Showing 312001 words to 315000 words out of 321711 words

Chapter 105 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt

in sha Allah, xa ku yi xumunci" Godiya Hansai ta dinga yi
ma Umma kamar xata ari baki, Umma ta bude jakarta ta ciro dubu biyar tace "Kiyi hakuri da wannan sai
mun sake dawowa, duk da gobe ko jibi xa mu xo din tare da Jiddah ta yi maki gaisuwar yar uwarta in sha
Allah" Har bakin mota Hansai ta raka Umma duk jikinta a sanyaye, har ranta take son rayuwa tare da
Jiddah gatan da bata gwada mata ba tun ubanta na da rai har ya rasu tana son ta gwada mata yanxu duk
da bata da komai, so take kawai ta ja ta a jiki tamkar bibalonta, tana ganin Abuturrab ta duka tana
gaishesa, ya amsa a takaice ya xaga ya shiga driver seat ta bi sa da ido, Umma ta bude gaba ta xauna tana
daga ma Hansai hannu har suka bar anguwar, sosai taji tausayin matar, lallai kam ita taga kamun Allah tun
a duniya. Suna komawa gida da hoton Abban Jiddah Hajja tace Inaaa ai hoton baxai kwana ba aje a nuna
ma mijin Hajiya Fatima kawai, haka suka shirya da ita da Umma, da Jiddah da Abuturrab xuwa gidan Hajiya
Fatima bayan isha.....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp


Tun da suka shiga compound din gidan Hajiya Fatima Hajja ke washe baki tace "Toh kun ga dai, ai basu
wani nuna su masu kudi bane da suka je can gida duba Jiddah, to haka ake son mutum wanda bai da burga
ko fafa, kuma da irinsu ya kamata ayi xumunci, naji dadin yanda suka tsaya kan jiddah har ta ji sauki, ji
yanda babbar er nan tata me mota ta dinga kula da Jiddah a asibiti tana nan nan da ita, to kuwa idan ma
ku baxa ku yi xumunci da su ba ni dai xan yi" Abuturrab dake ta kallonta yace "An ce maki suna xumunci da
mutan Masar ne?" Hajja ta juya da sauri baki bude ta kallesa tace "Meye da Masar din?" Bai sake tanka ta
ba har suka shiga parlon Hajiya Fatima, sosai Hajiya Fatima tayi welcoming dinsu ta kawo masu fruits iri iri
a tray da bottle water ta ajiye masu, Hajja sai wani murmushi take tana kallonta tace "Kinga yanda kika yi
din nan? Wllh haka suke yi a Masar.... Kya ga kayan marmari iri iri a tray an ajiye ma baki, ko jarkan madara
da cinyoyin kaji" Hajiya Fatima tace "Ikon Allah..." Hajja tace "Wllh, kin san daga Masar nake, daga xuwa
bikin jikana shine na rashe a Najeriya, suna can suna ta kewana kullum sai sun kirani kira me motsi ta waya
mun gaisa" Hajiya Fatima tace "Allah sarki, da kawai kiyi xamanki tunda kin dawo Baaba" Hajja tace "Inaaa
xan iya kirga maki sau nawa na ci kaza tun Dawowata kasar nan, can kuwa gasu nan baja baja har sai ka
ture, ke dai kawai ayi harka er nan" Hajiya Fatima ta dinga murmushi, Umma ta kalli agogo tace "Hajiya sai
kika gan mu da daddare ba notice" Hajja ta amshe tace "Wllh kuwa ni na takura a taho ko min dare don ba
a wasa da lamari me muhimmanci irin wannan, na lura in dan ta su ne sai dai a shashantar da xancen a
hau wata sabgar can, kinga kenan yarinya bata da makubuli, sannan idan aka samo danginta ai babu
