Showing 147001 words to 150000 words out of 321711 words
Chapter 50 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt
slice bread din
ta ajiye saman tray, sannan ta dau tray din ta fito, a hankali take tafiya xuwa dakin Ahmad, ta fi minti daya
tsaye bakin kofar kamar me contemplating kafin tayi knocking a hankali, jin shiru ta sake kwankwasawa
gently, bude kofar dakin aka yi ta koma baya tana kallonsa kamar yanda shi ma yake kallonta.....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last
bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd
getting rid of any skin problems
Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta
samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar
rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata
masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda
zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada
Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240
Juyawa yayi ya koma cikin dakin, ta karasa ta ajiye tray din a saman carpet din dakin, sannan ta mike tana
kallonsa tace "Ina kwana?" Dauke idonsa yyi ya koma ya xauna gefen gado, ta juya ta fita ta kullo masa
dakin, ya kai hannu ya dafa kansa hade da lumshe ido. Karfe sha daya Jiddah ta fito dakinsu bayan tayi
wanka ta shirya, Umma dake xaune parlor tare da Aunty Nafisah ta kalleta tace "Ke kin karya kuwa
Jiddah?" Jiddah ta karaso ta duka kasa kusa da kujera tace "Eh Umma" Aunty Nafisah dai sai kallonta take,
ita dai kawai taji tana son Jiddah ganin bata da wani alama na hayaniya sannan tana da respect, Umma
tace "Toh tafi ki daura shinkafa... yanxu xaki ga ranan tayi" Jiddah tace "Toh" sannan ta mike ta nufi
kitchen, Aunty Nafisah ta bi ta da kallo har ta shiga sannan ta kalli Umma tace "Tun da ta dawo nan bata
koma gidansu ba amma?" Umma tace "Aa bata je ba, to me xata je tayi, her parents are late, kishiyar
mamarta ce a gidan ai, and I don't think she knows any of her relative gaskiya" Aunty Nafisah ta buda ido
sosai tace "Amma kuma da mamaki ace dangin iyayenta basu nemeta ba har yanxu ai ko, Ummi tace min
kusan 2 nd half months kenan fa, ae baxa ace bata da wasu dangi ba..." Umma tace "Wannan kuma ae a
gun Aliyu xa a samu information din nan, tunda mu ko gidan nasu ma bamu sani ba har yau balle wani
nata, and i don't even think it's necessary for now nan gaba duk xata nemesu idan Allah ya yrda wannan
dole ne, yanxu dai i want her to get educated first, hakan kadai ne gatan da xa a iya yi mata" Aunty Nafisah
tace "Haka ne kuma, amma da na xo naga yarinyar ban so Aliyu ya saketa ba wllh, yarinya ce me hankali da
natsuwa sosai, kin ga ai da Ummi tayi dacen surka ta gari, amma wannan mata da aka kai jiya banga
alamar abun arxiki ba, don naga alamar idonta a tsakiyar kanta yake, snn na ga kamar suna da wani alaka
da ban san na meye ba da Aunty kuma ban ji dadin hakan ba, idan ma don yana son auren wannan ne ya
sa ya saki Jiddar ai da sai ya hadasu su biyun tunda Allah ya hore masa...." Umma ta ta6e baki tace
"Wannan kuma shi ya jiyo, Jiddah dai tayi masa nisa sai hange daga nesa yanxu, dama Allah ya hadasu ne
