Yace "Toh Allah ya sauwake...
Allah ya kara lafiya, i need to leave now" Kai kawai ta gyada masa ya bude front seat ya shiga ya tada
motar suka bar asibitin ta madubi yake kallon Jiddah ya ga yanda ta wani hade rai, yayi kasa da murya yace
"Baby" ko kallonsa bata yi ba ta kauda kanta.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_
Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*
If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp
Jiddah ce xaune dakin bak'i tana yanka fruit din kankana a tray, xaune daga gefe daya kan darduma Hansai
ce, Hansai tace "Ina ta son xan maki wata magana Jiddah" Jiddah ta daga kai ta kalleta ta dau tray din
watermelon din ta ajiye a gabanta tace "Ina ji Baabarmu" Hansai tayi kasa da murya tace "Shekarun baya
da dadewa akwai wata aminiyar mahaifiyarki ana ce mata Sadiya, baabarki tace min tun bata yi aure ba
take tare da Sadiya hasalima Uwar sadiya ta san kakarki sosai ina jin kamar sun ma yi kawance, to a da dai
Sadiya ta auri wani me rufin asiri a unguwan sanusi, don lkcn da Mahaifiyarki ma ta rasu wllh xuwan Sadiya
uku tana son xata daukeki ta rike ki amma duk na hana, a xuwan karshe ma ba ta dadin rai ta bar gidana
ba, nace kada ta sake dawo min gida, to wannan dalili ne yasa har yau bata sake waiwayo inda muke ba, to
a lkcn har gidanta na sani a can unguwan sanusi don mun je sau uku da Baabarki a lkcn da take da rai,
yanxu dai ban san ko tana nan har yanxu ba, ni nasan ko kadan ne Sadiya baxata rasa sanin wani abu a kan
mahaifiyarki ko kakarki ba, xai iya yiwuwa ita Baabar sadiya sun ta6a wani hira da kakarki ta fada mata
wani abun game da asalinku, shine nace kiyi ma mijin ki magana ko xa mu je gidan Sadiya idan yaga da
halin yin hakan" Jiddah dake ta sauraronta tace "Toh Baabarmu xan masa magana in sha Allah" Hansai tace
"Toh maa sha Allah...." Xaunawa Jiddah tayi don dama a durkushe take a dakin, Hansai tace "Aa tashi ki tafi
gun mijinki ai dare yayi kuma haka" Jiddah tace "Xan jira idan kin gama in kai tray din kitchen" Hansai tace
"Xan kai da kaina, ki tashi ki tafi sai da safe" Jiddah tayi mata sai da safe sannan ta mike ta fita... Xaune ta
tarda Abuturrab yana operating laptop Little Jiddah na jikinsa tayi bacci, Ta cire Hijab din jikinta ta linke
don dama tayi shirin bacci, ta xauna gefensa ta jinginar da kanta da shoulder dinsa tace "Dee" Jawota yyi
jikinsa yace "Baby kina stressing kanki da yawa fa, u need housemaid seriously, kullum cikin gyara gidan nn
kike ba dare ba rana" Tayi murmushi tace "Sai kace wani aikin duniya?" Kashe laptop din yayi ya kwantar
da little Jiddah, ya jawota jikinsa yana kissing lips dinta, bata yi sanya wajen biye masa ba.... bayan an idar
da sallan Asuba ya dawo masallaci ta basa d'an labarin da Hansai ta bata, ya d'an yi shiru sai kuma yace
"Alright in the evening sai mu tafi tunda tace ta san gidan" Jiddah tace "Allah ya kai mu" A hanxarce Jiddah
ta gama wanke few plates da aka 6ata a kitchen ta goge ko ina sannan ta fito tana kallon agogo, Abuturrab
na xaune parlorn yana kallon wrestling ta nufesa ta xauna kusa da shi tace "Dee baka kira ayi fill din gas din
ba till now" Ya jawota jikinsa yana kallon agogo yace "Sai mun dawo Baby, hope u are done now?" Tace
"Eh na gama, ince ta sauko??" Yayi kissing din lips dinta yana murxa hannunta yace "Yeahh Baby" Mikewa
tayi ta wuce sama, bude dakin da Hansai take tayi ta shiga ciki, Hansai na xaune kan carpet da Little Jiddah
tana daure mata dogon gashinta da colorful ribbons, babu abinda wannan yarinyar ta mance bata dauka
ba na ubanta, ko kadan bata kama da Jiddah ta ko ina sai ta beauty point da haskenta da ta dauko...