wanda xai ta gadara da ita babu gaira ba dalili, to in gaya maki shine na basu shawaran aje duk inda matar
uban Jiddah take a amso hotunan uban nata sai mu taho mu nuna maki, amma dai ina shi mai gidan naki
yake tukun?" Hajiya Fatima tace "Yana sama Hajiya" Hajja ta kalli Umma tace "Mika mata hotunan ta gani,
idan mu bamu san fuskar mijinta ba ai ita ta sani" Umma ta xuge zip din jaka ta ciro hotunan Baban Jiddah,
Hajiya Fatima ta taso ta amsa tana kallo with much interest, waje ta nema ta xauna ba tare da ta shirya yin
hakan ba tana ta maimaita kallon hotunan guda hudu dake hannunta babu ko kiftawa, Hajja tace "Toh
kinyi shiru, gaya mana ai xaki yi ko yana kama da mijin ki ko baya yi" Hajiya Fatima ta dago ta kalli Hajja,
tayi shirun kusan 5 seconds sai kuma ta sauke ajiyar xuciya tace "Bari in kai masa Hajja...." Daga haka ta
mike ta wuce sama, Hajja ta gyara xama tayi kasa da murya tace "Da kyar idan ba mijin ne baban Jiddan
ba, kawai dai yayi guduwansa ya dawo cikin gari yayi aurensa sbda wahalan duniya ya ishesa, ita kuma ina
jin mijinta ya mutu ya bar ta da narka narkan 'ya ya da uban dukiya" Abuturrab ya dakatar da ita so pissed
off yace "Menene haka don Allah?" Hajja tace "Aa kar ka min tsawa daga na fadi gaskiya xaka hayayyako
min, ko kai baka ga yanda jikinta yayi sanyi qlau ba? Ai taga mijin nata ne a hoton, nan kuma bata san ya
ta6a aure har da ya ya ba..." Umma tace "Kin ga mu ba abinda ya kawo mu gidan nan ba kenan Hajja, ya
xaki dinga irin wannan maganganun a gidan mutane?" Hajja tace "Toh ba sai in ji duka ba, daga fadan
gaskiya sai ai min caaa, ko gabanta ance maku baxan fada hakan ba tunda ba tsoron wani d'an banxa nake
ba" Ita dai Jiddah ta kasa dago kanta, Abuturrab yace "Umma wai wa yace ta biyo mu ne?" Hajja tace
"Uwarka Ramlah tace in biyoku don bana xagi Hauwa ko Usman ba tunda basu min komai ba..." Saukowan
Alhaji Ishaq da Hajiya Fatima ya sa Hajja tayi shiru, Ya karaso parlon ya gaida Hajja, Abuturrab ya gaishesa,
sannan suka gaisa da Umma, ya xauna a one sitter yana kallon Jiddah da ta ki dago kanta gabanta na
faduwa yace "Ya jikin naki?" Jiddah ta dago da kyar lokaci daya hawaye ya kawo idonta jin muryar tasa
kamar Abbanta ne yayi magana, cikin sanyin murya tace "Na ji sauki" Yace "Allah ya kara afuwa" Hajja tace
"Ameen dai, ka dai ga hotunan da aka kai maka, ince kai ne a jikin hoton ko?" Ya girgixa kai yace "Ba ni
bane Hajiya, amma nasan ina da alaka da koma waye a hoton, nasan wanda ke jikin hoton nan jinina ne..."
Hajja tace "Yo ai ya rasu aka ce tun tale tale, ga er tasa dai can a xaune...." Alhaji Ishaq ya kara kallon
Jiddah yace "Ya sunan baban naki?" A hankali Jiddah tace "Yusuf" Alhaji Ishaq ya jinginar da kansa da
kujera yayi shiru, sai kuma ya kalli Hajiya Fatima bayan few seconds yace "Ina khaleesat?" Mikewa Hajiya
Fatima wanda kana ganinta kasan gaba daya a sanyaye take ta tafi dakin khaleesat, sai ga su sun dawo tare,
Hajja na ganin Khaleesat ta bude baki tace "Lahhh kaga wllh suna yanayi da Jiddan er kace wannan din?"
