Showing 210001 words to 213000 words out of 321711 words
bakin ciki ya mayar da shi
gun danginta ya sake aurota a gantale, su ma dai dangin nata matsiyata ne, kawai sun mayar da 'ya kaza
don yaje yyi masu fafan yana tukin jirgin sama, to meye kuma tukin jirgin sama Allah na tuba abinda
matsayinsa da d'an acaba da d'an taxi daya a idon duniya, wato sbda hassada sai ya ga ta yanda yarima zai
aureta ko??" Cije yatsa Hajja tayi sae kuma ta rushe da kuka tace "Wllh mun fi awa biyu da mutumin nan
muna garari a hayin rigasa, katon ya gilla min karya wai an rushe gidansu Jiddah daga karshe ma gaya maka
ne kawai ban yi ba Usman wllh a tsakiyar titi ya yasar dani yyi wucewarsa kamar mara galihu duk na hada
xufa, har ya kai ya kawo mutane suka xata almajira ce idan an xo wucewa sae a mika min ashirin, goma...."
Sosai Hajja take kuka tace "Ni a tarihin duniya ma ban ta6a jin an haifi me hali irin na Aliyu ba, kuma a bisa
dokan Masar duk wanda xai iya aikata abinda ya aikata to xae iya kashe rai babu ko darrr, shi yasa ma ake
garkamesa a gidan gyaran hali, ni dae xan xuba ido kawai in ga hukuncin da xaka dauka a kan wannan d'a
naka Usman, dalilin abun nan da Aliyu ya aikata sae zumunci ya tarwatse ya daidaice ya lalace wllh, don ba
Yarima kadai ba.. hatta mutan Bauchi sae sun kullaci Aliyu, daga nan kuma sae a fara gaba tsakanin Bauchi
da kaduna, to wa xai so haka??" Ta kara fashewa da matsanancin kuka tana kwance ha6ar xaninta tana
salallami, ta mike ta fice daga parlon tace "Tirrrrrr" A karo na farko Abba ya kalli Abuturrab da har sannan
ya ki raising kansa, Abba ya gyara xama speaking calmly yace "Yanxu kai ka tabbatar ka koma an sake daura
maku aure da yarinyar nan Aliyu? Are u very sure about this" Sai a sannan Abuturrab ya daga kansa ya kalli
Abbansa amma ya kasa cewa komai, Abba yace "I'm asking you...." A hankali yace "Ehh Abba" Abba yace
"To da yaushe kaje aka mayar da auren?" Cikin sanyin murya Abuturrab yace "Before i got married to my
recent wife..." Abba ya gyada kai yace "Ohkk that's good, wani sadakin ka kai kenan?" Abuturrab ya
sunkuyar da kansa yace "Ehh" Abba yace "Nawa ka kai?" Abuturrab ya share xufar forehead dinsa yace
"150k" Abba ya gyada kai cike da gamsuwa yace "Ohkk that's fine" Ummi ta rike ha6a tana kallon Aliyu da
abinda ya fi mamaki, Umma kam dariya ma abun ya fara bata sai taji kamar film, hakan yasa bata san
sanda ta dinga murmushi ba tana gyada kai, Mikewa Abba yayi Abuturrab ya bi sa da kallo kamar
idanuwansa xa su fito ganin ya nufi bedroom dinsa, kallon Ummi yayi ya marairaice mata amma ya kasa
cewa komai, gaba daya hankalinsa ya tashi sosai, ita kuwa sai kallonsa take har sannan tana rike da ha6a,
Abba ya fito daga dakinsa rike da paper and pen, Alhaji Lawal ya dakatar da shi yace "Let's talk first Alhaji
Usman" Abba ya ajiye takardan hannunsa gaban Abuturrab kafin yace komai Abuturrab ya hade
hannayensa cikin breaking voice yace "I am sorry Abba, wllh i can't, i can't plsss...." Ai bai jira mai Abba xai
kuma cewa ba ya mike ya fice daga parlon, duk suka bi sa da kallo. Babu yanda Alhaji Lawal bai yi kokarin
ganin yayi convincing Abba yayi hakuri da abinda Abuturrab ya aikata ba, he should calm down before
making any decision... but all his effort prove abortive, har Alhaji Umar ya sa baki don ganin Abba ya janye
wannan kudirin da ya dauka amma Abba ya ki sauraron kowa, kana ganinsa kasan ya hau sama sosai,
Ummi dai sai kallonsa take haka ma Umma dake parlon har sannan, Alhaji Umar yace "Ka fahimce ni Alhaji
Usman ba don muna tsoronsa ya sa xa mu saurara masa ba, akwai abubuwan dubawa da yawa...." Abba ya
dakatar dashi yana girgixa kai yace "Kasan Allah Umar?? Wllh wllh sai ya saketa, wllh baxai xauna da ita ba,
xan nuna masa i birth him...." Yana kai wa nan ya mike ya fice daga parlon......