don ya fiddota daga kangin rayuwar da take ciki a gun kishiyar uwarta, mu kuma mu riketa, indan ta ni ce
kada ma ya nuna ya ta6a saninta har abada" Aunty Nafisah ta girgixa kai tace "Aa kar ki ce haka Hajiya
Ramlah, ai kuwa har gobe bata da kamarsa don shine silar duk wani abun alkhairi da xai sameta a rayuwa
ko kuma ince yake kan samunta a rayuwa, ni da xai nutsu yasan inda ke masa ciwo ya maida hankalinsa ma
yace xai maidata...." Umma ta kalleta da sauri tace "Ya maida ta ina?" Aunty Nafisah tace "Ya maidata
dakinta suyi xaman aure, ai saki daya yayi mata ko??" Umma tayi wani dariya tace "Xancen kike so Nafisah,
Ai Aliyu ya makara, ke kinga walakanci da cin kashin da ya dinga ma yarinyar nan? Wllh kare baxai ci ba, Ai
shi da auren Jiddah kuma sai kilan ko a lahira idan ana auren, amma dai a nan duniya kam ya gama
aurenta, babu wani abu da xai sake hadata da shi, yaje can ya rungumi matarsa da ya auro jiya" Aunty
Nafisah tace "Aa kar kice haka Hajiya baki san ikon Allah ba..." Umma tace "Wllh wllh kinji rantsuwar
musulmi ko Nafisah? Aliyu have nothing to do with this girl again, Allah xai fiddo mata da dai dai ita wanda
xai ga mutuncinta ba wanda xai dinga da na sanin aurenta ba yana cusguna mata sbda wasu dalilansa mara
tushe" Aunty Nafisah tace "Ai bata yi kama da warce aka cusguna ma ba Hajiya... Dama can shiru shiru ce
yarinyar" Umma tace "Da kika xo kika ganta da kyan gani ba, karewa ma tun ranan da suka tare ya saketa,
sakin walakanci, sannan ya ajiyeta a gidan sbda shi isasshe ne, yayi ta wahal da yar mutane kamar wani ya
aikesa ya aurota tun farko, kawai ki bari Nafisah amma babu wani abu da xai sake hadata da Aliyu da izinin
Allah, ba dai wajena take ba" Tsit Umma tayi duk suna kallon Abuturrab da ya fito daga dakin Ahmad...
kananun kaya ne jikinsa hannunsa rike da phones dinsa, ya karaso cikin parlon ya xauna kafin yace komai
Umma tace "Waye wannan???" Ya d'an kalleta sai kuma yyi murmushi yace "Ina kwana Umma" Kin
amsawa tayi tana kallonsa with surprise, ya kalli Aunty Nafisah ita ma ya gaisheta, da mamaki tace "Yaushe
ka shigo gidan nan Aliyu??" Yace "Daxu..." Umma tace "Ita kuma Amaryar fa?" Yace "Suna can da
kawayenta" Umma tace "Da sassafe ka baro gidan kenan??" Yace "Ehh" Aunty Nafisah tace "Ikon Allah, to
amma har yanxu ana yayin kawayen amarya su kwana gidan amarya ni Nafisah?? na xata an daina wannan
jahilcin tuntuni ai..." Umma tace "Atoh nima shi na gani, da nayi magana Hafsah kirjin bikin ce min tayi ai
Amaryar sun yi magana da Aliyun kuma ya amince kawayenta su kwana tun ma ba a kawota ba, dalilin da
yasa na kama bakina nayi shiru kenan bana son tashin hankali, shi yasa da su Maimoon suka ce xasu kwana
gidan nima bance komai ba, a raina nace kowa ma ya kwana tunda haka ne" Abuturrab dai kallon Umma
kawai yake don basu yi haka da Aneesah ba, Aunty Nafisah tace "Aa gaskiya wannan ba yi bane kuma bai
kamata ba, Allah kuma ya kyauta" Umma tace "Ameen dai, kayi breakfast dai koh?" Yace "Eh nayi..." tace
"A can gidan aka kai maku?" Yace "Aa a nan nayi" Umma ta kalli kitchen sannan ta kallesa da mamaki tace
"A ina ka ga breakfast din, mu yan gidan ma yanxu muka tashi ai" Ya shafa kansa yace "Aa ta kawo min..."
