Showing 270001 words to 273000 words out of 321711 words

Chapter 91 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt

gari neman masu kawo mana dauki, da yake a Masar haka ake,
kawai fita titi xaka yi ka sanar da abinda ya dameka a kawo maka dauki har cikin gida...." Sai kuma tayi
shiru tayi tagumi, sai kuma tace "Kai ni ban ma son magana wllh, abinda ya dameni ya tsaya min a rai
daban, yanxu me na ma Hafsah jama'a da xata garkame min baki? Me na mata xata ajiye min mummunan
laya da garkamemen kwadon jaraba a jiki don a rufe bakin da nake ma annabina salati? Ba fa abinda nake
sai salatin da zikiri da wannan bakin nawa" sai kuma ta fashe da matsanancin kuka tace "Allah ya isa, Allah
ya isa wllh, to yanxu da Aliyu bai gani ba kurma xan dawo ko bebiye?" Umma dai sai danne dariya take,
Hajja ta rushe da wani kukan takaici tace "Wllh baxan bar xancen nan haka ba sai kace er banxa warce bata
da gata? Allah sai an bi min hakkina ta fadi ma'anar layar nan da kwado da ta bar min a daki, so tayi in
dawo kamar Hauwa babu uhm babu um um ko kuwa? Wlh abun ya gigita ni, sannan ban gaya maku ba har
da wani farfesu ta kawo min da yake Allah bai yi ni me kwadayi ba nasa aka kai kwararo aka juye shege, to
da na ci ya kenan bin ta xan tayi kamar jela a baya koko?" Hajja ta mike tana kuka tace "Tunda uwata ta
haifeni ban ta6a ganin haka ba wllh, yanxu xuwa xanyi kaf in kira 'ya yana da 'ya yan mijina in sanar dasu
wannan abu da ya faru, don a gaskiya idan abu ya sameni ba yarda xa su yi ba..." Hajja ta fyace majina tace
"Sai kuma abu na karshe wannan yarinya Nanisa take ko wa?? To wllh ta fi karfin Aliyu, don idan ta samu
waje xata yi fiye da yin Hafsah a gidan Aliyu, don dama bakinsu daya kuma er kawarta ce duk yan iska ne
masu bin boka da malamai, don haka yanda aka sallami Hafsah to ita ma a sallameta don hada iri da su
bashi da amfani, hada iri da su bala'i ne...." Aneesah ta fashe da matsanancin kuka tace "Don girman Allah
kar a rabani da Aliyu, wllh ina sonsa kuma na dau alkawarin xan xauna lafiya da shi, don Allah ayi min
afuwa kar a rabani da shi, wllh ina sonsa" kuka take sosai, Hajja ta sha kunu tace "Wllh baxa ki xauna da
jikana ba ki kashesa ki kashe matarsa, ke yar banxa ce, ke yar da6a ce, banda d'an da6a wa xai yi abinda
kika yi yau? Inaaa xama da irin ku sai tsinanne" Cikin kuka Aneesah tace "Sharrin Shaidan ne Hajja, don
Allah ku rufa min asiri wllh baxan sake ba kar ku rabani da mijina" Hajja tace "Idan Hafsah tayi ta'amali da
laya to fa wnn wllh har bokan xata iya dinga kawowa cikin gidan tana boyewa don naga idonta ya fi na
Hafsah budewa, kun dai ga abinda Hafsah ta jefa min a daki daxu ban ji ba ban gani ba, wai kar inyi magana
kamar ita ta halitto min bakina, to Allah yatsine mata albarka, in sha Allahu baxata gama da duniya lafiya
ba, wnn bakin nawa da ya tsole mata ido shine ajalinta, bana komai fa sai salati da zikiri amma ta nemi
garkame min baki" Hajja ta nemi waje ta fashe da matsanancin kukan takaici, Umma ce ta dinga bata
hakuri, ta share idonta ta mike tace "Amma duk Usman ne ya ja mana, don da bai auro Hafsah ba baxata