*Masu neman littafin Jiddatul Khair complete sae ku yi payment ku xo ku sameni da evidence* 👇🏻
Wa.me/+2347087865788
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Abuturrab na bedroom din Umminsa ta shigo, tun da ta gansa ta dauke kai ta tafi gaban mirror tana cire
jewelries dinta, bayan ta gama ta nufi kofa xata fita yyi karfin halin cewa "Ummi" juyowa tayi ta kallesa, ya
sauka kasa on his knees ya hade hannayensa pleadingly yace "Ummi don Allah ki ma Abba magana,
interpose pls, nasan ke baxa ki juya min baya ba, pls don't say no to me Ummi, don girman Allah don't let
him force me do wat will ruin me, baxan iya ba..." Ummi dake ta kallonsa tace "Ikon Allah!! Aliyu lkcn da
kake abubuwan ka kana shawara da ni ne?" Yace "Ummi i don't know how to open up to you about this, i
don't know where to start from, and I don't know how u will take it, idan ban yi hakan da nayi ba i might
ruin my self, don girman Allah kiyi hakuri ki yafe min Ummi, i only did what will favor me till end" Ummi
tayi wani murmushi ta girgixa kai tace "Aliyu kenan, but i am sorry i can't nd won't do anything about this,
wannan batun ya fi karfina coz Abbanka ya dauka da xafi kuma ko na minti daya ban ga laifinsa ba duk
abinda ya aiwatar dai dai ne, he is doing what is right, i see no reason we will birth a child dat will keep on
controlling us" tana kai wa nan ta fice daga dakin, ya bi ta da kallo xuciyarsa na bugawa yana jin wasu
xufan na keto masa a forehead, dafe kansa yyi na kusan minti goma, daga karshe ya mike ko minti daya bai
kara a gidan ba ya fice... Tun da Umma ta koma gida take xaune dakinta ta ma rasa takamaiman tunanin da
xata yi, ita wllh sai take ga kamar a mafarki duk abubuwan nan suke faruwa, lkci lkci take bude baki ta rike
ha6a tana sake imagining da jinjina halin Abuturrab, yanxu komawa yayi ya sake auran yarinyar nan duk ya
maida su shashashai gantalallu, ta ma rasa ko takaici take ji, haushi take ji, ko bakin cikin abinda Abuturrab
ya aikata take, ko a tarihi bata ta6a jin shigen abinda Abuturrab yayi ba, wato yaron nan yayi mugun
rainasu bai daukesu bakin komai ba, baya kuma tsoro ko shakkan kowa, tafe hannu tayi tana salati. Bayan
magrib tana xaune kan darduma hannunta rike da carbi tayi nisa tunanin da take tana kallon Jiddah dake
jera mata goggagun kayanta da me wanki da guga ya kawo a press, to meye manufarsa a kan marainiyar
nan kuma yanxu?? Me yake nufi da su for the second time, wato idan ba a dau kwakkwaran mataki kan
wnn abinda yaje yyi ba sun xama shashashan da gaske kawai, Ko kadan bata ji haushin reaction din Abba
ba this time around kuma she is supporting him 100%, Aliyu xai gane ba shi da wayo.... bude kofar
bedroom din aka yi amma ba duka ba, kuma ba a shigo ba, daga Umma har Jiddah kallon kofar suke, sai
kuma aka yi sallama kasa kasa, still not coming inside the room, Lkci daya Jiddah ta dau muryarsa, kamar
yanda Umma ma ta dau muryan amma sai ta hade rai tace "Waye wannan?" Shigowa dakin yayi kansa a
kasa bayan yyi pushing door din slowly, Umma har ta mance rabon da ya shigo mata daki, Jiddah dai bata