Aunty Nafisah da Umma duk suka kalli kitchen din, dai dai nan Jiddah ta fito, Aunty Nafisah tace "Jiddar ce
ta kawo maka kenan" Yace "Ehh" Umma dai bata sake cewa komai ba ta ci gaba da kallon tv abunta. Ana
kiran azahar Jiddah na kitchen tana gyara kayan miya da xata yi blending tayi stew, Aunty Nafisah da
Umma kuma na can daki aka bude kofar kitchen din, da sauri ta juya ya shigo ciki ya kulle kofar, jikin
cabinet ya jingina ya rungume hannunsa yana kallonta, Tana ci gaba da gyara kayan miyan da take tace
"Akwai abinda xa a baka ne?" Yace "Aa.." Ta d'an kallesa sannan ta ci gaba da aikinta yace "Ajiye aikin nan
ki saurari maganar da xan maki" Ba musu ta ajiye wukar hannunta ta wanke hannunta a sink sannan ta
juyo tana kallonsa, bai yarda sun hada ido ba, yace "Instructions uku xuwa hudu xan baki" Ita dai bata ce
komai ba tana ta kallonsa, yace "Na farko cikin instructions din shine ni bana son kina gaisheni a duk inda
xaki gan ni... na biyu kuma duk sanda kike da bukatan wani abu ko wani iri ne ki dau wayar Maimoon kiyi
min text ba sai kin gaya ma Umma ko wani ba, that is my responsibility, na uku kuma duk sanda su Umma
xa su je can gidan mu you look for excuse da xai sa baxa ki bi su ba, kafin in baki instruction din karshe ina
son ki fara gaya min shekarunki" Jin tayi shiru ya hade rai yace "Magana nake maki, shekarunki nawa??" a
hankali tace "Baabarmu tace sha bakwai" Yace "Ohk, akwai wani da yace maki kin isa ki dinga xama kin
hira da maxa ne?" Tayi shiru tana kallonsa, yace "To instruction din karshe kenan babu ruwanki da wani
namiji koma waye shi, idan kuma aure kike so sai ki gaya min in ji, i will settle that" Tace "To amma kuma
ae kace min kar in sake nuna ma na sanka, kuma yanxu gashi kana...." Katse ta yayi yace "Ae shi yasa nace
ki daina gaisheni, kinga ae wanda baka sani bane baka gaishesa" tace "To kuma ai baxa ka so ka tambayi
wanda baka sani ba yayi maka wani abun kuma..." Kallonta ya dinga yi da mamaki, tace "Tunda ban sanka
ba ni baxan tambayeka ka min komai ba" yace "Amma ai ban sanki ba a lkcn da na taimakeki a hayin
rigasa, why didn't u turn down d offer" ta d'an yi murmushi tace "Aa ka san ni mana, ai awara nake yi
sannan kuma kana xuwa siya, kaga ai ka san ni..." Yace "To bari ki ji in gaya maki abinda baki sani ba, duk
wani responsibilities dinki har gobe a kaina yake sbda wani dalili da ban...." Bude kofar kitchen din aka yi
duk suka juya, ya fasa karasa abinda xai fada, Umma ta shigo kitchen din, ko kallonsu bata yi ba ta dau
abinda xata dauka ta fita, Abuturrab ya kalli Jiddah yace "Na gama gaya maki abinda xan gaya maki" Daga
haka ya juya ya fice daga kitchen din ta bi sa da kallo. Makullin motarsa ya dauka a dakin Ahmad ya fita ya
bar gidan bai sallami kowa ba... Umma ce xaune daki inda take shiga ba nan take fita ba tana kallon Jiddah
dake durkushe saman carpet ta sunkuyar da kanta ta kasa cewa komai duk jikinta yayi sanyi, Umma tace
"To idan har baxan dinga gaya maki ki ji ba to xa a fara jin kanmu wllh, ina ruwanki da shi da har xaki ma
tsaya ki sauraresa daga farko? Meye hadin ki da shi??" Cikin sanyin murya tace "Umma kiyi hakuri baxan
sake ba in sha Allah" Ita dai Aunty Nafisah na tsaye jikin mirror tana kallonsu, Umma tace "Ke duk cin
mutuncin da ya maki har kin mance da xaki sauraresa idan ba wauta da rashin sanin ciwon kai irin naki
ba??" Jiddah ta girgixa mata kai kawai, Umma tace "Toh tashi ki fita, shi kuma xan ga uban da xai sake
dawowa da shi gidan nan ai..." Mikewa Jiddah tayi ta fita, sai da ta kulle kofar Aunty Nafisah tace "Hajiya ni
ban ga wani aibu ba don yayi magana da ita, ba fa rabuwar tijara ko rashin mutunci suka yi ba,, assuming
he meant any harm toward her da tun farko bai shiga rayuwarta da xummar taimaka mata ba har ma