lika ma d'an sa Nanisa ba, don haka wannan yarinya Nanisa ba matar xama bace, kar tayi ma Aliyu fiye da
yanda Hafsah tayi ma Usman, ni dai na baku shawara xanje in kwanta in nutsu ko xan gano dalilin wannan
laya da kwado da aka bar min a daki" daga haka ta nufi kofa ta fita parlon. Aneesah na kuka cikin rawan
murya tace "Abba don girman Allah ayi min afuwa wllh baxan sake ba, wannan ma sharrin shaidan ne"
Umma sai hararanta take jin yanda ta iya cewa sharrin shaidan, Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "Tashin
hankali da fitina ba shi da amfani Aneesah, yanxu ke abinda kika yi yau kinga kyautuwansa? Riban me kika
ci banda tashin hankali da ji ma kanki ciwo?" Aneesah dai sai girgixa kai take tana hawaye, Abuturrab ya
hade rai don ko muryarta wllh ya ji bai son ji, Ummi tace "Ki tafi ki ba mijin ki hakuri" Tashi tayi ta tafi
gabansa ta durkusa cikin rawan murya tace "Kayi hakuri Captain, na dau alkawarin baxan sake creating
wani problem ba a xaman mu plss pardon me" kin kallonta yayi balle ya bata amsa, Abba ya sauke
boyayyen ajiyar xuciya, nasiha ya shiga yi masu gaba daya su ukun, Ita dai Jiddah kanta na sunkuye, ya dau
kusan 20mins yana nasihar daga karshe ya juya kan Abuturrab yace "And you... Kaji tsoron Allah ka xamo
me adalci a tsakaninsu, that's all i have to say" Abuturrab ya dago kansa a hankali yace "Toh Ummi idan har
tana son xama da ni, dole xan ja mata layi da some set of people, jan layi na har abada, that is only if she
wish to stay with me..." A hankali Aneesah tace "In sha Allah" Yace "Better!!" Ta juya ta kalli Umma sannan
ta koma kusa da ita ta durkusa cikin sanyin murya tace "Umma kiyi hakuri, hakan baxai sake faruwa ba in
sha Allah" Umma tace "Ai ba kayana kika walakanta ba, me kayan xa ki ba hakuri" Ta kalli Jiddah, sunkuyar
da kai tayi kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Kiyi hakuri... ki gafarceni" Jiddah ta girgixa mata kai
kawai don bata ma san me xata ce ba, Ummi tace "Allah ya gafarta mana ga baki daya, Allah ya baku
xaman lafiya dauwamamme, ya kada fitina" cikin sanyin murya Aneesah tace "Ameen"


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




FZ BEAUTY SUPPLEMENTS
Dealer in all kind of dietary supplements such for skin whitening, skin glowing, weight gain, slimming, flat
tummy, infection killers, dark spots removers, fertility booster, Hips boosters, Breast firming and Enlarging,
Teeth whitening, eye, joint, stretch marks, and for marital pleasure. All supplement are available for
wholesale and retail. For more information contact FZ via wa.me/2348143821028

FZ Beauty Supplements
Dealer ce ta supplement masu qara fito da kyaun mace ko namiji, hadi da qarama garkuwar jiki kuzari.
Muna sayarda Supplemnt kamar na qarin duwawu, akwai wanda zaya taimaka wurin dawoda martabar
Nono, akwai na rage qiba da tumbi, akwai na rakwainuwa, akwai na tada komada, akwai masu saka hasken
fata da qyalli, akwai na infection, akwai na saka hasken ido da hakori sannan akwai na gyaran turaka. Muna
maraba da mai sayen daya ko sari. Wa.me/2348143821028