Kyakkyawa ce yarinyar ta karshe, kamar er india, Tana ganin Jiddah ta 6ata fuska xata yi kuka, Hansai tace
"Lah ji min yarinya wai ta 6ata fuska daga ganinki, lafiya fa nayi mata wanka na shiryata babu ko tari"
Dariya Jiddah tayi tace "Baabarmu wai ki sakko mun gama" Hansai tace "Toh gani nan fitowa, dauketa ku
tafi sai ki karasa daure mata gashin tunda ta fara haka baxata yarda ba kuma" Jiddah ta karasa ta dau
daughtern nata ta fita daga dakin, dakinta ta fara shiga ta dauko Veil dinta da handbag sannan ta sauka
kasa, Little Jiddah na ganin Abuturrab ta fara mika masa hannu tana masa dariya, she looks so happy
seeing him, mikewa yayi ya amsheta yayi kissing Cheek dinta affectionately yace "I love u cute Mamina"
rungumesa yarinyar da bata wuce shekara daya da wata bakwai ba tayi, Abuturrab ya mika ma Jiddah dake
kokarin yafa veil dinta car key yana kallonta, ta xumburo baki tace "Aa ni baxan iya ba, kullum sai ka dinga
min wayo kana bari na da tuki" murmushi yayi yace "Toh amshi er ki sai inyi driving din" Little Jiddah ta
makalkalesa xata yi kuka, Jiddah ta rike ha6a tace "Dama idan xai koma aiki sai dai ya tafi da ke, baxai bar
min ke ba..." Dariya Abuturrab yayi yace "Salon kiyi kuka idan na tafi da ita" Yana fadin haka ya jawota yayi
mata side hug yace "Na lura kishi kike yi da Ummi na fa" Jiddah tace "Toh ba gashi baka da time dina yanxu
ba sai dai nata" A tare suka fita parlon yana cewa "Ni ko nake da time dinki, during d day dama time din
Mami ne, ke kuma throughout the night time dinki ne kinga equation balanced" Jiddah tayi murmushi
kawai ta amshi car key din a hannunsa, Hansai ce ta fito daga parlor ganin makulli jikin kofa ta kulle sannan
ta cire makullin ta nufi motar ita ma, duk da ba da sanda take tafiya ba amma har lkcn bata tafiya dai dai...
Abuturrab na kallon Hansai ta madubi yace "Wani anguwan ma kika ce?" Hansai tace "Unguwan Sanusi"
Suna isa gidan luckily har lkcn Sadiya bata tashi ba don gidan mijin nata ne, wanda shi ma ya rasu ya bar
mata 'ya ya, duk da Sadiya bata ganesu ba, haka ta shimfida masu tabarma a tsakar gida tana bin su da
kallo tace "Sannunku da xuwa" Hansai na murmushi tace "Hansai ce fa Sadiya naga kamar baki gane ni ba"
Sadiya tayi shiru tana kallon Hansai, sai kuma ta mike da sauri tace "Hansan Amina?" Hansai na
murmushin karfin hali tace "Ni ce Sadiya, kinga ga Jiddah nan" Sadiya ta saki wani salati tace "Jiddah er
wajen Marigayiya Amina?" Sai kuma ta fashe da kuka ta dago Jiddah ta rungumeta tace "Allah sarki
rayuwa, sannunku da xuwa Jiddah, ashe da rabon xamu sake ganawa Hansai, sannunku da xuwa, Allah
sarki rayuwa" Hansai dai sai kirkiro murmushi take, Sadiya tace "Toh ina bibalo?" A hankali Hansai tace
"Allah yayi mata rasuwa" Sadiya ta saki salati ta nemi waje ta xauna tace "Yaushe ni Halima?" Hansai tace
"Yau kusan shekara uku kenan da rasuwanta" Sadiya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya gafarta
mata Hansai, Allah ya ji kanta, wayyo rayuwa" Hansai dai ta sunkuyar da kanta, Sadiya tayi tagumi tana