iyayensa su santa, kawai dai abubuwa sun faru ne yanda Allah ya tsara amma kar kice xaki raba
xumuncinsu...." Umma tace "Ni fa bance ta masa rashin kunya ko taki girmama sa ba Nafisah, kawai so
nake ta rike maraicinta tayi abinda ke gabanta wato karatu, ganin cewar ita ba class dinsa bane yasa yayi
mata duk abinda ya mata ba wani abu ba, ba gashi dai yanxu ya auri class din tasa ba, to a kan me xa ta ci
gaba da sauraronsa?" Aunty Nafisah tace "Toh Allah ya kyauta" Umma tace "Ameen" Aneesah na xaune
parlor tare da kawayenta uku dake ta shirye shiryen tafiya, duk sun cika parlon da surutu ita dai bin su
kawai take da um um, amma tayi nisa tunanin da take, duk da how moody she is throughout d day bata
yarda kawayenta sun lura ba, bude kofar parlon aka yi duk suka daga kai, Abuturrab ya shigo da sallama da
shi kadai yaji kayansa, kallonsa Aneesah ta dinga yi babu ko kiftawa, ya karasa cikin parlon yana kallonsu
Fauziyya with smile on his face yace "Kun yini lafiya" Fauziyya tace "Lafiya lau ango, jiya kuma sai muka ji
ku shiru shiru kai da abokanka..." Abuturrab yace "Ohh yeah, toh kun ki bar min mata ku tafi, and all my
frnds that are suppose to escort me sun koma saboda aiki, shi yasa nace to bari dai nasan xuwa yau xa ku
tafi ku bar min amaryata, na daga kafa jiya, amma ashe i am mistaken kuna nan dai" Dariya duk suka yi
banda Aneesah da ta kauda kanta imagining how to punish him, Fauziyya tace "Da ka kwantar da
hankalinka ma yanxu shiryawa muke xa mu wuce in sha Allahu" Yyi murmushi yace "Toh ba sai na haura
sama ba kenan bari in jira ku a mota, sai in ajiye ku train station...." Naja tace "Mun ko gode Captain" Ya
d'an saci kallon Aneesah suka hada ido ya kashe mata one eye, ta wani sha kunu, ya juya ya fita parlon, har
bakin motarsa ta raka kawayen nata da jakunkunan kayansu, a kan kafada ta yafa gyalen yyi mata kallo
daya ya kauda kai duk kawayenta suka shiga motar suka sallami juna sannan ya kalleta sai na dawo, bata
tanka sa ba ta shige gate din gidan, ya ja motarsa ya wuce. Aneesah na komawa ciki ta haura sama ta shiga
parlonsa ta dau wayarta ta kira Aunty, aunty na dagawa tace "Ya dawo?" Tace "Ehh yanxu ya shigo, amma
ya tafi kai su Fauziyya tashan jirgin kasa" Aunty tace "Toh kar ki wani nuna masa komai, kiyi kamar abinda
yayi jiya bai baki haushi ba kinji, kiyi hakuri... Sannan ki kula duk yanda Safara'u ta ce maki haka xaki yi
anjima kada ki yarda mistake ya shiga..." Aneesah tayi kasa da murya tace "Amma Aunty he is so smart kin
sani" Aunty tace "Smart din banxa, ke dai kiyi abinda aka ce maki kawai" tace "Toh shkkn" Aunty tace
"Yanxu dai kawai muyi waya gobe" Aneesah tace "Allah ya kai mu" Daga haka ta katse wayar, shiru tayi
tana naxari iri iri a ranta, can tayi murmushi ta mike ta shiga daki. Abuturrab na ajiye su a train station din
rigasa ya ciro dubu ashirin din da yayi withdraw kafin ya je gida ya mika masu, nan kuma yayi masu sallama
yayi wucewarsa ba tare da ya damu yasan ko akwai jirgin ko babu ba, a ransa yace idan ma babu sai su
wuce park, a hankali yake driving ya shiga d'an layin wanda ke shimfide da kwalta, dai dai layin gidan mai
anguwa ya samu waje yayi parking sannan ya sauka ya karasa layin da kafarsa, saman tabarman dake kofar
gidan ya xauna bayan ya gaisa da dattijan da suka wayesa a wajen, yana jiran mai anguwan da aka ce masa
ya shiga gida ya fito yanxu, wani dattijo yace "Ya iyalin naka?" Abuturrab yace "Lafiya lau Alhmdlh" Dattijon
yace "Madallah, Allah ya maka albarka" Abuturrab ya sunkui da kansa yace "Ameen" ba a dau lkci ba mai
anguwan ya fito, ganin Abuturrab yace "Ikon Allah, sannu da xuwa Malam Ali" Abuturrab ya gaishesa da
ladabi bayan ya xauna, mai anguwa yace "Ya kaje gida ranan? Nayi ta kiran layinka baya shiga kuwa"
Abuturrab yace "Allah sarki, Ina jin na kashe wayar ne" Mai anguwa yace "Toh madallah, ya aiki fa...."