Bayan few seconds Abba ya kalli Umma yace "Furnitures din na nawa aka siya mata?" Umma ta gyara
xama tace "2.3m" Abba yace "Shkkn, xa a san yanda xa ayi, Allah ya rufa asiri" a takaice Umma tace
"Ameen" kallon Jiddah tayi tace "Tashi ki dauko min jakata a parlon Ummi mu tafi, dare na yi Jiddah..." A
hankali Jiddah ta mike ta nufi kofa Abuturrab ya bi ta da kallo, sai kuma ya kalli Umma, bayan fitar Jiddah
da few seconds ya kalli Abba yayi kasa da murya a hankali yace "Allah ya kara girma Abba, mun gode"
Abba yace "Ameen" mikewa yayi ya nufi kofa da sauri, Aneesah ta bi sa da ido har ya fita, sai kuma ta daga
kai ta kalli Ummi cikin sanyin murya tace "Nagode Ummi, Allah ya kara girma" Ummi tayi murmushi tace
"Ameen, sai ayi ta hakuri kuma" mikewa tayi ta fita parlon ita ma, Umma dai ta ta6e baki ta kalli Abba ta ga
Ummi yake kallo.... Jiddah na shiga parlon Ummi ta dau jakar Umma da wayarta dake ajiye saman kujera
xata fito aka bude kofar parlon, ta daga kai da sauri, suna hada ido ta sauke nata idon har ya iso inda take
tsaye, ya jawota kusa da shi yyi wrapping hannunsa daya a bayanta ya dago kanta yana kallonta yayi kasa
da murya yace "How are u feeling now?" Ta dauke kanta tace "Fine" Da damuwa yace "Are u sure? Me kika
ci a gidan Umma daxu? Where u able to eat?" Tace "Na ci" yace "Kina kai mata jakar ki fito mu wuce gida
yanxu" Ta xaro ido tana kallonsa, ya hade rai yace "To bin ta xa ki yi?" Kafin tace komai aka bude kofar
parlon, da sauri ta turasa ta koma baya, Aneesah ta shigo parlon babu ko sallama, kallo daya tayi masu ta
wuce dakin Ummi fuskarta a daure ta kulle kofar, Abuturrab ya bi ta da wani harara, Jiddah dai bata ko
kalleta ba ta bi gefensa xata wuce ya rikota da damuwa yace "Are u serious bin ta xa ki yi Jiddah? Kin ga fa
gobe xan koma aiki" Ta kallesa a hankali tace "Toh ni baxan iya ce mata a'a ba" amsar jakar da wayar yayi a
hannunta yace "Ki tafi dakin Hajja ki jira ni" Bai jira me xata ce ba ya nufi kofa ta kasa cewa komai ta bi sa
da kallo har ya fita, direct parlon Abba ya koma ya shiga da sallama bai bari sun hada ido da Umma ba ya
ajiye mata jakarta da wayarta a gefe kansa a kasa yayi masu sae da safe, daga haka ya fita daga dakin,
Ummi ta bi sa da kallo sae kuma ta mike ta bi bayansa, tana fitowa Main parlor tace "Aliyu" Abuturrab da
har ya nufi dakin Hajja ya juyo yana kallonta sannan ya dawo, tace "Tafiya xa ku yi gidan naka yanxu?" Ya
sunkuyar da kai yace "Eh Ummi" tace "You should be taking them both then" Ya daga kai ya kalli Ummi
amma ya kasa ce mata komai, Ummi tace "Ka tsaya kallona ko da matsala ne?" a hankali ya girgixa mata
kai, tace "Toh sae da safe, sae ayi ta hakuri kuma, Allah ya baku xaman lafiya" ko kadan ransa bai so haka
ba, bai yi niyyar komawa da Aneesah gidansa yau ba, amma babu yanda ya iya, Ummi ta tafi bangarenta to
meet Aneesah, shi kuma ya tafi dakin Hajja, Hajja na xaune tana matsar kwalla a hankali tana kallon Jiddah
tace "Ke tunda aka haifeki kin ta6a gani ko jin haka? Me na mata da ta nemi garkame min bakin da Allah ya
tsaga min? Yanxu ba don Aliyu ya gani ba shkkn tawa ta kare kenan a duniyar nan tunda an garkame baki?