jimamin mutuwan Bibalo, Hansai ta dago tace "Dama mun xo gunki ne Sadiya tare da fatan Allah dai ya sa
kinsan wani abu game da kakar Jiddah da mahaifiyarta" Sadiya tayi shiru, sai kuma tace "Toh, amma dai
duk abinda ni na sani baxai kai wanda mahaifiyata ta sani ba, idan kun ga babu damuwa to mu tashi mu
tafi gidan Mamanmu yanxu, tana nan anguwan ita ma" Hansai tace "Wannan ba damuwa bane" Fita suka
yi gidan gaba daya suka shiga motar Abuturrab, Abuturrab ya gaida Sadiya dake gaishesa a back seat
sannan ya nufi hanyar da tace masa ya bi, bai yi niyyar shiga gidan ba amma haka Sadiya ta matsa ya shiga
ayi komai a gabansa kawai, babu yanda ya iya haka ya sauka ya kulle motar yana rungume da little Jiddah,
duk da ba wani tsufa mahaifiyar Sadiya tayi ba amma yanayi na rashi da halin rayuwa ya sa duk ta wani
yakune kamar warce ta shekara tamanin a duniya, bayan sun gaisa Sadiya ta gaya ma mahaifiyar tata
abinda ke tafe da su, Mahaifiyarta ta dinga kallon Jiddah tace "Yanxu kuna nufin jikar Maijiddah ce wannan
Sadiya?" Sadiya tace "Ita ce Inna" Inna ta girgixa kai tace "Allah me iko, ikon Allah ya fi gaban haka, Allah
sarki rayuwa, Allah ya gafarta ma maijidda, Allah ya Rahama mata, Allah ya raya xuri'ar da ta bari" Duk
suka amsa da Ameen, kamar yanda Hansai ta sanar ma Sadiya abinda ke tafe da su a can gidanta haka ta
sanar ma Mahaifiyarta abinda ya kawo su, Inna tayi shiru sai kuma a hankali tace "Toh, ita dai Maijiddah
nasanta a lkcn tana aikatau a gidan Alhaji Labaran, tace min asalinsu yan kasar Nijar ne, amma bata ce min
ga garinsu a Nijar ba gaskiya, ni kuma bata ta6a ce min ai ga abinda ya kawo ita da er ta Amina Nigeria ba,
sai amsa daya da ta bani a lkcn da nayi mata tambayar, tace min ita kawai tana son nisa da yan uwanta da
garinsu ne ta rike er ta har Allah ya raya mata ita, wato Amina kenan, ko a lkcn da kudinsu na Nijar da yawa
a jikinta tayi ta ajiya bata komai da su wllh, ni idan ban manta ba har zinarai maijidda na da su a jaka, ni
kuma ban gaya maku dalilin haduwarmu da kawancen mu ba, to a lkcn nima ina aikatau a gidan aminin shi
Alhaji Labaran din wato Alhaji Sama'ila, don haka wani lkcn na kan yi ma matarsa Hajiya Kande rakiya xuwa
wajen matar Labaran ita kuma ana ce mata Hajiya Bilki, to kun ji dalilin sabawar da muka yi da Maijidda
kenan har muka dawo kamar yan uwa, ni kuma a lkcn aurena ne ya mutu, mata me kirki da gaskiya da
amana, wnn dalili yasa Hajiya Bilki ta rike ta da kyau, don su suka aurar mata da er ta Amina ga Isuhu,
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a gidan kuma Allah yayi mata rasuwa don tana ta ciwon da ba a san daga
ina ba, sun kashe mata kudin asibiti bayin Allahn nn ba na wasa ba, amma har ta koma ga mahaliccinta ba
a gano kan ciwon nata ba, Allah sarki yanxu xancen da nake maku daga matar har mijin babu su suma duk
sun rasu, sai dai ya 'yansu da jikoki, basa ma garin kaduna ynxu gidan ma na samu labarin sun siyar, to ni
shkkn iya abinda na sani a kan Maijidda kenan, er mutan Nijar ce dai" Hansai ta sauke ajiyar xuciya tace