Abuturrab yace "Aiki Alhmdlh, Dama na xo tasha ne shine nace bari in karaso mu gaisa" Mai anguwa yace
"Ai ko mun gode Malam Ali, ya iyalin taka dai?" Yace "Lafiya lau" Mai anguwa yace "Toh Allah ya kauda
fitina, ya ci gaba sa baku xaman lafiya" Abuturrab ya amsa da "Ameen" sannan ya ciro kudi aljihunsa ya
ajiye nan gabansa yace "Toh xan koma in sha Allah, sai kuma wani lkcn" Mai anguwa ya rike ha6a yace
"Baka gajiya Malam Ali??"
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
*EXCLUSIVE FABRICS &MORE* provides you with exclusive, and Affordable fabrics such as laces,
Ankara,materials shoes,bags and so much more on wholesale and retail EXQUISITE, AND AFFORDABLE
THANK U
LOCATION: LAGOS
*EXCLUSIVE_FABRICS_AND_MORE* Na siyar da kaya kamar Laces, Atampopi, Materials, Jewelleries,👡👠👜👛
da dai sauran su
Tana maraba da masu siyan daya koh sari
Location : Lagos
Tana aika kaya duk inda kake da yardan Allah
09080058848
Abuturrab yyi parking kofar gidansu ya kashe motarsa ya sauka, suka gaisa da Mai gadi sannan ya shiga
cikin gidan, bbu kowa parlon duk yan biki sun watse, ya wuce dakin Hajja ya bude kofar ganin Mahaifiyar
El-Basheer xaune dakin ya sa shi yin sallama, Hajja dai kallo daya tayi masa ta ci gaba da xancenta tana
cewa "Wllh baki ganta ba, babu sa wa babu hanawa, don dai kawai ni ina komai cikin sirri ne banda haka
da har sunan yarinyar sai in fada maki ynxu, kuma ni ba abinda yasa na kara samun kwarin gwiwa sai ganin
yanda Bashir din yayi na'am da xancen nawa, wllh ko musu d'an arxikin bai yi ba, da dai su o'o ne har
ubana dake rami sai ya xaga, shi sa kika ga nayi ta ja baya da bikin nan ba ruwana aje a kunyata ma yarana
ni a banxa, ai xamana Masar ya koya min iya xaman duniya, nasan yanda xan xauna da ko wani gantallale
lafiya babu me jin kanmu" Murmushi kawai Hajiya Safinah mahaifiyar El-Basheer ke yi, Abuturrab ya
karaso ya xauna kasa yace "Ina yini Mummy?" Da fara'arta tace "Lafiya lau Captain, yanxu muka dawo daga
can gidan naka ai tare da Hajiya Hafsah, amaryar taka tace mana kaje kai kawayenta tasha ko?" Yace "Ehh"
tace "Toh maa sha Allah, Allah ya bada xaman lafiya, ya kauda fitina tsakaninku" Yayi kasa da kai yace
"Ameen" Sai a sannan ya kalli Hajja yace "Ina yini" Da sauri tace "Aa, ka dai gane ma idonka, lafiya lau na
wuni wllh" Ya mata wani kallo ta gefen ido, Hajja tace "Kina ji na Safinah" Mummy tace