yarda ta kalli kofar ba don kamar kuwa ta san kallonta yake, Umma ta buda hannu da sauri tace "Ya aka yi
xaka shigo min daki babu sallama?" Ya sauke idonsa daga kallon Jiddah ya karasa cikin dakin yana tafiya a
hankali ya xauna nan saman carpet, yyi kasa da murya yace "Ina yini Umma?" As if in a hurry tace "Lafiya
lau, ya aka yi?" Shiru yayi ya sunkuyar da kansa, Jiddah ta bar gyaran da take ta rufe press din ta nufi kofa
ta fita, sannan ta kullo masu kofar. Cikin sanyin murya Abuturrab yace "Umma i know i wronged u all,
kuma ni bani da bakin da xan baku hakuri, coz i don't deserve being forgiven, But Umma i want u all to get
this... A Mistake repeated more than once is a DECISION, No mistake is repeated twice because the second
time it's not longer a mistake but a CHOICE, this is my Decision and my Choice Umma" Ya hade Palm dinsa
gathering much courage yace "This shouldn't be used against me plss, ku yi hakuri ku sassauta min, I don't
have the strength to bear being denied my Choice, kuyi hakuri don Allah Umma..." Umma da ke ta masa
kallon mamaki ta dakatar da shi tace "Ur Decision and Choice?? Lokacin da kayi watsi da namu decision din
mun hakura ko bamu hakura ba Aliyu?? Kai don baka da kunya da tsoron Allah har xaka iya sake komawa a
aura maka Jiddah?? Yarinyar da kafi karfinta? Yarinyar da ba class dinka ba? Yarinyar da ka dinga kunyan
nuna ma duniya cewar ita ce matarka? Yarinyar da kayi ma sakin walakanci ka toxartata? Tsakaninka da ita
fa abinci da suturan sakawa shi ma duk don kada Allah ya tambayeka ne... Get out from my sight plss Aliyu
" Abuturrab ya girgixa mata kai ya marairaice yace "Noo plss Umma, kar ki min haka ke ma, i have no back
up" Cikin tsawa Umma "Ohk so kake ince ka dau Jiddah ku tafi ko me? Haka kake son ji??" Ya girgixa kai
cikin sanyin murya yace "Aa Umma, so nake kawai ki taimaka ki sa baki Ummi da Abba su sassauta min,
don nasan baxan iya tsallake hukunci daga garesu ba, su yi min komai amma kada su ce in sake sakinta don
girman Allah" Umma tace "Kaga ka xo kawai ka sa min ciwon kai Malam, ba don halina ba tashi kaje sae da
safe i need rest, kuma kada ka sake xuwa min gida da batun Jiddah, ko me kake son fada kaje ka samu
ubanka ko Ummi, but don't come to my house again, get out pls..." kallonta ya dinga yi, ta mike ta cire
hijab dinta ta linke ta xauna gefen gado tana ci gaba da jan carbinta fuskarta a daure, a sanyaye ya mike ya
yi mata sae da safe ya nufi kofa ya fita. A kofar gida Abuturrab yyi parking ya shiga cikin gida, wani kamshin
bala'i ne ke tashi tun daga balcony har cikin gidan, ya bude kofar parlon ya shiga, ko ina na parlon sae
walkiya yake don neatness, ya xauna saman kujera ya jinginar da kansa dake sara masa ya runtse ido
xuciyarsa na bugawa, ya fi minti talatin a haka, sae ga Aneesah xata tafi kitchen da cup din hade hadenta
na Maman Farida me kayan yan gayu da ta gama sha🙄, ta xaro ido ganinsa ta ajiye cup din a kasan parlon
ta nufesa da sauri tace "My captain? Yaushe ka shigo?" K'in bude ido yyi, ta xube gefensa giving him a hug