Yace "Ya ta ce, don a shekaranjiya da na shigo parlon ma nayi tunanin wannan ce a xaune" Hajja ta saki
salati tace "Ikon Allah ya fi gaban haka, toh yanxu kai baka da wani d'an uwa da ya 6ata ko ya shiga duniya
shekaru aru aru ba a gansa" Alhaji Ishaq ya d'an yi murmushi yace "Ina dai neman Alfarma a bamu ita
wannan yarinya mu tafi can garinmu gun mahaifiyata da ita, xa aji komai daga bakin ita mahaifiyar tawa
idan munje" Hajja tace "Yanxu mahaifiyarka na nan da ranta?" Yace "Tana nan Hajiya" Hajja tace "Huhuhu,
to ko gobe kace mu tafi ba sai mu tafi ba d'an nan, idan ya so a bamu daki kawai mu kwana a nan gidan"
Umma ta kalli Hajja haka ma Abuturrab, Hajiya Fatima tayi murmushi tace "An baku Baaba, Allah ya kai mu
goben lfya" Umma ta d'an yi murmushi tace "Amma da dai a bari jikinta ya d'an kara kwari ko xuwa jibi ina
ga xai fi ko..." Hajja ta kalleta da sauri, sai kuma tace "Toh ai ba wasan yara bane wannan da xa a bari har
jibi Ramlah, yanxu dai ki tashi Aliyu ya maida ku gida ni da Jiddah mu kwana nan din kin ji dai an bamu
daki, idan ya so idan kinga xa aje garin dake tunda ke ce uwar rikonta sai ki fito da sassafe ki riske mu
sannan a kama hanya, amma ba batun da xa a bari har jibi bane wannan kinji Ramlah" Abuturrab ya dinga
kallon Hajja kamar ya shaketa, Umma tace "Allah ya kai mu goben, Hajiya bari mu kama hanya dare na yi"
Hajja na kallon Aliyu tace "Sai ka amshi makullin daki na wajen Hauwa ka debo min kayana kala biyar, ita
ma Jiddah ka bamu makulli mu bude gidanka mu shiga ta debi kayanta" daga haka ta mike tana kallon
Jiddah tace "Tashi mu tafi sama a nuna mana dakin, Allah ya kai mu goben lafiya" Hajiya Fatima ta mike
tana murmushi tace "Mu je a kai ku dakin" Jiddah sai kallon Abuturrab da ya hade rai take, Hajja tace "Toh
ki taso mana ina maki magana" Tashi tayi a hankali ta bi bayansu Hajja, Alhaji Ishaq dai murmushi kawai
yake, Umma ta mike tace "Toh Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya Alhaji, sai da safe" Yace "Ameen,
Allah ya tashe mu lafiya, mun gode kwarai" Abuturrab ma yayi masa sallama sannan suka fita da Umma.
Bayan Hajja ta ci tayi nakk wajen karfe sha daya, tana xaune kan katon gadon dake dakin da aka basu daga
kasa kuma shinkafa ne da miya da coslow ga soyayyen kaji sai farfesun kifi da aka masu sharp sharp, tana
kallon Jiddah da duk bata da walwala tayi kasa da murya tace "Ke baki ga wani kankanban da Ramlah keyi
a gaban shi me kama da baban nan naki ba, to ko sonsa ta ji ta fara yi wa ya sani, kinsan mijinta xai shekara
goma sha daya da rasuwa kuma ta ki aure, to idan ba sonsa take ba meye na wani make murya tace a bari
sai jibi aje garin, ina ruwanta?? Wllh ban ta6a ganin haka ba tunda aka haifeni, idan ma sonsa take matar
gidan nan dai ta fi karfinta" Murmushi kawai Jiddah tayi Hajja ta gyara kwanciya tace "Atoh, ni ba ruwana
wllh" Washegari karfe takwas Alhaji Ishaq suka dau hanyar garin gombe, Ali ne ke driving din Abban nasa
na xaune kujera me xaman banxa, Hajja da Jiddah sai Hajiya Fatima na xaune back seat.... Da yamma suka
iso cikin garin gombe, Ali yayi parking a kofar gidan kakarsa, shi da Abbansa suka shiga masallaci yin sallan
La'asar Hajiya Fatima tayi leading din su Hajja xuwa cikin gidan har parlon Hajiya Dada warce ita ce
mahaifiyar Alhaji Ishaq, Hajiya Dada ta dinga masu sannu da xuwa baxa ka ta6a cewa ta kusa dari ba don
