Showing 321001 words to 321711 words out of 321711 words
Chapter 108 - Jeedderhh by Khaleesat Haiydar.txt
Ramlah dake xaune ta daga ma Jiddah hannu tana murmushi, Jiddah ta daga mata hannun ita ma
smiling at her, gaida few visitors dake parlon tayi, sai ga Hajja ta fito daga dakinta sanye da kaya na alfarma
ta sha gwal a wuya da kunne tana taku dai dai, Akwatunanta uku fal da kaya ana biye da ita da shi.. Wai
ashe Masar Hajja xata koma shine yan rakiya xuwa airport suka cika gidan Alhaji Usman, yan kano ne, yan
Bauchi ne, har ma da yan zaria, Umma na murmushi tace "Hajja kuma sai Masar" Hajja na daga shoulders
ta nufi kofa tana cewa "A bi min akwatuna a hankali kar su yi ko kwarzane a cuce ni, mu a Masar a nutse
ake jan akwati" Dariya Maimoon ta dinga yi har da saukowa daga kan dining, Ummi ta mike da su Umma
suka bi bayan Hajja suna murmushi, Abba da Mai martaba da sauran brothers dinsu duk suka fito
compound jin Hajja ta fito bayan awa daya da ta dauka tana shiri a dakinta, kace wani karamin biki ake yi a
compound din gidan saboda mutane, a haka duk suka nufi airport don a private jet xa a kai ta kano sannan
ta hau jirgi xuwa Masar..... Waige waige ta dinga yi a airport tana neman Jiddah tana ganinta ta yafito ta,
Jiddah ta nufeta Hajja ta jawota kusa da ita tace "Toh Allah ya kaddara saduwan mu Jiddah ni xan koma
Masar kuma ban jin xan sake dawowa kasar nan" A hankali Jiddah tace "Aa xaki dawo Hajja" Hajja ta
girgixa kai tana kyabe baki tace "Lala, abubuwan kasan nan duk ba tsari, toh me xan dawo yi?? ni dai ina
'ya ta ta ke?" Jiddah tace "Tana hannun Yaya Bashir" Hajja ta d'an waiwaiga ta tabbatar babu idon kowa a
kansu ta kamo hannun Jiddah ta saka mata gold na dankunne tace "Gashi ki ajiye ma 'ya ta, tana shekara
biyu cif cif ki saka mata kuma kada kice ma ko wani shege ni na bata balle a kullaceni suce ban ba ma
yaransu ba to me na hada da su? ko shi gantallalen Aliyun kar ki gaya masa don babu abinda na hada da
shi ma din" Rungumeta Jiddah tayi cikin sanyi tace "Mun gode Hajja Allah ya kara girma, Allah ya kai ki
lafiya, in Allah ya yarda mu ma muna nan xuwa wataran" A haka suka rabu da Hajja ana ta daga mata
hannu har ta hau matakalan jet din tare da mai martaba da Abba da Alhaji Umar, sai ta juya tana
fuskantarsu kafin ta shiga jirgin ta daga masu hannu gaba daya sai kuma ta fashe da matsanancin kuka tace
"To a yayyayafe.... mu dai mun koma Masar!!!" Me Abuturrab xai yi banda dariya little Jiddah dake
hannunsa na tayasa.
*kada a manta littafin Jiddatul Khair na kudi ne, ba kyauta ba, a xo a sauke hakki a xauna lafiya sisters and
brothers*
It's 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!😃
A
✍🏻nan kam na ajiye alkalamina na kawo karshen littafin _Jiddatul Khair_ darussukan dake ciki Allah
ubangiji ya sa mu amfana da shi, kura kuren ciki kuma Allah ya yafe min....😰
Na sadaukar da littafin nan xuwa ga beloved Dad dina, Alhaji Bello Ahmad.... Ur daughter Jiddoh is always
proud of u Papa, Allah ya baka kwanciyar hankali na har abada, ya kara maka budi da daukaka, ya kareka
sharrin masu sharri, ya kara maka lafiya da duk sauran musulmai Ameeeen🥰
Gaisuwa ta musamman xuwa ga mahaifiyata Hajiya Hajarah, she is my first love, my world, my role model
and my everything, Allah ya bar min ke Hajiya yaya, Allah ya kara maki lafiya ya karo arxiki me albarka, My
Siblings Ahmad, Maryam, Yahaya, Fatima, Khadija, Aliyu, Ilham, Sudais, Fadeel, Papi auta, Lil Khaleesat,
Baby, Haneef, Ashraf, Jamcy, Humaira, Yusuf Black, Mujaheed, Big Ilham, Aneesah, i love u all!! Allah ya
albarkace ku gaba daya, ina sonku har raina, small mummies...., Aunty Rukky, Anty Didi, Uwar Ashraf ur
daughter Jiddoh is greeting with respect, Allah ubangiji ya jibanci lamuranku.... Hajiya Pc (Sadiya Chamo)
ga gaisuwan ku dake da tawagar Khaleesat's palace, duk na gaisheku ina sonku fisabilillah, Hafsat Ado i
greet and appreciate you sis...🥰😘 And finally my lovely fans, words alone isn't enough to express my
feelings toward u guys, billah ina sonku, ina alfahari da ku, ina maku fatan alkhairi da fatan gamawa da
iyaye lafiya Ameen!!!
Taku har ko da yaushe, Hauwa Bello Jiddah A.K.A Khaleesat Haiydar✍🏻
Na bar ku lafiya😊