"Toh mun gode sosai Inna, Allah ya saka da alkhairi" Tace "Allah ya maku albarka" Jiddah dai duk jikinta
yayi sanyi sosai, Inna tace "Kawai ku je kuyi ta addu'a in da rabon Jiddah xata gana da dangin uwarta xata
gana da su wataran, Allah kadae yasan dalilin da Maijidda ta baro kasarsu da yar ta da bata wuce shekara
goma ba ta dawo Nigeria" Godiya Abuturrab ya kara yi ma Inna ya ciro dubu biyar ya ajiyeta mata, sannan
suka bar gidan nata, bayan sun ajiye Sadiya a gidanta suka koma gida. Da daddare Jiddah na kwance jikin
Abuturrab tayi lamo, tun bayan dawowarsu ya lura she is moody ya shafa fuskarta a hankali yace "Not
again wife, akwai wani abu da kika nema kika rasa ne a rayuwa yanxu? U have ur fathers relative that are
firmly there for u always, tunda gashi sun canxa min ra'ayi ba wai don na so ba, u will be starting ur higher
institution next month in sha Allah, non of my penny was used, they paid for everything, isn't that for the
sake of the love they have for u?" Kasa ce masa komai tayi wasu hawaye masu xafi na sauka idonta, ya
rungumeta sosai yace "bana son haka Wife, kina daga min hankali sosai" Cikin sanyin murya tace "Kayi
hakuri" Yace "Definitely one day, one time, u will meet with ur Maternal relatives in sha Allah, xa mu tafi
Umra soon sai ni dake muyi wannan addu'an a can, sai ki ga Allah ya amsa.... In sha Allah" Cikin sanyin
murya tace "In sha Allah" Washegari Karfe goma saura Jiddah ta gama duk abinda take, bayan Hansai tayi
breakfast ta shiga gidansu Hajiya Fatima, ita kuma Jiddah suka fita tare da Abuturrab, shi ke driving din,
tana xaune front seat rike da Little Jiddah a kafarta, motoci ne sun kai biyar anyi parking kofar gidansu
Abuturrab, Abuturrab ya nemi waje shi ma yayi parking ya sauka, Jiddah ma ta sauka, ya amshi little Jiddah
a hannunta suka shiga cikin gidan, ganin guards din palace din bauchi ya gane uncle dinsa ma na gidan,
Tun daga nesa yake kallon El-Basheer dake tsaye tare da Ahmad, ya karasa suka fara gaisawa da Ahmad
sannan ya mika ma El-Basheer hannu yana kallonta, El-Basheer yace "And i am hoping u will be unblocking
me this very moment" D'an murmushi kawai Abuturrab yayi yana patting shoulder dinsa yace "I neva did
block you brother" Jiddah ta sunkuyar da kai ta gaishe su, El-Basheer na ganin little Jiddah ya wara ido yace
"Waow, and at last, my wife is born..." Karasawa tayi ya amshi yarinyar a hannunta yace "Waoow she is so
cute" Jiddah na kallon Ahmad tana murmushi tace "Aunty Ramlah fa yaya Ahmad?" Yace "Tana ciki"
Juyawa tayi ta karasa cikin gidan, Maimoon ta taso da sauri ganin Jiddah ta rungumeta cike da murnan
ganinta tace "Mrs Aliyu" Jiddah na murmushi tace "Mrs Yusuf" Dariya kawai Maimoon tayi, Jiddah ta janye
jikinta ganin su Ummi a parlon tace "Bari in gaida su Ummi" xaunawa kasa tayi gefen Ummi ta gaisheta,
Ummi ta amsa da fara'a, ta mike ta tafi kusa da Umma tana jin kamar ta rungumeta tana murmushi tana
kallonta tace "Umma ina yini" Umma tace "Lafiya lau Daughter, ina Ummin?" Tace "Tana wajen yaya
Bashir"