Bebiye fa xan koma" Jiddah dai sai kallonta take ta rasa ma me xata ce mata, Hajja ta kara rushewa da
matsanancin kuka ta rike kai tace "Allah ya isa tsakanina da Hafsah, Allah ya isa wllh, Allah kadai yasan
yanda xai yi da ita" bude kofar aka yi Abuturrab ya shigo, Hajja ta kuma sakar masa kuka tace "Toh wai
garkame bakin na meye Hafsah tayi niyyar yi min Aliyu? Ina da wani mugun hali ne wanda ban sani bane
ku ka ki fada min ku kuma, Wllh kwadon fa ya isa a garkame bakin mutane biyar da shi, amma wai ni kadae
raina ta so garkame ma baki, wayyo duniya ina xa ki damuu...." Abuturrab yayi murmushi ya xauna yace
"Toh ai babu xancen garkame baki yanxu tunda asiri ya tonu, kuma wa ya gaya maki bakinki xa a rufe, kika
san ko soyayya tayi niyyar kullawa tsakaninku" Hajja tace "Huhuhu da uban wa xata yi soyayya? Sai dai tayi
da uwarta dake kabari wllh" Abuturrab ya shafa kansa yace "Mu xa mu tafi sai da safe" Hajja ta sauke ajiyar
xuciya tace "Toh cikin kwalaben xata je ta kwana?" Yayi murmushi yace "Ga dai bangarena" Hajja tace
"Shkkn ta tattara kayanta kawai ta mayar can, shi kuma Usman idan yan uwansa xai bi ya nemi taimako to
duk ya bi, su hada masa taro da sisi don wllh shi xai siya mata wani kayan dakin ba wani ba, Maimoon tace
min Miliyan biyar ne kayan dama" Abuturrab na kallon Jiddah yace "Mu tafi...." Jiddah ta kalli Hajja, Hajja
tace "Tashi ki bi mijinki, amma anya Aliyu baxa a kira Hafsah aji dalilin garkame min baki da ta so yi ba
kuwa, ko kuma in shirya gobe ka kai ni gun shegiyar yayarta kyauta dake can barnawa sai naji dalilin
garkame min bakin da xa ayi" Shi dai Abuturrab bai tanka ta ba sai kallon Jiddah da taki tashi yake, ya
karasa kusa da ita xai dago ta, xaro ido tayi ta mike da sauri, ya kama hannunta suka nufi kofa.... Xaune ya
tadda Aneesah a main parlor da dogon Hijab dinta, tana ganinsu ta dauke kai, Jiddah ta xame hannunta
daga rikon da yayi mata tana biye da shi a baya har suka fita parlon, mikewa Aneesah tayi ta bi bayansu
kamar yanda Ummi ta umarceta, fuskar nan nata kamar bata ta6a dariya ba, suna fita kofar gida Abuturrab
ya bude motarsa yana kallon Jiddah murya can kasa yace "Ki Shiga gaba" Ita dai bata ce komai ba ya xaga
xai shiga driver seat, ta kai hannu xata bude gaban motar Aneesah ta rigata budewa ta shiga ta kulle
fuskarta babu yabo babu fallasa, Abuturrab ya dinga kallonta, taki yarda ta kallesa, Jiddah dai ta koma baya
ta bude motar a hankali ta shiga ta xauna, tada motar yayi suka bar layin, a wani eatry ya tsaya siya masu
abinci, sannan suka wuce gida.... Abuturrab ya ajiye abincin hannunsa a parlor yana kallon Jiddah da ta
nemi kujera ta xauna fuskarta babu walwala, tuni Aneesah ta haura upstairs, tayi tsaye a corridor ganin
kofar dakinta a wangale, ta karasa da sauri tayi turus bakin kofa gabanta na faduwa ganin yanda dakinta ya
dawo kaca kaca an tarwatse komai na ciki, bin dakin ta dinga yi da kallo ta kasa kwakkwaran motsi, can ta
juya ta sauko downstairs bata ko kallesu ba, kamar xata tashi sama ta nufi waje, Abuturrab dake xaune
kusa da Jiddah ya bi ta da kallo, takalminta ta dauko xata wuce sama yace "Idan kin gama abinda xa kiyi ki
sakko, i have one or two things to say" Ta juya ta masa kallon gefen ido sannan tayi wucewarta sama,
takalmin ta saka ta shiga cikin dakin tana takawa a hankali kar ta taka kwalba, ji tayi kamar ta rushe da
kuka ganin yanda furnitures dinta suka koma, tayi saurin goge hawayen da ya kawo idonta ta dau wayarta
ta fito daga dakin, ta dawo parlor ta nemi kujera ta xauna tana kallon hanyar dining, Abuturrab ya ta6e
baki ya gyara xamansa yace "Dama ce maki xanyi you can use the visitor room upstairs har ayi clearing