da sauran kwarinta, sauran yaran nata duk suna gidan suna jiran isowar Alhaji Ishaq, wanda shine babban
yayansu, su ma dai suka dinga welcoming dinsu... Bayan kusan minti ashirin Alhaji Ishaq ya shigo ciki tare
da Ali don sai da ya tsaya gaisawa da 'yan anguwan da suka dinga kawo masa gaisuwa wanda hakan kadai
xai sa ka fahimci yana siyasa ne. Hajja na kallon Jiddah bayan ta idar da sallah ta rike ha6a tace "Ke kiga
kantamemen gidan da suka gina ma tsohuwar nan kamar baxata mutu ba..." Jin Jiddah bata tanka ta ba ta
kyabe baki ta jawo warmers da aka tula masu a dakin, Hajiya Fatima ce ta shigo duk tayi serving dinsu
abincin sannan ta fita, Hajja ta kara rike ha6a tace "Lallai manyan mutane ne, sai kace ina gidan kabiru don
ma dai wahala bai isheni ba ai da babu uban da xai sa in bar gidan Kabiru yanda kika ga haka fa haka ake
min a fadar nan ta Bauchi, to amma ni din ce wahalalliya inyi ta rabe rabe a kaduna ana hantara ta" Wajen
karfe biyar Hajiya Fatima ta yi ma Hajja da Jiddah iso xuwa babban parlon Hajiya Dada, yaranta biyar a
duniya kuma duk suna xaune parlon, maxa biyu mata uku, ko wannensu kana gani kasan nera ta xauna ne
kawai, Jiddah ta sunkuyar da kanta bayan ta gaishesu gaba daya, su kuma suka dinga gaida Hajja ana
tambayarta ya gajiyan hanya, bayan an gama gaishe gaishe Alhaji Ishaq ya mike ya isa gun mahaifiyarsu ya
durkusa ya mika mata hotunan hannunsa yace "Dada kin gane waye wannan a hoton nan?" Hajiya Dada ta
dau gilashinta ta saka tana kallon hotunan da kyau, wani murmushin takaici tayi tace "Wannan ai Yusif dina
ne, bana ce maku yana nan raye ba babu wanda yake yarda dani ana ganin kamar xaucewa nayi, nasan
yusif bai mutu ba, to ina yake yanxu? A ina yake?" Hajja ta daga hannu tace "Aa mu dai ya rasu kusan
shekaru biyar kenan, sai dai ga er cikinsa nan a kusa da ni..." Hajiya Dada tayi shiru tana kallon Jiddah, sai
ta fashe da kuka tana girgixa kai, duk kowa yayi shiru a parlon, a hankali ta fara magana tace "A shekaru
kusan hamsin da suka wuce a kasar nan ina jin babu wanda ya kai mu shiga tsananin rayuwa da rashi da
muke ciki da ni da mai gidana da abokiyar xamana, mai gidan namu ba shi da komai sai gona daya tak shi
ma gadon mahaifinsa ne da ya ci, Yusuf shine d'a na na uku, ita kuma kishiyata Kulu a lkcn tana da ya ya
biyu ita ma duk maza, duk da rashi irin na mai gidanmu Malam Sunusi haka ya dau son duniya ya daura ma
Yusif don duk cikin yaran nasa ma ya fi kama da shi, babu abinda ya raga ma Yusif komai yi masa yake toh
ashe hakan na kona ma ita kishiyata kulu rai ni duk ban sani ba, mai gidanmu ya sha siyan karamin dabba
idan ya d'an samu kudi ya kawo gida yace a kiwata ma yusif, komai na gidan nan yace yusif, kwatsam
watarana muka wayi gari babu Yusif babu dalilinsa a cikin gida, neman duniya dai a garin nan na gombe
anyi amma ba a ga yusif ba, a lkcn yana da shekaru 4 kacal a duniya, na shiga tashin hankali da baya
faduwa yanxu haka, wato mahaifinsa ma ya fi ni shiga tashin hankalin, ita kanta kishiyar tawa kullum cikin
tayani kuka take, amma ya muka iya da wannan kaddara? Bayan shekaru biyu babu wani labari na ganin
yarona muka tabbatar baxa mu sake ganin Yusif ba ya 6ata ne na har abada, amma ni dai ban cire rai ba
kullum addu'a nake Allah ya bayyana min shi, kusan duk dare sai nayi kukan 6atan yusif dina, bayan