tace "Oyoyo my husband nayi missing dinka sosai wllh, amma dai yanxu daga kano kake ko? Don da naji ka
shiru kuma I can't reach u tun shekaranjiya nace to kilan kano kaje..." Bude idonsa da ya canxa kamanni yyi
ya mike, lkci daya yace "I want to be left alone Aneesah" daga haka ya wuce sama ta bi sa da kallo ganin
kamar xai tashi sama, sai kuma ta tashi ta bi bayansa da sauri, bangarensa ya nufa yana shiga dakinsa ya sa
makulli duk da xanin gadon dakin a gyare yake haka ya yaye ya bude press ya dau wani xanin gadon ya
shimfida sannan ya dau duvet ya kwanta ya rufe har kansa. Har kusan asuba Abuturrab bai yi bacci ba,
gashi ya ji gaba daya bai da strength din tashi yayi sallah, har alwala sae da ya daure ya je yyi duk da he is
cold amma daga karshe kwanciya yayi without praying, sallan asuban ma a daki ya samu yayi, he wished all
this wasn't happening, he wish all this will turn out to be a dream, his heart is to weal for all this... Ya kalli
wayarsa jin shigowan message, mikewa yyi ya dau wayar ya xauna gefen gado, ganin message din na
Abbansa ne ya ki budewa ya ajiye wayar xuciyarsa na bugawa, yana nn xaune har rana ta fito, kwanciya yyi
jin kansa yyi masa nauyi sosai yana kuma sara masa, lkci daya bacci me nauyi ya daukesa... Hannu ya ji a
forehead dinsa ya bude ido da sauri, Aneesah ce xaune gefensa tana kallonsa da damuwa tace "Are u okay
captain? U are restless even in sleep, and it seems u are developing fever, ko dai duk stress din tafiyar ne?"
Yayi kokari ya mike xaune ya cire hannunta a kansa yace "Hey i am okay" ta daure fuska tace "How will u
tell me u are okay ga temperature dinka is saying it all, dubi fa yanda jikinka ya fara xafi" Ya hade rai yace "I
said i am okay Aneesah, me yasa ma zaki tasheni ina bacci tukun?" Tace "Aa wnn ba bacci kake ba, bacci
babu nutsuwa duk ka wani firgice kamar wanda yyi ma sarki karya?" Sauka yyi daga kan gadon ya fita dakin
ta bi sa da kallo baki bude. Ummi ce xaune bedroom din Umma tayi tagumi kana ganinta kasan abun
duniya ya dameta, Umma na kallonta tace "Toh ke sae kika yi masu shiru Yaya?" A hankali Ummi tace "Toh
me xance? I was speechless Ramlah... I was mute all through, har yana cewa i should provide him in less
den 24hrs or we both face the consequence" Umma ta mike cikin daga murya tace "Toh aje a hakan, kin
san komai din ko da yanda xa ayi da ke?? Tabbas da goyon bayanki Aliyu yake duk abinda yake yi, sai aka yi
yaya? Da akwai yanda xa ayi da ke ne? Ko wani ya haifar maki Aliyun?? Kuma ina ce dae ba kashe mutum
yaje yayi ba auren sunna yaje aka daura masa da shaidu ya dawo gida, to wanda bai fasa ce wa ke kike
xugasa ba... tunda munafuka annamimiyar matarsa ta daga hankali ta rikice kamar ita aka yi ma kishiya ba
dole shi ma ya birkice ba, ita kuma Hajja tunda babu abinda ta iya sai son kai da son abun duniya da rashin
alkibla ba dole ta gigice ba ita ma, ae tun ba yau nake nuna maki irin bambancin da take nunawa kiri kiri a
kan 'ya ya ba, to wllh a da ina jin babu wanda ya kai ni bakin ciki da takaicin abun nan da Aliyu ya koma ya