dakunan naku, Jiddah kuma xata tsaya bangarena till then...." Aneesah ta kallesa da sauri, calmly tace "A
saboda me?" Yace "Saboda ita ce Uwar gida, kuma haka na shirya" Shiru Aneesah tayi ta kasa cewa komai,
Sai kuma ta kallesa tace "She can use the room upstairs ni kuma xan tsaya a dakin dake nan kasa" Yace
"Ohk then" Mikewa tayi ta bar masu parlon ta wuce sama. Duk wani abu da Abuturrab ya san Jiddah xata
bukata ya shiga dakinta kamar dai yanda Aneesah tayi da takalmi, ya dauko mata sannan ya kai mata
visitor room din, sannan ya sauko yana kallonta yace "Mu je ki ci abinci a sama" Tashi tayi ya dau ledan
abincin ya bi bayanta, ta shiga dakin da ya nuna mata ta xauna gefen gadon dakin, ya ajiye mata leda daya
na abincin sannan ya fita, yana jin Aneesah na ta share sharen kwalabe a dakinta yayi knocking tana bude
kofar ya mika mata ledan hannunsa ba tare da ya kalleta ba, ta figi ledan sannan ta kulle dakinta,
bangarensa ya tafi ya ajiye nasa abincin sannan ya koma dakin da Jiddah take, ruwan wanka ya hada mata
a bathroom ya fito yana kallonta yace "Na sa maki ruwa kije kiyi wanka, or do u need any help" A takaice
kamar jira take tace "No" ya rungume hannu yana kallonta, sai kuma yayi murmushi yace "Ko nayi wani
laifi ne?" Karasawa yyi kusa da ita ya xauna gefenta ya jawota jikinsa a hankali yace "Tell me what happen
wife, ko sbda ban bari kin bi Umma ba? To me xaki bi Umma kiyi bayan ga mijin ki?" Ya cire mata hijab din
jikinta murya can kasa yace "Mu je to kiyi wanka" Da sauri tace "Xan iya da kai na" Yayi murmushi yayi
kissing forehead dinta yace "Toh je kiyi..." Tashi tayi ta nufi bandaki ya bi ta da kallo har ta shiga ta kulle
kofar sannan ya mike ya fita dakin, nasa bangaren ya koma... Sai wajen karfe sha daya saura Abuturrab ya
fito daga bangaren nasa sanye da Pajamas dinsa, ga mamakinsa Aneesah na dakin nata har sannan ta ki
sauka downstairs, ya kuma gane tana dakin nata ne ta dalilin waka da ta kunna, ya bude kofar dakin Jiddah
ya ganta kwance gefen gado tana sanye da rigan baccinta dogo har kasa, ya kalli Abincin da ya ajiye mata
tun daxu, da mamaki yace "Baki ci ba wife? Why? Ko baki son shinkafan ne? Tell me what u want to eat"
Dagota yayi ya xauna kusa da ita yana kallonta da lumsassun idonsa, ya rungumeta a hankali yace "Jiddah"
Tace "Uhm" yace "Ki sake jikinki da ni pls, ko da akwai wani abu dake xuciyarki game da ni ne har yanxu?
Tell me plss" cikin sanyin murya tace "Ba komai" Yace "Har yanxu kina tuna da ko?" Ta lumshe idonta tace
"Ehh" yace "Gaya min me kike tunawa..." A hankali tace "Ina tuna...." Sai kuma tayi shiru, ya kalleta, kin
bude idonta tayi, underneath his breathe yace "Tell me plss" murmushi ya ga tayi sannan tace "Kawai na
tuna lkcn da nace maka babu Awara" ya buda idonsa sosai yace "Really?" Tace "Uhm, da kuma lkcn da ka
xo kace.... In yi hakuri" Murmushi kawai yake yana kallon kyakkyawan fuskarta, ya kai bakinsa kunnenta a
hankali yace "Ni kuma ina tuna lkcn da na dinga ganin ki a sararin samaniya a duk sanda nake piloting jirgi,
duk na waiga a sky ke nake gani" ta bude ido a hankali tana kallonsa, Dagota yayi ya dau abincin nata da
bata ci ba ya fita dakin da ita yana rike da hannunta suka tafi bangarensa, a nan parlonsa ya xaunar da ita
ya bude abincin ya dau cokali ya deba ya kai bakinta, ta kai hannu xata amshi cokalin tace "Xan ci da kai
na" Yace "Aa ni xan baki" babu yanda ta iya haka ya dinga 6ata abincin da kansa, sai dai bata ci da yawa ba,
ya kyaleta ta tafi bathroom ta wanke bakinta, kafin ta fito


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login