shekara 49 da 6atan Yusif wato ina maganan shekaru biyu da suka wuce kenan, bayan shi mahaifin Yusif ya
ma rasu da kusan shekara goma kenN, Kishiyata Kulu ta dinga ciwo kamar dai ba na tashi ba, tun bayan
haihuwar nan nata biyu dama kuma bata sake haihuwa ba, daya yaron nata rasu, dayan kuwa na garin
Legas ko waiwayarta baya yi shekaranmu takwas kenan rabonmu da shi, komai dai na bukatar yau da
kullum da ku ka sani kai hatta gidan da take ciki 'ya yana suka siya mata tunda Allah ya hore masu, tana dai
cikin rufin asiri amma ciwo dai ya ki ci ya ki cinyewa, wai sai ana gobe Kulu xata mutu naje dubata da yake
kullum sai an kai ni gidan a mota, shine take rokona gafara tana kuka, nace gafarar me kuma kulu, me kika
min, nace mata ni baki min komai ba wllh kulu, lafiya muka xauna dake har xuwa yanxu... Hajiya Dada ta
fashe da kuka tana girgixa kai tace "Wai a nan Kulu ke ce min ai ita ta ba ma kaninta Saleh Yusif ya kai sa
garin kano kawai ya bar shi a kan hanya sbda kawai Malam Sanusi na yawan yi masa waka yana cewa ya
mallaka masa gonarsa kwaya daya tak... Toh a daren ranan Kulu ta rasu, ni kuwa ya xan yi? Nace na yafe
mata, a nan take kuma na sa yan uwan Yusif a buga gidan jaridu a kai labarin gidan radio har ma da
talabijin ko Allah xai sa Yusif ya ji ya nemo mu, amma shiru kake ji, har snn kuma ina ji a raina Yusif bai
mutu ba, ashe ma rai yayi halinsa...." kuka take sosai, Hajja tayi tagumi tace "Amma Allah ya tsine ma
wannan mata kulu, Allah ya kara mata nauyin kasa, Allah ya matse kabarinta" Cikin Kuka Dada tace "Aa na
yafe mata wllh, dena fadar haka na yafe mata" Hajja ta bude baki tace "Tabdi, yanxu ashe uban Jiddah da
gatansa yayi ta galantoyi tun yana karami a kaduna, to kuwa wllh da yasan da wnn labari da kyar idan ya sa
ma Jiddah wannan sunan da ya sa mata, don ita ma kulun ce ai, da yasan matar ubansa ce ta gantalar da
rayuwarsa wllh baxai sa ma yar sa kulu, ni har naji na tsani sunan duk da sunan surkata ce dai" Dada na
kallon Jiddah cikin kuka tace "Taho kusa da ni Hauwa..." jiddah ta goge idonta a hankali ta mike ta isa kusa
da kakar tata ta xauna, Hajiya Dada ta rungumeta tana shessheka tace "Ko ba komai ai xan ganki in ji dadi,
ko ba komai xan kalleki in tuna da masoyina Yusif, nayi farin cikin da Allah bai dau raina ba sai da na ga jinin
Yusif" Hajja ta fashe da kuka tace "Allah ka tsine ma wnn mata dai kulu, ko ya xata yi da hakkin da da uwa a
kabari, ashe tun tale tale ake rashin gaskiya a duniya ban sani ba, tirrrr" Hawaye kawai Jiddah ke yi a jikin
Hajiya Dada, Hajiya Fatima ta fi kowa farin ciki a parlon nan, she was so happy Jiddah is closely related to
her Husband, tun da ta ga Jiddah dama ta san da wani abu dake boye a kasa, she just like her for no
reason, xurfin cikin mai gidanta bai sa ya ta6a bata labarin d'an uwansa da ya 6ata shekaru masu yawa da
suka wuce ba, sauran yaran Hajiya Dada sun yi farin ciki sosai su ma da ganin daughter din d'an uwansu da
ya bace shekaru hamsin kenan don su kansu ba wai saninsa suka yi ba sai a labarin mahaifiyarsu da take
yawan yi masu duk sanda ta tuna da shi, Hajiya Dada ta goge idonta tace "Ina mahaifiyarta?" Hajja tace
"Ahau, ance tun tana jaririya uwar ta rasu, a hannun matar uba ta taso tana ta gallaza mata tana bata
tallan awara da doya da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login