aikata ba, amma yanxu kuwa sae in da karfina ya kare, ae auren sunna yaje aka daura masa, in dai a kan
Hajja da makira shegiyar matar nan Hafsah ne sae iya inda karfina ya kare, aure kuma ya riga da ya je yyi
babu yanda aka iya da shi, shi kansa Abban sae yayi hakuri tunda dae ba sata yaje yayi ba ko wani mugun
abu" Ummi dae kallonta kawai take bata ce komai ba, Umma na huci tace "Ba kallona xaki yi haka ba Yaya,
fitowa xaki yi kanki tsaye ki goyi bayan d'an ki tunda abun haka ne, ki nuna masu ae fa shirun da kike yi ba
tsoro bane, kuma kina da iko a kan Aliyu ba Ubansa kadai ba" Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "I am not
against him dama Ramlah, kawai dae nayi shiru ne don kada uban da baabarsa suce ae goyon bayansa
nake, amma kinga a hakan ma ban fita ba sunce da sani na yake komai har auren farkon ma, kuma wllh for
months now yana ta son yyi min magana duk ina lura da shi amma ya kasa sae yyi kamar xae yi sae kuma
ya wayance, ke akwai ranan da har daki sae da na shiga da shi kamar xae fada kuma ya fasa, sae dai yace in
taya sa da addu'a kuma no matter how everything will turn out kar inyi fushi da shi, kin kuma san sa da
xurfin ciki, ni dae nasan duk sallolina biyar bana masa fashin addu'a kuma ina masa fatan alkhairi a duk
lamarinsa, duk wani abu da xai cucesa ina addu'an Allah ya nisanta sa da shi, don haka ni i am not against
him going back to marry Jiddah, bayan ya saketa da watanni ni kaina nayi masa takaicin hakan barin ma
idan aka duba halin da yake ciki tun bayan auren nasa na biyu, kwata kwata bai yi dacen mace ba, tafiyar
nan da yayi kusan duk bayan kwana biyu sai ta xo gidanmu amma ko sau daya bata shigowa bangarena da
sunan gaisheni, duk sanda Allah yyi muka hadu a main parlor sai ta gaisheni a can bbu wani ladabi, ga
uban kazanta da yake complain a gidan nasa...." Umma tayi wani dariya tace "Ai kadan ya gani, sannan ni
abinda ya fi tsaya min a rai ita Hafsah da ta xakalkale har tana ikirarin ba dai ya kunyatata ba me take nufi?
Ita ta isa ta hanasa karin aure ko yin abinda yake ra'ayi ne? To wllh tana ji tana gani xan wanke Jiddah tsaf
in kai ta gidan Aliyu da kai na, sai in ga ko xuwa gidan xata yi ta fito da ita, duk da dai xai ci ubansa kafin
hakan ma ya faru" Ummi dai tayi murmushi bata ce komai ba, Umma tace "Ina baki shawara da kakkausan
murya yaya, kar ki raga ma duk wanda ya gaya maki babu dadi a kan case din nan, ko Hajja ban cire ba
wllh, shi kuwa ki barbade toka a idonki ki wankesa wankin babban bargo shi Abban idan ya sake attacking
dinki, ai shiru ba hauka bane, me yasa sai da aka bari na bar gidan aka maki ca?? Toh in sha Allah har su
gama duk abinda xa su yi a kan case din nan a can xan dinga yini" Tana kai wa nan ta nufi kofa tana cewa
"Bari in kawo maki abinci" Ummi tayi tagumi can kasan ranta tana jin tausayin d'an ta, karfin hali tayi ta
gaya masa maganganun da ta gaya masa jiya a daki, ta rasa dalilin da yasa ko kadan bata ji haushinsa ba, ta
dai yi mamaki ainun amma ba wai haushin sa ba, daukar wayarta tayi ta sake kiransa still ta ji a